Showing 9001 words to 12000 words out of 231718 words

Chapter 4 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14677

hannunsa, ƙuri tayi masa da Manyan idanunta, da suke farare ta tass, Ganin yadda ta kafeshi da Idanu, kamar bata taɓa ganinsa ba, yasa Captain ya ƙara ware mata manyan idanunsa yana sane.

Maimakon yaga tayi ƙara, sai kawai yaga ta saki Teddyn tare da ta zuwa wajansa da gudu. Zamewa ya yi kaɗan yana gyara zamansa, saboda ciwon jikinsa.

"Abbi"
Yarinyar ta ce, tana tsayawa gaban Captain tare da leƙa fuskarsa, Murmushi ya sakar mata, itama ta washe white teeths ɗin ta, tana ƙara zura kanta tare da leƙa fuskarsa sosai. Faruk dai ikon Allah yake kallo, tunda aka kawo yarinyar take kuka, amma yanzu gata harda dariya.

"Abbi"
Ta kuma cewa tana nuna masa ciwon jikinsa sai kuma tace "Shhhhhh" tana kwaɓe fuska tare da Girgiza kanta, alamar bata son ganin ciwon gaba ɗaya. Musamman daya kasance a jikin Abbi ɗinta.
Fuskarta ya tallafo, a zuciyarsa yana jinjina kyan da Ubangiji ya yi mata, mai fisgar Hankalin jama'a. Caraf yaji ta kama tafin hannunsa wanda yasa Captain saurin rufe ido, sai kuma ya buɗe lokaci guda!.

"How are you?"
Cewar Captain yana buɗe idanunsa akan innocent face ɗin ta, bata san mene yace ba, amma sosai taji sautin kamilalliyar muryarsa a kunnanta, ta samu kanta da ɗaga masa kai tana faɗin "Abbi"
Ya fahimci kalmar “Abbi”. Ita kawai ta riƙe cikin bakinta, idan ba Captain ba, kallon kowa take matsayin wani abu daban.

"Sir yanzu wanne suna za'a ce mata, tun da naga ko sunanta ba ta sani ba?"
Gently Captain ya kalli Faruk, sai kuma ya kalli fuskar yarinyar kafin ya rufe idanunsa yace.

“ABRA KHAMAL KHAMIS BUBA”
"Abra...?" Faruk ya ɗan zaro ido ya maimaita a zuciyarsa, kafin yace "Allah ya raya, Abra.." "Amin, thank you" cewar Captain

Faruk yace "Amma yallaɓai, naji ka haɗa sunan nata da naka, ba za'a nemo iyayenta ba kenan?"

Shiru Captain yai, bai bawa Faruk amsar tambayar da yai masa ba.

Abra kuwa ta ƙurawa tea ɗin dake gefen Captain Idanu, shima ya Kalli tea ɗin, da hannunsa ya yi mata alamar zata sha ne? Domin ba zai iya yin ihun magana ba. Ta ɗaga masa kai tare da faɗin "Abbi" hannunsa yasa tare da ɗaga ta Cak zuwa saman cinyarsa, a nutse yake bata tea ɗin tana sha, sai da tasha sosai ta janye bakinta, idanunsa akan Faruk yace.

"Wannan kan nata, abuɗe kamar ƴar arna, kai kuma kamar maye ka zuba mata ido Mtwss"

Murmushi Faruk ya yi, tare da ɗauke idanunsa daga kan Abra yace "Haka aka ban ita nima, idan maye ni me zan da Abra sai dai Abbin Abra"

Murmushi kawai Captain ya yi, a hankali kuma yaji numfashi Abra na sauka alamar tai bacci kwance a nan jikinsa. Yatsarsa data saka a baki tana tsotsa ta ɗauka nata ne, shi ya zame a hankali yace.

"She is sleeping, come and pick her up" ya faɗa yana hura iska sosai a kunnanta, Just to confirm abinda yake tunani, amma ko motsawa ba tayi ba, sai ma firgita da tayi tana riƙe hannunsa tace "Abbi"
Captain bai ce komai ba, amma har zuciyarsa yake tsananin so da tausayin Abra. Faruk ya ɗauke ta, yana yin waje
"Tell Madam Halima, that she should took a good care of her, ina tsoran Barrack.". Faruk ya jinjina kai.

Babu jimawa da fitar Faruk, Na'ima ta shigo, hakan yasa ba taga Abra ba sam, tana zuba ƙamshi sosai ta Ƙarasa wajan Captain, tare da zama gefensa tace "Man"
Hannunta ya kama tare da murzawa "Wife" ya faɗa a taushashe, ƙamshinta na ɗaukan hankalinsa, shi kansa dauriya yake sosai a kanta.
"When will you be discharged?" Na'ima tayi magana tana bin Captain da wani irin kallo, mai kama da zallar buƙatar mata ga mijinta.

"to tomorrow or the day after" yace yana kissing lip's ɗinta, ta rufe idanunta, ya yi mata side hug, tare da ƙurawa cikinta idanu, wanda ya girma sosai saura kaɗan EDD nata ya cika.

Wayar Na'ima ta ɗauki ringing, ta yi wani kalar zabura tana tura baki gaba, Captain ya yi Murmushi, a hankali ta ɗauki wayar daga cikin wayar akace "Waye ne?"
Na'ima tace "Nice Granny"
tace "Kewa?"
Ta ce "Na'ima" da sauri Granny dake cikin wayar tace
"Auzubillah, wata abace Na'ima kuma? Kinga ba ruwana dake, cewa zan daman ki kirani, irin kiran nan mai motsi" kashe wayar Na'ima tayi dake akwai Wi-Fi sai ta kira number Granny a V.c Fuskar wata tsohuwa ta bayyana a screen ɗin wayar Na'ima, tana hakimce akan kujera ta lafta wani glasses a Fuskarta, a cewarta kwana biyu baki ke son kamata. Ganin fuskar Na'ima, yasa Granny runtse idanunta tace "A'a me zan da naki fuskar kuma? Maza kamo min fuskar Kamalu" Captain Khamal ya ɗura kansa a kafaɗar Na'ima, a sanyaye ya ce.

"Granny" fashe masa tayi kuka sosai tace "Allah ya isa, Allah ya isa, Allah dai ya isa har sau uku" ya yi Murmushi ya ce "Ɗaya ta Isa" da sauri tace "Wlh bata isa ba, guda goma na su yi, amma na barta a guda uku, kuma gaba ɗaya da matarka Na'ima nake, ai ba uwata bace da zanji tsoranta"

Captain dai ya kasa cewa komai, Granny tana matse Idanunta tace "Abinda matarka tai min, Allah kaɗai na barwa, shi yasan yadda zai da ita, banda haka mace bata san darajar ɗan fari ba, tai ta gantali da narkeken ciki a gaba, duniya duk ta lalace da ɓata gari, haka kurum ta haɗu da wani mayen ya lashe ɗan Tun a ciki? To ya bazan mata Allah ya isa ba? Nifa shi yasa tun farko nace kawai kayi mata huɗu ko wacce tayi ta kanta, amma yanzu zanta shela wacce taga Allah taga Ma"aiki ta aureka"
Captain ya kalli Na'ima data haɗe fuska yace "Granny, Soon zan ƙara mata ai..." Granny ta waro Idanunta tace "kace Allah?" Ya ɗaga mata kai.

Tayi ƙasa da murya tace
"To ai kaga haka yafi? Nayi magana cikin azanci, kuma ka fahimcen, Amma wannan matar taka mai kama da sadaka yalla sam ba tai min ba, ƴar banza ce, tana kallon kuwa a wulaƙance"
Haka tai ta surutu daga ƙarshe ta kashe wayar. Na'ima ta cika tai fam, Captain ya jawota yana matseta yace "Sorry, Wife... Zo kiji".

Kwanan Na'ima huɗu wajan Captain a gidan da aka ware masa, shi kuma yana Hospital, kullum sai Faruk ya kawo masa Abra, amma basu taɓa samun Na'ima a wajan ba, hakan ya yi wa Captain daɗi, dan yasan rikicin Na'ima, Abra kullum da kuka take barin Wajan Abbi ɗinta.

Yana zaune, cikin wasu ƙana nan kaya masu kyau, a hankali aka turo ƙofar tare da shigowa, tunda ta Shigo yake binta da kallo, idanunsa ya ɗauke cikin sanyin jiki Salima ta Ƙarasa tare da faɗin "Ya jiki dear?" Captain ya yi mata banza, wajansa ta Ƙarasa kafin ya tashi ta riƙe ƙafarsa tare da fashewa da kuka sosai tace.
"Dan girman Allah, kaji tausayi na Khamal, ka daina azabtar dani da soyayyarka"
Daka bakin ƙofa akace "Kutirin Ubanki zaici ba tausayi ba, Shegiya karuwa mai bin mazan mutane"

Da sauri Salima ta miƙe tsaye, shi kansa Captain a rikice yake kallon Na'ima, tana zuwa ta ɗauke Salima da maruka tace "Wlh wlh sai naga bayanki, akan mijina sai na kashe mutum, mijina nawa ne kawai, da ƴa ƴan da zan haifa masa, karuwa kawai" Salima ta haɗe fuska tace "I am not a prostitute" Na'ima ta cire mayafinta, ko cikin jikinta bata gani ta shaƙo wuyan Salima tace "Na faɗa karuwa, idan ba karuwa ba gantalalliya wace za tana bin mijin wata tana cewa ya so ta? Wlh sai na kashe ki na kashe Captain na kashe kaina, gaba ɗaya mu tafi lahira ai mana hisabi a can, babu wata banzar data isa ta shiga rayuwar mijina, ina son mijina fiye da komai" da ƙyar Captain ya ƙwace Salima da ga hannun Na'ima, tare da daka mata tsawa yace "Stop this nonsense, Na'ima." With so much surprise Na'ima ke kallon Captain. Ya kalli Salima yace "Get out"

Salima ta kalli Na'ima ta ce "Zaki gane da karuwa kike magana, Wlh sai na shigo gidan ki, sai na auri Mijinki, sai na rabaki dashi"
Wani ihu Na'ima ta saki, ta shiga ƙundumawa Salima zagi, tana ƙoƙarin ɗaukan wata kwalba zata kwaɗa mata, Captain ya riƙe Na'ima yace "I Said Get out, Salima" fita Salima tayi. Na'ima ta fashe da kuka sosai, Captain ya kasa ce mata komai ya jata jikinsa sosai ya rungome ta yana faɗin "meyasa kike hakane? Matar nan soja ce ga ciki a jikinki ba kya tsoron tai miki illa?".

"Wallahi in dai akan ka ne, bana tsoronta" ta ƙarasa Maganar tare da zame jikinta daga nasa tai waje.


G.Y Bulama hospital and Merternity.
Dr G.Y ya kalli mutumin dake gabansa kafin yace "ranka ya daɗe, zamu shiga tiyata da ita"

Mutumin yace "Dr Ka taimaki matata, I don't want to lose her" yanayin yadda yai maganar zaka gane, tsohon ɗan boko ne.

G.Y yace "Tunda ka kawo kuɗin aikin da wuri, Don't worry, she will be fine insha Allah". Yana faɗin haka ya nufi theatre room inda aka kai matar mutumin.

Ƙyakƙyawan yaron dake kusa da Mutumin a ƙalla ze shekara goma sha ɗaya, kamarsa ɗaya sak da mutumin yace "Abu, Mami na"

Mutumin ya shafa kan yaron nasa yace "Mami zata samu lafiya, stop crying My son" yanayinsu ya nuna suna da cikakken ilimi sosai. Both arabi da boko.

Dr G.y ya kalli matar dake kwance akan gadon tiyata, cikin jikinta sai juyawa yake, duk abinda ke cikin nata shima wahala yake sha sosai, ya matso yazo duniya.

Cikin ko in kula ya kalli wata Nurse yace "Ina wannan yaron mai ciwon Sikila?"
Tace "Yana male Ward"

"Shine wanda za'a ƙarawa jini, Iyayensa sune masu kuɗin nan?" Ta ɗaga masa kai.

yyace "Ok a ɗauki 1 Pints of blood, da aka ajiye na wannan matar, naga irin jinin su ɗaya, sai a kaiwa iyayensa su bada 50k a sawa yaron"

Nurse ɗin tace "Dr ita kuma matar fa? C.s za'ai mata fa,kuma zata buƙaci jini immediately in an fito da ita, ai bai dace a ɗauki nata ba"

Dr G.y ya nemi waje ya gyara tsayuwarsa yana faɗin "Who is the boss between me and you?".

Cikin girmamawa tace "kai ne Sir" yace
"So do as i said, is hardly for her to survive"

Kamar za tai kuka Nurse ɗin tace
"Amma aka amshi kuɗin aiki har 180k, Dr? But You can still try to help her."

Dr ya haɗe rai sosai ya ce "Ke nan, zuwa asibitin duk a banza? Ra'ayi na ne haka, har a gado aka kwantar da ita, and bance ba za'ai mata komai ba, za'a cire abunda ke cikin nata, but she's hypotensive and at the same time she has hyperglycemia, is hardly for her to survive".

Nurse ɗin tai zuguum tana kallon cikin tiyatar in da matar ke kwance, take ta jujjuya kanta, alamar tana jin jiki.

Wani likitan ne ya shigo cikin tiyatar, yana faɗin "an haɗa komai?"
G.Y ysce "Eh an haɗa komai mu shiga"

Suka je suka kewaye matar, sukai mata allurai aka kashe daga cikin ta zuwa ƙafafuwan ta, sannan suka fara ƙoƙarin yankata, GY ya samata ruwa da allurai a ciki sannan suka fara aikin.

Suna tsaka da yi numfashinta ya fara sama yana ƙasa, SPO2 ɗinta was very low, ga PR ɗinta was very high.

Da sauri ɗaya likitan yace "what's going wrong? GY wace allurar ka sa mata a ruwan nan ne?"

GY ya gaya masa, ya duba ruwan ya ɗakko kwalaban alluran ya duba, a take ya zare ido yace "GY ka manta she's hypertensive ne? Kuma allurar ai ba ita bace".

Da sauri GY ya duba tabbas yayi kuskure gurin saka allurar, na da nan suka tsaida ruwan, suka cigaba da ƙoƙarin ciro ɗan, amma yaron haka suka ciro shi babu rai.

Tuni ta galabaita matar, ta fita hayyacinta ba ta gane koma, ga jini da ya ɓalle kamar an kunna famfo, da ƙyar su ka ɗinke cikin nata, Amma ta ƙasanta jini sai ambaliya yake, ɗaya likitan yai mata duk alluran da suka kamata, amma jini be tsaya ba, ya kalli GY Yace "maza maza da an kaita ward, a saka mata jini, sannan ƴan uwanta su sake kawo wani jinin".

Mutumin nan da ɗansa suna tsaye aka fito da matar, gaba ɗaya abunda aka rufeta da shi, jini ya ɓata har ɗiga yake, aikuwa yaron ya bi bayansu da sauri

GY ya kalli Nurse yace "maza aje lap, a ɗakko jinin nan a sakamata".

Nurse tace "Doctor, har ka manta kace a siyarwa da iyayen yaran nan me sickler?"
Ɗaya likitan yace "GY harƙallarka tayi yawa Wallahi, yanzu ya za muyi da matar nan, she needs blood urgently, naga ance she has hyperglycemia, a bani glucometer in sake gwadawa"

Sai dai yana gwadawa ya ga sugan nata yai ƙasa sosai, ya duba file ɗinta, tun da tai awo a Asibitin, ba'a taɓa cewa tana da sugar ba sai yanzu.

"Waye ya duba sugarn nan kan a shiga tiyata"

Nurse ɗin dake biye da su tace "Nurse Bintu ce"

"Yaushe ta zama Nurse? Ba food hygiene tai ba? Dan me za ta dinga aikin Nurses, gaskiya GY Asibitinka da gyara".

Duk wannan mujadalar, yaron na tsaye a bakin ƙofa, yaji duk abunda suke faɗa.

Ya ja da baya ya koma in da ya baro mahaifinsa, cikin damuwa yace "My son, kayi mana Maminka addu'a"

Shiru Yaron yai bai ce komai ba, Su GY suka fito a tare ya kalli mutumin yace "Sai dai kuyi haƙuri, mun rasa ɗan da ke cikin ta, ita ma kuyi ta Addu'a muna kan ƙoƙarin ceto ranta ne"

Ba su kuma yi musu wani bayani ba, suka wuce, yaron ya kama hannun mahaifinsa ya ja shi zuwa ɗakin da take ciki, tana kwance jini na ta ɗinga daga kan gadon da take!



For seven days now, Captain is being treating in the military hospital, in Naija State military base.
Chief of Army staff ne, da General Ibrahim, da Chief Commander tsaye a cikin Room ɗin, Chief ya kalli Captain yace "Congratulations Captain, we were confirmed that today you will be discharged "

Captain yace "Thank you, sir"
Chief ya ce "akwai Good news, but it will be surprising.." Captain ya ware idanunsa sosai, Chief Commander ya yi Murmushi kafin ya kalli Captain ya ce.
"Jirgi na jiranka an gama komai, Allah ya ƙara sauƙi Captain, kai na musamman ne" General dai hararar Captain yake, yana tunanin yadda zai ga bayansa.
Gaba ɗaya fita sukai waje. A hankali Captain ya fito cikin wata farar singlet irinta sojoji yana ƙarewa harabar Barrack ɗin kallo. Tunanin yadda zai tafi da Abra yake ga Na'ima, gashi Chief ya tilasta sai an bincka iyayenta.
Yana tsaye yaga Faruk ya nufu wajansa, Captain ya ce "What happened?"
Faruk ya Girgiza kai yace "Abra" a hargitse Captain yace "Abra What? Don't tell Anything mara kyau akan Yarinyata" Faruk yace "Abra was missing, tun safe babu Abra gaba ɗaya n duba cikin Barrack ɗin nan babu ita... Abra ta ɓata!.

Bright pens
Nimcyluv
Zee kumurya
Ayushercool✍🏾🤘🏼

'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
[9/30, 8:55 PM] Abk: *✷DARE DA DUHU✷*

_Bright pens of✍🏾_
Nimcyluv
Ayushercool
Zee kumurya

*3......*
Elegant Online writers

_Ƙirƙirarren labari ne, ba mu yi shi dan cin zarafin wani ko wata ba, idan yai kamanceceniya da rayuwar wani ko wata Arashi ne🫣_

_Littafin DARE DA DUHU haƙƙin mallakar mu ne, bamu yar da a juya shi ta kowace siga ba, ko a sashi a wata kafa ba ba tare da izinin mu ba_





Dafe kansa dake barazanar tarwatse masa ya yi, tare da taune lips ɗinsa na ƙasa cikin taurin zuciya.

Likitan da ya je nemo yarinyar bai ganta ba ya dube shi, cikin girmamawa da son kwantar masa da hankali ya ce. "Ka kwantar da hankalinka Sir, Insha Allah, za'a ganta"

Runtse idonsa ya yi, gently ya ƙara buɗe su yana kallon su ya ce. "Where is my phone?"

Likitan ya ce. "Tana nan tare da uniform ɗinka, da za'a yi maka surgery ne aka cire su." Bai ce komai ba sai alama da ya yi masa da hannu akan ya kawo masa wayar. Likitan ya sara masa sannan ya fice. Gyara masa kwanciya ɗayan Likitan ya yi, shi ma ya fice.

Lumshe idonsa ya yi yana tuna Jamil da Danniel cikin jini a kallon ƙarshe da ya yi musu, sosai mutuwar su take dukan zuciyarsa. Numfashi ya fesar mai zafi lokacin da ya tuno fuskar ƙaramar yarinyar da ya gani, bai san me yasa ya ji ya damu da ita ba a cikin zuciyarsa, ji yake yi kamar ya fizge drip ɗin hannunsa ya fita ya nemo ta da kansa. A fili ya furta

"Where is She?What kind of situation is she in? who will take care of her?" Ya yi maganar cikin damuwa. he just felt worried about the little girl.

General Ibrahim A.M ne yake ta kaiwa da komowa a cikin office ɗinsa, shi kaɗai cikin tsananin ɓacin rai. Lokaci ɗaya ya koma mazauninsa ya zauna yana fesar da wani numfashi mai zafi, duk da kasancewar office ɗin da A.c amma gumi ne kawai yake tsatstsafo masa ta ko'ina a jikinsa. Hannunsa dafe da kansa sai karkaɗa ƙafafuwansa yake yi.
Da ƙarfi ya buga table ɗin gabansa tare da faɗin. "Damn it!"

Wayarsa ce ta fara ruri tana neman agaji, tsaki ya ja har kiran ya katse bai bi ta kan sa ba, dan ba ta shi yake ba. Sai da aka yi masa 4 missed call sannan ya janyo wayar cikin ɗacin rai a fusace ya ɗaga ba tare da ya duba mai kiran ba.

Daga cikin wayar wata shaƙaƙƙiyar murya ya ce. "An samu bacin rana!"

Ajiyar zuciya General Ibrahim ya sauke yace
"Har da na Inuwa ma duk an samu Gwaska."

Gwaska ya ce "Ba a taɓa mun
Ɓarna irin wannan ba tunda na fara harkan nan, ya akai haka ta faru?." Cikin ɓacin rai General ya ce. "Ba za ka gane baƙin cikin da nake ci da wannan Nasara da yaran nan suka samu ba, ban taɓa tunanin hakan za ta faru ba, a yanda na san ka na san taƙadirancinka ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login