Showing 171001 words to 174000 words out of 231718 words
Chapter 58 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
damu."
"Tom shikenan, Allah ya kai mu ya ba da sa'a."
Nasiha Abbi ya cigaba da yi wa Salman, wanda ya zaɓi komawa China ne ba don karatu ba kamar yadda ya ce wa Abbi, don shi a karan kansa ya san babu abin da zai fahimta, ya yi hakan ne kawai don ya nesanta kansa da duk wani abu da zai dinga tuna masa da Abra, saboda a kodayaushe gani yake kamar za ta dawo su cigaba da rayuwa, zuciyarsa ta kasa ɗaukar dangana da rashin Abra, ta kasa haƙurin rashin ta. Shi ya sa yanke wannan shawarar ko zai samu salama.
Ganin yadda ake ta zuwa yi wa Adnan gaisuwa ya sa Hajiya Mama ta saka aka yi masa rubutun dangana take ba shi yake sha, saboda babu daɗi a dinga ganin shi a birkicen da yake, don ba shi da maraba da mahaukaci. Alhamdulillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu, cikin kwana biyu ya fara dawowa cikin hayyacinsa, ya rage surutan da yake yi. Sai dai ba um ba um'um, sai ya wuni baiwa kowa magana ba, abinci kuwa da ƙyar yake yin 3 spoon a yini, sai ruwan bunu da Hajiya Mama take matsa masa yake sha. Gabaɗaya ya lalace ya zama abun tausayi, duk wannan abubuwan har yanzu Abba ba ya shiga harkarsa, ko Kallon inda yake ba ya yi, abun har ya fara damun Hajiya Mama.
A hankali yake tafiya kamar zai fadi saboda rashin ƙwarin jikinsa, hannunsa ɗaya dafe da kansa dake yi masa wani irin ciwo, ɗayan kuma ya ɗora a kan ƙirjinsa da ya ji ya yi masa nauyi. Da kyar ya iya ƙarasawa compound din gidansu, cikin haki ya dubi direban Hajiya Mama wanda ya zuba ido masa cike da tausayawa, muryarsa ko fita ba ta yi sosai ya ce. "Kai ni gidana." Direban kamar ya yi magana sai kuma ya fasa ya miƙe ya nufi parking space, a galabaice Adnan ya mara masa baya.
Da kallon tsantsar mamaki mai gadi yake bin Adnan da shi lokacin da ya fito daga mota, don da farko ma bai gane shi ba, sai da ya nutsu sosai ya gane mai gidan ne. Yana gaishe shi amma ko tsayawa saurar shi bai yi ba.
"Ikon Allah, gaskiya mu ji tsoron duniya, yanzu yallaɓai ne ya koma haka? Ya rame ya ƙara duhu sai idanu ƙwala-ƙwala da suka ƙara fitowa, ga saje da sumar kansa duk sun yi wani iri, kamar ba shi ne ɗan gayun nan mai tafiyar jaruman Maza ba, Taɓdi! Allah dai ya sa mu dace." Mai gadi ya faɗa yana bin bayan Adnan da kallo.
Ƙofar parlour'n a buɗe take, tun ranar da Abra ta fito ta faɗi take a haka, shi ma ranar da ya dawo bai tsaya rufewa ba jin tana asibiti. Hannunsa na rawa ya buɗe ƙofar ya shiga, cak ya tsaya idanunsa cike da hawaye yana kallon gurin da take yawan zama a parlour'n.
"Angel don Allah ki fito, na san kina cikin gidan nan, za ki fito daga ɗaki ki tarɓe ni yanzu kamar yadda kika saba ko? Na san ba ki mutu ba, nan kika zo kika ɓuya." Ya ƙarashe maganar tare da nufar ɗakinta yana kuka wiwi. Tura ƙofar ɗakin ya yi da ƙarfi yana kiran sunanta. Ƙamshinta da bai bar ɗakin ba har lokacin ya ziyarci hancinsa. Kan gadon ya ƙurawa ido, cikin fatan ya gan ta a kwance kamar yadda ya saba ganin ta lokuta da yawa a baya.
"Adnan, don Allah ka sauwaƙe mini wannan ƙaddararren auren naka."
"Me ya sa za ka ɗauki fansa a kaina? me na yi maka? Mene laifi na? Don Allah kar ka cutar da ni akan abin da ba ni na aikata maka ba."
"Ina son ka Adnan, don Allah kar ka juya mini baya."
Maganganunta da ta yi masa a mabanbantan lokuta cikin kuka suka yi masa kuwwa a cikin kunne, kamar a yanzu take durƙushe tana roƙon shi.
"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un! Wallahi ina son ki matata, ki yafe mini ki dawo gare ni, na yi nadama da dana sanin cutar da ke a rayuwata." Adnan ya faɗi haka cikin kuka tare da faɗawa kan gado saboda jirin da ya kwashe shi. Ranar da ya fara ganin innocent face ɗinta a school ya tuna, da ranar da suka haɗu a cafeteria har ya ɗauke mata wayarta, da ranar da ya ɗauke ta suka je restaurant daga nan ya kai ta gida. Wani irin kuka ya fashe da shi lokacin da ya tuna yadda ta so shi, ba tare da wani jan rai ba, ta so shi saboda Allah ba don komai ba, amma ya butulce mata, ya muzguna mata, ya ƙunƙuta wa rayuwarta, gashi nan ta tafi ta bar masa duniyar.
Sosai yake kuka tare da bubbuga kansa a jikin gado, muguntar da ya dinga yi mata kala-kala na faɗowa a cikin ransa. Babu abin da ya fi damun shi irin yadda yake zuwar mata ta ƙarfi a mu'amalar Aure, amma ba ta taɓa hana shi ba ko ta nuna rashin jin daɗin ta akan hakan, saboda ta san haƙƙinsa ne. Sai abu na biyu da ya yi mata wanda ba zai yafe wa kansa ba, ranar da ya kawo karuwa gidan, ba ya bin mata, hasalima ya tsani karuwar mace, amma saboda ya ƙuntata mata ya samo karuwar ta dalilin wani abokinsa da yake harkar, ya dinga tattaɓata duk da ƙyanƙyamin ta da yake yi. Saboda kawai ya ɓata wa baiwar Allar da ba ta ji ba, ba ta gani ba.
Dama ana dawo da rayuwa baya, da ya dawo da tasa ya goge duk abin da ya yi wa Abra, ya maye gurbinsa da sanyata farinciki da jin daɗi, sai dai kash! Ba shi da wannan damar. Miƙewa ya yi a haukace ya buɗe wardrobe ɗinta ya shiga ɗebo kayanta yana shinshinawa tare da yin surutai irin na fitar hayyaci. Gabaɗaya ya hargitse ɗakin da sunan neman inda ta ɓuya yake, cikin haka ya ga wayarta a ƙasan gado. Jiki na rawa ya ɗauko ya kunna, ya yi sa'a da guntun chaji a ciki, kuma wayar babu key. Direct Gallery ya shiga ya fara kallon pics ɗinta da short videos.
"Why Abra? Me ya sa za ki tafi ki bar ni? Ya Allah ka ɗauki raina cikin gaggawa, domin rayuwata ba ta da amfani idan babu Angel." Ya ƙarashe maganar tare da cillar da wayar saboda wani irin tari da ya turniƙe shi. Daidai lokacin direban da ya kawo shi ya shigo parlour'n, saboda tun ɗazu Hajiya Mama take kiran shi akan ya dawo da Adnan gida, ta shiga ɗakin Adnan ba ta gan shi ba sai ta fito harabar gidan ta tambayi mai gadi ko ya kan shi? Ya sanar mata ya ga driver ya ɗauke shi sun fita. Bai gan shi a parlour'n, hakan ya sa ya nufi ɗakin da yake jiyo ɗan motsi ya yi sallama, jin ba a amsa masa ba ya sa shi kutsa kai ciki ya tarar da Adnan cikin mawuyacin hali.
Ganin yadda Adnan yake tarin kamar wadda ake zarar ransa ya sa ya kama shi cikin sauri suka fita. Fuskarsa duk dagaje-dagaje da hawaye da majina, ga gefen kansa ya fashe saboda buga kansa da ya dinga yi, gaban jallabiyar jikinsa ya jiƙe sharkaf da hawaye da gumi. Suna dawowa gida Hajiya Mama ta ce su tafi asibiti kawai, don a lokacin har ya sume. Kwanansu uku a asibitin aka sallamo shi, duk da bai warke ba amma ya fara jin sauƙi, bayan sun dawo gida Hajiya Mama ta same shi a ɗaki yana sana'ar tasa ta tunani, zama ta yi a kusa da shi cikin sanyin murya ta fara magana.
"Adnan, ka takura sai an sallame ka mun dawo gida, to mun dawo ɗin, amma don Allah ka cire damuwa da tunanin da ka saka a cikin zuciyarka, ka ji likita ya ce jininka ya hau sosai, sannan kuma ciwon zuciya na daf da kama ka, ko so kake ƴarku ta rayu marainiya ba uwa ba uwa?"
Girgiza kai ya yi a hankali.
"To ka daina, ka bar wa Allah komai sai ka ga ya ba ka wata wadda ta fita."
"Babu macen da tafi Abra a duniya Mama, ba zan taɓa samun mai haƙuri da ladabinta ba, na riga na yi babbar asara a rayuwata." Ya faɗi haka cikin kuka.
"Wai yaushe za ka bar kukan nan ne, kamar ba namiji ba? Namijin ma Jarumi irinka, ka zamo mai tawakkali mana da miƙawa Allah al'amuranka, sai ka ga ya kawo maka komai cikin sauƙi."
"Na cutar ita! Na zalunce ta! Na ƙuntata mata, akan abun da ba ta da masaniya a kai, na yi nadama mara adadi."
"Ashsha! Shi ya sa ba komai zuciya take faɗawa mutum ya bi ba, domin ita ba ta da ƙashi, ka tafka babban kuskure a rayuwarka Adnan, ka yi wauta."
Bai ƙara magana sai kansa da ya kifa akan pillow yana sassauke numfashi, girgiza kai Hajiya Mama ta yi ta tashi ta fice. Parlour'n Abba ta je ta same shi yana waya, bayan ya gama ta dube shi ta ce. "Alhaji don Allah ka sassauta fushin da kake da yaron nan, ko ya samu sauƙi a rayuwarsa, kwanansa uku a asibiti amma ba ka je ka duba shi ba."
"Ni na ce fushi nake da shi ne? Abin da yake so ya ga dama ya aikata, to me zan yi masa kuma? Da na sani da kaico ne yanzu ya fara gani a cikin rayuwarsa."
"Subhanallahi! Kar ka yi masa baki mana Alhaji."
"Ba baki na yi masa ba, amma ni da ke da shi duk mun san *ABIN DA KA SHUKA* shi za ka girba, don haka bai ma fara girɓar abin da ya shuka ɗin ba, tukunna dai."
Hajiya Mama ba ta kuma magana, don ta san idan Abba ya yi irin wannan fushin ba mai iya sakko da shi, sai ya ga dama ya sakko da kansa.
4 weeks later
Mami ce zaune a ɗakinta rungume da A'isha Humairah tana yi mata wasa, ita kuma ta yi mata ƙuri da ido. Wata irin ƙaunar yarinyar Nai'ma take yi, musamman yanzu da kammaninta suka juye sak na Mamanta. Sai da ta yi bacci sannan ta kwantar da ita a kan gado ta ɗauki wayarta ta kunna data ta shiga WhatsApp.
Reply na messages ta dinga yi, bayan ta gama ta tafi status ta fara kalla. Wata irin zabura ta yi lokaci ɗaya ta miƙe tare da cillar da wayar tata, kamar wata mahaukaci ta ƙwalla ƙara tare da murza idonta.
"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un! Allah ka sa idona ne yake mini gizo abin da na gani ba daidai ba ne, no ba zai yiyu ba ma, babu ta yadda za a yi kwana uku da yin arba'in ɗin Abra hakan ta kasance, na san ma ba gaskiya ba ne." Ta ƙarashe maganar tana girgiza kai cikin tsananin firgici, ban da bugawa da ƙarfi babu abin da ƙirjinta yake.
It's paid book. 09047871750
[11/4, 7:56 PM] Abk: A ruɗe Mami ta sake duba wayarta domin gani take kamar idanunta bai nuna mata daidai ba. Babu yadda za'ai ace hakan ta kasance domin ba abune mai sauƙi ba,
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un na shiga uku ni Na'ima" ta furta a fili lokacin data ƙara tabbatar da abin gsky bawai gizau ba amma zuciyarta ta kasa gasgata hakan.
Jikinta na rawa ta ƙara duba status ɗin Uncle Shureim a karo na babu adadi, ƙurawa Invitation ɗin idanu tai zuciyarta na bugawa da ƙarfi ganin sunan Major Khamal Khamis and Salima Ibrahim Haroon.
Zaman ƴan bori tai ta jima ba taga abin daya ɗaga mata hankali irin wannan ba, kafin ta dawo daga tunani ta ƙara ganin matar Uncle Shureim tai status da Invitation na ɗaurin aure ta saka
_Wish You all the best babban yaya, Ubangiji ya baku zama lafiya yasa matarka ce har Abada. I'm so happy mun samu abokiyar hira_
Da ƙyar Mami ta Ƙarasa karanta rubutun dake ƙasan Invitation ɗin sbd yadda jikinta ke rawa da ɓari tashin hankali ya bayyana saman fuskarta shin da gaske ne? ko ƙarya ne? ko dai wani ne mai irin sunan mijinta,
But how can that be possible ta ya ya ne Major zai aure ba tare data sani ba?
Ganin kanta na neman kullewa na rashin gane gskyar abun yasa Mami da sauri taiwa Matar Uncle Shureim reply da.
"Amin. But waye zai aure?" Matar Uncle Shureim ta jima tana dariya ganin rainin hankalin Na'ima sai kuma tai mata reply da.
"Abbin Salman da Marigayiya Abra kakan Aishatul-humaira" tai mata reply da hakan tana tun tsira dariya.
Da sauri Mami ta kashe datar idanunta na cika da hawaye baƙin ciki da kuma yadda Major yaci amanarta tare da ci mata zarafi da can bai mata kishiya ba sai yanzu?
Me kishiya zata zo yi a cikinsu? Kishiyar ma wannan tsinanniyyar karuwar Salima. Number Anuty Suwaiba ta kira tana ɗauka ta fashe da kuka sosai tama kasa magana baki ɗaya.
Daga cikin wayar Anuty Suwaiba taja tsaki cikin faɗa ta ce "Mtwss Malam kin kira kuma zaki cika mini kunne da ihun banza wani abin ne ya faru? domin nasan wannan gidan naki baya rabo da issues kamar gidan haya ko yari" cikin kuka Mami ta ce.
"Na shiga uku Anuty Suwaiba Major Aure zai, kishiya zai yi mini dame zanji da rashin Abra ko da kula da Aishatul-humaira ko da masifar kishiya ba zan iya ba" kuka take sosai kamar ranta zai fita batun auren Major ya Girgizata ya zo mata hanyar da sam ba tai tunani ba.
"Aure? Shi ne yace miki aure zai ƙara?" "Ai ya shige wai, domin Shureim da matarsa sun ɗora Invitation na ɗaurin a status ɗinsu, kuma matar Shureim ta tabbatar mini da hakan,
Yanzu Abbin Salman ya kyauta mini kenan? Dame na ragesa tun ina amarya bai yi mini kishiya ba sai yanzu samu jika?"
Tsaki Anuty Suwaiba taja kafin ta ce "Matsalata dake rashin tunani wani lokacin Na'ima, wace jikar waye kuma ya haifa miki, ai da baki gangancin riƙe Abra tun farko ba da Khamal bai isa ya rainaki har haka ba,
Kin riƙe uwa yanzu zaki riƙe abin data haifa kamar baki san ciwon kanki ba wlh....," da sauri Mami ta ce "Look Anuty Suwaiba shawara na kira ki bani akan wannan mugun abin dake shirin faruwa dani, a baya nayi Kuskuren riƙe Abra da zuciya ɗaya, yanzu kuma nayi ladama riƙon da naiwa Abra ba shi zanwa Aishatul-humaira ba, da zuciya ɗaya zan riƙe ta,
Ki bani shawara kawai idan zaki bani idan kuma ba zaki iya ba shikenan but please ki daina sako mini zancan Abra kina fama mini mikin dake zuciyata ne"
"Ok haka kika ce? To kada ki sake kirana akan issues ɗinki tunda kina gani ba zan iya miki komai ba ki zauna kici miji tare da yaran riƙo" tana faɗin hakan ta kashe wayar.
Abin duniya yaiwa Mami yawa sai kawai ta fashe da me tai maka mene yasa zai mata kishiya bayan yanzu basa samun saɓani.
Sai da tayi kukanta ya isheta kafin ta tashi sbd kukan Aishatul-humaira da yaji.
Yana kwance saman Royal bed ya rufe idanunsa tare da rungome pillow. A yanzu ko sarari tunani bashi da shi, ya daina surutai da kiran Abra. Amma ya tattara komai ya ajiye a cikin zuciyarsa.
Ba zai taɓa yafewa kansa ba akan cutar da Abra dai ya yi, abubuwa da yai mata sai dawowa cikin ƙwaƙwalwarsa suke. Runste idanunsa yai sosai sbd tuna mganarta da yai.
"Ka barni a jikinka ɗomin jikinka nake buƙata" ƙankame pillown yai yana jin kamar ya kurma ihu amma ba hali Allah sarki a lokacin ita kaɗai ta san me take ji a jikinta.
A hankali aka turo ƙofar bedroom ɗin nasa, Hajiya Mama ce ta shigo riƙe da mug wanda ta haɗa masa coffee a ciki zama tai gefen gadon cikin sanyin murya ta ce.
"Haba jarumin maza tun safe yau baka fito ba, are you okay?" Juyowa yai tare da mirginawa ya ɗora kansa a saman cinyar Hajiya Mama.
"Mama ba zama Mutumin ƙwarai ba bani da imani Mama" rufe masa baki tai tana faɗin "Subuhanallahi kul ka sake jin irin haka a bakinka Adnan,
Babu musulmin da babu imani a zuciyarsa, kai ta astagafirullah tare da neman yafiyar Ubangiji, akan laifukan daka aika ga Abra,
Ubangiji mai jini kuma mai gani ne zai dubi zuciyarka ya sassauta maka abin da kake ji, ina da tabbacin Abra ta yafe maka, ko baka nemi yafiya wajanta ba?"
"Na nema, amma na cutar da ita da yawa" shafa kansa Hajiya Mama tai cikin damuwa ta ce.
"Shi ya sa a kullum nake ce maka ka rage zafin zuciya Adnan, babu inda zata kai ka sai ladama yanzu dame hakan yai kama? Kada ka manta A'isha Yaya ta ce, she's my sister mene yasa ban ɗauki mataki ba ni? Mene yasa Professor bai ɗauki mataki ba a matsayinsa na mijinta sai kai?"
"Am sorry Mama nai laifi ki yafe mini"
"Ka nemi yafiyar Ubangiji Adnan, shi ne zai yafe maka laifukan ka, and wannan zaman naka ya fara damuna kada ka samu matsala da zuciyarka"
Tashi yai zaune sosai idanunsa akan Mama yace "Ina son komawa wajan aiki, idan ina zaune ni kaɗai bana iya cire tunani Angel a raina"
"That's good ni ma hakan ya yi mini, yanzu ka sha wannan coffee ɗin kai wanka ka shirya ka fita ko lasvegas ne kasha iska" Girgiza kai kawai Adnan yai domin ya ɗauki Al'ƙawari duk abin da zai sanya shi farin ciki ba zai taɓa aikata shi ba, zai ta zama a haka har zuwa ƙarshen tasa rayuwar.
Coffee ɗin ya fara sha a hankali Hajiya Mama na kallonsa cike da so da ƙaunar ɗan yayar ta ta A'isha. Har mamakin yadda Abra ta sakawa ƴarta suna Aishatul-humaira tai. Yana gama sha ta fita da mug ɗin shi kuma ya shiga bathroom.
After 20 minutes.
Walking slowly ya fito daga part ɗinsa cikin wata dakakkiyar shadda amy colour wacce ta amshi dark skin ɗinsa yai kyau sosai amma ya rame sosai idanunsa sun faɗa sai dugun hanci. Murmushi Hajiya Mama tai ta ce "Allahamdulillah, Masha Allah First born and last born sai yanzu naji daɗi shalalena" ta faɗa tana rungomesa marairaice mata fuska yai kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce.
"Ina Abba?"
Juyawa tai sai