Showing 180001 words to 183000 words out of 231718 words

Chapter 61 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14697

a gurin ki? Ɗan gidan waye a garin nan? Don ba zai yiyu ba sai mun je an kira iyayensa an yi wa tufkar hanci, akan me zai dinga taɓa ki?"

"Kai Inna ya na ga duk kin tsora ta?"


"A'a, kar na tsorata? Na san mugun nufin shi a kan ki?"

"To Inna daga ganin shi ba ɗan garin nan ba ne, irin yan gayun nan ne yan birni, sai ma kin ji ƙamshin da yake mai daɗi." Ta ƙarashe maganar tana murmushi.

Tsaki Inna ta yi ta ce. "Ko ma ɗan ina ne ba ruwana, bari Musa ya fito daga wanka mu je gidan mai gari". Ganin da gaske Inna take sai Ƴar Baba ta ce. "To ƙarya ma nake yi duk abin da na ce miki." A ƙufule Inna ta ɗauki mafirficin kaba za ta kwaɗa mata tana faɗin. "Ja'irar kashi, wato kin mayar da ni kakarki ko?" Kafin maficin ya sauka a jikinta ta kwasa da gudu ta yi ɗaki tana dariya. Musa da ya fito daga bayan gida a lokacin shi ma dariyar yake. Yana ajiye bokitin hannunsa ya ce. "Wani lokacin Inna kamar ba ki san halin ƴar Baba ba, ta zo ta zauna ta tsara miki zance na ƙarya, ke kuma ki hau kai ki ta banbanmi, sai kin gama ta ce ƙarya take." Inna ta ce. "Na daina yarda da ita ai, ja'ira kawai, Allah ya shirya mini ke."


Ita kuwa tana shiga ɗakinta ta yi tsalle ta faɗa kan katifarta, haka kawai ta ji mutumin da take haɗuwa da shi ya tsaya mata a rai, ta rasa me ya sa kuma da Inna ta ce za ta kai ƙarar shi gurin mai gari ta yi saurin cewa ƙarya take, ita da take jiran ƙiris mutum ya yi mata abu ta kai shi ƙara. Tsaki ta ja a fili ta ce. "Ƙila ma aljani ne, ɗan baƙi kawai, bai san ma ni na fi son farin mutum ba, ta ƙarashe maganar tare da murguɗa baki. Tunowa ta yi wata ƙawar su ta haihu jiya, hakan ya sa ta miƙe ta fice daga ɗakin don zuwa ganin ɗa.

"Inna zan je na ga jaririn Atine." Ta yi maganar tana saka takalmi.

"Ki bari a yi Sallah mana, ko kuma gobe da safe kya je."


Diddira ƙafa ta fara yi tare da faɗin. "Don Allah ki bar ni na je, duk su Lantana fa suna can tun ɗazu."

"Allah ya tsare." Inna ta faɗa a takaice, don ta san idan ta hana ta ma zama zata yi ta cika musu kunne da ihu, don ba ƙaramin aikinta ba ne.


Bayan Magriba Abbi ya sauka a Kano, direct gidan Ammi ya wuce, saboda ta kira shi akan tana son ganin shi. Bayan sun gaisa Ammi ta gyara zama ta ce. "Babana, ɗazu matarka ta kira ni tana ta kuka akan wannan auren da za ka ƙara, don Allah ka tausaya mata ko ɗaga bikin nan ne a yi mana, ka ga har yanzu tana cikin alhinin rashin Abra, wallahi tausayi take ba ni, duk ta bi ta ɗaga hankalinta." Cikin ladabi Abbi ya ce. "Ko shekara za a ƙara akan Auren nan idan aka tashi yi sai Nai'ma ta ƙara ɗaga hankalinta Ammi, kuma kin ga babu daɗi biki saura kwana biyar sannan a ce za a ɗaga saboda wani dalili mara ƙarfi, an riga an gama buga IV an raba, yarinya sun fitar da anko sun yi komai, sai a ɗauke mu ƙananun mutane." A sanyaye Ammi ta ce. "Shikenan, Allah ya tabbatar da Alkhairi ya ba ku zaman lafiya, Allah ya ba ka ikon yin adalci a tsakanin su."

"Amin Ammi, bari na ƙarasa gida don sauka ta kenan na ce driver ya fara kawo ni nan, idan na je na yi wanka na huta zan je gidan Iman, ta dame ni akan za su yi Mother's day da sauran su."


"Da ka rabu da su Babana, muna cikin alhinin mutuwar Granny da Abra babu wasu bidi'ebidi'e da za mu yi."

"Na mata maganar hakan ni ma, amma ta ce mini ai ba kiɗa za a yi ba, kamar walima abin zai tashi, za a ci a sha ne kawai."

Ammi ta ce. "Toh shikenan, Allah ya kai mu."

Ya amsa da Amin tare da miƙewa ya yi mata sallama ya tafi.




Sai kusan isha'i ta baro gidan Atine, tana tafe ita kaɗai cikin sauri ta ji ta yi karo da mutum. Cikin masifarta ta buɗe ba ki za ta yi magana amma maganar ta kakare, sakamakon ganin wanda ba ta yi zato ba. Adnan ne shi ma ya dawo daga inda ya je, hannunsa riƙe da torchlight yana haska hanya. Duk da ba ta kalli fuskarsa ba amma ƙamshinsa ya sanar mata shi ne.

"Innahu Sulaimanu wa'innahu bismillahirrahmanirrahim." Ta faɗa tare da ja baya cikin tsoro da faɗuwar gaba, don zuwa yanzu ta fara tantamar anya ba aljani ba ne? Duk inda ta yi sai sun haɗu.

"Angel!"

Ya faɗa cikin murmurshi tare da haske fuskarta. Turo baki ta yi ta ce. "Wai kai a ina ka san ni ne? Don Allah ka daina bibiya ta, ni fa ban san ka ba ban taɓa ganin ka ba."

"To ai yanzu kin san ni ko?" Ya yi maganar yana ƙoƙarin kamo hannunta."

"Na shiga uku! Wai da wa Allah ya haɗa ni ne?" Ta yi maganar tare da tattare siket ɗinta ta manna da gudu. Da kallo ya bi ta har ta ɓace wa ganin shi, zuciyarsa cike da mamakin yadda ta ƙware a iya gudu haka.

"Who is she?" Ya tambayi kan shi cikin rashin sani, yana son sanin wacece ita da gidan da take da tarihin rayuwarta, don kamar su da Abra ta fi ƙarfin a ce kama ce kawai, sai dai in da wata alaƙar, domin hatta muryar su iri ɗaya ce, yadda suke magana ne kawai ya banbanta.

Kamar kodayaushe cikin gudu ta ƙarasa gida, tana tafe tana murguɗa baki da zancen Adnan a cikin ranta. Labarin na cin ta a rai amma ba ta faɗa wa Inna ba, saboda ɗazu ta riga ta ce mata ƙarya take.


Nai'ma na zaune a main parlour ta yi tagumi abun duniya duk ya bi ishe ta Abbi ya yi sallama fuska babu walwala. Ba ta amsa masa ba sai ma haɗe rai da ta yi. Kallon yadda ta rame ta lalace ya yi, sai ya ji tausayin ta ya tsirga masa, takaicin ta na kiran Ammi da ta yi ya fara gushewa daga cikin ransa. Jakar hannunsa ya ajiye tare da zama a kusa da ita, cikin taushin murya ya kira sunanta.

"Na'ima"

"Kar ka ƙara kiran sunana, don bai dace da bakin macuci azzalumi mayaudari irin ka ba, wallahi Khamal ka ci amanata." Ta yi maganar cikin kuka.

Ɗage kafaɗa ya yi ya ce. "Idan kina ganin wannan borin da botsarewar da kike ne zai saka na fasa aure to ki cigaba, amma ki sani idan kika kai ni bango duk abin da ya faru ki kuka da kan ki."


"Ko me zai faru sai dai faru, ƙarkari ka ce ka sake ni ko? To ka sake ni ɗin sai me?"

"Okay, maganar kayan faɗar kishiya, kuɗi kike so ko kaya?"

"Ban sani ba, ba na son komai naka Khamal, idan ka ga ina yawo tsirara don Allah kar ka siya mini ko ƙyalle, ka bar ni in cigaba da yawo a haka."


Girgiza kai kawai ya yi bai ce komai ba ya wuce part ɗinsa. Kuka ta fashe da shi mai tsananin gaske tare da ɗaukar pillows ɗin kujera tana cilli da su, ita kaɗai ta san me take ji a cikin ranta, ita kaɗai ta san zugi da raɗaɗin da zuciyarta take mata. Kamar wata mahaukaciya ta miƙe ta shiga ɗakinta da gudu ta ɗauki wayarta ta kira numbern Mama, bayan ta ɗaga ta fara magana cikin kuka. "Mama da gaske auren nan zai yi, don Allah ki faɗa mini mene ne mafita, na rasa madafa." A fusace Mama ta ce. "Taurin kanki ne ya yi yawa Na'ima, na faɗa miki ki ajiye wannan yarinyar ki baro masa gidansa amma kin ƙi." Kallon A'isha Humairah dake bacci ta yi, a raunane ta ce "Ba zan iya tafiya in bar ta ba Mam......"


"Sai ki ta zama ciwon zuciya ya kama ki akan Namiji." Mama ta katse ta da faɗin haka tare da kashe wayarta. Tsugunnawa ta yi ta kifa kanta a jikin gado tare da toshe bakinta da hannunta, gudun kar ta tashi A'isha daga bacci, ta shiga rera kuka mai ban tausayi.




Washegari ta tashi da zazzaɓi da matsanancin ciwon kai, da ƙyar ta iya tashi ta yi sallar asuba ta ba wa A'isha Humairah abincinta ta ci. Tana kwance Khamal ya shigo ɗakin, ko Kallon shi ba ta yi sai ma juya masa baya da ta yi daga kwancen da take, wasu hawaye masu ɗumi na zuba akan kuncinta. Bai kula ta ba shi ma ya ɗauki A'isha ya yi mata wasa tare da shishshilla ta, ita kuwa sai dariyar ƙuda take masa. 500k ya ajiye a kan madubi, yana duban Na'ima ya ce. "Ga kuɗi nan duk da kin ce ba kya so na ajiye miki, sannan gobe masu jere za su zo, idan akwai wani abun da kike buƙata bayan wannan sai ki sanar mini." Idan kuɗin da ya ajiye sun yi magana to Nai'ma ta tanka masa, ɗan murmushi ya yi ya kwantar da A'isha a gabanta, ba zato ta ji ya yi kissing forehead ɗinta tare da faɗin. "Sai na dawo uwargidan major Khamal Khamis." A zuciye ta ce. "Kar ma ka dawo, ka zauna a inda zaka je." Ta ƙarashe maganar tare da goge inda ya yi kissing ɗin." Tattausan murmushi ya sakar mata ya juya ya fita.


"Ƴar Baba! Ƴar Baba."

"Wai don Allah Inna ba za ki bar ni na yi baccin nan ba." Ƴar Baba ta faɗa tana tashi zaune.

"Ko kasa ce ke sai kin tashi kin yi wanke-wanken can, don gidanku idan kin je gidanki haka za ki na kwanciya kina bacci ki bar gida da ƙazanta."


"Gaskiya Inna kin daina so na yanzu, dama can Babana ne kaɗai yake so na, da yana raye babu mai tashi na daga bacci." Ta yi maganar cikin hawaye. Inna ba ta kuma magana ba ta fice daga ɗakin, tashi ta yi ta bi bayan ta ta kama wanke-wanken. Bayan ta gama ta share tsakar gida tare da wanke banɗaki. Inna ta ce. "To ko ke fa ƴar albarka, sannu da aiki, Allah ya saka da Alkhairi, yanzu sai ki wanke baki ki yi wanka ki zo ki ci abinci."


"Ni dai ba zan yi wanka yanzu ba sai rana ta fito, safiya ce fa."


Inna ta ce. "Kar ki yi ɗin, ke da ba a miki gwaninta, gwara ki koya tun yanzu, don watarana na asuba ma za ki yi ko na tsakar dare." Zunɓura baki ta yi ta ce. "Alkur'an ba zan yi wanka da tsakar dare ba, sai ka ce wata sabuwar aljana." Inna ta ce. "Idan lokacin ya zo kar ki yi, ki zo ki karya ni ki je ki karɓo mini gyaɗa, yau ma ki ƙara zubar mini da ita, ki ga yadda zan yi dake a gidan nan."

"Allah Sarki Babana, Allah ya ji ƙan ka, saboda ba ka nan kullum sai an mini faɗa."


Inna ba ta kula ta ba ta cigaba da sabgogin gabanta.


Kamar yadda Abbi ya faɗa washegari ƴan uwan amarya suka zo suka yi jere a part ɗin da aka gyara, duk da ƙofar shigar shi ta cikin main parlour take amma ba su haɗu da Nai'ma ba, don ƙin fitowa ta yi daga ɗaki. Abinci ma sai Aunty Iman Abbi ya yiwa waya ta aiko aka kawo musu. Zaman kaɗaici ya ishi Nai'ma, ga shi tana ta kiran Salman a waya ba ta samun shi, hakan ya sa ta kira wasu cousins ɗinta guda biyu suka zo don taya ta zama. Ganin yadda ta tayar da hankalinta duk ta fige sai abun ya ba su mamaki. Ɗaya daga cikinsu mai suna Wasila ta ce. "Me zan gani haka? Cuta kika yi ne Na'ima? Ko duk alhinin yi miki kishiyar ne?" Maimakon ta ba ta amsa sai ta fashe da kuka, da ƙyar suka rarrashe ta ta yi shiru. Ɗayar mai suna Hajara ta ce. "Haba Aunty Na'ima, yanzu akan kishiyar kike haka? Ai idan ta zo ta tarar kina haka sai ta raina ki."


"Mene ma ba zan yi ba, kun fi kowa sanin irin so da ƙaunar da nake wa mijina, amma ya ci amanata yake ƙoƙarin yin aure, me na rage shi da shi da bana masa?"


"Haƙuri ake yi Aunty Nai'ma, abun da ciwo amma sai kin danne zuciyarki, idan kika yi haƙuri komai zai wuce."

"Ba ni da wannan haƙurin kuma ba zan iya yi ba, wallahi ba don A'isha ba da tuni na bar masa gidansa, don ko ganin shi bana ƙaunar yi, ji nake kamar na cinna wa gidan wuta duk mu ƙune."

Da sauri Wasila ta ce. "Subhanallahi! Me ya yi zafi shi ba wuta ba Na'ima? An sani kishiya babu daɗi, amma ya za mu yi sai haƙuri. Ki rage damuwar nan da kike, tunda mijinki yana son ki ni ban ga abun damuwa ba, domin na tabbata duk macen da Khamal zai so a bayan ki take. Yanzu ki tashi ki yi wanka mu je a yi miki wankin kai da ƙunshi da gyaran jiki, duk da lokaci ya ƙure amma ba za ki zauna haka ba, yadda Amarya za ta zo fess ke ma haka za a gan ki."


Na'ima ta so ƙi amma suka tursasa mata, dole ta haƙura ta miƙe suka tafi ita da Wasila. Hajara kuma ta ɗauki kuɗin da Khamal ya ajiye ta tafi kasuwa ta yo sayayyar kayan sawa da takalma da jaka da mayafai masu kyau da tsada, wanda Nai'ma za ta yi fitar biki da su, daga kasuwa direct gurin tela ta biya ta ba shi kayan tare da cika masa kuɗi saboda ɗinkin urgently suke buƙatar shi. A daren yau ba su yi bacci ba sai da suka canza sabbin labulaye da Carpets part ɗin Nai'ma, suka sauya tsarin parlour'n da na kitchen, sai parts ɗin ya yi kyau ya haska shi ma.


Wasila da Hajara Ya da ƙanwa ne, the same Mother the same Father, mahaifiyarsu ce k'anwar babansu Na'ima, suna da hankali su da sanin ya kamata, don shawarwarin da za su amfane ta suka dinga ba ta. A ɓangaren ta ita ma sosai ta ji daɗin zuwan su, sai ta ji dama tun saura sati ɗaya bikin ta kira su.


Yau kwata-kwata Adnan ba su haɗu da ƴar Baba ba, hakan ya jefa shi cikin damuwa, ya dinga zagayawa a garin ko Allah zai saka ya gan ta amma bai gan ta ba.


Washegari ta kama ranar Alhamis, ranar aka yi kamun amaryar Abbi kamar yadda aka tsara. An sha shagali sosai abin ya ƙayatar duk da ba a yi ƙida ba, manyan malamai mata aka kira suka yi wa'azi mai ratsa zuciya. Amarya ta sha pictures, dangin Abbi sukai ta ɗorawa a status, amma Nai'ma ba ta gani ba. Don ƙwace wayarta Wasila ta yi ta ce ba za ta ga abin da zai ɗaga mata hankali ba, don ta san halinta. Daren yau Na'ima ba ta iya runtsawa ba, kwana ta yi tana kuka tare da tunanin daga gobe Khamal ya zama nasu su biyu, za ta fara sharing ɗinsa da wata.




Rana ba ta ƙarya, yau juma'a ranar ɗaurin Auren Abbi da amaryarsa Salima. Ba ƙaramin Dauriya Nai'ma ta yi ba ta shirya cikin wani tsadadden farin less mai adon red, bi sa takurawar su Wasila. Har gida Hajara ta kira wata mai make up ta zo ta yi mata. Duk da idonta a jeme yake saboda kuka amma ta yi kyau, sai dai ramar ta ta fito sosai. A'isha Humairah ma an mata kwalliya cikin sabbin kaya masu kyau white and red, tana rungume a jikin Nai'ma tana bacci bayan ta ci ta ƙoshi. Ƙawayen Nai'ma da wasu daga cikin danginta sun zo tun safe, don ita ma ranar za ta yi nata taron. A tsarin ta ba za ta yi taron komai ba, amma su Wasila suka dage sai an yi, don ƙin yin taron zai saka mutane su gane halin da take ciki na damuwa a kan auren, hakan zai saka kuma a yi mata dariya ne.


Misalin ƙarfe goma sha biyu na rana suna zazzaune a bedroom ɗinta ita da su Aunty Suwaiba, ana ta dannar ƙirjinta, masu zuga ta akan ta yi hauka na yi, masu ba ta shawarwari na gari wanda za su amfane ta na yi. Ita dai duk ba fahimtar su take ba, don hankalinta gabaɗaya ba ya jikinta, yanda take jin zuciyarta kamar ta tashi tay ta zunduma ihu, ganin abun take tamkar a mafarki, wai yau ita za a yiwa kishiya? Ita da ta gama cika baki a cikin ƙawaye da dangi akan Khamal ba zai taɓa ƙara aure ba, amma ya watsa mata ƙasa a ido. A haka Abbi ya shigo ya same su cikin shirin shi na tafiya gurin ɗaurin Aure, ya fito tsaf a angon shi, ba za ka taɓa cewa ya ajiye ɗa kamar Salman ba. Bayan sun gaisa da mutanen ɗakin sai suka tashi suka fice don ba su guri.


A hankali ta ɗago kanta dake sunkuye ta zuba masa ido, tunda ya shigo ta ji sallamar shi gami da ƙamshinsa da ya cika ɗakin ta sunkuyar da kanta, ya yi matuƙar yi mata kyau ba kaɗan ba, farar shaddar jikinsa ba ƙaramin haska shi ta yi ba. Shi ma kallon ta yake yi cikin wani irin yanayi hakan ya sa idanunsu suka sarƙe cikin na juna, ranar da ya fara ganin ta a rayuwarsa ya tuno, ya sani Nai'ma tana son shi ba kaɗan ba, shi ma kuma yana son ta, matsalar ta kawai zafin kishi.




Ganin yadda ta rame sai ya ji tausayin ta mai ɗimbin yawa ya cika masa zuciya, a hankali ya taka ya ƙarasa ya tsugunna a gabanta tare da ɗora hannunsa a kan nata dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login