Showing 165001 words to 168000 words out of 231718 words

Chapter 56 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14671

zuwa theatre room ɗin da Abra ke ciki, ƙwace ya sameta jikinta sai rawa yake ga wani jini dake zuba ta ƙasanta, harshenta ya zazzago idanunta ya fito waje kana ganinta kasan jijjiga take "Yaya, Yaya Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" gaba ɗaya Salman ya riƙice ya kama Abra ya Rungome yana sakin kuka tare da faɗin "Don Allah Yaya ki tashi, kada kiyi mini haka wallahi ba zan ƙara tafiya na barki ba" ciki wahala da fitar hayyaci Abra ta riƙe Salman tana faɗin "Ina son ka Salmanun-faris, ina son ka, i love You kai ne daidai da rayuwata Salman, ka biyoni muje idan kana so na da gaskiya"

"Ina son ki yaya, burina na kasance dake matsayin matata Yaya ki tashi na maki al'ƙawarin ba zan nan asibitin ba, sai kin zama matata i promise you Abra" hancinsa taja tana riƙesa gam gam "Salman na baka Aishatul-humaira ka riƙeta wajanka, kayi aure ka bawa matarka ita, soyayyar da kake mini ta koma kan Aishatul-humaira Salman, Ubangiji bai ƙaddara zamu zama abu ɗaya ba, ka yafe mini Salman......,"

Ɗit! Ɗit!! Ɗit!!!
Na'urar jikinta ta fara ƙara alamar numfashinta na sama yane ƙarewa, da sauri Abbi ya shigo ganinsu a haka yasa a kiɗime ya fara faɗin "La'ilaha illallahu Muhammadur Rasulullahi Sallallahu alaihi Wasallama" ya shiga faɗa da ƙarfi caraf Abra ta amsa ta shiga nanatawa a bakinta, gaba ɗaya Salman ya zare sai jijjigata yake ganin haka yasa Abba kama Salman amma yaƙi ya ƙara rungome Abra yana faɗin "No!!!! Don't do this to me Angel kada ki barni Yaya, yaya kece rayuwata ina son ki kada ki barni wallahi ƙarya kike babu inda zaki tafi dole mu rayu tare babu inda zaki yaya" daidai lokacin Likitoci suka shigo da gudu idanun Abra sukai sama har lokacin tana riƙe da hannun Salman. Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Abba kawai yake faɗa, Dr ya duba Abra muryar Abba na rawa ya ce "Dr ya dai?" Girgiza kai Dr yai domin bai taɓa ganin mutuwa mai tsayawa a rai kamar ta Abra ba "Sai haƙuri, Abra died!" Ya faɗa tare da jan farin yadin dake bed ɗin ya rufe mata fuska. Miƙewa tsaye Salman yai ya ce "Daman na sani, barci take tana farkawa zata ce ta fasa tafiya ta barni, Abbi kalli yaya ita ce komai tawa kalli yadda Abra ke barci" kasa mgn Abbi yai sai jawo Salman da yai jikinsa ya rungume amma gaba ɗaya jikin faris rawa da tsoma yake ga wani zafi da jikinsa ya ɗauka. Abba ya ce "Allahu Akbar Allah ya jiƙanƙi Abra Ubangiji ya sanya can tafi nan Allah yasa Aishatul-humaira ta zama garkuwarki rana gobe ƙiyama.." daidai lokacin Adnan ya faɗo cikin room ɗin idanunsa akan Abra wacce take ƙwance samɓal an rufeta da farin yadi. Juyawa yai ya kalli Abbi wanda yake rungome da Salman dake ta sumbatu kafin ya juya ya kalli Abba cikin rawar murya ya ce "Ina matata Abba?" Kasa mgn Abba yai da sauri Adnan ya Ƙarasa wajan gadon hannunsa na rawa ya yaye rufar da akai mata, Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un fuskar Abra yaci karo da ita idanunta rufe ruf sai haske da fuskarta tai sosai juyawa yai ya kalli Abba yana ƙoƙarin mgn jiri ya kwashe sa ya faɗi a wajan a sume babu numfashi, salati Abba ya fara likitoci suka ɗauki Adnan a wani gadon marasa lafiya, Mami da Hajiya Mama suka shigo banda kuka babu abin da suke, Ammi kasa shigowa tayi. Ganin wasu likitoci sun fara janye gadon da gawar Abra ke kwance akai yasa, Salman fasa ihu tare da faɗin "Yaya..." ya faɗa yana rike gadon tare da fara jijjiga gawar yana kiran sunanta kukansa ya tsaya domin gani yake she's still alive a koda wanne lokacin zata iya tashi tace "Faris ƙanina" Abbi mutuwar tsaye yai Sai ajjiyar zuciya yake saukewa da gske ne abin da likita ya faɗa Abra ta mutu? Jiri ne ya fara ɗaukansa ya zube a wajan saman qwiwoyinsa zufa na yanko masa,ƙam Salman ya riƙe gawar Abra yana surutai Mami ma haka, da ƙyar Abba ya zame Salman "Ka cikani yayata bata mutu ba, ba zata mutu ta barni ba wlh wasa take mini zata rama abin da nayi mata ne, barci take na faɗa muku" Sai kuma ya sulale a jikin Abba babu numfashi.




Littafin kuɗi ne, mai so ya tuntuɓe mu ta wannan numbern. 09047871750
[11/2, 2:22 PM] Abk: Sannu a hankali ya dinga binsa a baya, a motarsa, duk da gudu yake tamkar zai tashi sama, baya kula da abin da yake gabansa balle yanayin tuƙin da yake yi.
You tune yayi, ya cigaba kwarara gudu kamar mahaukaci. Harabar wani Asibiti ya shiga da motarsa, a ƙoƙarin da yake na ya cimmasa, motarsa ta yi faci, cikin sauri ya kashe motar ya tsallaka titi, ya shiga cikin Asibitin shima, sai dai Asibitin ƙato ne sosai bai san ina zai nufa ba balle ya ganshi, haka ya gama bulayinsa da leƙe leƙensa bai gano shi ba, haka ya juya ya bar Asibitin.


A hankali ya motsa ƙafafuwansa, tare da ƙoƙarin buɗe idanunsa da suka yi masa nauyi, jin kansa yake tamkar an ɗora masa dutse, sannu a hankali ya buɗe idanunsa tangararau, ya shiga ƙare wa ɗakin kallo. Cikin ƙasa da mintuna biyu, ƙwaƙwalwarsa ta shiga tariyo masa abinda ya faru, sa'oin da suka shuɗe. A razane ya miƙe zaune tare da wani irin shouting "No! Ina mata ta take, Abra, Abra! Abra ki amsa mana, kin ganni nan zo mu tafi gida".

"Adnan me kake yi hakane, shikenan ayi mutum babu tawakalli kamar ba musulmi ba".

Cikin hanzari yai waiwayo ya riƙe hannun Mama ya ce "Hajiya Mama, an fito da Abra daga tiyatar ko? Eh haka ne, an ciro mana babynmu, Abra is under special care of doctors, bari in je in duba jikinta".

Usman da ke gefe ya ƙaraso kusa da Adnan ya dafa shi ya ce "Sp, ka dawo hayyacinka mana, Abra is no more mun rasata, kayi mata Addu'a, dan ita tafi buƙata".

Hankaɗe Usman Adnan yayi, ya fara ƙoƙarin sauka daga kan gadon, amma Usman yayi ta maza ya danne Adnan, Mama ta kira likitoci, suka zo suka maida Adnan bacci ta hanyar alluran da ake masa.

Na'ima ce zaune a kan gadon marasa lafiya kusa da Salman, ta rungumeshi a jikinta tana kuka, Salman sai surutai yake yi "Mami, dan Allah kar ki ce mini da gaske na rasa Abra har abada, dan Allah ki tasheni daga baccin da nake yi, she's my life, ina sonta Mami".

"Salman we miss her, Allah ya fi mu ƙaunarta, shi ya bamu ita kuma ya karɓeta, Salman na rasa 'yata, tun da nake a rayuwata ko mutuwar mahaifina ban ji ta kamar yadda naji mutuwar Abra ba, na rasa 'ya ta, 'ya mai biyayya da tsananin ƙaunata, Allah yayi miki rahama Abrana" Na'ima ta ƙarasa maganar, tana rushewa da kuka, mai cike da tsantsar damuwa da nadama.

Salman da idanunsa suka yi jawurr, ya kalli Mami ya ce "Mami ina Abbi, mu tafi da gawar Abra Kaduna ayi mata sutura a can".

Mami ta ce "Salman, kwanan Abra biyu a kabari, nan bana hayyacina, kaima ka suma suka tafi da gawar, aka yi mata jana'iza a gidan su mijinta, kuma babanku ya ce ba zaman makoki, kuma saboda rasuwar granny ma na can a gadon asibiti, Abbi ya tafi can wurinta".

"What?! Mami a yiwa Angel sutura a binneta ban sani ba? Wayyo Allah na rayuwa shikenan ni da ita har Abada, ko sallama ba muyi ba, halinki na gari ya biki. Mami dan me za'a kaita gidansu Adnan kamar bata da galihu, mu meye amfanin mu?".

"Faris, gidan mijinta ne fa, a nan yafi cancanta a mata sutura".

Rungume Mami yayi ya sake fashewa da kuka ya ce "Mami, ki daina kirana da wannan sunan, kina karya mini zuciya, Angel ita ta raɗa mini sunan nan, yanzu ta tafi ta barni, dama ni na Aureta na rayu da ita zuwa yanzu".

Jin Surtan Salman na neman wuce ƙa'ida, ya sanya Mami ta rungumeshi tana ta karanta masa Adduoi daban daban.


3days back

Tun da ya koma Asibitinsa ya kasa zaune ya kasa tsaye, yayi shiru yana tunanin wasu abubuwa da suka shuɗe a rayuwar sa. Kamar mahaukaci haka ya fita reception, ya tattara ma'aikatansa gaba ɗaya, sai da ya fara ƙare musu kallo, sannan ya ce "Wacece a duty 3days back?"

Aka nuna masa Nurse ɗin da take on duty.

Ya kalleta ya ce "Ranar wace allura kika yiwa matar nan, bayan kin bar office ɗina?".

"Wadda kace na yi mata ce" ta faɗa ba ƙwarin gwiwa.

"Wacce nace ki mata?".

"Amm, na manta sunanta bari in ɗakko kwalin"

Kafin ta dawo, ya sa aka binciko file ɗin da aka duba Abra a ciki.

Ya duba hoton mai File ɗin, amma ya ga ba fuskar Adnan ba ce a jiki, ya ɗau sheet ɗin da aka yi documenting ɗin case ɗin Abra a jiki, ya duba yana tsaka da dubawar Nurse ɗin ta dawo da kwalin allurar a hannunta.

Ya karɓa ya fara dubawa, jifa yai da kwalin allurar ya shaƙo hijjabinta jikinsa yana rawa ya ce "Are You mad? Kin taɓa ganin an bawa mai ciki wannan allurar? Kin yi kisan kai ana nema a ɗora zargin a kaina a rufe mini Asbiti, kin yi hauka ne?" Nan take idanunta suka yo waje ta fara nishi da ƙyar, sai da ma'aikatan wurin suka haɗu da kyar suka ƙwaceta.

Yana wani irin huci, ya kwafe lambar wayar jikin mai file ɗin nan ya fice, jikinsa na wani irin rawa, gaba ɗaya ya rikice kalaman matashin nan da yayi masa, da hoton yarinyar da ya gani ya jefa shi. Ya shiga tsananin tunani, dan son gano dalilin da ya sanya wannan yarinya ta ke kama da shi, shi dai a rayuwarsa ya san 'yar sa guda ɗaya ce tal, amma mai ya haɗashi kamanni da wannan kyakywar balarabiyar yarinyar?.

"A wane hali take sanadin allurar da aka yi mata, an fita da ita daga Asibitin nan tana zubar da jini bana wasa ba, ko ta rayu? Ko kuma ta haɗu da wani ciwon sanadin allurar? Wane laifi na yiwa wannan matashin yaro?"

Dafe kansa yayi da yake jin tamkar barazanar tsagewa, wani irin ɗaci na tasowa daga ƙirjinsa zuwa maƙogwaronsa, ga wani irin jiri da yake ɗibarsa, tun da yake bai taɓa dana sanin wasa da lafiyar wani ba, irin yadda aka yi wasa da lafiyar yarinyar nan da bai da tabaccin yanzu tana raye ko ta mutu oho, sannan yana son gano alaƙar da ke tsakanin sa da yarinyar, da har wannan matashi yake danganta ta da zama 'yar sa, alhalin 'ya ɗaya gare shi.




"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Mama wai ina Abba ne? Dan idan ke ba zaki gaya mini gaskia ba na san shi zai gaya mini, a nuna mini ɗakin da mata ta ke dan Allah, na tashi daga baccin da nake haka dan Allah ku haɗani da mata ta" Adnan ya cihaba da surutai tamkar mahaukaci.

Tsawa Mama tayi masa "Adnan meye haka kake ne kamar ba musulmi ba? Ƙarshe wanda muka fi ƙauna a duniya shi ne Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, amma Allah ya karɓe shi baya duniya mun haƙura mun dangana, sai kace a kanka a fara yin rashi, duk kabi ka gallabi kan ka, ba zaka iya miƙa lamarinka ga Allah ba?".

Cikin kuka Adnan ya ce "Yanzu Mama ta tabbata Abrana ba ta raye, ta tafi ta barni kenan?".

"Zan maka ƙarya ne?".

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un! Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ka yafe mini. Allah Ina son matata, Allah.. Allah".

"Kai kar ka mana saɓo, Addu'a zaka yi mata kawai".

Miƙewa yayi ya sakko daga kan gadon, ya nufi hanyar fita, Mama ta ce "Ina zaka kuma?".

"Zanje in ga gawarta ne, in mata addu'a in mata kallon ƙarshe".

"To yau kwana uku da rasuwar Abra, kwananta uku a gidanta na gaskiya".

Zaro jajayen idanunsa yayi ya ce "Mama kwana uku fa kika ce? Akan me za'a rufeta ban gama ganinta ba? Mama meyasa?".

"To wa zai tsaya jiranka, ka fita hayyacinka kana ta sambatu, allurai aka yi ta yi maka, kwana uku kenan an binneta" ɗora hannu yayi a ka, ya zube ƙasa a gurin yana sake fashewa da kuka, just rembering the bad memories he makes with her, how bad he treated her, da sauran abubuwa marasa daɗi. Yayi kuka yayi kuka, sai da hawayensa suka bushe ya kalli Mama ya ce "Mama ina Abba ne?".


"Kakar mahaifin Abra, wadda suke cewa Granny ce ta rasu jiya, saboda rasuwar Abra, tun da ta faɗi shikenan, ita ma jiya ta rasu, suna wajen zaman makoki, amma Salman da sirikarka suna Asibitin nan muna tare da su, amma basu sani ba, dan kar a sake ɗaga musu hankali, yanzu ka tashi kayi wanka da alwala, ka zo ka ci Abinci ka rama salloli duk na ji ance ruwan da aka dinga saka maka ba zai bari kaji yunwa ba".

Kallon Mama yake, ita a tunninta har wani Abinci zai iya ci?.
Har yaje yayi alwala ya tada salla, ya sanyawa ransa cewar mafarki yake yi, kuma zai farka.



Lokaci ɗaya Salman yayi wata irin muguwar rama, yayi duhu fararen idanunsa sun yi jawur.
Mami na ta rarrashinsa ya ci Abinci, amma yaƙi sai zubar hawaye kawai yake yi.

Hajiya Mama ce tayi sallama a ɗakin na su, Mami ta amsa, Mama ta zauna suka gaisa tare da sake yiwa juna gaisuwa da kuma tambayar masu jiki.

Mama ta ce "Salman ya dangana, Adnan kuwa sai fama nake da shi, haryanzu sai shirme yake yi, wai shi mafarki yake yi".

Mami ta girgiza kai ta ce "Dole ya shiga cikin ɗimuwa Allah ya basu lafiya gaba ɗaya, ya jiƙan Abra".

Mama ta amsa da Ameen, sannan ta ce "Amm na e Yakamata muje a duba jaririyar can ta cikin kwalba".

Mami ta ce "Ni Wallahi tun da na rasa 'ya ta na manta da ita, shikenan bari muje, ni Major tunda yace mini zasu je Kano su dawo haryanzu shiru, na kirashi a waya sai yace mini zasu dawo, ina son in koma gida saboda masu gaisuwa".

Mama ta ce "Eh ina ga ya bari ne ku ƙara samun sauƙi".

Mami tace "Sauƙi kuma ai sai a hankali, amma har mu koma ga Allah ba zamu warke daga wannan rashin ba" tayi maganar tana share hawaye.

Mama ta ce "Kiyi haƙuri, duk zaman jiranta muke yi".


Haka suka tafi Nursery, wurin da aka sanya Aishatul Humaira a kwalba, ake cigaba da rainonta kasancewar ta bakwaini.

Mami ta ƙurawa yarinyar ido, gata 'yar mistula sai uwar suma cunkus a kanta, ga dogon hanci kamar na babanta, sai farar fatar Abra da ta ɗakko, take ta hasko Abra lokacin da aka kawo mata ita tana yarinya, da yadda ta fara azabtar da ita, kawai ta fashe da wani irin kuka ta ce "Ni dama wannan 'yar ce ta mutu, aka bar mini tawa 'yar, wayyo Allah na Abrata, har Abada ba zan manta zaman da muka yi ba, kuma ba zan daina kewarki ba 'ya ta, ki yafe mini".

Hajiya Mama tace "Kiyi haƙuri, shi Allah ba a tsara masa yadda zai yi, shi ya san hikimar karɓe uwar ya bar 'yar"

Haka tayi ta rarrashin Na'ima, suka biya ta duba Adnan, shima duk ya ƙara rama, sai uban dogon hanci irin na 'yar sa. An kuma yi masa allurar bacci, amma yana yi yana surutai.


Kwanakin Abra shida da rasuwa, sannan Abbi ya aiko da mota, Ya ce a tafi da su Salman, Hajiya Mama ta ce zata yi musu rakiya, suje ta ƙara musu gaisuwa.
Adnan kuwa ko gaisuwa an hana ayi masa, saboda likitoci sun kafa doka sosai a kansa, idan ba abi an kiyaye ba ƙwaƙwalwarsa zata iya samun matsala.

Kafin su Mami su tafi, ta tambayi yadda za ayi da Aisha, ko zasu tafi da ita, amma likitoci suka ce haryanzu ba ta yi ƙwari ba, sai an sake barinta.

Gaba ɗaya hankalin Mami yayi gida, dan haka tace su bar Aisha, a dawo daga baya a ɗauketa, dan ta ita bata ƙi Aishan ta mutu ba, a dawo mata da Abra, ta nuna mata soyayyar 'ya da uwar da Abran tai ta roƙa a baya ba ta samu ba.


Ga Mamakin Naima, maimakon ta ga an yi hanyar gida, amma sai taga an yi hanyar gidansu Ammi, ba ta yi mamaki ba a zatonta a can ake zaman makokin Abra, tun da gidansu ba kowa ba ta nan, sai dai bayan zuwansu suka riski labarin cewar makoki biyu ake yi, dana Abra da na Granny Innalillahi wa Innalillahi raji'un, tashin hankali ba a sa masa rana, da mutane da 'yan uwa sun dangana, amma zuwan Naima da Salman ya sanya mutuwar ta dawo sabuwa aka dinga koke_koke.
Kwanan hajiya Mama ɗaya a Kaduna, tare da su Mami, sannan ta koma Kaduna, saboda hankalinta yana kan Adnan da ta baro shi a Asibiti.




Zaune yake a falonsa, ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya, yayi shiru ya ƙurawa saman roofing, kusan kwanaki bakwan nan, baya iya bacci, hoton yarinyar nan fes ya ƙi barin idanunsa, zuciyarsa na cike da zullumi da son sanin tana raye ko kuwa? Sannan zuciyarsa ta kwaɗaitu da son sanin sahihiyar alaƙar da ke tsakanin ta da shi. Ya koma Asibitin da matashin yaron nan ya shiga babu adadi, amma bai ga ko alamar zai ga mai kama da Adnan ba.
"Doctor wai meke faruwa ne, gaba ɗaya ka canza mai ya faru?" Ta faɗa tana zama a kusa da shi.

"Bakomai" ya bata amsa a taƙaice.

"Kamar yaya bakomai? Ba ka ko cin Abinci, ka daina zuwa wurin aiki, kuma kace mini bakoma".

"Nace miki bakomai, ki ƙyaleni Please".

"To naji zan ƙyaleka, magana ce dama nake son mu yi, Yaron nan da yake zuwa wurin Meenal ne yake son ya turo iyayensa, da tun wancan satin ma ya so ya turo, amma an musu rasuwa wai matar abokinsa ce ta rasu, kuma abokin nasa na Asibiti babu lafiya, amma yaushe za su sameka ko zuwa sati na gaba ne sai su zo ku yi magana".

"Ke ki ƙyaleni na ce, ba wannan ne a gabana ba yanzu!" Yayi Maganar cikin tsawa.

"To ko ma meye a gaban naka Allah yayi maka magani, amma dole ayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login