Showing 75001 words to 78000 words out of 231718 words

Chapter 26 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14707

shawagi?"

Shiru Ilya ya yi bai ce komai ba, ƙwafa ta yi tana ƙara bin tsoffin matan da kallo cikin yatsina fuska kamar ta ga kashi. Ɗaya daga cikin Matan ne ta tsuguna akan gwiwoyinta cikin kuka ta ce. "Hajiya dan Allah ki yi haƙuri, neman taimako muka zo, ki taimaka mana kamar yadda Ubangiji ya taimake ki." Kallon sama da ƙasa ta yi mata cikin raini ta ce. "Nan ba gidauniyar taimako ba ne Malama, don haka ku tattara tsummokaran ƙafafuwanku ku bar mini parlour, kafin ku gama cika shi da wari da tsami. Mutane sai mutuwar zuciya, ba za ku fita ku nema ba sai yawon maula." Mtss ta ja tsaki tare da ɗaukar wayoyinta. Cikin gargaɗi ta kalli Ilya ta ce. "Ka fitar mini da su daga parlour kamar yadda ka shigo da su, ka jirayi hukunci kuma na shigo mini da matsiyata cikin gida da ka yi." Ba ta jira amsar shi ba ta shiga ƙwala kiran sunan Asabe da sauran abokan aikinta, jiki na rawa suka fito daga wani ɗaki dake cikin parlour'n, umarnin sake tsaftace parlour'n gami da saka masa turare ta ba su sannan ta haye sama, cikin izza da ɗagawa tamkar wata matar Shugaban ƙasa.




Baby ce ta kalli Ihsan, da har zuwa wannan lokacin, tana kwance akan gado.
A ɗan hasale Baby tace "waike Ihsan meye haka ne? Ki tashi ki shirya Abuja zamu tafi yanzun nan, cin uban wancan ɗan iskan".

Ihsan ta yamutsa fuska tace "Wallahi Baby, haryanzu jikina na yi mini ciwo sosai, kin san na zubar da jini sosai".

"To ai shiyasa dan ki fanshe wahalar ki, ya sa nace ku shirya mu tafi Abuja, bana jin Alhajin Janna Sosai, yana da sakin hannu, Amma shi wannan sojan nake son ki wankar mana, tunda mutumin banza ne shi, ga rowar tsiya, Wallahi ko mu ɗau tsiraicinsa muyi blackmailing ɗinsa".

Ihsan tace "Wallahi tsoro nake ji Baby"

"Au tsoro, kwanta zaki ga tsoro, dalla ki tashi ki shirya ba zaki sha wannan wahalar a banza ba, kuma idan muka je kar ki gaya masa an cire cikin nan kice kuɗi zai baki kije ki cire"

Haka Baby ta sata a gaba, ta tashi tai wanka ta shirya, su uku suka hau motar Baby, suka nufi garin Abuja.


Major ya kasa ya tsare, akan Lallai a tsananta bincike a gano, dalilin mutuwar sojojin nan da ake tuhumar yadda hatsaniya ta ɓarke, har sukai faɗa a tsakaninsu, amma abubuwa gaba ɗaya sun cakuɗe, an hargitsa abubuwan, yadda Binciken zai bada wahala, wanda duk plan ɗin General Ibrahim ne.

Ba tare da an samo bakin zaren ba, a dole Abbi ya shirya komawa gida.

Washegari ya kama Saturday, around 3pm bayan Abra ta gama ayyukan gida tana kwance akan kujera 3 seater tana browsing wani assignment da aka ba su a wayarta, Na'ima da Khamal suka shigo cikin parlour'n. Idanun Abra akan wayarta ta amsa musu sallamar da suka yi tare da gaishe su, saboda hankalinta gaba-d'aya yana kan assignment ɗin, so take ta yi ta gama dan yana da wahala, gashi kuma da yawa.

Dinning area su Na'ima suka ƙarasa, Khamal ya zauna ta fara zuba masa lafiyayyen abincin da Abra ta girka. Bayan ta gama ta saka masa spoon ta saci kallon Abra ta ce. "Man, ban san me yake damun Daughter ba, yanzu ta koma always busy with her phone." Cikin rashin damuwa Khamal ya ce. "Kin manta yanzu yar jami'a ce ita? Ai dole sai tana fama da browsing da karatu kodayaushe."

"To me yasa Salman shi ba ya haka?" Ta tambaye shi tare da zama a kusa da shi."

"Ta fi shi serious ne."

Cikin takaicin abun da Khamal ya faɗa ta ce. "Gaskiya ban yarda ba, yarona ma babu lefi, abun da na fi tunani kawai ita da akwai abun da take yi a wayar bayan karatun."

Khamal ya dakata da cin abincin da yake ya ce. "Ban fahimce ki ba, me kike nufi?" Duk da Na'ima ta tsorata da yanda ya tsare gida amma ta dake zuciyarta ta ce. "Ni nake zaune da yaran nan kodayaushe a gida, kuma duk wani motsin su a kan idona yake, ta haka na gane yawan amfani da waya da Abra take yi, koda yaushe waya tana hannunta, har cikin dare idan na je duba ta ina hango hasken screen ta cikin blanket ɗinta, alamun ba bacci take ba waya take latsawa. Yanzu ma ka lura fa da muka shigo, ko ɗauke idonta daga kan wayar ba ta yi ba."

"Shi ne me? Ba ki ga papers ɗin dake gabanta ba, may be tana discussing something important related to her study ne, wanda yake buƙatar full attention ɗinta akai."

Cikin baƙin cikin rashin sanin haɗin kai Na'ima ta ce. "Haka ne, ni ma ba wani abun nake nufi ba, kawai ina so a bincika ne in ma wanin abun ne a yiwa tufkar hanci tun wuri."

"Babu ma komai, na san tarbiyyar da na bawa yarana, na kuma yarda da su, dan haka ki daina irin wannan tunanikan, just pray for them, Allah ya kare mana su daga aikata dukkan wani abu mara kyau."

Cikin yaƙe ta ce. "Ameen Mijina." Khamal ya cigaba da cin abincinsa, yayin da Na'ima ta shiga saƙe_saƙen yanda za ta ƙara ɓullo masa, akan makircin da take son ƙulla wa Abra. Ba ƙaramin baƙin ciki ta ji ba a yanzu da ya ƙi bawa maganarta muhimmanci, ta so ya karɓi wayar ya ga abubuwan da ta tura a ciki, ba tare da ita kanta Abran ta san da su ba, ta san idan ya gani kashe Abra ne kawai ba zai yi ba, saboda yanda ta san shi da takatsantsan da tarbiyya akan Ƴaƴansa.

Cikin kwanikan nan da suka wuce mai turawa Abra text na love messages bai fasa ba, duk da ba kowanne take reply ba, saboda ta yi ta yi ya faɗa mata wane ne shi ko ya tura mata pics ɗinsa amma ya ƙi. Sai dai ta rasa me ya sa idan ta ga message ɗinsa take jin nishaɗi a cikin zuciyarta, ba ta gajiya da karanta messages ɗin nasa ko kaɗan, har ta haddace lokutan da yake tura mata, idan ya ƙara mintuna bai turo ba ta dinga duba wayarta kenan, tana jin vibrate za ta duba da sauri, idan shi ne ta buɗe ta karanta cikin sauri, idan kuma Company ne ta yi tsaki ta ajiye wayar.

Yau Monday, misalin ƙarfe bakwai da rabi Abra ce tsaye a gaban mudubin ɗakinta tana gyara rolling ɗin mayafin abayar dake yane a kanta. Wayarta dake kan mudubin ta yi vibrate alamar shigowar saƙo. Ɗauka ta yi ta duba, ganin Mr unknown ya sa ta buɗe da sauri ta fara karantawa.

"God Morning My Angel, da fatan kin tashi lafiya? Na san yanzu kina shirin tafiya school, Allah ya kiyaye hanya ya ba da sa'a, have a nice day Princess!"

Murmushi ta yi a saman leɓɓenta tare da lumshe ido ta buɗe, zuciyarta cike da son ganin Mr unknown ɗinta. "Yaushe zan gan ka? A ina zan gan ka? Mutum ne kai ko Aljan da kake sanin duk wani moment ɗina?" Ta tambayi kanta a hankali tana kallon fuskarta ta cikin mudubi, still tana murmurshi.

"Angel!"

Muryar Salman da ba ta san time ɗin da ya shigo ɗakin ba ta doki kunnenta.

"Na'am Faris." Ta amsa tare kallon shi.

Wani irin kallo yake bin ta da shi bai ce komai ba.

"Wannan kallon fa? Mu je in ka gama shiryawa, dama kai nake jira."

"Kin yi kyau sosai kamar na sace ki." Ya faɗa cikin siririyar murya.

Tana murmurshi ta ce. "In ka sace ni Salman ka kai ni ina?"

"Gidana." Ya ba ta amsa cikin confidence.

Jinjina kai kawai ta yi ba tare da tunanin komai akan maganar tasa ba, ta ɗauki jakarta tana shirin fita Salman ya ce. "Where is your facemask?"

"Yau ba zan saka ba gaskiya, damu na yake yi."

Dan haɗe rai ya yi ya ce. "Ki saka, yana ina in ɗauko miki." Cikin shagwaɓa ta ce. "Ka fiya takura Faris, don Allah ka ƙyale ni." Bai kula ta ba ya janyo drawer inda ya san tana ajiyewa ya ɗauko sabo ya miƙa mata. Da farko ƙin karɓa ta yi, sai da ta ga kamar ransa ya ɓaci sannan ta karɓa, cikin marairaicewa ta ce. "Ka yi haƙuri Bro zan saka." Ɗauke kai ya yi alamun he is angry with her.

"Zan saka fa, Please kar ka yi fushi, ka san bana iya jurar fushinka." Ta yi maganar kamar za ta yi kuka. Sakin fuskarsa ya yi ya ce. "Ya wuce cry cry Baby, kawo in saka miki ma da kaina, sai ya fi yin kyau." Ba ta yi musu ba ta miƙa masa. Idanunsa a cikin nata yana narkar da su ya saka mata, bayan ya gama ya kashe mata ido ɗaya tare da sakar mata wani tattausan murmushi. Turo baki ta yi ta ja karan hancinsa da ƙarfi, ta ce. "Gashi nan ka lalata mini rolling ɗina."

"I'm sorry the best among the best." Ya faɗa cikin kulawa.

Na'ima ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, cikin faɗa ta ce. "Ba za ku makarantar ba ne? Kun tsaya kuna shiririta ko? Tun ɗazu driver yana jiran ku."

"Ga mu nan fa Mami." Cewar Salman.

Harararar shi ta yi ba ta ce komai ba ta juya ta fita.


Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423  Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal.

Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750.



Kamar kowacce Monday yau ma around 12 su Abra suka tashi, ta zauna a inda ta saba jiran Salman tana tsimayin shi. Shiru-shiru har 1 ta wuce bai zo ba, wata irin yunwa Abra ta ji tana ƙwaƙular hanjin cikinta. Cikin ƙosawa da zaman gurin ta ɗauko wayarta ta kira shi, har 3 missed call ta yi masa amma bai ɗaga ba. Miƙewa ta yi dan a yanda take jin yunwa ba za ta iya jiran har ya zo ba tare da ta ci abinci ba, Cafeteria ta nufa direct cikin tafiyarta mai tattare da nutsuwa da ɗaukar hankali.


Bayan ta zauna ta yi order'n abun da take so ta ɗauko wayarta ta fara latsawa kafin a kawo mata. Haka kawai ta ji ta a takure tunda ta zauna a gurin, gyara mask ɗin fuskarta ta yi, ya rufe mata har saman hancinta, kyawawan idanunta ne kawai a waje. Duk da haka ba ta ji ta daidai ba, ɗago kanta ta yi a hankali tana kallon mutanen gurin, Cafeterian da ɗan jama'a amma kowa sabgar gabansa yake yi. Duk yadda ta so daurewa amma ta kasa, wani irin ido mai kaifi ta ji yana yawo a cikin jikinta alamun akwai wanda yake kallon ta. Slowly ta juyar da kanta gefe, lokaci ɗaya wani irin daddaɗan ƙamshi mai saukar da nutsuwar zuci ya ziyarci hancinta, ba ta san lokacin da ta lumshe idonta ta buɗe ba, ƙamshin ya yi mata kamar ta taɓa jin shi. Wata irin faɗuwar gaba ce ta ziyarce ta, lokacin da ta tsinci idanunta a cikin mutumin da ba ta taɓa tunanin sake ganin shi ba, ta ma manta da shi gabaɗaya a cikin rayuwarta. Cikin sakanni ƙwaƙwalwarta ta tuno mata inda take jin ƙamshinsa, a jikin i.d card ɗinta ne, tun ranar da ya ba ta har yau ƙamshinsa yana nan manne a jikinsa. Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tare da saurin janye idanunta daga cikin nasa, wani irin abu ta ji yana yi mata yawo a jinin jikinta, gabaɗaya sai ta rasa nutsuwar zuciyarta ba tare da ta san dalili ba. Juyar da kanta ta yi daga ɓarin da yake, cikin ƙoƙarin daidaita nutsuwarta gudun kar a gane yanayin da take ciki. Wayarta dake hannunta ce ta fara vibrate, dubawa ta yi ta ga Salman ne yake kiran ta.



Jikinta ne ya hau rawa, ta kasa ɗaukar wayar, saboda wanda ta gani ya ja kujerar gabanta ya zauna.

Kamar kullum, yau ma kasa ɗaga idanunta tayi ta kalleshi, sai wani irin bugu da zuciyarta keyi, tamkar zata tsaga ƙirjinta ta fito.

Dubansa ya kai kan screen ɗin wayarta, yaga sunan Faris akan screen ɗin.

Ɗan taɓe baki yayi, a daidai lokacin kuma aka kawo mata Abincin da tayi order, aka ajiye a gabanta.

Sai dai haryanzu ta kasa ɗago kanta, sai wasa da take da yatsun hannunta.

"Eat your food, i have something to discuss with you" yai Maganar yana tura mata plate ɗin Abincin gabanta.


Kamar gunki haka Abra ta zama, gashi da ƙyar take numfashi, saboda tsoro ga uban facemask a fuskarta, gefe ga Salman na ta rangaɗa mata kira, ba ƙaƙƙautawa.

"I said you should eat your food, zamu yi magana sauri nake".

Ɗago fararen idanunta tayi ta kalle shi, karaf ta sanya idanunta cikin nasa, saurin janye nata ta yi daga nasa.
Yayin da shi kuma ya cigaba da kallon ta yana nazartar ta.

Ya ɗan fesar da iskar bakinsa ya ce "Well, tun da ba zaki ci Abincin ba, ni bari inyi abunda ya kawo ni, ina da abun yi."

Abra a ranta ta ce "Ikon Allah".

"I am Sp Adnan Aliyu Matawalle, so na san maybe na takura miki, saboda yawan bibiyar ki da nake yi. So ni ba yaro ne ƙarami, ba shiririta ce ta kawo ni gurinki ba. Amm ina tunanin ina son mu kasance ƙarƙashin inuwa guda dake, duk da bai kamata in tunkare ki kai tsaye in sanar da ke ba, sai na nemi iznin mahaifinki, ina son zan Aure ki ne, idan ba damuwa ina son ki bani Address ɗin gidanku, zan zo".

Zaro ido ta yi, tare da jin wata mummunar faɗuwar gaba, ta ina zata fara kai shi gidansu? Tukuna ma haka ake neman Aure ba soyayya ba komai, sai kace dole?".

"Kin yi shiru"

In a cracking voice ta ce "Ni karatu zan yi, Abbinmu zai mini faɗa".

"Kina nufin ba zaki yi Aure ba kenan?".

"Ni dai gaskiya Abbi zai mini faɗa".

"Ai Abbin naki zan fara samu, ni zan same shi".

Shiru Abra ta yi, ba ta sake cewa komai ba.

"Bana son ina magana ayi banza da ni, ki bani Address ɗin, ina sauri zan koma Kaduna ne".

Shiru ta kuma yi, ba tace komai ba.

Kallon wayarta dake sake vibrating ya yi, ya miƙe tsaye ya sa hannu ya ɗau wayar da ID card ɗinta, ya watsa su a aljihunsa yace "Idan kin shirya, kya iya nemana, sai ki karɓi wayarki"

"Dan Allah ka bani wayata" Banza yai mata ya nufi hanyar fita daga gurin.

Miƙewa ta yi domin ta bishi, tana bin shi tana masa magiya, amma ko waiwayowa bai yi ba, ya buɗe motarsa ya shige, ya ja ya bar gurin.

Abra ji tai kamar ta ɗora hannu a ka ta kurma ihu, ita yanzu ina zata sake ganinsa? Gashi ta ji yace Kaduna zai tafi.

A hankali tace "Wayyo Allah wayata, me zance a gida?".


Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423  Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal.

Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750.
[10/1, 2:40 PM] Abk: A gigice Baby ta cillar da jakar hannunta, cikin waro ido ta kurma wani uban ihu tare da ficewa daga ɗakin hotel ɗin a ruɗe. Ƙarasawa Janna ta yi ta shiga girgiza ƙafar Ihsan cikin kuka da tsananin tashin hankali.

Ɗaya daga cikin ma'aikatan hotel ɗin ne ya hawo sama da sauri jin kururuwar Baby.

"Hey, Lafiya kike mana wannan kwakwazon?"

Kasa magana Baby ta yi, nuna masa ɗakin kawai take yi da hannu tare da toshe bakinta. Shiga ɗakin ya yi cikin sauri, cak ya tsaya tare da dafe ƙirjinsa cikin firgici.

"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un!" Abun da ya furta kenan a fili idanunsa akan gawar Ihsan dake kwance cikin jini malel-male. Da sauri ya juya ya fita ya je ya sanar da Manager na hotel ɗin abun da yake faruwa.


After some minutes
Su Janna ne zaune a police station mafi kusa da hotel ɗin, idanuwansu sun yi luhu-luhu alamun sun ci kuka sun gode Allah, sai zazzare idanuwa suke yi cikin firgici.

D.p.o dake bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya ya dubi wani jami'i ya ba shi  umarnin ya shigar da Janna cikin cell, kuka ta fara tare da yi masa magiya tana ba shi haƙuri, tsawa ya daka mata wanda ta sa su duka suka razana, ba shiri ta yi shiru ta shiga jujjuya kai. Tasa ƙeyarta jami'in ya yi har cikin cell.

"Ki nutsu, tambayoyi zan miki, kuma ki faɗa mini gaskiyar abin da kika sani, domin idan ma kin mini ƙarya zan gano daga baya, kuma hakan ba zai haifar miki da ɗa mai ido ba." Cewar D.p.o yana kallon Baby da jikinta ke tsuma.

"In...insha Allahu zan faɗa maka gaskiya yallaɓai."

"Good." Ya faɗa cikin gyaɗa kai.

"Mene ne alaƙarki da wacce aka kashe?"

"Ƙawata ce."

Jinjina kai ya yi ya ce. "Tsawon wane lokaci kuka ɗauka tare? Kuma a ina kuka haɗu?"

"4 Years back, a makaranta muka haɗu, A.b.u Zaria, course ɗinmu ɗaya da ita."

"Okay, shi ne aka haɗa baki dake kenan aka kashe ta?"

Cikin kuka Baby ta ce. "Wallahi ba haka ba ne Yallaɓai, ba ni da masaniya akan kisan Ihsan, ta yaya ma za a haɗa baki da ni a kashe ta? Ƙawata ce fa." D.p.o ya ce. "Ku ƴan wanne gari ne?"

"Dukanmu ƴan Kaduna state ne."

"Kaduna? Amma me ya kawo ku Abuja?"

Shiru Baby ta yi ta fara sosa kanta tana rarraba idanuwa.

"I'm toking to you my friend." Ya faɗa cikin tsawa.

Zabura ta yi ta ce. "Mun zo ganin wani mutumi ne?" Ya ce. "Wane wanin? Daga Kadunan kuke yanzu?"

"A'a, muna zaune a school hostel ne, daga can muka zo nan."

Jinjina kai ya yi cikin nazartar ta ya ce. "Okay, cigaba da bayani, gurinwa kuka zo?"

Cikin rawar murya ta ce. "Wani tsohon Soja ne, ita ƙawar tamu da aka kashe muka rako nan Abuja, don ta gana da shi akan wani abu." Tattara hankalinsa gabaɗaya D.P.O ya yi a kanta ya ce. "Wanne abu ne wannan da kuka taho tun daga Kaduna har Abuja saboda kawai su yi magana a kansa?"

Baby tana hawaye ta ba shi labarin duk abun da ya faru tsakanin Ihsan da General Ibrahim, ganin ba ta da mafita, kuma tana son ta kuɓuta daga zargin su da ake yi. D.P.O ya ce. "Kin tabbata abun da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login