Showing 48001 words to 51000 words out of 231718 words

Chapter 17 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

Advertisement

28 Feb 2025

14917

ta buɗe what's app ɗinta, saƙo ne ya shigo, ta buɗe ta shiga dubawa, hotunan Abra ne da shiga kala kala, da kuma wasu hotunan Salima tare da Abra, lokacin tana ƙarama sosai, daga ƙasan hotunan aka rubuta thank you for adopting my Child.

Zaro ido tai tace "What? Khamal ni zaka cuta?" Hannunta ya hau rawa ta saki wayar a ƙasa.

Khamal ne ya shigo ɗakin yana faɗin "My dear, har kin kwanta ne? Gajiyar ce ta hana a zo in da nake yau"

Ya ƙara so yana ƙoƙarin riƙo hannunta, saurin ja baya tai tace "kar ka kuskura ka taɓa ni, tsawon shekaru kana raina min hankali, da na yunƙura zan magana se ka dan kwafar da ni, ka cika ni da daɗin baki, yau ƙarya ta ƙare na gaji"

Cike da rashin fahimta yace "to ai ni sam ban gane akan me kike magana ba"

"Ai dama ba zaka gane ba, tun da ka daɗ kana munafunta ta, meye wannan?" Tai maganar tana miƙa masa wayarta.

Ya karɓa ya kalli hotunan, sannan ya ɗan taɓa baki yace "naga hotuna, sedai ban san daga in da aka samo su ba, na gaji da yi miki bayani, wannan ba ze wuce makircin Salima ba, ni na gaji da yi miki bayani". Ya ƙarasa maganar yana ajiye wayar.

"To Wallahi a wannan karon na gaji da wannan wasan kwaikwayon, ka ɗau 'yarta ka mayar mata, ba zan cigaba da riƙe 'yar Zina ba, se ta bar min gidana"

Khamal yaji tamkar ta soka masa mashi a ƙirjinsa yace "kar ki sake kiran 'ya ta da 'yar Zina, alamu sun nuna min Abra ba ta jin daɗin zaman gidan nan, a gabana ki nuna kina sonta, amma Allah kaɗai ya san me kike mata idan ba na nan, Wallahi Na'ima na kama ki da wani abu na rashin gaskiya akan Abra, Aurena da ke ya ƙare"

"Eh ya ƙare ɗin, se ka Auro Salima ku cigaba da rainon Abran, ko ka kai ka Auri Abran"

Khamal ya ga idan ya tsaya, yana cigaba da sauran Na'ima, za suyi ba daɗi dan haka ya fice ya bar mata ɗakin a fusace.

Salman ne ya shiga ɗakin Mami, ya tarar da ita tana ta bala'i.

Cike da rashin fahimta yace "Mami, wai akan me kike maganganun nan? Kamar fa ji nai kina cewa Babar Abra"

"Eh, Abra ba 'ya ta bace ba ni na haifeta ba? Shekarun baya babanku ya zo min da ita, ya raina min hankali akan cewa tsintar ta yai a daji, ashe haifarta yai shi da wata karuwa, amma ya dinga rainamin hankali, to Wallahi se ta bar gidan nan".

Jikin Salman ya ɗau rawa yace "Maa....ma...mi, kin san ko me kike cewa? Abran ta wa ce karuwa ta haifa? Impossible Mami, Abra 'yar ki ce, mu biyu kika haifa".

"Shut up, ni ban haifeta ba, kai ka ɗai na haifa!!!



LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.
[9/30, 8:55 PM] Abk: *DARE DA DUHU*

Brigh pens✍️
Nimcyluv
Ayushercool
Zee Kumurya

                *P.....13*
Elegant online writers

Domin samun complete litattafanmu, ku yi following ɗin wannan accounts ɗinkin a Arewabooks


https://arewabooks.com/u/nimcyluv
https://arewabooks.com/book?id=




*Albishir ga Makarantar littafan Hausa, ga masu buƙatar bugaggen littafin TSINTACCIYA wato hard copy a satin nan zai fita kasuwa... Wato ya keson mallakar nasa Bugaggen na takarda ya yi magana a wannan number 08119237616*



LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.





Kafin Salman ya gama tantance abunda Mami ke faɗa masa, ya ji saukar muryarta cikin tashin hankali tana faɗin.
"You are my son, not Abra. Abra karuwa ce ta Haifawa Ubanka, ya zo ya ke ci mana amana, Salman, believe me ya fifita son da ya ke maka akan Abra, yarinyar da babu wanda yasan asalin wacce Shegiyar karuwar ce uwarta, Khamal ya raina min hankali Your father hurt us, deceived us"

Ta ƙare maganar tana sakin kuka da ƙarfi, ita kanta bata san lokacin da maganganun suke fitowa da ga cikin bakinta ba, wani irin zafi Zuciyarta ke yi mata, wanda ya sanya ta kasa controlling kanta, har ta kai ta dayin Revealing secrets tonan asirin shekara da shekaru.

Salman zama ya yi kamar wani gunki, ya kasa tantance abunda Mami ke faɗa masa, his thoughts stopped.
Komai nasa ya tsaya, ya kasa yadda ko fahimtar abunda ta ke faɗa akan Abra, shi tsoran Mahaifiyar tasu ne ma ya fara kamashi, ta ya ya zaka haifi ɗa a cikin ka kace wai karuwa ce ta haifa? This is impossible.

Juyawa ya yi a hankali zai fice da ga cikin ɗakin, Mami tayi saurin Miƙewa tsaye, jikinta na rawa ta fisgo Salman baya tare da sanyawa ƙofar key. Salman ya ɗaga idanun shi wanda su kayi jajur, a hankali kuma ya ce.

"You are too tired Mami, za ki samu headache fa, ki kwanta ki huta"
Girgiza masa kai ta yi ta ce  "listen to me Salman, at least listening to your mother Salman, Wlh Allah Abra ba ƴa ta bace, I have nothing to do with her, ban taɓa shayar da ita nono na ba, Everything that happens is your Father's plan, I'm just pretending, na gaji da yadda ya ke fifita ta akanmu da mu ke dolensa"

Tuni jikin Salman ya fara rawa, tunaninsa ya rabu kashi-kashi kowanne da abunda yake faɗa masa, "Salman Mahaifiyarka ce, ba zata yi maka ƙarya ba" wata zuciyar ta gaya masa.
"Salman kada ka yarda daman can Mami ba son Abra take ba, tana nuna masa rashin so irin na ɗan fari ne kawai"

A raunane yace "Mami ke fa Uwa ce? Ta ya ya zaki dinga sheganta ƴar da ki ka haifa? Me Yaya tayi maki Maki? You don't love her, that's all, but stop harassing her ki dai na sheganta ta don Allah"

Da Mamaki Mami tace.
"Salman kana tunanin zan maka ƙarya? Mene yasa kai ban ce bani na haifeka ba? Mene yasa bance ban shayar da kai nono na ba? Mene yasa ban sheganta ka ba? Because you are my son, my blood, biological son. Kai na ɗauki cikin ka, naji zafin haihuwar ka, na raineka. kasan akan Abra nayi haihuwar da ban shirya ba? Na haifeka saboda bala'i a kitchen, Gaba ɗaya Abra ta ɗauke min wani jin daɗin rayuwa da farin ciki? Tun kana cikin cikina na fara samun matsala da mahaifinka, shiyasa na ke ta ƙoƙarin nesanta ka da ita, kai ɗan sunna ne ka daina haɗa kanka da ƴar karuwa.....,"

"Mami!!!!!!"
Salman ya faɗa jikinsa ko'ina rawa yake, ya kasa ɗaukan maganganun ta wanda suke neman haukata masa ƙwaƙwalwa, saboda muninsu. Cikin rawar Murya ya ce.
"Ba zan yarda ba, Yaya ƴar kice kamar yadda nake ɗan ki, that's all"
Mami ta kalli Salman sosai ta ce "Kana nufin zan maka ƙarya Salman?" Shiru ya yi mata kansa a ƙasa amma idanunsa sunyi jaa sosai sai numfashi yake fitarwa, ji yake kamar mafarki ya ke.

"Kana tunanin zan maka ƙarya, kaf dangina da na mahaifinka da wa ka ga ta na kama? Akwai me irin siffarta?" Salman dai ya yi shiru, kansa na ƙasa bawai bai yarda bane, gaba ɗaya bashi da nutsuwar fahimtar Maganar tata.
A zafafe Hajiya Na'ima tace "Answer my questions Salman Khamal Khamis?"  Salman ya ɗaga kansa tare da kallon Mami a hankali ya ce. "Ban ƙaryata ki ba Mami, na kasa yadda ne kawai...,"

Ɗauke shi tayi da ƙyakƙyawan mari tace "Ni nayi kuskure tun farko, to kaje duk uban wanda zaka tambaya kaje ka tambaya Abra Shegiya ce, Abra TSINTACCIYA ce, Abra ƴar karuwa ce...!!"
Tana faɗin haka ta koma saman gado ta zauna, Da sauri Salman ya nufi ƙofa zai fita.

"Salman"
Mami ta kira sunansa da ƙarfi, kiran da ya sanya ya yi saurin juyawa tare da kallon direction ɗin da take zaune, da hannu tai masa nuni da ya zo.
Bai mata musu ba ya Ƙarasa wajanta kansa a ƙasa, hannunsa ta kama muryarta na rawa tace.

"This is an secret between us, ba wai dan ba ni da gaskiya ba, saboda ina son in kasance da kai da kuma Mijina, idan ka faɗawa wani ko wata cewa ni na faɗa maka, Mahaifinka zai datse igiyar auren dake tsakaninmu, I don't like that Salman, I love my husband, i so much love your father shi ya sa nake ta zaune har yanzu, sannan ina fatan za ka nesanta kan ka da ga wannan yarinyar"

Kallonta kawai Salman ke yi, bai taɓa ganin Mami na kuka ba sai yanzu, mene gaskiyar Al'amarin? Ta shi ya yi jiki a sanyaye sai da ya je bakin ƙofa Mami ta ce.
"Ka saka a ranka, ba zan taɓa so da ƙaunar Abra ba, ina kishinta sosai kishin kuma akan ka ne, duk wani plan da muka shirya da Khamal akanka ta wargatsa, She take away my happiness, she destroyed my house, to the extent ta fini kima a idon mahaifinka"
Tana faɗin haka ta saki kuka sosai, gaba ɗaya matar data kirata a waya ta gama wargatsa mata lissafi.

Da sauri Salman ya bar cikin ɗakin jikinsa na ɓari, ko Kallon gabansa ba ya yi tashin hankali ya bayyana akan fuskarsa, yana zuwa ɗakinsa ya faɗa kan gado tare da jan duvet ya lulluɓe jikinsa, wani irin zazzaɓi mai zafi ya rufe shi, he can't believe cewa Abra ba ƴar Mami bace, har yanzu ya kasa yarda ko kuma fahimtar hakan.
Shiru ya yi haƙoransa na haɗuwa waje guda, ya zama kamar wani zautacce, ya kasa yadda, bacci ya ƙauracewa idanunsa how could he believes that Abra ba sister ɗinsa ba ce, yadda ya ke jin ta a ranshi, ya sa maganganun Mamin su ka kasa tasiri a zuciyar sa, sai dai kuma ko me za'ayi ba zai taɓa yadda Abra karuwa ce ta haifawa Abbi ita ba, bacci ɓarawo shine ya sace Salman cikin dare.

Gefen Hajiya Na'ima kuma, daren black night ya zame mata, Babu wanda ya yi baccin kirki sai Abra. Wacce ake ta Masifa a kanta, she slept peacefully, ba ta san me yake faruwa ba.

Gajiyar da Abra ta yi, bai hana ta tashi tun 7 na safe ba ta fara gyara gidan, ba tai Mamakin yadda ta ji gidan shiru ba, Faris ne kawai ya tsaya mata a rai, domin tasan da wuri yake fitowa ta yata aiki.
Tana tsaye a kicthen, sanye da pech ɗin pyjamas ta ɗora hijab akai, wuƙa ce a hannunta tana yanka Onion  With red pepper wanda Zatai using da shi, wajan yiwa Abbi ƙosan da yake so. Few minutes ta gama haɗa ƙullin ƙosan da ya sha kayan ƙamshi da Egg.
Tana gama soya ƙosan, ta ɗakko malkaɗɗan ƙullinta na kunun gyaɗa, wanda ya sha haɗin, Danyar gyaɗa, Dafaffiyar
shinkafa, sugar, madara, Leman tsami, Filawa. 15 minutes to 20 ta kammala kunun gyaɗar, tana gamawa ta haɗawa Salman Smoothies. Haɗa komai ta yi akan dining table, zuciyarta fal tunanin abinda ya hana Salman fitowa.

Cikin sanyin jikin nan nata, ta yi wanka ta shirya cikin wata blue ɗin Abaya mai stones, ta yi rolling kanta da Vail ɗin, Oval shape face ɗin ta, ya sake fitowa kyanta na ƴan matanci, ya bayyana a fili da Wahala mace ta kalli Abra bata sake Kallonta ba, balle kuma namiji. Ƙyakƙyawan idanunta ta ja ta rufe tana jin yadda hearing aid ɗin nan sometimes yake damunta.

Flat shoe ta saka ta nufi Main Parlour, amma ga Mamakin ta har zuwa lokacin babu kowa a parlourn, da fararen idanunta take bin cikin wajan dining table da kallo, a nutse ta nufi bedroom ɗin Salman domin tabbatar da lafiyarsa.
A hankali ta tura ƙofar ɗakin, Salman na kwance har lokacin idanunsa biyu, bawai barci ya ke ba, Ƙamshin turarenta kawai ya shaƙa wanda ya tabbatar masa Yayarsa ce, da sauri ya rufe idanunsa yana ƙara narkewa jikin bargon daya rufe jikinsa da shi.

Abra ta kalli Salman, cikin sanyin murya ta ce."You haven't woken up yet?" Ƙara rufe idanunsa Salman ya yi.

"Faris"
Abra ta ƙara kiran sunansa tana yaye bargon daya lulluɓe jikinsa da shi, Shiru ya sake yi ma ta baya son ko haɗa idanu ya yi da ita. Kamar Abra za ta yi kuka ta ce.
"Please Faris wake up, It's already morning"
Ta faɗa a sanyaye kamar mai raɗa. Tana ƙoƙarin zare bargon da ga jikinsa baki ɗaya, Salman ya yi saurin riƙewa tare da juyowa baki ɗaya zuwa inda Abra take zaune.

Kallon juna su kayi, shi dai bai Magana ba, sai bin ta da ido da yake. Abra ta ce.
"Barcin me kake haka?"
Idanunsa ya mayar kan hannunta data riƙe bargon, sai kuma ya ware idanun shi ya ce.
"Yaya.."
Abra ta kwaɓe fuska ta ce "Ba wani yaya, kawai ka je kayi wanka sai muyi breakfast, ka ga yau har Smoothies na yi maka"

Salman ya Girgiza kai idanun shi a ƙasa yana kallon hannunta ya ce.
"Ba wannan ba yaya" "to mene?" Abra ta faɗa da ɗan sauri ganin gaba ɗaya Salman baya cikin mood ɗin sa, langwaɓar ma ta da kai gefe ya yi cikin ƙasa da murya ya ce.
"Have you forgotten?"
Ta ware idanunta, sai kuma ta ce "Na manta"
Murmushi kawai ya yi ma ta yana Girgiza kansa da ke masa ciwo.
Ganin ya yi shiru kuma ba shi da alamun mgn Abra ta ce "Kayi shiru?"
"A'a ba komai yayata"
Ta ce "to tashi ka yi wanka" ya dafe kansa ya ce
"Ke yaya wannan wankan kamar ibada, kai na kemin ciwo sosai, sanyi-sanyi na ke ji"

Jikin Abra na rawa ta ce.
"You're sick Faris? Me ke damunka? Kayi wanka bari na kawo maka breakfast nan, sorry ƙanina" ɓata fuska Salman ya yi
"Yaya wai dame kika fini ne?" Abra ta ce "kamarya?"
Ya Girgiza ma ta kai yana rufe idanu Calmly ya ce "Nothing!!"
Shiru gaba ɗaya suka yi, Abra har ranta take jin babu daɗi, bata so ko kaɗai Faris ya yi ciwo musamman yanzu da taga idanun shi ya yi jaa, ta ƙara tabbatar da ciwon kai ya ke sosai.

"massage my head Angel"
Zama ta yi a gefen gadon idanunta a kansa tana kallon fuskarsa mai kama data Maminsu sak, a hankali Salman ya kwanta yana ɗora kansa a cinyar Abra, cikin nutsuwa Abra take masa massage ɗin yatsun hannunta gaba ɗaya a cikin sumar kansa wanda ya ke saman cinyarta, bayan ciwon kai hadda zazzaɓi.

"Faris"
"Uhm Angel Abbi's daughter, alfaharin Faris"
A sanyaye Abra ta ce.
"I love my mother Faris, I want to be with her"

Da sauri Salman ya tashi zaune ya ce.
"Mene yasa kike son damun Kan ki ne har haka yaya? Nifa idan kina cikin damuwa wlh na fi ki shiga damuwa, na faɗa maki komai lokaci ne, ita fa Mami karar ɗan fari take maki, amma kullum muka haɗu da ita sai tace min tana sonki, tana alfahari dake.. Mami loves you more than me"

Idanun Abra na cika da hawaye ta ce "da gaske ka ke Faris? da gaske Mami tana so na?"
Kai kawai ya ɗaga ma ta, yaƙi yarda ya kalleta, yana tuna maganganun Mami na jiya, masu ɗaci da tsayawa a rai.
Miƙewa ta yi ta ce "to kayi wanka ka fito yanzu ko?" Kai ya ɗaga ma ta kawai, ita kuma ta fita a hankali yabi bayanta da kallo.

Abbi ta samu zaune saman dining table hannunsa riƙe da mug yana shan kunun gyaɗa, da idanu ya bita a kullum mmki da girman Abra yake, har tsoran kyanta ya ke.
"Good morning Abbi"
"Mrng Abbin's daughter"
Zama ta yi tana haɗa tea ta ce "Abbi yau kun makara, Mami bata fito ba?" Murmushi ya yi mata yana ajjiye mug ɗin hannunsa ya ce.
"Na tashi, ina duba wani abu a system, Mami bata jin daɗi. Ina ƙanin naki?"

Abra ta marairaice fuska kamar zatai kuka ta ce.
"Abbi Faris ma baya jin daɗi, ka kira masa doctor ya duba sa shi da Mami"
Abbi ya ɗan yi Murmushi ya ce "My dear, Salman namiji ne, ba mace kamarki ba. Shi ya sa yake raina ki komai na kuka ne a wajanki?"

Abra ta ce.
"Abbi da Salman kawai nake hira fa, idan ya kwanta ciwo bana jin daɗi sai na ji zazzaɓi ya kamani" cike da tausayawa Abbi ya ke kallon Abra.

Kafin ya yi magana Salman ya fito cikin tattausan farin yadi mai kyau irin na Abbinsa, sai ƙamshi yake abinka da farin bafulatani ya yi wani irin kyau. "Mrng Abbi, yaya haɗa min tea pls cikina"
Da sauri Abra ta shiga haɗa masa tea ɗin tana faɗin "Sorry Faris, sorry" Abbi ya kalli Salman ya ce "Ya jikin?" A hankali ya ce "felling much better Abbi" amsar tea ɗin hannun Abra ya yi ya fara sha, sai da ya shanye tas. Kana ya sha Smoothies ɗin da dankali.

"Abbi bari na duba Mami"
Abbi ya ce "a'a kiyi zamanki, ta sha magani barci ta ke" Salman dai bai ce komai ba. Da ga ƙarshe ya miƙe tsaye Abra ta ce
"ina zaka?" Ya ɗan kalleta ya ce "Yaya ki koyi zama ke ɗaya fa, ni da ba mace ba nayi ta zama a gida"
ta marairaicewa ta ce "Abbi ka ji shi ko?" Abbi ya ce
"Ina jinsa, but he's right kada ya zama namamajo" nan da nan idanunta ya cika da hawaye Salman ya matsa kusa da ita yana ma ta dariya ya ce.
"To kawai ki yadda ni ne babba sai in dinga zama kullum a gida" da sauri ta ce
"Na.... Na yarda pls Faris gidan babu daɗi fa" ya ɗaga ma ta gira yana gyara zaman hular kansa ya ce "Sorry Angel, yanzu zan dawo wani abokina zan duba"

Miƙewa tayi ta ce.
"To zan rakaka, kaga sai ka rakani Saloon ko?" Ya ce
"kada muyi haka dake yaya, ke ba matata ba, ke ba ƙawata ba, duk inda zani kice zaki yanzu zan dawo"
Abra ta saki kuka kamar ita ce ƙarama ta ce.
"Pls Faris ai ba zan bika ciki ba, kawai a waje zan tsaya sbd kada ka daɗe"
Salman ya ce.
"Ki zauna a waje yaya? Kuma ke sai ki zauna ɗin baki san mace sirri ba ce?"

Sai a lokacin Abbi ya saka baki cikin maganar ya ce.
"Ƙyaleshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login