Showing 195001 words to 198000 words out of 231718 words
Chapter 66 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
kuma ƙara jin ta bakin yarinyar a karo na biyu" Abbi ya jinjina kai gaba ɗaya hankalinsa ya yafi zuwa inda zai ga mai kama da Abransa ya fito a hankali ya ce "Masha daga namu ɓangaren muma haka abin yake, zamu samu yarinya ta maye gurbin ƴar uwarta Sannan mu samu bayanin da zai taimaka mana wajan gano asalin abin da yake faruwa, ina kuka tsinceta?"
"To a yadda murgayi ya faɗa wata rana yaje wajan gari gefen jeji domin duba wasu magunguna na itace, acikin wannan lokacin ne kuma ya tsinci Yarinya a ƙasa ita kaɗai, sai a sannan ya fahimci kamar ƴan daba ne suka shigo cikin jejin domin sama sama yake yajin ƙarar bindigogi, ya ɗauki yarinya kawota wajan ƴan sanda suka ce sun bashi domin babu wasu iyayenta da za a samu, suka saka mata suna Afra wannan shi ne abin da muka sani"
"Ikon Allah, Ubangiji mai yadda ya su" Nan Abbi ya faɗa musu yasa ya tsinci Abra da komai har kawo rasuwarta "Yanzu ina ita yarinyar take, ai Wannan abin bana wasa bane muna buƙatar ta cikin familynmu" Inna ta shiga kiran sunan ƴar Baba fitowa tayi a ɗaki cikin ƙyakƙyawan shiga mai kyau, Abbi ya tsora mata idanu dauriya kawai ya yi da bai je ya riƙeta ba, yana ƙara jinjina girman zatin Ubangiji da ƙuddirarsa. Zama tayi tana gai da Abbi suna haɗa idanu da Adnan ta tura masa baki, ya yi mata kallon ki tausaya mini. Kawo ya gyara zama ya ce "Ƴar Baba zan ƙara tambayarki a karo na biyu kina son Adnan zaki aure shi ya sadaki da iyayenka na gaskiya?" Afra na ƙoƙarin magana Sallamar Salman ta daki kunnenta juya sukai banda adnan da zuciyarsa take cike da fargaba.
Mutuwar tsaye Salman ya yi lokacin da idanunshi ya sauka akan Afra bakinsa na rawa ya ce "Yaya...!!!"[11/16, 6:44 PM] Abk: A gigice Salman ya ƙarasa wurin da 'yar Baba ke zaune, ya rirriƙeta yana girgiza kai "Abbi ban gaya maka ba? Dama na san Angel ba ta mutu ba" ƙura masa idanu Afra ta yi, tana bin fararen idanuwansa da kallo, Masha Allah ga wani daddaɗan ƙamshi da yake fitarwa.
"Talk to me Angel, dan Allah ki yi magana Yaya".
A ɗan shagwaɓe Afra ta ce "Kai ka cikani" wani malolon takaici ne ya ƙule zuciyar Adnan, ya yunƙura yana ƙoƙarin ɓanɓare Salman daga jikin Afra.
Hankaɗe shi Salman ya yi, yana sake rirriƙe Afra.
Abbi ne ya ɓanɓaro Salman daga jikin Afra, yana faɗin "haba Faris, your sister is no more, wannan ba ita bace 'yar uwatta ce"
Dafe kai Salman ya yi, ya rintse idanunsa yana sauke ajiyar zuciya, ya kwanta a jikin Abbi yana ta maida numfashi. Tsura masa idanu Afra ta yi, gaba ɗaya tausayin Salman ya kamata, lallai suna matuƙar so da ƙaunar wannan yayar ta ta.
"Inna wannan ne baban nawa?" Tayi maganar tana kallon Abbi.
Abbi ya yi murmushin ƙarfin hali yana ƙarewa Afra kallo, idan ba wanda ya yiwa Abra kyakykyawan sani ba, babu yadda za ayi kace ba Abra ba ce ba.
"Ni ne na tsinci 'yar uwakki, na riƙeta na raineta, har zuwa lokacin da Allah ya karɓeta. Kamar ki ɗaya sak da ita, tabbas da a wani wurin na ganki zan iya cewa Abra ce"
Idanun Afra ya cika da hawaye ta ce "To ina babana, suwaye iyayenmu? Me yasa suka yar da mu? Ko mu ba 'yan halak bane?"
Abbi ya ce "Kul kika ƙara faɗar wannan maganar, ku 'yan halak ne nine nan uba a gare ku baki ɗaya".
Sosai Afra ta sake fashewa da kuka tana girgiza kai.
Abbi ya ce "Ka bita a hankali, haka Abra ma take da yawan kuka" A hankali Salman ya gyara zamansa ya jingina da jikin Abbi, yana cigaba da bin Afra da kallo. Ita kuwa yadda Salman ya kashingiɗa jikin Abbi ne abin ya burgeta, da alama shima shagwaɓaɓɓe ne.
Kawun su Afra ya ce "To yanzu ya muke ciki da batun neman Auren yarinyar nan da kuka zo?". Nan da nan Afra ta sake tsuke fuska tana harar Adnan.
Abbi ya ce "Wani hanzari ba gudu ba, me zai hana a jinkirta batun neman Auren nan, yarinyar nan ta samu nutsuwa a karo na biyu sai a sake tambayar ta. Sannan dan Allah ina roƙon wata alfarma, ina son ku bani Afra in tafi da ita gidana, tun da ina kan neman iyayensu, kuma ko ba komai Yarinyar da Abra ta rasu ta bari, zata samu shaƙuwa da kusanci da 'yar uwar mahaifiyarta".
Aikuwa Inna ta ce "Ai wannan abu ba mai yiwuwa bane, a gaskiya ba zan iya bada Afra ba, shekara da shekaru ina rainon a bata rana tsaka a rabani da ita ba, gaskiya ba zan iya ba" ta ƙarasa maganar a hasale.
Adnan dai ya rasa bakin Magana, sai bin su da ido kawai da yake yi, yayin da 'yar Baba ke ta zubar da hawaye, wanda ita kanta ba ta san dalilin hakan ba.
Salman ba kunya ya tashi, ya ƙarasa gaban Afra ya zauna, ya tsura mata idanu wanda sai da hakan ya takurata, ta ji jikinta na tsuma, saboda kwarjinin da ya yi mata.
"Yaya" ya furta a sannu. A hankali ta ɗago fararen idanunta ta kalleshi, duk da bata san dalilin kiranta da hakan ba.
"A duk lokacin da nake tare da Abra, babban abin da yake jefani a cikin damuwa da tashin hankali, shi ne zubar hawayenta, kamar yadda ta rayu da son ganin Farinciki da murmushi a fuskata, dan Allah ki daina zub da hawaye, ina ganinki ne kamar Abranmu, ni haryanzu ban yadda ba ke ce Abra ba, dan Allah ki bimu gidanmu ki maye mana gurbin Abra, duk da mahaifiyata na kula da Little, amma little na kewar mahaifiyarta. Ko zaki so ta rayu ba tare da sanin kowa nata ba, kamar yadda kuka rayu a mabanbantan duniyoyi ke da 'yar uwakki, dan Allah ki Angel ki taimakawa rayuwarmu, we still needs you in our lives, Ni, Little, Mami Abbi da sauran su"
Inna kuwa kuka ta fara yi, tana share hawaye, tana faɗin "Wallahi ba mai rabani da 'ya ta, ba in da zata je"
Kawun Su Musa ya ce "Hajara, wannan kukan da kike kina ba za su tafi da ita ba ba shine masalaha ba, dan Yarinyar nan ba zata cigaba da zama ba tare da an san suwaye iyayenta ba, wataƙila tafiyar ta su da ita ya zamana silar sanin in da iyayenta suke ba"
Nan aka shiga jayayya, ɓangaren su Abbi suna roƙon a basu Afra, Inna kuma ta dage ta ce ba zata bayar ba, Adnan ka sa jurewa ya yi, ya tashi ya bar gidan ya zauna a waje.
Sai da Inna ta ga an fi ƙarfinta, sannan ta amince ta ce sai an je wurin mai gari ayi abu a hukumance, kar a gudar mata da 'ya.
Haka kuwa aka yi, aka je gaban maigari, aka kuma sake yin bayani, maigari ya sake jadadda musu bayanin yadda aka tsinci 'yar Baba da irin riƙon da marigayi ya yi mata.
Nan Abbi shima ya kuma yi masa bayanin yadda ya tsinci Abra a daji wurin yaƙi, tare da nuna musu hotunan Abra, tare da yi musu bayanin buƙatar sa na a bashi Afra.
Da haka sai da aka dangana da wurin 'yan sanda, na wannan ƙauye, in da file ɗin Afra tsintar Afra yake, aka sake kaɗe File, Abbi yayi amfani da ƙarfin kaki a wurin, aka yi rubutu tare da amincewa zai tafi da Afra.
Sai bayan la'asar su Abbi suka koma gidan su Afra, nan Baffa suka tabattar mata da cewa, an bawa Abbi izinin tafiya da Afra. Ita kanta Afra gaba ɗaya ta kiɗime, da jin wannan batun, tana da burin ganin iyayenta a rayuwarta. Salman kuwa ji yake tamkar Abran sa ce ta dawo rayuwarsa, babban jin daɗin sa shi ne tafiya da za su yi da Afra gida.
Inna ta rungume Afra tana ta kuka, saboda sabo, shi kansa Yaya Musa sai da ya yi kuka, saboda 'yar Baba akwai shiga rai, tsawon shekarun da ta yi a tare da su, ba su taɓa rabuwa tsawon lokaci ba, sai dai yanzu rana tsaka an musu fin ƙarfi an raba su da ita. Haka Inna ta haɗawa Afra kayanta, tana kuka Afra na kuka su Abbi suka taho da ita.
Yau Little rikici take ji, saboda zazzaɓi da yake ɗan damunta, Mami sai fama take da ita amma sai koke koke take yi, da ƙyar ta samu ta yi bacci, ta kwantar da ita a falo, ta shiga kitchen a gurguje tana gabatar da ayyukanta, dan tun da Abra ta yi Aure, ba ta yadda a kawo mata mai aiki ba, saboda ba ta son ƙazanta.
Tana girki tana Mamakin yadda aka yi Su Abbi suka daɗe haka ba su dawo ba, wayarta ta ɗauka ta kira Abbi, amma bai ɗaga ba, ta kira Salman, shima sai da ta yi masa kira biyu sannan ta samu ya ɗaga.
"Hello Mami, Ina daughter na?"
"Kai na kiraka in ji ya akai na ji ku shiru, amma kana mini zacen daughter".
Faris ya ce "Mami muna nan tafe da wani abin mamaki mai girgiza zukata".
Saroro Mami tayi ta ce "Faris bana son shirme, wane irin abu ne haka?"
Jiki a sanyaye Faris ya ce "Mami ki kwantar da hankalinki, muna Lafiya mun kusa shigowa cikin Kano insha Allah".
"To shikenan, Allah ya kawo ku lafiya" ta ajiye wayar tare da komawa wurin da ta ajiye Little amma ba ta nan. Da sauri ta ƙarasa tana ɗaga filon kujera, amma ba ts ga Little ba.
"Ki daina wahalar da kan ki, ni na ɗauketa kin ajiye yarinya a kan kujera, idan ta tashi ta faɗo baki da asara, ko da yake ba abin mamaki bane, ita ma zaki mata irin riƙon da ki ka yiwa babarta ko?" Cewar Salima da ke wa Mami Magana cike da gadara.
Wani marurun takaici ne ya tokarewa Mami wuya, amma cike da salo na goggaun matan da suka kwana biyu a duniya, ta yi murmushi ba ta tankawa Salima ba, dan ba ta fi sa'ar Abranta ba, ta nemi wuri ta zauna a kan kujera, ta fara cin Abincin ta.
Salima ta so Mami ta tanka mata, ta yaga mata rashin mutunci son ranta, amma sai ta ga saɓanin abin da ta yi tunani.
Mami ta cigaba da kallo, tana sipping tea, suka jiyo Little tana ta tsala kuka, daga sashin Salima, da sauri Salima ta tafi ta ɗauki Little, sai dai juyin duniya, amma little ta ƙi yin shiru, sai cilla ƙafafuwa take tana rintse idanuwa, ba shiri ta fito da ita a kafaɗarta, tana miƙawa Mami ita.
Maimakon Mami ta karɓeta sai ta miƙe, ta bar falon.
Salima ta rasa yadda za ta yi da Little, gashi ita ba ta saba da kukan yaro ba.
Tun a hanya suka rabu, Adnan ya nufi Kaduna, dan zuciyarsa ba zata iya jure cigaba da kallon Afra tana furta ba ta son sa ba, yana ji yana gani, Abbi Salman, da Afra suka nufi Kano, sai dai Adnan tun kan ya ƙarasa Kaduna, wani irin zazzafan zazzaɓi ya rufe shi, gaba ɗaya al'amura sun cakuɗe masa, bai san ya zai yi ba idan har ya rasa Auren Afra a wannan karon, bai san abin yi ba. 'Allah sarki Abra, a kallon Farko da na yi mata, na ga tsoro a fuskarta, bayan nasarar kauda tsoron fuskarta da na yi, na maye gurbinsa da tsananin soyayyata a zuciyarta, sai dai kash na yi wautar da na sanya ƙiyayyata a zuciyar Abra, har kan ta rasu take sanar mini da bata ƙaunata, Allah ya jiƙanki matata ya yafe mini, Allah ya sa 'yar uwakki ta yadda ta Aureni' yayi Maganar yana zubar da hawaye.
Afra tsayawa ta yi tana ƙarewa harabar gidan kallo, da ganin yadda sojoji ke kaiwa suna komowa a harabar gidan, ta jinjina Arziƙi da Allah ya yiwa mariƙin Abra, sai dai jikinta duk a sanyaye yake, dan tun yanzu kewar ƙauyensu ta fara damunta, sai dai ba ta da burin da ya wuce ace ta sadu da iyayenta, komai talaucinsu komai muninsu.
Kukan little ne ya karaɗe gidan, Abbi ya shigo falo da sallama, ya tarar da Salima tana tsaye tana ta jijjiga little da ke tsala uban ihu. Ya ƙarasa ya karɓeta a hannunta, yana faɗin "Garin yaya aka barta take kuka haka?".
Salima ta ce "Oho, ajiyeta ta yi a falo tai tafiyarta ta barta"
Abbi ya karɓeta, ya nufi sashin Mami a fusace "Na'ima wane irin sakarci ne haka, zaki tafi ki bar Yarinya tana kuka a falo, kin san ƙyuya take kin barta da Salima sai kuka take mata, yanzu da tsautsayi ya sanya mun taho da mahaifin yarinyar nan, haka zai zo ya tarar da ita tana kuka".
"Kar ka sake yi mini tsawa Khamal, baka san maiya faru ba kawai ka zo ka sani a gaba da faɗa, kar ka kuma yi mini tsawa, bani yarinyata, kuma Wallahi matarka ta kuma ɗaukar mini ita saina wanka mata mari" ta ƙarasa maganar tare da fizge little daga hannunsa.
Shiru Mami ta yi, ta tuna watarana da ta taɓ haɗa baki da ƙawarta suka yiwa Abra sharri, har Major ya mareta, ashe haka Abra take ji idan ta yi mata ƙazafi. Wasu hawaye masu fitowa da ɗacin zuciya suka faa sakowa saman kuncinta.
Abbi ya yi ajiyar zuciya ya ce "Ki zo muje falo, ki ga wani abu".
"Ba abin da zan gani, kaje ka ƙyaleni kawai"
Major ya ce "Abin yana da mahimmanci, ki zo muje".
"Kaje ka nunawa matarka bani ba, ita ya dace taga abu mai mahimmanci daga gareka bani ba".
"Ko da kuwa abin da ya shafi Salman ne ko Abra?"yai Maganar yana kallonta. Sai kuma jikinta ya yi sanyi, Abbi ya sanya hannu ya janyo hannun Mami zuwa falo.
Afra kuwa tun da ta shigo, tangamemen hoton Abra ne da Salman ya yi mata maraba, babu yadda za'ai ka kalli hoton kace ba ita bace a jiki.
Jikinta ne ya hau rawa tana nuna wa Salman hoton. Salman ya taka ya ciro hoton ya miƙawa Afra ya ce "This is your sister, we are really missing her" yayi maganar ba tare da ya iya tsayar da hawayen da suka taho masa ba.
Salima kuwa bin su ta dinga yi da ido, tana son tayi magana, amma ta kasa magana, saboda yadda Salman ke mata kwarjini, sam yaron baya sakar mata fuska a matsayinta na matar mahaifinsa.
"Yanzu ta mutu? Yayata ce ko ƙanwata ce, ko mu biyu ne? Babu wanda ya sani sai Allah, me yasa ban haɗu da ke kan ki mutu ba? 'yar uwata me yasa kika tafi ban ganki ba, a rayuwata ace ko sau ɗaya naga jinina, yanzu idan ba a gano iyayenmu ba fa, shikenan kin mutu kin barni ni ka ɗai haba 'yar uwata" tamkar mahaukaciya, haka Afra take gunjin kuka, Salman ya karɓe hoton yana share mata hawaye, ganinta yake ba ta da banbanci da Afransa.
Mami ce ta fito tana hura hanci, hannunta ɗaya riƙe da Little, ɗaya kuma yana cikin na Abbi. Wata irin mummunar faɗuwar gaba ce ta ziyarci Mami, jikinta ya hau rawa bakinta ma haka.
Nema take ta saki Little, Abbi yai sarin karɓeta daga hannunta.
"Major me nake gani? Abra ce fa? Abra ce ko baka ganinta ne?".
"Calm down please, ba Abra bace ba kalleta da kyau".
Cikin tsawa ta ce "Ta yaya zaka cemini ba Abra bace, kalleta fa a kusa da Faris, Abra ba ta mutu ba kenan, ko kuma fatalwa ce" Salman ya taso da sauri ya karɓi Little, Mami kuwa gaba ɗaya ta birkice, Abbi ya zaunar da ita, amma ta kasa nutsuwa, sai nuna masa Afra take tana cewa Abra take gani.
Abbi ya yiwa Afra nuni da ta zo, Afra ta taso ta ƙaraso gaban Mami, aikuwa ta rirriƙeta ta ce "Abrana, Wallahi Major Abra ce kalleta fa".
Abbi ya kalli Afra ya ce "Afra, ga maman 'yar uwakki, ita ce ta riƙe Abra, wannan jaririyar kuma, ita ce wadda ta rasu ta bari, ki gaya mata ke ba Abra ba ce".
Afra ta riƙo hannun Mami cikin nata, tana hawaye ta ce "Mamanmu, ba 'yar ki ba ce wadda ki ka rasa, amma zan iya cewa 'yar ki ce ta dawo gareki, kamar 'yar uwata nima tsinta ta aka yi, aka riƙeni a wani ƙauye har na girma, mijin 'yar uwata ne yaje ƙauyenmu ya ganni, shima da fari cewa ya yi, ni matarsa ce amma daga baya ya gano, ba ita bace, ni sunana Afra ana ce mini 'yar Baba a garinmu, ni a ƙauye na tashi, Abranki kuma a birni, mijin Abra ya ce ta fini hankali da nutsuwa, da rashin hayaniya, ni kuma... Sai kuma tai shiru tana murmushi, a lokacin da hawaye ke zuba daga idonta.
"Major yanzu kana nufin ba Abra na ba ce?".
"Ba Abranki ba ce, 'yar uwatta ce" Nan Abbi ya yiwa Mami bayanin komai.
Mami ta rungume Afra a jikinta tana wani irin kuka, tamkar zata shiɗe, Afra ma ta rungumeta tana kuka.
Salima ta ce "Sweetheart, nifa ban gane meke faruwa ba, wannan ba ita ce 'yarka ta hoton nan da aka ce ta mutu ba?"
Abbi ya ce "Ba ita bace, zan miki bayani".
Adnan kam ko da ya isa garin Kaduna, a Asibiti ya samu masauki, saboda yadda zazzaɓi da ciwon kai suka rufe shi, sai da aka sa masa ruwa sannan ya wuce gida.
Ko da Adnan ya jewa Hajiya Mama da Abba abin da ya faru Abba ya ce "Lallai wannan lamari akwai ban mamaki a cikin sa, dan haka zuwa jibi insha Allah, zan shirya in je Kano da kai na".
Adnan ya ce "Dan Allah Abba idan ka je kace su bani Auren Afra, zan iya rasa raina idan ba sameta ba".
"In ka rasa ranka Allah ya jiƙanka, ai Nagode Allah da ya sanya yarinyar ta ce bata sonka, ni dai Adnan ba zan kuma yin jagoranci a nema maka Aure ba, da mahaifiyarka ma ta mutu dangana na yi, kaima in ka mutu Allah ya jiƙanka".
"Abba dan Allah, kai mini rai, na tuba nabi Allah na bika, ba zan sake maimaita kuskuren da nayi a baya ba"
"Sai kuma kayi Adnan, idan har ina raye babu mai aura maka 'yar uwar Abra, kaje can ka