Showing 150001 words to 153000 words out of 231718 words
Chapter 51 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
masa emojin rufe fuska. A hankali ta kai hannu ta shafa cikinta, tana jin yadda wata zazzafar soyayyar shi take zagaye ko wani gurbi na zuciyarta. Abbi bai san tana da ciki ba, shi ya sa yake mata zancen karatu, ta sanar masa dai ta yi ciwo, amma ba za ta iya faɗa masa tana da ciki ba. Sai dai ita ma tana son ta cigaba da karatun, damuwar da take ciki ne ya sa ta manta da babun shi, tunin Abbinta kuma a yanzu ya dawo mata da son karatun, ko ba komai idan tana zuwa school ɗin zai rage mata damuwa tare da ɗebe mata kewar kaɗaici. Sallama suka yi da Abbi ta miƙe ta nufi ɗakin Adnan.
Tana shiga ta tarar da shi yana shiryawa, alamun bai jima da fitowa daga wanka ba. Kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kanta, saɓanin shi da ya ƙura mata ido. Cikin haɗe rai ta ce. "Magana na zo mu yi Adnan."
"Ba ni da lokaci." Ya faɗa tare da ɗauke idonsa daga kanta.
"Kamar ya ba ka da lokaci? Maganar karatuna ce to ba wani abu ba, Abbi ya mini magana ya ce ya kamata zuwa yanzu na koma school, kar a mini nisa da yawa.
Kallon sama da ƙasa ya yi mata ya ce, "Lallai wuyanki ya isa yanka, wato kwana biyu na sake miki shi ya sa har kika samu damar faɗa mini magana son ranki, saboda ba ki jibgu ba ko? To darajar cikin jikinki kike ci, domin duk ranar da ya bar jikinki sai na fanshe duk bashin da kika ɗauka."
"Is not my concern, ka yi ko ma mene ne, ni yanzu maganar karatuna nake maka, ya ake ciki?"
"To ba za ki cigaba ba, ke da karatu har abada in dai a gidan Adnan Aliyu Matawalle ne, saboda karatu na masu asali, gata da ƴanci ne, ba na TSINTATTU irin ki ba."
Littafin kuɗi ne, ki/ka biya kafin ku karanta. Don neman ƙarin bayani 09047871750
[10/27, 11:38 AM] Abk: Kallonsa take cike da takaicin yadda gaba ɗaya yake son ɗauke mata dukkan wani farin ciki na rayuwarta.
"I am your husband and I have control over you, karatu ne ke dashi har abada sai a lahira idan anayi, Everything I know will make you happy so I prevent it from happening.. Ki daina wahalar da kanki kina wahalar min da unborn okey"
"Zaka iya hanani farin ciki, amma baka isa ka ɗauke mini raina ba, duk wahala duk tsananin nasan Ubangiji yana tare dani kuma shi ne zai saka mini akan cutar da kake aikatawa a gareni,
I'm your wife amma na zama jaka a wajanka mara ƴan ci, ka sani ko Ubangiji baya kama bawa da laifin da bai san ya aikata ba,
balle Mutum akwai haƙƙina a rataye a wuyanka"
Tana faɗin hakan ya juya, har yaje baƙin ƙofa ta tsaya ba tare data kallesa ba tai Murmushi wanda yafi kuka ciwo ta ce.
"Ciki? Ur unborn. Uhm you are doing wrong Sp Adnan Aliyu Matawalle, kayi gaggawar cire son abin da ke cikina daga zuciyarka, domin babu tabbacin zai haifeshi,
Ba zan taɓa haihu da kai ba, inma na haihu zan shaidawa abin da na haifa cewa ubansa ba Mutumin ƙwarai bane. Azzalumi ne, Macuci ne, mayaudariya, mara imani ne, bashi da tausayin ƴa mace a ransa balle matarsa wacce tayi sanadin zuwan yaron duniya.
Na tsaneka wallahi bana ko ƙaunar ganinka"
Ta ƙare maganar wani raunataccen kuka na ƙwace mata, domin duk yadda ta kai ga hqr da kuma ɗauke kai na abin da yake mata, zuciyarta ta kasa ɗauka. Bata taɓa tunanin masoyinka zai juye zuwa maƙiyinka ba, ita a yanzu ta daina yi wa Adnan kallon maƙiyi, kallon makashinta take masa wanda yake ƙoƙarin kassara rayuwarta dayin sanadiyar Zuwanta zuwa koshewa.
"Whatever Abra, i like your style ƙarfin halinka yana ban sha'awa. Ciki kuma idan kin fasa cirewa baki haifu cikin wannan mugun azzalumin uban naki ba, wanda ya maida son zuciya, halinsa, ɗabi'arsa da kuma bangon da yake jingina ni dake shege ka fasa, wawiyya. Get out of my room mumu"
Kukanta ne ya tsaya sai kallonsa kawai da take tana sauke ajjiyar zuciya a wahale, domin gaba ɗaya hanyar shaƙar numfashinta toshewa tayi for some minutes. Juya tayi zata fita ya yi saurin cewa.
"And if anything happens to my unborn ki kuka da kanki"
"Idan fitsari banza ne kaza tayi mana? zaka iya ɗaukan cikin ka mayar zuwa naka" murmushi Adnan ya yi ganin abin na su ya zama kamar drama cikin shafa ƙirjinsa yana watsa hannunsa zuwa sama ya ce...
"Tunda nai cikin, ai hakan mai sauƙi ne yarinya. Kuma da kike mgnar kaza mene? Ai ni ne wanda zan faɗi haka tunda gudunmawata yafi yawa wajan samar da cikin"
Banza tai masa tare da ficewa daga cikin ɗakin zuciyarta babu daɗi gaba ɗaya. Idan tai tunanin saɓawa Adnan sai kuma ta tuna makomarta. Ita sam ba haka ta san ana rayuwar aure ba, ta karanta a Omdatul ahkam, Zadil zaujen, da sauransu. Koda yake daman ya ce bai aureta saboda yana son ta ba, ya aureta ne sbd hutar ɗaukan fansa da kuma rayuwa da abin da ya yi a zuciyarsa.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un. Wayyo ni Abra What should I do?" Ta tambayi kanta lokacin data ke zama a kan kujerar parlourn. Idanunta ya yi jaa sosai daman yawan azkar da karatun Alqur'anin da take yana ɗauke mata damuwar da Adnan ke cusa mata a zuciya. Sulalewa tayi a saman carpet tare da kwanciya sbd yadda take jin ƙasusuwan jikinta na mata zafi da ciwo kamar zasu karye. Ga matsanancin ciwon kai duk da yunwar da take ji amma hakan bai sa ta miƙe ba, gaba ɗaya gaɓoɓin jikinta sun saki a nan wajan barci ta ɗauketa.
Cikin dare wani zazzafan zazzaɓi ya rufeta ruf, banda huci babu abin da jikinta keyi, sai rawar ɗari take hatta idanunta ta kasa samun zarafin buɗewa balle ta samu ƙarfin qwiwar barin parlourn. Sunayen Allah ta shiga shiga furtawa cikin zuciyarta da kuma neman ɗauki daga garesa.
Kiran sallar Subhi da ake yi ne ya sanya Adnan motsawa bakinsa ɗauke da addu'ar tashi daga barci, gently ya buɗe idanunsa wanda sukai masa nauyi duk da kwana biyu baya iya barci abubuwa da yawa ne suke damun cikin tunaninsa. Miƙewa yai tare da ɗaukan wayar, ƙuri ya yiwa screen ɗin wayar tamkar mai neman wani abu, amma ya kasa fahimtar mene yake nema ɗin?.
Kai tsaye Bathroom ya nufa ya sakarwa kansa shower tare da ɗaura alwala. Da sauri ya zuwa Arabian jallabiya ya fito zuwa parlourn da nufi shigewa masjid.
Sai dai fitar numfashinta da sauri ya ankarar da shi, manyan idanunsa ya zaro waje ganin yadda ta zazzago daga saman kujerar zuwa ƙasa jiki na rawa ya Ƙarasa yana faɗin.
"Abra! Ke Abra mene haka" Adnan ya faɗa yana ɗan bubbuga kafaɗarta, ganin ko motsi ba tayi. A hankali ya zameta tare da ɗagota baki ɗaya a karo na farko ya nufi part ɗinsa da ita,
A zuciyarsa yana mmkin abin da ya jefata cikin wannan halin ko ciwon nata ne ya motsa? Juyawa ya yi bayan ya kwantar da ita a saman makeken gadonsa ya nufi masjid.
Abra na jin duk abin da yake faɗa kawai bata da kuzarin motsawa ne balle ta buɗe idanunta, tana nan kwance ya dawo kai tsaye kuma wayarsa ya ɗauka ya kira number likitar data dubata, cikin ikon Allah aka ɗaga kiran.
"Hello, I Adnan Aliyu Matawalle speaking, Abra's husband"
"Oh Yeah. How is she is everything ok?" Dr ɗin ta tambaya domin tana kan bakin aiki sbd kwana tayi hospital shida nayi kuma zata bar wajan zuwa gidanta.
"Allhmd, sai matsalar zazzaɓi yanzu haka dashi ta kwana ga wayan ɗaukewar numfashi" ya faɗa a sanyaye sbd ganin har yanzu cikin duhun asubahi ne. "Don't worry, zazzaɓin zai daina sai cikin ya yi ƙwari Maybe kalar nata laulayin kenan. A kula dai sbd cikin fari ne"
Shafa kansa yai kamar zai shiru sai kuma ya ce.
"Insha Allah. Zazzaɓin fa?" "Be with her, sanyin jikinka zai taimaka wajan sauke zafin jikin nata" jinjina kai ya yi kana yai mata gdy tare da kashe wayar yana bin Abra da kallo musamman lafaffan cikinta.
Mami ce ta fito daga cikin bedroom ɗinta ta ɗauki wanka sai baza ƙamshi take, cike da muradin shawo kan Abbi ta nufi nasa sashin. Yana zaune a Parlourn dake part ɗinsa hannunsu riƙe da coffee yana sha a hankali, gabansa kuma system ce ya doƙufa wajan yin searching na abu.
Sarai yaji shigowar ta, sanin amsa Sallama ɗaya cikin abin da Musulunci ya zo dashi, ya sa ya amsa can cikin maƙoshi, bare daya kalli ko inda take ba.
Rashin sakin fuskar Abbi yasa duk jikinta yayi sanyi, muryarta na rawa ta ce. "Good Mrng Man" nan ma ya yi mata banza kamar zatai kuka ta ce.
"Haba don Allah, na baka hqr nayi magiyar amma duk a banza, wallahi ban aikata lafin da kake tunanin nayi ba sai dai idan wani ke nufina da sharri,
Ka dubi abin nan ka yafe min ina jin babu daɗi ganin yadda muke rayuwa,babu rana kusa dani babu farin cikinka na shiga uku"
Hannunsa ya ɗaga mata ya ce "Point of corrections babu yaronki kusa dake, ba yaranki ba ok" "mekake nufi? Yanzu da ace Abra nan ai da naji sauƙin wani abun"
"Yanzu kika san muhimmancin Abra? ba fata kike daman ki rabu da ita ba. Ina tunanin You don't have to be worry about abin da kike so ke ya samu, just be happy and celebrate Na'ima"
Shiru tayi domin bata da gsky kuma daman dole wannan gorin yazo wata rana. Kallonsa tayi ta ce "Ina son magana da kai"
Shiru ya yi mata ta ƙara cewa.
"Ina magana"
"Naji ai, bani da lokacin ki ne Na'ima"
"Amma mene ya sa please nifa matarka ce, abin da zan faɗa yana da muhimmanci" miƙewa ya yi tare da ɗaukan system ɗin sa ya nufi cikin bedroom.
"Magana zan maka akan Salman" sai a lokacin ya juya ya kalleta sosai kafin ya saki murmushi ya ce.
"Ke ya shafa kuma kada ki sake zuwar mini da batu akan haka, abu ɗaya na sani duk abin da ya samu yarona sai nayi Shari'a dake" kafin tai magana wayar Abbi dake kan kujera wacce ya manta ta, ta fara ringing kafin ya Ƙarasa Mami ta ɗauki wayar.
"Salima ta faɗa a fili" ganin yadda sunan Salima ke yawo akan screen ɗin wayar karɓar wayar ya yi yana answering tare da faɗin.
"How are you Salima"
Zuciyar Mami ta buga wata zufa na yanko mata jiki na rawa ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Salima? Wannan Shegiyar yarinyar again na shiga uku ni Na'ima"
Miƙewa tayi zata bi bayansa kafin ta Ƙarasa ya yi saurin rufe ƙofarsa tare da murza mata key. Abin duniya ya isheni Mami ta rasa ta ina zata fara, tana buƙatar sanin halin da Salman ke ciki, gefe guda kuma tunanin Abra na addabar Zuciyarta a kwana biyun nan, gaba ɗaya ta rasa mafita ga kuma masifar dake shirin samunta na Salima, mene haɗin ta da mijinta? Me ya sa ta dawo garesa? Ko dai har yanzu tana bibiyarsa itace bata sani ba. "Na kashe kai na" bata da sauran wanda zata faɗawa damuwarta a yanzu, domin ko ta sha giyar wake ba zata ƙara neman shawara wajan Anuty Suwaiba ba. Ta riga ta gane hatsin ba tsaba.
Yau ya kama Weekend ne cikin jerin watannin da Abra tayi a gidan Adnan a satin ƙarshen watan da zai sanya ta cika wata biyar cif a gidan aurenta. Amma duk tsayin kwanaki da kuma satittika zuwa watannin data riska babu wata rana data zame mata ranar farin ciki, tun ranar da aka kawota gidansa matsayin Amarya har zuwa Yanzu da take cika wata biyar dayin aure. A hankali ta ɗora hannunta a saman cikinta wanda ya fara girma sosai kasancewar ta mara jiki yasa cikin fitowa ya zauna das ƙasan mararta ya ƙara mata kyau na jiki. Amma tana nan yadda take a rame tai duhu sosai kamar ba ita ba. Fararen idanunta da suke a buɗe ta lumshe a karo na farko taji soyayyar abin da yake cikinta ya ratsa Zuciyarta. Musamman yanzu da take jin gilmawar abin da ke cikin nata, tabbacin yana cikin lafiya. "Banso aka samar dakai ta wannan hanyar ba, nasan ba zaka jure ganin wacce ta haifeka cikin uƙubar mahaifinka ba, amma zan tabbatar da cewa ba kayi masa kallon uba ba, zan shaida maka irin wahala da azabtarwar da mahaifinka ya yi mini, tun bayan rabuwata da Salman nake jin kamar na rabu da dukkan wani farin cikina. Amma yanzu sabuwarka cikin mahaifa ya sa naji na samu wani abokin rayuwar wanda zai maye gurbin Salman a zuciyata" hawayen da take ta ɓoyewa ne suka sakko mata cikin sauri ta goge ta ce. "why should i cry? Cry for no reason nayi Al'ƙawarin ba zan sake zubar da hawaye akan azabtarwar da Adnan ke min ba, zanyi hawaye na dalilin rashin sanin asalina da tushena" kukan da yaci ƙarfinta ne yasa ta kasa faɗin sauran maganar wanda kamar suke fitar da kansu bata shirya faɗar su ba.
Mai aikin Hajiya Mama ce ta fito daga kitchen tare da kallon Abra ta ce "Hajiya ƙarama an gama lunch ɗin, na kawo maki nan?" Girgiza kai Abra tayi cikin sakin fuska bayan ta share hawayen idanunta ta ce. "Bana jin zanci abincin nan Laure, kawai ki zuba yadda zai maki kici sannu da ƙoƙari"
"Ko babu yawa ya dace ace kinci sbd abin da yake cikinki ya samu kyakkyawar kulawa" Abra ta kalli mai aikin cikin tunani sai kuma ta ce "Shin abin da yake cikina zai samu illane game da rashin cin abincin nawa?" Da sauri mai aikin ta ce "Sosai, domin sai Kinci shima sai samu wanda zaici, rashin cin babbar illa ne zaki iya haifar babyn babu girma ko kuzari". Murmushi kawai Abra tayi ta ce "Ok thank you" "na kawo maki ko kaɗan ne?" Abra ta girgiza kai ta ce "ba zan iya ci ba Laure, ni bana jin wata yunwa" daga baƙin ƙofa suka ji ance "Idan kin gama aikinki jeki kawai" Laure ta juya ta kalli Adnan jiki na rawa ta gaida shi bai kula ba, da sauri ta nufi sashin da aka bata.
Rufe idanu Abra tayi kamar mai bacci, a hankali Adnan yake binta da idanu yana mmkin lalacewar da take a kullum, ba ƙima, hasken ya dishe sai ƙirji kamar zai fasa riga ga kuma yadda cikin ya sake fitowa fili. Taɓe bakinsa ya yi irin ko a jikinsa ɗin nan kafin ya nufi kitchen babu jimawa ya dawo ɗauke da plate na abinci dambu ne, wanda ya sha kayan lambu da kuma zallar hatta yaji gyaɗa da zogala sai ƙamshi yake. Zama ya yi very close to her yana kame iyayen tare da faɗin "zaki iya zama da yunwa until unborn ɗina ya samu abincin, dan haka get ready zanyi feedings babyna"
Ɗauke fuska tayi tare da ƙoƙarin Miƙewa zata bar wajan, amma gaba ɗaya jikinta ya saki sosai take jin ciwon jiki da wani zazzaɓi na cikin ƙashi. Hannunta ya kama yana mayar da ita zaune kafin ya ce.
"Kina tacin albarkacin abin da yake cikinki, shine dalilin da yasa nake raga maki,amma ke baki ganin hakan ko? Nidai duk abin da ya sameki matsalarki ce kawai ki tabbatar jinina lafiya yake"
Bata kulasa ba, ko fuskarsa bata ƙaunar gani nesa take da dukkan abin da zai sanya tai masa mgn ko yai mata. "Dole kici abincin nan Abra" a ɗan fusace ta ce "to ana dole ne? Don girman Allah dan darajar iyayenka ka rabu dani, stay away from me don Allah" ta faɗa tana runtse idanunta sbd kissing bakinta da taji ya yi a hankali. Plate ɗin abincin ya ajjiye a gefe tare da jawota jikinsa hannunsa ya ɗora akan cikinta yana lumshe idanunsa.
"Kina cewa kin tsaneni, bayan so na da kike yasa idanunki ya rufe kika kasa fahimtar son da Salman yake maki, hakan na nufin duk wata ƙiyayya da zaki nuna min iya baki ne bai kai zuciya ba Angel" harara ta watsa masa ta ce.
"Na soka a lokacin da nake tunanin zaka zame farin ciki, abokin rayuwa, zaka zama mai tausayi a gareni, da bani garkuwa, na soka a lokacin da nake ganin kyawawan halaye a tattare dakai. Amma wallahi wallahi Allah babu sonka a zuciyata, ban taɓa tsanar wani ba, ban taɓa jin akwai wani rai da zanji bana son ganin ko fuskarsa ba irin kai. Sp Adnan Aliyu Matawalle! Abra Khamal Khamis hate you. I hate you na tsaneka wallahi bana ƙaunar ganinka, zakai ladama, zakai dana sani ka rubuta ka Ajjiye zakai kuka da idanunka"
Tana faɗin hakan ta miƙe tsaye jiki babu ƙauri ta nufi hanyar part ɗin ta. Cikin zafin nama Adnan ya sha gabanta ya ce "Ke har kin isa ki furta kalmar tsana a gareni? Wallahi ƙarya kike kina sona, kuka? Ko mugun azzalumi Ubanki mai zuciyar fir'auna bai sanya na zubar da hawaye ba, balle abin da ya haifa. Ki rubuta kema ki ajjiye a duk sanda nai kuka sbd ke a ranar wallahi zan daina duk wata mugunta da nayi miki, a lokacin zan fita daga sabgarki a lokacin zan zubar da makaman ɗaukan fansa na" Murmushi kawai tayi tana mmkin muguwar zuciya irinta Adnan a hankali tana jan numfashi ta ce. "Ta ina zan san kayi kukan? Abin zai zo maka ta hanyar da bakai tsammani ba, ka tsammaci abin da baka tsammani shi ne kawai" tana faɗin hakan tai ɗakin ta. Ya daɗe tsaye yana tunani ya kasa fahimtar komai.
Har dare Abra bata fito ba, Adnan bai je inda take ba, balle yasan halin da take ciki, taci ko bata ci no one's know. A gefe guda kuma soyayyar abin da ke cikin Abra take da masa mugun kamu. Misalin 12 na dare tana kwance nannaɗe cikin duvet hannunta kuma ɗaya riƙe da azkar amma ko iya karantawa ba tai ba, ta dai riƙe kawai a wajanta ne. Tsaye ya yi a kanta cikin ko in kula ya ce "Madam nazo amsar haƙƙina ne" Shiru tai masa ganin tai shiru yasa shi faɗin "Ko ba