Showing 90001 words to 93000 words out of 231718 words

Chapter 31 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

Advertisement

28 Feb 2025

14892

ta ta, ta sa hannu ta ɗau wayar, tare da kwanciya akan lafiyayyen gadonta.

"Angel shine ko ki neme ni, balle ki ji yana je gida ko?".

Tace "Na neme ka mana"

"A ina?".

"Addu'a na yi maka, Allah ya kaika lafiya".

"Na ji, na kuma gode, amma ai Yakamata ki kirani ki ji ko naje lafiya".

"Ba kai ne kai mini tsawa ba kafin ka tafi".

Adnan yayi dariya yace "Fushi kike kenan? Ai idan nace bana son abu, bana buƙatar sake maimaitawa, amma ke se kiyi biris, shiyasa nai miki tsawa, amma na dena kinji My wife".

Tayi ajiyar zuciya tace "to ya kaje gida?".

"Ba na so, tun da sai da na roƙa".

"To nima ban haƙura ba da kai mini tsawa".

Abra ba dai shiririta ba, ya faɗa a ransa, ya dinga janta da hira, har kusan ƙarfe goma na dare, sannan sukayi sallama.

Duk ɗokin da Abra take idan Abbi zai dawo, a wannan karon sai ta shiga fargaba da zullumi, dan bata san ya zai ɗauki Maganar Adnan ba idan Mami ta gaya masa.

Da daddare Hajiya Na'ima ta sami Major a ɗakinsa, suna cikin hira ta ce "to kai fa 'yar ka magana ta ɗakko".

"Wace Maganar kenan?".

"Ta zo ta sameni da wani batu, ta ce mini in sanar maka ita Aure ta ke so".

"What? Abran ce ta gaya miki haka?"

"Ƙwarai kuwa, tace mini Aure take so, dan ta kawon wanda take so ɗin har gidan nan ya zo jiya".

"Dan meyasa kika bari wani yazo mini gurin 'ya ta ba da izinina ba?".

Hajiya Na'ima tace 'ban gane ba, ta zo ta sameni da Magana, kuma sa ince mata a'a".

"Tambayar ki nake dan me wani zai zo mini gida gurin 'yata ba da izini na ba? Kuma ita Abran zan sameta, karatu za tayi ba Aure ba".

"Wai me kake nufi ne da yarinyar nan? Idan ba ai mata Aure yanzu ba sai Yaushe, kai da ɗanka kun hana kowa ya zo gurinta da sunan yana son ta, wai ni ko kai ke son yarinyar nan ne?".

Major yayi murmushi yace "Ina son 'ya ta mana, amma kin manta ni ne ubanta, ko har kin manta 'yar da karuwa ta haifa mini ce?"

Hajiya Na'ima ta kwantar da murya, ganin yana nema ya maida Maganar wani na daban.

"Major dan Allah ka duba lamarin nan, yarinyar nan tum da har ta riga ta furta tana son Auren nan, ni banga dalilin da zai sa ka ce saita gama karatu ba sannan za'ai mata Aure, yarinyar nan Allah yayi mata kyau me ɗaukar hankali, baka tunanin abunda ka iya faruwa a jami'ar da ka tuarata.
Shi kuwa Aure garkuwa ne ga 'ya mace, idan akai mata Aure zata samu wata kariya daga sharrin mazan jami'a da lalacewa".

"In kinga ɗa ya lalace a makaranta, to dama can lalataccen ne, amma ni 'ya ta ba lallatacciya bace, kuma ba gazawa nai da ɗaukar ɗawainiyarta ba, dan haka a ƙyalemini 'ya ta".

"Yanzu kana ganin lamarin nan ba abun dubawa ba ne? Ita fa da bakinta ta ce mini Auren ta ke so".

"Na'ima, ba zanwa Abra Aure yanzu ba, na gama Magana" yana faɗin haka, ya tashi ya bar mata ɗakin.

Shiru ta yi tana tunanin, meye mafita al'amura na neman su kwaɓe mata, ga Salman na neman bijiro da wata Magana, ga mahaifinsa ya dage baze aurara da Abra yanzu ba, dole ta yi wani abu a kai, dan kar abunda ta ke gudu ya faru, wato Salman ya auri Abra.



Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423  Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal.

Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750
[10/3, 2:40 PM] Abk: Miƙewa Na'ima ta yi ta nufi ɗakin Abra.

Tana kwance idanunta a lumshe cikin damuwa da fargabar yadda Abbinta zai karɓi maganar Adnan, saboda Adnan ya takura mata akan maganar Aure daga daren jiya zuwa safiyar yau, ya sanar mata har ya faɗa wa Abbansa ya ce Next week za su zo tambayar Auranta, ga rashin saka Salman a idonta, tun jiya kafin ya tafi Ball ba su ƙara haɗuwa ba, ta kikkira wayarsa kuma ba ya ɗauka, ga Mr unknown sai Text yake mata na magiyar yana son duk rintsi duk wuya kar ta rabu da shi, soon zai bayyana a gare ta.


"Abra! Abra! Abra!"


Ta tsinkayi muryar Mami a cikin kanta, a hankali ta buɗe idonta tare da tashi zaune cikin sanyin jiki. Zama Na'ima ta yi a gefenta ta ce. "Ke lafiya kike kuwa?"

Numfashi ta sauke ta ce. "Lafiya ƙalau Mami." Taɓa baki Mami ta yi ta ce. "Idan ma akan maganar Aurenki ne ki kwantar da hankalinki tamkar an yi an gama, abun da nake so dake kawai idan Abbinku ya tambaye ki kina son Auren ki ce masa eh, shi ne kawai solution. Gyaɗa mata kai Abra ta yi cikin kunya, mamakin abun take, wai ita ce yau ake maganar za a yi Auranta, abun da ba ta taɓa tunanin yin shi nan kusa ba.


"Yawwa ƴar Albarka, fatanmu kawai Allah ya kai mu lokacin mu sha biki." Na'ima ta faɗa cikin murmurshi tare da dafa kafaɗarta.

Rufe fuskarta ta yi da hannunta tana murmurshin ita ma. Yau kam ta gasgata maganar Salman da yake ce mata Mami tana son ta, for the first time in her life ta goyi bayan abun da take so, kuma har ta zauna tana yi mata magana cikin kulawa da fara'a, hakan ba ƙaramin farinciki da jin daɗi ya haifar mata ba. Kwantar da kanta ta yi akan kafaɗar Mami, wata muguwar harara Na'ima ta gallawa kan Abra, a ranta tana jin tamkar ta shaƙe ta har lahira, amma a fili sai ta shiga shafa kanta.


"Mami yau Salman ya fito kuwa?"

"Wai mene damuwarki ne akan hakan? Tun da kika tashi sai tambaya ta Salman kike, yaro ne shi ko jariri da za a saka masa ido irin haka?"

"Mami may be fa ba shi da lafiya ne." Ta yi maganar kamar za ta yi kuka.

"Lafiyar kenan, don lafiya ita take sa a ji shiru, da wani abu yana damun shi ai da tuni mun sani." Na'ima ta faɗi haka tare da zame kan Abra daga jikinta ta miƙe ta fice.


Bin ta da kallo Abra ta yi, zuciyarta cike da mamakin Mami, yanda Mami take nuna over caring akan Salman da damuwar shi amma yau ta ga kamar ko a jikinta da rashin fitowar tasa, don ɗazu ma a da za su yi breakfast ta ce za ta kira Salman ganin bai fito ba hana ta Mamin ta yi ta ce ta ƙyale shi, cikinsa ne ai ba na wani ba.

Tashi ta yi da sauri ta gyara hular kanta ta fice zuwa ɗakin Salman.


Yana zaune akan bedside drawer hannayensa duka a cikin sumar kansa yana yamutsawa Abra ta yi knocking Kofar ɗakinsa. Ko ba a faɗa masa ba ya san ita ce, kamar ya share ta kamar yadda ya yi mata ɗazu amma sai ya kasa, numfashi ya sauke tare miƙewa ya je ya buɗe ƙofar.

"Bloody what happened to you?" Abra ta faɗa kamar za ta yi kuka.


Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi tare da lumshe idonsa, kaso mafi yawa na damuwa da ɓacin ran da yake ciki ya fara gushewa, sakamakon tozali da kyakkyawar fuskar Angel ɗinsa gami da shaƙar sassanyan daddaɗan ƙamshinta. Juyawa ya yi ya koma ya zauna a bakin gado ba tare da ya ba ta amsa ba.


Ƙara tashi hankalin Abra ya yi ganin yanayinsa kamar yana cikin damuwa, bin bayansa ta yi da sauri ta dafa kafaɗunsa idanunta cike da ƙwalla ta ce. "Faris please talk to me, me ya sa jiya ba ka fito ba? Ko dinner ba ka yi ba, yau ma ba ka yi breakfast ba."

Ganin tana shirin fashewa da kuka ya kama hannunta ya zaunar da ita a gefensa, idanunsa cikin nata ya ce. "Ke ce Angel, kin hana zuciyata sukuni, jiya ko bacci ban iya yi ba." Ya yi maganar cikin tsantsar damuwa.

"Innalillahi! Ni kuma Faris? Me na yi maka?"

Shiru ya yi bai ce komai ba sai hannunta da yake murzawa a hankali tare da sauke ƙananun ajiyar zuciya, bai san ya yi missing ɗinta over ba sai da ya gan ta yanzu a kusa da shi, ba ƙaramin daure zuciyarsa ya yi ba na hana kansa ganin ta ba a jiya, ya kwana cikin ɓacin rai da takaicinta ita da Mami.


"My Faris ka faɗa mini abun da na yi maka mana, tun kafin ka faɗa mun na yi maka alƙawarin ba zan kuma ba, I'm sorry please, ka san bana son ganin ka a irin wannan yanayin na damuna ko?"

"Abra! ashe zaki iya yin Saurayi har ya zo gidan nan ba tare da na sani ba? Ashe akwai abun da zaki iya ɓoye mini a rayuwarki?"




Ƙasa ta yi da kanta cikin rashin ganin kyautawarta, amma ita ta yi hakan ne saboda gudun ɓacin ransa, ashe ta yi gudun gara ne ta tadda zago, kuma ba ta yi tunanin zai sani ba, yanzun ma ta san Mami ce ta faɗa masa.


"I'm sorry Bloody." Ta faɗa cikin raunin murya.

"Hmm, kin san ba zan iya dogon fushi dake ba ne shi ya sa kike mini abun da kika so, babu komai."


"Haba Salman, don Allah kar ka ce haka, kai ma ka san ba haka ba ne."

"Ya ya ne?"

"Bana son ɓacin ranka ne, kai ma ka sani."

Kama haɓarta ya yi ya saka idanunsa a cikin nata dake cike da hawaye, cikin raunin murya ya fara magana. "Angel dama za ki iya tafiya ki bar ni? Dama akwai ranar da za ki bi wani alhalin gani? Please My Baby ki tausayawa ɗan ƙaninki, kar ki bar ni Pleaseee!" Ya ƙarashe maganar da jan harafin ƙarshe cikin wata irin siga.

Lumshe idonta ta yi ba tare da ta shirya hakan ba, ko kaɗan ba ta ɗauki kalaman Salman da wata manufar ba, ta ɗauke su matsayin tsananin shaƙuwar dake tsakinsu ce ta saka ba ya son su rabu. Ba tare da ta buɗe idonta ba ta ce. "Ni ma bana son na yi nesa da kai My Faris, amma ka san ai aure dole ne, watarana dole na y......"


"Na sani Angel, za ki yi aure, amma ba da wani ba." Ya katse ta da faɗin hakan cikin kaushin murya.

Buɗe idonta ta yi tare da waro su waje ta ce. "To da wa zan yi?"

"Da mijinki, wanda yake ƙaunarki fiye da kowa a duniyar nan, wanda ya yi shekaru yana dakon son ki a cikin zuciyarsa."

Murmushi ta yi tare da cire hannunsa daga kan fuskarta ta ce. "To ai shi ne wanda...."

"Ba shi ba ne."

Ɓata fuska ta yi ta ce. "Ta yaya ka sani? Ni ma fa ina son shi." Runtse idonsa ya yi da sauri yana jin tamkar ta soka masa mashi a cikin zuciyarsa, cikin wata irin murya ya ce. "Please Angel kar ki ƙara faɗar haka a gabana."

"Why?"

"Kawai."

"Shikenan, ni mu bar wannan zancen, ka taso mu je ka ci abinci, jiya da ƙyar na iya bacci saboda rashin sanin halin da kake ciki."

"I'm Okay." Ya faɗa a tak'aice.

"Kana son ka gan ni a cikin damuwa ne Faris? Ba ka san yanda nake ji ba idan na gan ka haka, Please ka taso mu je ka ci abinci." Ta yi maganar kamar za ta yi kuka.

Ganin yanda ta nuna damuwarta a kansa sai ya ji wani sanyi a ransa, cikin shagwaɓa ya ce. "Sai dai in zaki ba ni a baki." Da sauri ta ce. "To zan baka, ni dai burina ka ci abincin." Bai ce komai ba sai hannunta da ya kama ya ɗora akan ƙirjinsa, saitin zuciyarsa, yana bin ta da wani irin kallo mai kashe jiki ya ce. "Ji yanda zuciyata take bugawa saboda ke Angel." Murmushi ta yi cikin wautar rashin sanin abun da yake nufi ta yi sama da hannunta ta shafi kuncinsa ta ce. "Ka daina damuwa bloody, ba abun da zai raba ni da kai."

"Sure?"

Gyaɗa masa kai ta yi tare da jan karan hancinsa da ɗan ƙarfi. Ɓata fuska ya yi ya ce. "Kin takura wa hancina Angel, ko dan kin ga ya fi naki kyau ne?"

"No, daɗin ja ne da shi kawai." Ta yi maganar tare da ƙara jan hancin nasa. Murmushi suka yi a tare cikin tsananin shauƙin junansu da suke ji a cikin ransu, daidai lokacin Mami ta turo ƙofar ɗakin da ƙarfi.



Cikin ɓacin rai take duban su ɗaya baya ɗaya, tsayar da idanunta ta yi akan Abra cikin haɗe rai ta ce. "Me kike anan? Wai ku ba za ku taɓa girma ba ne? Goɗai-goɗai dake kin wani taho ɗakin ƙaninki, wanne irin shashanci ne wannan?" Sunkuyar da kai Abra ta yi tare da faɗin. "Ki yi haƙuri Mami."


"Dalla ni ta so ki wuce, tun ɗazu Abbi na neman ki, na je ɗakinki ba kya nan, na jira ko kina toilet amma shiru, dama na san babu inda za ki yi sai nan."


Jiki a saɓule ta miƙe ta fice cikin mamakin yanda Mami ta koma mata sak ta da, kamar ba ita ce ta gama yi mata magana cikin kulawa da ƙauna ba ɗazu.


"Wato ko gaishe ni ban isa ka yi ba ko Salman?"

"Zan gaishe ki mana Mami, na ga kina magana ne shi ya sa, ina kwana?"




"Ban sani ba, ka riƙe gaisuwarka bana so, mara kunya kawai, har ka yi girman da za ka dinga irin wannan abubuwan ko? Yaushe na haife ka? Yaushe na gama goya ka a bayana?"


"I'm sorry."

"Sorry for your self." Ta ƙarashe zancen tare da jan tsaki sannan ta juya ta fita.


Bin bayanta da kallo Salman ya yi, cikin ransa yana faɗin, duk rintsi ba zai rabu da Abra ba, ba gudu ba ja da baya a soyayyar ta."


A parlour Mami ta tarar da Abra a zaune.

"Mami ina Abbin ban gan shi ba?"

"Ya fita zai amso saƙo, tun ɗazu yana ta jiran ki har aka kira shi ya fita." Na'ima ta faɗa ba yabo ba fallasa.

Gyaɗa kai kawai ta yi zuciyarta cike da fargaba, tsoron gamuwa da Abbi take tunda ta Na'ima ta ce ta faɗa masa maganar Adnan, addu'ar ta ɗaya Allah ya sa ya amince. Fahimtar hakan ya sa Na'ima ta fara kwantar mata da hankali, tare da jadda mata ta kafe akan ra'ayinta ko me Khamal zai ce mata.


"Abra burin kowacce Uwa ta gari ta ga aurar da ƴarta, shi ya sa kina mini batun yaron nan na ji daɗi a raina, musamman da na fuskance shi da gaske yake, ba kamar sauran samarin yanzu mayaudara ba, dan haka kar ki bari ya kufce miki, ki riƙe shi hannu bibbiyu."


"Insha Allah Mami na gode." Abra ta faɗa cikin gamsuwa, dan malaminsu na islamiyya ya taɓa faɗa musu cewa duk Uwa ta gari burinta da fatanta ta ga ta kai ƴarta ɗakin Mijinta. Wannan dalilin ya sa yau ta fara kawar da tunanin da Mami ba mahaifiyarta ba ce kamar yadda take tunani a baya. Ganin Salman bai fito ba ya sa ta miƙewa ta shiga ɗakinta don ta kira shi a waya ta lallaɓa shi ya fito ya ci abincin.




Tana ɗaukar wayar ta tarar da 3 missed call na Adnan, bin bayan kiran ta yi cikin sauri. Tana shiga ya katse ya kira ta.


"Amincin Allah ya tabbata ga kyakkywar Amaryata." Abun da ya faɗa kenan bayan ta ɗaga wayar.

Murmushi ta yi tare da zama ta ce. "Tare da kai."


"Ina kika shiga mijinki yana kiran ki ba ki ɗauka ba, na kasa komai saboda rashin jin daddaɗar muryarki mai mantar da ni inda nake."

Dariya ta yi ba tare da tunanin komai ba ta ce. "Na je ɗakin Faris ne."

Shiru ya yi na 2 seconds sannan ya ce. "Faris, Faris dai, magana ɗaya sai kin ce Faris."

"Faris is my best friend, he is my everything at all."


"Ko?" Ya tambaya cikin gatse.

"Yeah." Ta ba shi amsa iya gaskiyarta.


"Ina son na maye gurbin Faris a cikin zuciyarki ko ma na zamo fiye da shi. Now tell me, me Abbi ya ce game da maganata, na san yau Sunday yana gari."


"Mami ta faɗa masa."

"Ya amince?"

"Idon't know, amma duk yanda ake ciki zan sanar maka."

"Allah ya sa mu ji Alkhairi matata, ya nuna mana ranar da za ki kasance mallakina, ban san irin farincikin da zan yi ba a ranar Angel, because I love you will All my heart."

Murmurshi ta yi cikin jin daɗin kalamansa, hira suka cigaba da yi, Adnan na faɗa mata yanda yake tsananin ƙaunar ta, tare da son koya mata ƙaunar shi. Har sai da Mami ta shigo ta kira ta tare da sanar mata Abbin ya dawo.



Cikin faɗuwar gaba ta miƙe ta bi bayan Na'ima zuwa part ɗin Abbi, yana zaune akan kujera suka shiga, Na'ima ta zauna a gefensa Abra kuma a saman carpet ɗin dake shimfid'e a parlour'n.

"Sannu da hutawa Abbi." Ta faɗa kanta a ƙasa.


"Yawwa Daughter, Mamanku ta zo mini da wata magana jiya wadda ban amince da ita ba, ki faɗawa shi yaron da kika kawo shi gidana ba tare da iznina ba ya nemi wata, ke yanzu karatu zaki yi ba aure ba."


Dam zuciyar Abra ta buga, satar kallon Na'ima ta yi, Signa ta yi mata alamun ta faɗi duk abubuwan da ta ce mata.


"Dan Allah Abbi ka yi haƙuri ka amince wallahi ina son sh....."

"Shut up! Ni zan dinga faɗar abun da za a yi kina cewa ba haka ba? Wato har kin yi girman da zaki fara jayayya da ni ko? To na faɗa na kuma faɗa, ba zan yi miki aure yanzu ba karatu zaki yi." Khamal ya katse ta da faɗin haka cikin tsawa.

Kuka Abra ta saka ta fara bawa Abbi haƙuri, bai saurare ta ba ya ce ta tashi ta tafi. Kallon Khamal kawai Na'ima take yi cikin ƙunar zuci, cike da takaici ta ce. "Gaskiya Major abun da ka yi ba ka kyauta ba, wai mene dalilinka na ƙin son aurar da yarinyar nan ne? Ni fa ban gane ba, ko kwaɗata za mu yi mu cinye? Haba yarinya ta fi 20 years amma ka ce ba za ka aurar da ita ba wani karatu za ta yi, karatun me? Ai aure ba ya hana karatu, haka ma karatu ba ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login