Showing 105001 words to 108000 words out of 231718 words
Chapter 36 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
dare bayan ya kammala shirin kwanciya bacci sbd gobe tafiya ce da shi mai muhimmanci, a hankali ya gama saka rigar pyjamas ɗin kana ya zauna gefen gado yana kwanciya tare da sakin ajjiyar zuciya.
Wayarsa mai ƙirar iphone 13max pro ya ɗauka a nutse ya lalubi number ta tare da danna call ba tai wani rigging da yawa ba akai picking call ɗin.
"Bebbbb"
Ta faɗa cikin siririyar muryarta wacce bata fita sosai, saurare ɗaya kuma zakai mata kasan cewa mamallakiyyar muryar tana cikin damuwa.
"What happened to your voice?" A shagwaɓe ta ce masa "Nothing, how are you?"
"Good and you?"
Cikin salon taɓara ta ƙara narkar da muryarta ta ce "not good" a hankali Sp Adnan Aliyu Matawalle ya mirgina kaɗan yana jan pillow zuwa jikinsa.
"Lafiya? Jikin ne?"
Kamar tana gaban sa ta girgiza masa kai low ɗin voice ɗinta tasa keyi "No lafiya nake, I'm just wanted to see you please" wani kalar murmushi ya saki ya ce.
"Cewa zaki kina son ganin mijinki right?" Turo masa baki tayi ba tare da ta ce komai ba, kamar wanda ya ke Kallon ta ya ce.
"Allah ya baki sa'a a turo bakin nan a gabana yarinya"
"Me zakai to?"
Ta tambaya tana gyara kwanciyarta "idan Kinyi zaki gani, now tell ya Faris ya kiraki?" Kamar mai jiran kaɗan ta saka masa kuka sai ka ɗauka shi ne yai mata ba daidai ba, shiru ya yi mata tayi kukan yadda ta keso kafin ya ce.
"Cry... Cry... Cry as so much as you can" kukanta ta ƙarawa sauti sai da numfashinta ya fara fisga ya ce "Ya isa, kada na ƙara jin sautin kukan nan" ya faɗa babu wasa kuma alamar warning.
Shiru ta yi masa shi ma bai sake cewa komai ba, sai sautin bugun zuciyoyinsu dake fita lokacin ɗaya, idan akwai abinda Sp Adnan Aliyu Matawalle ya tsana ya ji mace na kuka, balle yanzu da ya kewa Abra kallon komai na rayuwarsa ta yaya zai so yaji kukan ta? Sam zuciyarsa ba zata jure ba. Kashe wayar ya yi baki ɗaya tare da kwanciya zuciyarsa babu daɗi.
Da ga can ɓangaren Abra lumshe idanunta ta yi hawayen da ke maƙale ya silalo zuwa saman fuskarta, tana ƙanƙame wayar a jikinta numfashinta na fita da ƙyar murya a daƙushe ta ce.
"Why Faris? Ban cancanci hakan a gareka ba, mene ya sa zakai nisa da duniyata? Mene ya sa zaka barni a lokacin da nake tsananin buƙatar ka kusa dani, please come back to me wallahi na maka Al'ƙawarin na fasa auren ba zanyi ba, ina jin tsoro gabana faɗuwa kamar wani abu ne ya sameka"
Wani raunataccen kuka ta saki sai da tayi mai isarta kafin ta miƙe zuwa toilet ta wanke fuskarta tare da ajjiye wayarta, fita ta yi da ga cikin ɗakin kai tsaye bedroom ɗin Salmanun-faris ta nufa ta ci sa'a a buɗe ya ke.
Tana shiga ta kwanta a kan gadon sa, tare da jan pillow ta rungome kewarsa na fisgarta, a hankali ta saka hannunta ta shafi laɓɓanta sai a yanzu Abinda Ya yi mata ya shiga dawowa cikin kwakwalwarta, tana ganin abun tamkar a mafarki ƙara ƙanƙame pillown ta yi domin ji tayi kamar yanzu ne Faris ke sumbatar bakinta.
"I miss You Faris, I love you ɗan ƙanina please ki sau ɗaya ne ka kirani just to say hi to me"
Washe gari da sassafe Mami ta shirya ta nufi gidansu sbd kiran da Anuty Suwaiba tai mata, Abra bata san tafiyar ta ba, sai farkawa tayi ta ga mata nan, daman Abbi ya koma wajan aiki.
Tana zaune a Parlour ita ɗaya kamar mayya tunanin Faris da Unknown ɗinta ya addabi zuciyarta, wayarta ce ta fara kawo haske ganin sunan da tayi Saved number Abbi ya sa ta ɗauka da sauri tana faɗin "Abbina"
"Sweetheart"
Abbi ya faɗa a taushashe yana gyara zamansa akan kujerar da ya ke zaune tare da sakin Murmushi. "Abbina gidan babu daɗi ni ɗaya ce Abbi please ka dawo min da Faris"
"Ohh na ɗauka zaki ce na dawo? Ni ba'a damu dani ba sai Faris Faris, ga kuma kamar Jaririya?"
Kamar ya ce tayi ta sakar masa kuka gaba ɗaya ta addabi zuciyarta da kanta baki ɗaya. Baya Abbi ya yi yana ta shi tsaye tare da goya hannunsa ɗaya a baya ya shiga takawa cikin nutsuwa.
"Zaki tarwatsa min zuciya sweetheart? Kullum kuka Ohhh yaaaa shiru da bakin ki a nan wajan"
Shiru ta yi masa sai ajjiyar zuciyar da ta ke saukewa wanda ya ke jinta sosai ta cikin wayar a kame ya ce.
"Ki daina kuka sbd Allah da kuma ni Abbinki bani da nutsuwa" a sanyaye ta ce "na daina Abbi ya aiki? Ka yi waya da Salman?"
"Kince ke ɗaya ce ko?"
Ya tambaya tare da yin rejecting questions ɗin ta."E,Abbi" jinjina kansa ya yi kafin ya ce.
"Ta shi kije Garden ki sha fresh air zaki ji sauƙin zuciyarki,amma idan kika sake kuka mun ɓata ba ruwana da ke" da sauri Abra ta ce "ban sakewa Abbi"
"That's my girl Abra Khamal Khamis smile"
Murmushi ta sakar masa "Thank you Abbi" bai ce komai ba ya kashe wayar baki ɗaya.
Wayar ta bi da kallo sai kuma ta miƙe tare da ajjiye ta a Parlour ta nufi Garden.
Uncle Faisal ne tsaye a gaban Mami sai Masifa ya ke. "Ni nace ina son Yarinyar nan kuma auren ta zan amma sbd an raina min hankali aka bawa wani ita, na cire kunyata har wajan fake father ɗin nata naje amma ya nuna bai amince ba"
"Saurara Faisal ni kake son tunawa asiri? Matsayin ƙanin uwa kake wajan Abra sai kuma kace kana son ta? Kasan abinda hakan ke nufi? Yana nufin tona asirin shekaru kusan ashirin ke nan, wanda kuma daidai ya ke dana rasa igiyar aurena, bana son shirman banza kada ka sake yi min magana akan Abra,banda masifa me zakai da ita?" Mami ta ƙare zan can cikin ɓacin rai da kuma damuwa.
A fusace shima Uncle Faisal ya ce.
"Igiyar auren ki bata gabana, kuma aure ne anyi mugani sai dai idan bana raye wallahi, Abra mallakina ce tun tana ƙarama nake fama da son ta a zuciyata to ayi mu gani idan tusa zata hura wuta"
Yana faɗin hakan ya fice da ga cikin gidan baki ɗaya, Anuty Suwaiba ta ce.
"Kan uba me Faisal ke nufi? Me zai aikata Na'ima ba kiga ta zama ba, idan baki son ki dawo gida mu jere matsayin zawarawa sai ki san
abinyi"
Dafe kai Mami ta yi cikin rashin sanin Abinyi ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
A hankali motar Fayyad ta shigo cikin Railway quarters ɗin yana zaune ɓangaren mai zaman banza sai Fayyad da ke driving yana tsokanar Sp Adnan.
"Da safe munyi waya baka ce min zaka zo ba, sai yanzu naji kira da ga sama wai kana airport"
Idanunsa akan gate ɗin gidan su Abra ya ce.
"To Ubana ne kai da zan faɗa maka? Ko shi bai san zan zo kano ba"
Parking Fayyad ya yi yana faɗin.
"Fitar min a mota to mara mutunci" kafaɗa ya ɗaga irin ko a jikinsa ɗin nan. Fita ya yi a motar Fayyad na faɗin "babu ko godiya?" Banza ya yi masa. Walking slowly ya nufi gate ɗin, yana zuwa gatekeeper ya buɗe masa ƙofar cikin girmamawa, gaba ɗaya sojojin da suke wajan suka gaishe sa dake duk sun san shi.
Wayarta ya fara kira amma bata ɗauka ba, ga shi ba abin ya shiga gidan kai tsaye ba, kuma ba zai iya komawa bai ganta ba, tafiya ce da shi zuwa Egypt. A hankali ya kalli ɗaya da ga cikin sojojin kafin ya yi magana wani ya ce.
"She's in the garden"
Hanyar Garden ɗin aka nuna masa, a hankali cikin nutsuwa da kamala ya nufi ciki, tun daga nesa ya hango ta ƙasan wata bishiya ta ɗora kanta akan wani ƙaramin dining dake wajan sai bottle water da ke kusa da ita, ta ɓoye kanta a hannayenta. Kamar mai bacci a hakan, har ya Ƙarasa inda take ya ja Kujera ya zauna bata sani ba.
Hannunsa ya sa baki ɗaya ya ɗagota, ganin bacci ta ke a hakan ya sa ya ɗan tsora mata shanyayyun idanunsa, yana ƙara yaba kyan da Ubangiji ya yi mata. Kumatun ta ya shiga bubbugawa daidai kunnen ta ya ce.
"Open your eyes Wife ga mijinki ya amsa kira"
Turo baki tayi ta ce
"Faris i knw one day zaka dawo gareni please kada ka sake barina" ta faɗa tana ƙanƙame jikin Sp Adnan Aliyu Matawalle tare da ɓoye fuskarta a ƙirjin sa a tunaninta Faris ne, domin bacci ta ke amma mafarkin sa ta ke.
Bakin ta Sp ya kama ya murza yana faɗin "Ohh Wannan Faris anya ba zan tayaki biko ba?" jin yadda ake murza bakinta ga Ƙamshin Pur oud da ke ratsa hancinta ya sanya tayi saurin buɗe idanunta da ke cike da bacci.
Haɗa idanu sukai ta ganta male-male a jikin mutum, jikinta na rawa ta fara ƙoƙarin sauka amma ya riƙeta sosai.
"Ba inda zaki, tunda a nan kike bacci gwamma kiyi a jikin mijinki" ya faɗa yana ƙara riƙe ta. turo baki tayi ta ce "ka cikani ba ruwana da kai" ganin abinda ya ke ƙoƙarin yi tayi saurin ɗauke fuskarta ta shiga dokan ƙirjinsa tana sakin kuka..
"Ba ruwana Allah ba kace ba zaka zo ba?kayi tafiyarka ni ban son auren na fasa"
"Baki son auren ko baki sona" kuka kawai ta ke sakar masa hadda shassheƙa, shiru ya yi mata yana ƙara riƙeta a jikinsa.
Washe gari bayan taiwa Sp rigima sosai a makaranta da ke a Kano ya kwana da ƙyar ya rarrashe ta, ta ce Faris ya tafi shima zai ta fi ya barta a haka suka rabo da al'ƙawarin zai dawo Soon. Har yamma tana shcl karatu ya fara ɗaukan zafi, da ƙyar ta ke yaƙi da zuciyarta wajan ganin tai karatu amma tunanin Faris da Unknown Kullum da su take kwana ta ke ta shi, wanne hali Faris ke ciki? Fushi ya ke da ita ko mene?. Waye Unknown mene ya sa kalamansa suke da tasiri a Zuciyarta yaushe zai bayyana gareta mene ya sa ya daina yi mata messages yanzu?.
Meenal ce tsaye a gaban makeken Bulama hospital, cikin nutsuwa ta shigo reception ɗin tana bin mutunan wajan da kallo. Wata mata dake riƙe da yarinya mai Sikila ta kalla kafin ta ce.
"Ya kike zaune da ita tana soma? Ko ba soma bane?" Kafin tai magana da ga bayanta akace "ku kaita Emergency room yanzu, ai mata duk abinda ya dace ban san mene ya sa kuke barin patient ba kulawa haka ba"
"Daddy"
Meenal ta faɗa daidai kunan Bulama, hannunta ya kama yana nufar office ɗinsa da ita ya ce.
"My dear zuwan ba zata?" Fari tai da idanu ta ce.
"Wallahi Daddy kawai naji ina son zuwa hospital naka, amma banji daɗin yadda naga marasa lafiya haka ba"
"Shi yasa na so ki karanci Ɓangaren lafiya amma kika watsa min ƙasa a idanu, gaba ɗaya basu da serious akan aikin su, banda muna da tsananin kulawa ban san zai dinga faruwa ba, wasu da ga cikin Likitocin kuma idan ba kuɗi basa duba mara lafiya"
"But this is not fair Daddy, yaya mutum zai idan bai da kuɗi gsky ana kulawa wanda ya taimaki wani sai Allah ya taimake sa" kallon Meenal Daddy ya yi kafin ya ce.
"That's why na ware ɓangaren marasa ƙarfi ana musu komai as voluntary"
Yana zaunar da itace a office ɗin ya fito da sauri yana haɗa kan Likitocin da nurse's ɗin ya ce. "Duk wanda suke reception a duba so kyauta don't make any mistake" kamar yasan Meenal zata zaga asibiti ganin komai lafiya wasu sai godiya suke ta ƙara gasgata girman tausayin Mahaifinta.
A hankali lokacin ya fara juyawa, satittika suka fara zama kwanaki har Ubangiji ya kawo satin bikin Abra Khamal Khamis da Sp Adnan Aliyu Matawalle. Shiri ake da ga ko wanne ɓangare, abinka da masu kuɗi sai ka rasa wanne ɓangare ne ya fi ji da bikin. Gefen Abra abin ba sauƙi ta rame sosai Kullum cikin kuka ta ke, gaba ɗaya ta tashi hankalinta akan Salman, wanda ya sa Ammi ta ɗauke ta zuwa can gidanta a can ake mata gyara jiki. Sp Adnan ango Kullum yana tare da amaryarsa a waya yana yin iya bakin ƙoƙarinsa wajan ganin ya faranta mata, gefe guda kuma har lokacin Abbi bai dawo ba, Khairy sai shige da fice suke domin sun haɗa plain na dinner a ɓoye ita da Usman da su Fayyad.
The day.
Yau ya kama ranar juma'a wanda ya yi dadai da ranar da za'a fara biki wato Kamu. Tun safe aka fara zuba decorations a harabar gidan Abbi sai ka ɗauka babban hall aka kama sbd tsarin wajan. Har yamma babu amarya babu labarinta, Hankali ta she Mami ta kira Khairy ta ce.
"Ummulkhairy ina Abra?"
Khairy da ke gidan kwalliya ta ce. "Mami ina gidan kwalliya Abra ma tana gidan da za'ai mata kwalliya"
"Ok call her immediately"
Katse kiran ta yi, khairy ta kira number Abra a kashe hakan ya sa ta kira number mai make up ɗin tana ɗauka ta ce.
"Hello don Allah Abra fa?" Mai make up ɗin ta ce "Tun 3 aka gama mata kwalliya na ce ta jira ta ce zata da ganta yanzu wajan 5 ake nema na yamma tayi kusan 2hours da tafiya"
A fili Khairy ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kanan dai ta gudu kamar yadda ta ce.....
Littafin kuɗi ne,biya ₦300 via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank... Idan katin waya ne zaka Turo 500 shaidar biya 08081012143
[10/10, 4:17 PM] Abk: Jiki na rawa, Khairy ta kira Mami tana salati tana salallami, Mami ta ɗaga wayar ta ce "Ya aka yi? Ta na ina ne, mutane sun fara taruwa fa?".
Khairy murya na rawa ta ce "Mami na kira mai kwalliyar ta ce mini tun uku, aka gama kwalliyar, kuma ta tafi".
Mami ta ce "Ta tafi taje ina?"
"Mami Wallahi ban sani ba, ba guri ɗaya muka je kwalliyar da ita ba, ni gurin da naje daban".
Mami ta ajiye waya tana faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yarinyar nan gidan ubanwa ta tafi ne? Ace an gama kwalliya tun uku amma har haɗu da rabi ba ta iso gida ba, ga mutane sun fara taruwa".
Anty suwaiba ta ce"Allah yasa ba guduwa ta yi ba".
Mami ta zare ido ta ce "Ta gudu ta je gidan uban wa? Lallai ma yarinyar nan".
Abu kamar wasa, ba Abra babu dalilinta, tun ana maganar ƙasa_ƙasa, har mutane suka fara jin halin da ake ciki.
Abokan aikin Adnan ne, suke ta shiri cikin shigarsu ta police, domin dai za'a yi parrate na ban girma ga Adnan da amarayarsa.
Usman ne ya kalli Adnan da ke ta haɗe rai ya ce "Wai haɗe ran me kake ne?".
Adnan ya ce "Am jealous ne, duk wannan garadan sai kun je kun kalle mini mata".
Aminu ya ce "Kai dalla ware, ai kaima gardin ne, sai kace a kanka aka fara Aure, ko da yake tsiyar mutum ya zama tuzuru kenan, duk sai ya fara behaving abnormal".
"Meye banbancina da kai? Har gara ma ni yanzu zan shige daga ciki, kai kana waje".
"Nima ina hanya ne" Usman yayi Maganar yana murmushi.
Daga haka suka kammala shirinsu, suka fara haramar tafiya gidansu Abra.
Granny ce ta shiga sashin Na'ima tana faɗin "Ke Na'ima, wai wace Maganar banza nake ji ne? Wai kamar Ana Abra ta ɓata, gidan ubanwa ki kai ta?"
"Haba granny, Ina kuwa zan Kai ta, daga zuwa kwalliya ba ta dawo ba".
"Ƙarya ki keyi, ana Magana kina wani ƙifta ido kamar ta Allah, ki fito da yarinyar nan duk in da ki ka kaita, kan in samo madoki in shemeki a gurin nan".
Ammi ce ta ce "Granny ki yi haƙuri, ya za'ayi ta aikata haka ga 'yar ta, Yanzu dai muyi ta addu'a, kuma a kira shi angon a sanar masa dan a san abun yi".
Granny ta ce "Wai ke Yaushe zaki gane kan makircin wannan yarinyar ne? Ai duk abun da akace tayi babu mamaki, yau duk abun da za'ayi sai an nemo mini jikata. Amm ke nace ina tabarau na ne? in ƙarewa wannan mara Kunyar kallo, in kalli idanunta sosai, dan ni idan na kalli idon mara gaskiya ina gane shi".
Ammi ta ce "Glass ɗinki yana in da ki ka yi salla, amma dan Allah ki dena wannan maganganun, bari a san abunyi, ko a tura wasu gurin mai kwalliyar".
Na'ima kuwa iya ƙuluwa ta ƙulu, ji take kamar ta rufe Granny da duka, shegiyar tsohuwa hayyataciya, sai tsawon rai kamar dabino, ta ƙi mutuwa kuma kullum cikin rikici take, tsawon shekarun da Na'ima tayi tare da Khamal Granny ba ta ƙaunarta sam.
Gida ya rikice ana neman Abra, ita kuma Granny ta rikice tana neman tabarau, ta ɗora da masifar cewa bayan sace Abra da Na'ima tayi, ta kuma sace mata glashinta, saboda baƙin hali.
Anty Suwaiba ta ce "Wai ke Na'ima ba wani mataki da zaki ɗauka a kan wannan sokuwar tsohuwar, shegen surutun tsiya kamar an jefeta a ka?".
"To ni ya zan yi da ita? Wannan kaidinta ya fi yadda kike tunani, yanzun nan za ta ƙullawa mutum sharri.
Ɗakin Salman Granny ta nufa, tana cigaba da zage Na'ima, Ammi ta ce "Granny me zaki yi a nan kuma?".
"Tabarau na nake nema".
"To mai ze kai glass ɗinki nan kuma? Na ga tunda muka zo baki je nan ba".
"A'a, ance idan raƙuminka ya ɓata ka neme shi har kura tandu, yo na sani ko wannan algungumar ta yi garkuwa shi ta kai ta ɓoye" ta ƙarasa Maganar, tana nufar ɗakin Salman.
Sai dai tana shiga ɗakin, ta ƙwala uban ihun da ya janyo hankalin 'yan biki.
"Gata nan ku zo gata!" Ta yi maganar cikin ihu.
Su Ammi na zuwa, suka tarar da Abra a zaune, fuskarta sharkaf hawaye.
Ashe tun bai fi uku da rabi ta dawo gida ba, ta shiga ta ƙofar baya, tabi ta kitchen ta shige ɗakin Salman abunta, kuma ta kashe wayoyinta.
Ammi ta ce "Abra, dama kina nan ki ka ɗagawa mutane hankali? Kuma kalli duk kin fara ɓata kwalliyar".
Cikin kuka Abra ta ce "Ammi Faris ɗina, zan yi Aure baya nan, dan Allah Ammi kice musu na fasa Auren nan a dawo mini da Faris ɗina".
N'a'ima a fusace ta ce "wannan wane irin sakarci ne haka Abra? Mun tara mutane kina neman ki bamu Kunya?