Showing 147001 words to 150000 words out of 231718 words

Chapter 50 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14813

ta kama ranar yanke hukunci, tun ranar Asabar Abbi ya tafi babban birnin tarayya Abuja, dan ganin shari'ar, Gwaska kuwa ya cika wandonsa da iska, ya bar Nigeria gaba ɗaya sai wasu daga yaransa aka kama.
Abin kunya har da tsofaffin manyan 'yan siyasa, da suka riƙe manyan muƙamai a ƙasa a wannan almundahana da aka aikata.
Bayan dogon turanci irin na kotu da alƙali ya gabatar, da faɗan manyan dokoki da ga cikin littafin da suke dogaro da shi gurin shari'a, aka yankewa General Ibrahim mai retire kisa ta hanyar rataya, abin da ya ƙara bawa mutane mamaki shine, hatta Manyan ƙusoshin gwamnatin nan, da aka samu da laifi hukuncin kisa aka yanke musu, abinda ba'a taɓa yi ba a ƙasa, amma aka basu damar ɗaukaka ƙara.
General Ibrahim duk ya rame, tsufansa ya fito, ga shi zamansa a gidan yari, cututtuka suka baibaye shi, yana ta fama da ciwon zuciya da kuma ciwon sugar.
Nan da nan jaridu da gidajen rediyo suka samu abin faɗa, ga lawyoyi duk sun karɓe masa 'yan kuɗaɗensa akan cewar zasu taimake shi yayi free.


Adnan tun da ya tafi gurin aiki, sai tunanin yanayin da ya bar Abra ya dame shi, saboda jikinta da zafi sosai kamar wuta, kuma babu alamar tana iya cin wani abu.
Tsaki yayi tare da ƙoƙarin cire tunaninta daga ransa, amma ya kasa ko yayi yinƙurin cigaba da aiki, da ya tuno ta sai yaji ya damu, ana haka Usman ya zo ya same shi a Office.
Yayi sallama amma maimakon Adnan ya amsa sai yayi tsaki, Usman ya kalleshi ya ce 'Lafiya kuwa ina sallama amma kana tsaki?".

Adnan ya kalleshi ya ce "Sorry, hankalina ne a wani gurin shiyasa".

"Ok, ya garin ya Madam kuma?".

"Wai kai ina ruwanka da Madam ɗin nan da kullum sai ka tambaye ta?".

"To tambayar ma laifi ce kenan?"

Adnan ya ce "Eh kusan haka, dan da bata lafiya ba zaka ganni a kan kujerar nan ba".

Usman yayi murmushi ya ce "Yayi mijin balarabiya".

"A daina tanka mini mata dan Allah, duk bakinku ya sa ta fara duhu"

"Eh tunda gamu mayu ba".

"Ni dai bance ba" Adnan yayi Maganar yana murmushi.

Adnan ya ce "Wai ni ya batun Meenal ne, na jika shiru, ka rigani haɗuwa da ita fa kan in haɗu da Abra, amma haryanzu shiru, kar kayi wasa da hankalin 'yar mutane fa".

Usman ya ce "Hmm"

"Ban gane hmmm ba?"

"Sp zancen babu daɗi ne sam, ni na fasa Auren Meenal"

"Amma mai yasa?"

"Abubuwan babu daɗi ne sam, amma zan maka bayani".

"Allah ya sa ba daga gurinka aka samu matsalar ba Usman?"

"Ba daga gurina bane, amma nasan ko kaine, abin da nayi shi zaka yi".

"To shikenan Allah ya tabbatar da alkhairi" suka gama hirar aikinsu.

Suna magana amma hankalin Adnan yana kan Abra, haka ya lallaɓa ya kai azahar, yayi sallah ya tafi gida.

Yana zuwa gida ya nufi ɗakin Abra, amma ya tarar ba ta ciki, kayanta da ta cire a ƙasa a tsakar ɗakin.
Ya buɗe ƙofar banɗaki, amma bata ciki.
Ya shiga ƙwala mata kira "Abra! Abra!"

Ya duba kitchen amma ba ta nan, ya tafi ɗakinsa amma nan ma ba ta nan.
Nan hankalin Adnan ya fara tashi, da ya tabbatar da Abra ba ta gidan gaba ɗaya.
"Ina yarinyar nan ta shiga haka?" Ya tambayi kansa, gashi babu waya a hannunta balle ya kirata.

Waje ya fita yana lelleƙawa, amma layin nasu tsit yake, ba kowa balle ya tambayi wani.
Bai sare ba ya shiga bi gidajen dake kusa da nasu, yana ƙwanƙwasawa yana tambayar masu gadi, idan Abra taje amma ko ina sai suce su basu ganta ba, ba taje ba.

Abra kuwa bayan ta isa titi, mai napep ta samu ta gaya masa sunan unguwar su Adnan, da suka isa unguwar, tace mai napep ɗin ya tambayi gidan Aliyu Matawalle.
Ya ce mata ai yasan gidan, ya kaita har ƙofar gidan.
Ta biya shi kuɗin motarsa, ta sauka ta shiga gidan tana bin bango, saboda tsananin ciwon da kanta yake mata, da kuma zazzaɓin da ya addabeta.

Mai aikin hajiya Mama ce ta buɗewa Abra ƙofar falon, tana ganin Abra ta fara murmushi tana mata sannu da zuwa, Abra ta jinjina mata kai kawai, ta wuce cikin falon ta zube a kan kujera tana maida numfashi. Mai aikin ce taje ta kirawo Mama, tana fitowa ta tarar da Abra a kwance a kan kujera, tana sauke numfashi da ƙyar.
Da sauri Mama ta ƙarasa in da Abra take tana faɗin "Abra lafiya kuwa?" Tayi maganar tana dafa kan Abra, jikin Abra zafi rau.
Mama ta kalli mai aikinta ta ce "Ɗauko mini wayata in kira likita".

Ta kuma kallon Abra ta ce "Ina Adnan ɗin yake?"

Cikin rawar murya Abra ta ce "Ya tafi gurin aiki, ni kuma naji zan mutu shine na taho nan"

"Amma wane irin rashin hankali ne Adnan yayi haka? Yaya za ayi matarka ba lafiya ka tafi aiki ka barta?"

Mama ta kira likita a waya, sannan ta sa aka haɗawa Abra Abinci, ba ta ci da yawa ba, ta dinga amai.

Likita ya ƙaraso gidan Hajiya Mama, ya yiwa Abra tambayoyi, ya yi mata allurai ya samata ruwa sannan yace da Mama "Idan jikin nata yayi sauƙi zuwa yamma shikenan, idan Allah ya kaimu gobe zan dawo in kuma duba jikin nata, sai ku taho da ita Asibiti for further investigation".

Mama tace "to shikenan"

Abra taji daɗin jikinta sosai, har sakwara Mama ta sa aka yi mata, ta samu ta ɗan ci.

Abra ta ce "Mama dan Allah ki bani aron waya in kira su Mami".

"A'a Abra, ba zaki kirasu ki ɗaga musu hankali ba"

Abra ta marairaice ta ce "Mama tunda nayi Aure fa ya ƙwace mini waya, bana waya da kowa a gida, ba ɗaga musu hankali zan yi ba".

'mai yasa ya ƙwace miki wayar?"

Abra ta ce "Nima ban sani ba"

Mama ta girgiza kai ta bata wayarta.

Wayar Abbi ta fara sanyawa ta kirashi, bugu biyu ya ɗaga "Hello Abbina".

"Daughter na, ya kike ya jikin naki?"

"Da sauƙi Abbi, ina Mami?"

"Mami tana bacci".

"Abbi ka tasheta ka bata muyi magana, tunda na bar gidan fa banyi waya da ita ba".

Duk da Abbi baya shiga sabgar Mami, amma saboda farincikin Abra ya tafi ɗakin Na'ima, ya miƙa mata waya. Ta kalleshi da mamaki ta ce "waye?".

"Ki karɓa kiji".

Ta karɓa ta kara wayar a kunnenta.

'Hello Mami"

"Na'am Abra"

"Mami ba kya nemana ko? Kin ƙi zuwa gidana"

Na'ima ta ce "Na nemi wayarki na ta shiga, kuma mijinki idan aka kira shi kullum baya nan".

"Mami to ba zaki zo ba?"

"Zan zo mana, amma jira muke a gama haɗa kayan garar ki, sai mu taho gaba ɗaya".

"Haba Mami, ni dai kawai ki zo dan Allah, in ba haka ba ni zan dawo gida".

"A ina kika taɓa ganin an yi haka? Ki kwantar da hankalinki zan zo insha Allah".

"To Mami yaushe?".

"Ba zan sa miki rana ba, amma zan zo insha Allah"

Bayan waya da Mami, Abra har su Ammi ta dinga kira a waya, tana musu koke koke, sukai mata alƙawarin za so zo.


Adnan fa hankalinsa yayi ƙololuwar tashi, ya rasa abin da yake masa daɗi, dan ya fara tunanin sanar da hukuma.
Kafin yayi hakan, ya ɗau motarsa ya nufi gidansu, cike da zullumi da tunani.
A falo ya tarar da Hajiya Mama, tana ganinsa ta ce "Yawwa dama kai nake nema".

"Lafiya kuwa Mama?".

"Dole ka tambayeni lafiya mana, ka fita ka bar Yarinya a gida babu lafiya, Allah yasa tayi kyan kai ta fito ta taho nan, a galabaice ta ƙaraso gidan nan".

Adnan ya ce "Alhamdilillah, dama nan ta taho?".

"Ban sani ba" Mama ta bashi amsa, Adnan ya sunkuyar da kai yana sosa ƙeya.

"Tana ɗakina, likita ya bata magunguna ya sa mata ruwa, yace gobe in Allah ya kaimu kuje Asibiti ai mata teses".

Adnan ya jinjina kai ya miƙe, ya nufi ɗakin Mama ya tarar da, Abra a kwance a kan katifa da ruwa a jikinta, hannunta ɗaya riƙe da wayar Mama.

"Da iznin wa kika fita ki ka bar gida? Kika bar mini gida a buɗe ba kowa?"

A hankali ta ɗaga idanunta ta kalleshi, ta ɗauke kanta ta mayar kan waya.

"Ba Magana nake miki ba".

"Dan Allah ni ka ƙyaleni in ji da kaina, idan ba haka ba Wallahi saina faɗi irin zaman da muke kowama yaji gayyar ta watse in huta da bala'inka da zaluncinka".

"Ni kike gayawa haka?".

"Na faɗa, idan kana da wuta ko Aljanna ka sani a ciki".

Ƙwafa yayi, ya fisge wayar hannun Abra ta Mama, ya fito falo.

Ya miƙawa Mama wayarta, Mama ta ce "Yauwa, maiyasa ka ƙwace mata waya ne? Ko waya bata yi da mutan gidan su".

"Wallahi Mama takura musu da koke koke take tana ɗaga musu hankali, a kan bata da lafiya".

Mama ta ce "ba hujja ba ce, ka bata wayarta, umarni nake baka, wannan ai mugunta ce, ka hanata waya da mutan gidansu akan me?".

"Shikenan zan bata, bari ruwan ya ƙare in ɗauketa mu tafi".

"A'a ka bari sai Allah ya kaimu dare"

Cikin ikon Allah zuwa daren, Abra ta ɗan watstsake sai rashin ƙwarin jiki.

Ji take kamar tace ba zata bin Adnan ba, amma ta dake ta tashi suka tafi. Suna tafe ba wanda yake tankawa wani har suka isa gida, kusan ƙarfe sha ɗaya na dare.

Ba ta saurari Adnan ba ta wuce ɗakinta, ta gyara ta kwanta.

Da safe kafin ya fita aiki ya shigo ɗakin, ya tarar da ita a zaune a kan gado, dan fitowarta kenan daga wannan aman da take.

Ya cillo mata wayarta ya ce "gata nan, kin haɗani da mahaifiyata ta sa na baki wayarki, amma Wallahi muddin kika kuskura naga kina waya da wancan sakaran yaron ko makamancin haka Wallahi sai na ƙwace".

"Wallahi ba sakarai bane, Faris ba sakarai bane dan ya fiye mini kai".

Da wani irin mugun kallo ya bi Abra "Ni kike gayawa wancan shashashan ya fini?".

"Eh, ya fiye mini kai, dan tsawon tasowata ya bani kariya da kulawa, kai kuma a zamana da kai ba abin da na tsinta banda ɓacin rai da tashin hankali a kan abinda ban san tushensa ba, wanda yayi maka laifin ma ban sanshi ba balle in san laifin da aka yi maka, dan haka na faɗa Faris ya fiye mini kai"

Janyota yayi daga kan gadon, ya tsaida ita a kan ƙafafuwata, "Wallahi Abra idan kika kuma Magana a kan wannan banzan Salman ɗin saina casa ki".

"Wallahi Salman ba banza bane, kar ka sake ce masa banza"

Sauke mata wani lafiyayyen mari yayi ya ce "Nine banzan kenan?".

"Wallahi Adnan kaci amanata, ba zan yafe maka ba, kai da Allah" hankaɗeta yayi a gurin ta zube, ya dinga wani irin huci, dan ya tsani yaji tana ambatar sunan Salman, sai dai ya ga Abra bata motsi, ga jini ya fara bin ƙafarta.
Sai kuma ya nutsu, ya sunkuya ya ɗagota, amma bata motsi sai jini da yake bin ƙafarta.

Sai kuma ya gigice, ya ɗagota jikinsa amma yaga jikinta ya saki, ba shiri ya miƙe ya gyara mata jikinta, ya sata a mota sai Asibiti.

6hrs later
Abra ta buɗe idanunta, dishi-dishi take gani, a hankali ta gama buɗe idonta, ta kalli ruwan da ke shiga jikinta, da ƙyar ta tashi zaune, Adnan ya taso daga in da yake, kan ya ƙaraso Abra ta fizge ruwan nan daga jikinta.

"Ke meye haka?" Ai bai rufe baki ba ta fara ƙoƙarin dirowa daga kan gadon.

Aikuwa jini ya ɓalle ta jikin cannula hannunta, Adnan ya ƙaraso ya riƙeta yana faɗin "Abra kin yi hauka ne?"

Duka ta dinga kaiwa Adnan a ƙirjinsa, tana ƙoƙarin fizgewa daga jikinsa.

"Abra ki nutsu meye haka? Akwai ƙaramin ciki a jikinki, da yake barazanar zubewa ki nutsu".

"Insha Allah sai cikin nan ya zube, Allah sai ya saka mini Adnan, insha Allah sai cikin nan ya zube ba zan haihu da kai ba".

Jinin da take zubarwa a hannunta duk ya ɓata masa jiki, Nurses ne suka shigo dan bawa Abra magani, amma suka tarar da halin da take ciki, da ƙyar aka dannenta aka yi mata allurar bacci, duk ta galabaitar da kanta.





Gargaɗi sosai likitan da ta duba Abra ta yi wa Adnan a kan a guji abin da zai dinga jefa ta a cikin damuwa, gudun kar a rasa ta ita da abin da ke cikinta, sannan ta ba ta bedrest na sati biyu. Ya kira Mama ya sanar mata halin da ake ciki, ta aiko mai aikinta ta kawo musu kayan buƙata, saboda ita ta je unguwa kuma wurin da nisa.


Sai bayan Magriba Abra ta ƙara farkawa, har lokacin Adnan yana zaune a gaban gadon da take yana latsa waya. Duk da wata irin kasala da take ji amma haka ta daure ta tashi zaune. Cikin kulawa ya ce. "Kin tashi? Ya jikin naki?" Wata uwar harara ta wurga masa ba tare da ta ce komai ba, sai dafe kanta da ta yi. Miƙewa ya yi ya ce. "Ba dai kan ne ke ciwo ba? Sannu, How are you feeling now?" Tsaki ta ja cikin takaici ta ce. "Shut up Malam! Haba, tun ɗazu sai ihu kake mini a ka, Please ka bar gurin nan in daina ganin ka don bana ƙaunar ganin ka ko kaɗan wallahi." Murmushi ya yi ganin yadda ta yi maganar cikin tsiwa, wadda ba ta dace da ita ba sam. Bai ce komai ba ya juya don kiran Likita, ganin drip ɗin da aka saka mata ya ƙare.


Lumshe idonta ta yi bayan ya fita, kalamansa na ɗazu ne suka dawo mata cikin kunnenta da yake cewa tana da ƙaramin ciki. Wasu hawaye masu ɗumi ne suka fara zuba daga cikin idonta. A fili ta furta. "Allah na gode maka da duk Yadda ka tsara rayuwata ta kasance, Allah ka ba ni ikon cinye jarrabawar cikinta." Slowly ta kai hannunta kan cikin ta shafa cikin wani irin yanayi, wanda ta kasa tantance na farin ciki ne ko akasin haka. The thing is so amazing to her, wai yau ita ce ɗauke da juna biyu? Za ta haifi girl or boy nan da wasu watanni? Za ta zama uwa ita ma?


Dawowar Adnan tare da wata Nurse ya katse mata tunanin da take. Saurin share hawayen fuskarta ta yi ba tare da ta bari sun haɗa ido da ɗayansu ba.

"Patient, ya jikin naki?" Nurse din ta faɗa cikin murmurshi.


"Alhamdulillah." Ta amsa mata cikin sanyin murya.


Bayan ta cire mata drip ɗin Abra ta dube ta in serious talk ta ce. "Don Allah Nurse ki taimake ni ki cire mini cikin dake jikina, ko ki faɗa mini abin da zan sha ya ɓare." Cikin matuƙar mamaki Nurse ɗin take duban ta, kallon Adnan ta yi ta ce. "A'a ba mijinki ba ne wannan? Ke kuwa me zai saka ki so rabuwa da Ni'imar da Ubangiji ya yi miki? Abin da wasu suke ta fafutukar nema ba su samu ba."

"Ni dai in za ki taimaka mini ki taimaka mini kawai don Allah."

Nurse din za ta yi magana Adnan da ya kafe Abra da ido ya ɗaga mata hannu tare da faɗin. "Don't worry, you can go idan kin gama yi mata abin da za ki mata, i will solve the problem."

"Okay, Allah ya ƙara lafiya."

"Amin, thank you."


Kuka Abra ta saka bayan Nurse din ta fice, cikin ɗaga murya ta ce. "Kome za ka yi ba zan bar cikin nan ya zauna ba, domin ba zan so na hahu tare da azzalumi mugu mara imani ba." Wani murmushi ya yi ya ce. "Tunda Mother ta haƙura ta haife ki da azzalumin mutum ke ma sai ki haƙura ki haifa, kin ga an yi 1/1 kenan." Ya ƙarashe maganar cikin ɗage gira. Saboda baƙin ciki kasa magana ta yi, sai kuka da ta kuma fashewa da shi. Still yana murmushi ya tashi ya koma gefen gadon tare da zama daf da ita, ƙoƙarin ja baya ta yi saboda ƙamshinsa da ba ta ƙaunar shaƙa ko kaɗan, amma ya hana ta aiwatar da hakan sakamakon hannunsa da ya sa ya zagaye bayanta da shi tare da ƙara matsawa jikinta. Yana bin ta da wani irin kallo ya ce. "Abra Mrs Adnan, yau babu faɗa da rigima a tsakaninmu, saboda farin cikin da nake ciki na samun new Unborn." Ya ƙarashe maganar tare da ɗora hannunsa a kan cikinta ya fara shafawa a hankali.



Cikin tsananin baƙin ciki Abra ta fizge jikinta, ji take kamar ta kikkifawa fuskarsa mari. Saurin riƙo ta ya kuma yi tare da faɗin. "Ki yi a hankali, kar ki illata mini gudan jinina." Tsaki ta ja ta juya masa baya ta kwanta, zuciyarta na mata tuƙiƙin baƙin ciki, ita kaɗai ta san abin da take ji a cikin ranta, Allah ya sani ba ta so haɗa zuri'a da Adnan ba, amma babu yadda za ta yi da ƙaddara.

"Me za ki ci?"


Ta tsinkayi muryarsa yana tambayar ta, banza ta bawa ajiyar shi. Shi kam ko a jikinsa, da gaske yake har cikin ransa yana ƙaunar abin da ke cikin Abra sosai, shi kansa ya yi mamakin faruwar hakan. Lumshe idonsa ya yi yana imagining ranar da Abra za ta haifa masa Baby, bai san irin farincikin da zai yi ba a lokacin.


Bai haƙura ba ya cigaba da tambayar Abra abin da take son ci cikin lallaɓawa, ita kuma ta ƙi kula shi ta bar shi yana ɓaɓatu shi kaɗai. A haka Hajiya Mama ta zo ta same su, ba ƙaramin farinciki ta yi ba da jin Abra na da juna biyu. Ta dinga nan-nan da ita tare da ba ta kulawa. Ita ta kwana tare da Abra, ta ce Adnan ya koma gida.


Washegari aka sallami Abra, Gidansu Adnan Hajiya Mama ta wuce da ita sai dare sannan Adnan ya zo ya ɗauke ta suka koma gidansu, tare suka tafi da mai aikin Hajiya Mama za ta zauna a gidan har zuwa lokacin da Abra za ta samu lafiya. Cikin ƴan kwanakin nan ta samu sauƙin tijara da takurar Adnan, don sosai yake nuna k'aunar cikin jikinta, amma in abin ya motso masa yana taɓawa. Ba ta kula shi saboda ba ta shi take ba, ta jinyar kanta take. Ga mai aikin Hajiya Mama tana ɗebe kewa sosai, don matar babu ruwanta tana da kirki.



Yau kwana biyar da sallamo ta daga asibiti, da daddare tana kwance a ɗakinta suna chatting da Abbi yake mata zancen karatunta.


"Daughter tunda an gama cin amarcin ya kamata a koma school kuma."


Murmushi ta yi cikin jin kunya ta tura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login