Showing 18001 words to 21000 words out of 231718 words

Chapter 7 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14675

da kallo, tana murmushi.

Faruk ya sarawa Khamal sannan ya zauna yana faɗin "Yallaɓai ya jikin?"

Khamal yace "jiki Alhamdilillah"

Na'ima kuwa kallonsu take cike da rashin fahimta, ina Captain ya samo 'ya har ta ke kiransa da Abbi, ta daɗe da sanin sa kenan?.

Khamal ya kalli Na'ima yace "Madam, a kawo musu ɗan abun taɓawa"

Ta miƙe ta nufi hanyar kitchen, zuciyarta fal wasi wasi da tambayoyi.

Khamal ya kalli Faruk yace "ya akai aka ganta?"

Nan Faruk ya gayawa Khamal duk abunda ya faru, Captain Khamal yai shiru tare da jinjina kai yace "Salima again?"
Shiru ya ɗanyi yana nazari, sannan yai ƙwafa, yana sake rungume Abra a jikinsa.

Ya nisa yace "Faruk, ashe abunda ya kuma faruwa kenan, an kuma kwashe ɗaliban jami'a?"

Faruk ya girgiza kai yace "bari kawai Captain, abun akwai tashin hankali, kullum abun ƙara worst yake, matsalar sake yawa take, kalli uban wanda muka kashe, da wanda muka kama, amma bayan ransom ɗin da suka buƙata har da se an sakar musu yaransu da muka kama, within seven days"

Khamal ya cije laɓɓansa na ƙasa, yana wani irin huci yace "Why? And When? Yaushe zamu samu 'yan ci, hankalinmu ya kwanta na 'yan ƙasa ya kwanta, har ɗan ta'adda yasan za'a bawa gwamnati tallafi, ya buƙaci wani abu a ciki, wannan wane irin abu ne, idan da gwamnati suke faɗa meye laifin innocent souls da suke sacewa suna cin zarafin su, yaushe hankalinmu ze kwanta? Gwamnatin mu na iya ƙoƙarin ta, mu kanmu jami'am tsaro muna namu ƙoƙarin, to a ina matsalar take? Waye me laifin?" Ya ƙarasa maganar yana huci.

Faruk yace "hakane, kowa yana ƙoƙari, amma akwai buƙatar mu gyara mu sake zage damtse gaba ɗayanmu, mutanen nan 'yan uwanmu ne, a cikin mu suke, meyasa za su zage su dinga kashe mu? Me mu kai musu? Akwai wani abu a ƙasa da yake buƙatar dogon Nazari".

Captain yai ajiyar zuciya yace "hakane, kuma idan aka tsaida hankali guri ɗaya, za'a a iya samo bakin zaren"

Faruk yace "hakane, Allah ya iya mana"

"Ameen" Khamal ya amsa.

Na'ima ta dawo Falon ta kawowa su Faruk snacks, da ruwa da lemo me sanyi.

Abra tai ta bin abunda ta kawo ɗin da kallo, Captain ya ɗakko donut ya miƙa mata. Ta karɓa maimakon ta kai bakinta, se ta hau leƙa ɗan ramin nan na jikim donut ɗin tana dariya, a zatonta abun wasa ne.
Sai da Khamal, ya ɗauka ya ci sannan ita ma ya nuna mata yadda za ta ci, sannan Abra ita ma ta fara ci.

Faruk da Khamal suka shiga hira abunsu, suna cigaba da tattaunawa akan matsalar tsaro, Abra na jikin Khamal tana ta kaɗa ƙafa tana ciye ciyenta.

Faruk ya miƙe tare da cewa "to Yallaɓai, ni zan tafi and Alhamdilillah na dawo da amanar da aka bani, ina fatan Ubangiji Allah ya taya riƙo, sannan ya ƙara maka lafiya"

Captain yace "Ameen ya hayyu ya ƙayyum, nagode ƙwarai Faruk, ka gaida gida".

Faruk ya juya ze tafi, Na'ima tace "a'a ya na ga kuma ze tafi ya bar yarinyar?"

Khamal yace "karki damu zan miki bayani"

Faruk ya juya tare da ɗagawa Abra hannu, itama ɗaga masa hannu tai tana masa murmushi.

Na'ima ta dawo da dubanta kan Khamal tace "Nifa ban gane ba, bayanin me za kai min?"

Khamal yace "Calm down baby, ki zauna mana"

Zama tai tana tura baki tace "Gaya min, meye ma'anar wannan abun? Wacece wannan yarinyar?"

Khamal ya gyara zamansa, ya gayawa Na'ima komai, tun daga tsintar Abra da yai har zuwa yanzu, sannan ya ɗora da cewa "A hukumance ma, hukumar mu sun san da zaman Abra a hannu na, za'a cigaba da neman iyayenta, in Allah yasa an samesu shikenan, idan ba'a same su ba ina son Abra ta cigaba da zama tare da mu a nan, mu riƙe ta tamkar 'yar da mu ka haifa".

"Dan Allah ɗan saurara mana Khamal, wai shekaruna nawa ne yanzu a duniya da har kake tunanin zaka iya raina min hankali? Wato ka mai da ni ma wata nusarar mahaukaciya, wadda ba ta san me take ba, kaje karuwa ta haifa maka 'ya, kuma ka ɗakko kace in riƙe kana cikin hayyacinka kuwa? Kai ina zaton sautin ƙarar bom da ka saba ji a daji ya taɓa maka ƙwaƙwalwa ba ka sani ba.
To bari kaji in gaya maka, wannan 'ya Wallahi ba zan riƙeta ba, ka mayarwa da uwarta can da kuka haifeta tare ta riƙeta, dama aiku sojoji ba wanda za'a bawa amana bane, wato uwarta na gudun abun kunya ba zata riƙe ba se ni, karkatacciyar bishiyarka me daɗin hawa, ni zan riƙe 'yar karuwa to Wallahi da sake"

"Shut up Na'ima!" Tsawar da Khamal yai mata se da ɗan cikinta ya juya, saboda tsabar razana da ta yi.

"Ni kike cewa na haifi 'ya da karuwa a waje? Na'ima yanzu shedar da zaki bayar a kaina kenan? Kin fi kowa sanik ni ba mutumin banza bane"

Cikin tsiwa tace "Abu na ɗan Adam kowane lokaci ai yana iya canzawa, kuma in da kake zuwan tunda ba wani ne yake binka ya ga me aikata ba, ai Allah kaɗai ya san me kake yi, dan haka Wallahi ba zan riƙe 'yar karuwa ba, ka maida ita gurin uwarta tun da wuri".

Khamal yace "Na'ima, nan gidana ne, kuma ko 'yar karuwa na kawo nace ta zauna, gida na ne ba naki ba, idan ba zaki iya riƙe Abra ba, zaki iya tattara kayanki ke ki koma in da kika fito".

A razane ta kalli Captain Khamal tace "yanzu zaka iya rabuwa da ni, da ɗanka na sunna da zan haifa akan 'yar da karuwa ta haifa maka Khamal?"

Yace "yes of course, idan ba zaki zauna da Abra ba, ni zan iya rabuwa da ke, kuma ko ki yadda tsintar Abra nai, ko kar ki yadda ki cigaba da zama akan bakanki cewar 'ya ta ce da na haifa a waje, wannan ke ta shafa amma Abra a nan zata zauna tare da mu".

Fashewa Na'ima tai da kuka, ta wuce bedroom ɗinta, ta cire wayarta da ke caji, ta shiga neman lambar Ammi, wato mahaifiyar Khamal, Ammi na ɗagawa Na'ima ta sake fashewa da kuka tace "Ammi dan Allah ku zo gidanmu akwai matsala, Khamal yaiwa karuwa ciki a waje, ta haihu tace ba zata riƙe ba, shine ya kawomin ita wai in ban riƙe ba ze sakeni"

Ammi tace "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Khamal ɗin?"

"Wallahi Ammi da gaske nake, dan Allah kuzo, kar baƙi ciki ya kasheni, dan Wallahi se da ya zaɓa ko ni ko ita, ba zan zauna da 'yar zina in raineta ba!".



COMMENT AND SHARE

BRIGHT PENS
NIMCYLUV
AYSHECOOL
ZEE KUMURYA

Domin ƙarin bayani, ku tuntuɓe mu akan
07063065680
09047871750





m selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*[9/30, 8:55 PM] Abk: *✷ DARE DA DUHU ✷*


Brigh pens✍️
Nimcyluv
Ayushercool
Zee Kumurya

*6.....*
Elegant online writers


LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank. IDAN KATIN WAYA NE #500 NE.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.


*_Masu son Littafin MIJIN MALAMA... Kuyi following Acct ɗin nan a Arewabooks👇🏾_*
https://arewabooks.com/u/nimcyluv



Cikin kaɗuwa Ammi ta ce. "Subhanallahi, Na'ima kin san me kike cewa kuwa? Baban nawa ne zai aikata wannan mummunan aikin?"

"Wallahi Ammi dagaske nake, kin san dai ba zan yi masa k'arya ba, ki zo ki ga yanda suke yi da Yarinyar, zaki tabbatar Ɗa da Mahaifi ne."

Jiki a sanyaye Ammi ta ce. "Wannan maganar ba ta waya ba ce, bari na kira Alhaji, za mu zo yanzun nan insha Allahu, amma dan Allah kar ki tayar da hankalinki da yawa, kin san a yanayin da kike ciki ba'a buƙatar ki saka damuwa a cikin ranki."

"Toh Ammi sai kin zo" Ta faɗi haka cikin kuka, zuciyarta na yi mata wani irin suya saboda tsananin kishi. Khamal ya shayar da ita ruwan mamaki, ba ta taɓa zaton haka daga gare shi ba, she trusted him over, ashe ya ce zai nuna mata halinsu na sojoji.

Cillar da wayar ta yi ta fito daga ɗakin kamar mahaukaciya, ko nauyin cikin jikinta ba ta ji. Zaune ta tarar da Captain a parlour kan kujera two seater, Abra na jikinsa ta yi bacci abinta. Kallon Television yake yi hankalinsa kwance tamkar babu wani abu na ɓacin rai da yake damun shi. Hakan ya ƙara k'ular da Na'ima, ta tsani wannan maziyar tasa, abu ya faru ya mayar da kai mahaukaci shi kuma ya dinga pretending like everything is okay.

Kamar zautacciya ta fara cillar da pillows ɗin kujera cikin kuka tana faɗin. "Wallahi Khamal ba ka isa ka tozarta ni ba, sai na kashe ka na kashe yarinyar in yaso nima a kashe ni!" Khamal dake bin ta da wani irin kallo cikin tsawa ya ce mata. "Na'ima! Wallahi kika sake wani abun ya samu Yarona da ke cikinki garin haukanki sai na nuna miki ɓacin raina, wanda baki taɓa ganin irinsa ba."

"Ya mutu ma ina ruwana Ni, kuma ɓacin rai ka daɗe baka nuna mun shi ba, ƙarƙari dai ka ce ka sake ni in tafi in bar maka gidanka, to idan ka sake nin sai me? Na ce sai me?" Tai maganar tana zazzare idanunta da sukai jawur, saboda azabar kishi da kuma kukan da tai.

A firgice Abra ta farka daga baccin saboda hargagin Na'ima, fashewa ta yi kuka tare da ƙanƙame Captain tana kiran sunan "Abbi".

Cikin tsana Na'ima ta wurga mata wani kallo tana huci kamar zata ci babu, ji take tamkar ta fizgo Abra daga jikin Khamal. Tsaki Captain ya yi ya miƙe tare da Abra a jikinsa ya shige bedroom ɗinsa yana rarrashin ta. Ganin haka yasa Na'ima fashewa da kuka tare da zama daɓas akan kujera, ganin yadda ya maida ita mahaukaciya.

"Khamal why? Me yasa zaka mun haka? Ban cancanci haka daga gare ka ba, kar ka saka mun tukwicin k'aunar da nake yi maka da cin amana."

Ta faɗi haka cikin sheshshek'a.

Ƙarfe biyar da mintuna su Ammi suka ƙaraso gidan, har lokacin Na'ima tana zaune a inda take, ta ci kuka ta gode Allah, sai wani irin haki take yi saboda tsabar ɗorawa kai masifa, ga nauyin ciki.


Tana jin ana knocking ta miƙe da sauri ta buɗe ƙofar, zatonta ya zama gaskiya su Ammi ne tare da Baffa.


Granny ce a gaba, baki buɗe take kallon Na'ima bayan sun shigo, tafa hannuwa ta shiga yi ta ce. "Na shiga uku ni Mari, wannan fita hayyacin naki da kika yi Na'ima na mene ne? Ko waya aka yi miki aka ce tsohuwa ko tsoho wani ya mutu?"


Na'ima ba ta bi ta kanta ba ta yiwa su Ammi sannu da zuwa cikin dauriya.

Kama hannunta Ammi ta yi cikin lallami ta ce. "Na'ima ba ki ji abun da na faɗa miki ba ne na cewa ki kwantar da hankalinki? Kin ga yanda kika koma kuwa?"

Sake fashewa tai da kukan tace "To Ammi ya zan yi? Ba ki ji yanda zuciyata take mun wani irin zafi da suya ba ne."

Baffa ya yiwa kansa mazauni ya ce. "Ina shi Khamal ɗin yake?"

"Yana ɗakinsa tare da Yarinyar." Na'ima ta faɗa cikin ɗacin rai.

"A'a, wacce yarinyar kuma? Me kuke zance akai ne? Me yake faruwa ne?"

Granny ta tambayi haka tana bin su da kallo.

Ganin babu mai shirin ba ta amsa cikin fusata ta ce. "Yau na ga jaraba, ya ina tambayar ku, kun mun shiru kun mayar da ni wata gantalalliya? Ni dama tun da na ga Buba ya dawo gida hankali a tashe na san da wata a ƙasa, na tambayi me ya faru kuma saboda ba'a ɗauke ni da muhimmanci ba an ce mun ba komai, duba jikin Khamalu kawai za'a zo yi, na zo kuma na ji ana wani zance na daban da ban gane masa ba."

Cikin girmamawa Ammi ta ce. "Hajiya ki zauna zaki ji komai yanzu."

"Wanne irin in zauna kuma kamar wata ruɓaɓɓiya? Ƴarki ce ni da zaki ba ni wannan umarni haka?"

Ammi ba ta kuma magana ba ta nemi guri ta zauna, Na'ima da take jin kamar ta tsinkawa Granny mari saboda takaici ta nufi ɗakin Captain ta fara yin knocking da ƙarfi.

Lokacin yana kwance idanunsa a lumshe, raba Abra ya yi daga jikinsa a hankali wadda ya samu ta koma bacci da ƙyar sannan ya miƙe a fusace ya je ya buɗe ƙofar. Ganin haka yasa Na'ima ta juya ba tare da ta yi masa magana ba, kamar ya share ta ya koma sai dai ya daure ya bi bayanta.

Cikin mamaki yake duban su Ammi ganin su zaune a parlour ba tare da ya san da zuwan su ba. kallon Na'ima ya yi cikin ɓacin rai, akan wannan 'Yar maganar shine ta ɗaɗɗako iyayensa suka zo? Siririn tsaki ya ja a hankali ya ce. "Sannun ku da zuwa."

"Granny ta ce. "Yawwa, ya jikin naka ɗan albarka? Na ga jiki ya yi kyau Masha Allah."

"Da sauƙi Alhamdulillah." Ya ba ta amsa ba yabo ba fallasa.

Baffa ya ce. "Nemi guri ka zauna mu yi magana." Bai yi musu ba ya zauna a saman carpet.

"Wacce yarinya ka kawo gidanka Khamal?" Baffa ya jefa masa wannan tambayar.

A nutse ya fara magana cikin ladabi. "Baffa a wannan operation ɗin da muka fita na tsinci wata yarinya k'arama daban ba'a cikin yaran da aka yi kidnapping ɗinsu ba...." Bayanin komai ya yiwa Baffa har yadda suka yi da Na'ima bayan an kawo Abra.

Cikin zuzuta Granny ta ce. "Huhuhu, yau na ga ƙarfin hali, Na'ima ashe dama ke ba matar rufin asiri ba ce ba mu sani ba? Na ɗauka ko dabba Khamalu ya kawo gidan nan baza ki ce uffan ba sai dai ki karɓe ta hannu bibbiyu. To gidan naki ne ko nasa? ban da jaraba irin taki mutumin ba shi da lafiya amma ki saka shi a gaba da fitina, kina fama da narkeken ciki haihuwa ko yau ko gobe maimakon a gan ki da carbi a hannu kina lazimi akan Allah ya sauke ki lafiya, amma ke ta neman bala'i kike? Tirrr da wannan abu."

Na'ima ta saka kuka ta ce. "To kuma a rasa mai riƙon yarinyar sai shi kaɗai? Cewa fa ya yi idan ba'a ga iyayenta ba a nan za ta cigaba da zama tare da mu."

Baffa yana duban ta ya ce. "Ki kwantar da hankalinki Na'ima, a yanayin da kike ciki ba'a son kina saka damuwa har haka a cikin ranki."

Ammi ta nisa ta ce. "Amma Khamal daga tsintar yarinya sai ka ce kana son ta zaka riƙe ta? Mene ma'anar yin hakan?"

"Wallahi first love ba da wata manufa nake son riƙe Yarinyar nan ba, tun kallon farko da yi mata na ji ina jin tausayinta sosai a cikin raina. Ni fa ban ga abun ɗaga hankali a wannan abun ba, me yarinyar za ta tsare mata in ta zauna a gidan? Ammi ke uwace ya rayuwar wannan yarinya za ta kasance idan ta faɗa hannun ɓata gari?"

Na'ima ta e "Ai dama dole ka ce haka tun da Ubangiji ya toni asirin ka, to wallahi sai dai ka zaɓa ko ni ko ita, amma ni dai ba zan zauna da ita a cikin gidan nan ba."

"Sai ki san inda dare ya yi miki, gida dai nawa ne kuma abun da na gama zan yi a cikinsa." Ya ba ta amsa cikin haɗe rai.

Tsawatar musu Baffa ya yi ya ce. "Ya isa haka! Ba zuwa muka yi mu saka ku a gaba kuna sa'insa ba."
Ya mayar da duban sa ga Na'ima ya ce. "Ki yi hak'uri ki bar yarinyar ta zauna a nan ɗin kafin Allah ya bayyana iyayenta, kar kuma ki saka a ranki na goyi bayan Khamal ne, a'a ko kaɗan, na san halin Khamal na san waye shi, ba'a shaidar ɗan mutum amma zan yabi Khamal akan ba ya aikata zina, tun daa da ba shi da mata bai yi ba balle yanzu da yake da ke. Taimako ne zai yi na riƙon yarinyar, domin idan ya bar ta ba'a san yanda rayuwarta zata kasance ba, duk da gwamnati za ta kula da ita tare da ba ta kariya amma nan ɗin sai ya fi safe."

Granny dake bin su da ido ta fashe da kuka ta ce. "Allah wadaran naka ya lalace, yanzu Na'ima saboda tsabar baki da ta ido mijinki kike dangantawa da zina? To ki je dan kanki, Allah kuma ya saka mana akan wannan k'azafi da kika yiwa jikana."

Ta share hawayen fuskarta tana mitsi_mitsi da ido ta ce. "Kin ci albarkacin cikin dake jikinki, amma wallahi da yau a bazawara zaki kwana a gidan Ubanki, domin kuwa ke ba matar mutunci ba ce, ja'ira da ido kamar an soya Aya."

Baffa ya ce. "A'a Hajiya a dai bi komai a sannu.."

Bai gama rufe baki ba ta hayayyaƙo masa da faɗin. "Na ƙi na bi a sannun, Sharrin zina fa ta yiwa jikana, ku kuma yana ɗanku kun zauna kuna yin abu wani lako_lako kun ƙi yin abu da jiki ki ɗauki mummunan mataki a kanta."

Ta ƙasan ido Na'ima ta dinga wurga mata harara. Nasiha mai ratsa jiki Baffa ya yi musu akan su ƙara hak'uri da juna, sannan ya yiwa Na'ima faɗa akan zargin da ta yiwa Captain, ya nuna mata hakan ba daidai ba ne, musamman da already dama ta riga ta san halin Captain, bai kamata daga ta gan shi da yarinya ta ce ƴarsa ba ce. Sannan ya ba ta hak'uri akan riƙon Abra da ya ce su yi, dan ya gani baro baro a fuskarta ba ta ji daɗin hakan ba ko kaɗan. Shi kuma Baffa haka Ubangiji ya yi shi, mutum ne mai faɗar gaskiya komai ɗacinta, ko da ba za ta yi maka daɗi ba sai ya faɗa, sai dai ka ji haushin sa. Ammi ma ta ɗora da ta ƴar nasihar da ban baki a gare su gaba-d'aya. Na'ima kawai jin su take yi amma ba ta fahimtar me suke cewa, ita kawai gani take yi sun goyawa ɗansu baya ne.

"Sai masifa da wasu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login