Showing 141001 words to 144000 words out of 231718 words
Chapter 48 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
mutuwar Malam tana da sanadi, har abada ba za mu taɓa mantawa da asibitin nan da mara mutuncin likitan da ya ƙi zuwa ya duba Malam ba, saboda Ubangiji ya ba shi dama sai ya yi amfani da ita ya dinga wulaƙanta talakawa marasa ƙarfi, maimakon ya yi amfani da ita ta hanyar da za ta kai shi ga shiga aljanna. To insha Allahu a dalilin wannan wulaƙancin nasa sai ya yi da na sani da nadama watarana, insha Allahu sai ya yi kuka da idanunsa."_
A jiya bayan mutuwar tsohon da Jamila ta dinga yi masa nacin ya je ya duba shi ya sauka ƙasa da niyyar fita ya ji tsohuwar tana wannan maganganun cikin kuka ta window'n baya na emergency room, a lokacin murmushi kawai ya yi ya wuce, cikin ransa yana mamakin ƙarfin hali irin na talaka, shi bai biya kuɗin da za a duba mara lafiyarsa ba kuma ya dinga masifa don ba a duba shi ba. Sai dai me? A lokacin da ya zo bacci sai maganganun nata suka dinga yi masa amsa kuwwa, tamkar a lokacin take faɗar su. Yau ma yana tashi ya ji maganar tsohuwar tana dawo masa, abin ya ba shi mamaki ba kaɗan ba, don ba wannan ne karon farko da aka taɓa jifan shi da miyagun kalamai ba, waɗanda suka fi wannan muni ma, amma ko kaɗan ba sa damun shi, tunda ya san a kan aikinsa yake.
Tsaki ya ja tare da jan numfashi ya ɗan buga table ɗin gabansa, cikin takaici da haushin zuciyarsa da ta damu da maganganun tsohuwar har take ƙoƙarin jefa shi cikin damuwa. Buɗe ƙofar office ɗin da aka yi tare da sallama ya saka shi buɗe kyawawan idanunsa.
Amsawa ya yi yana bin ta da kallo, Nurse Jamila ce. Cikin girmamawa ta ce. "Barka da yamma Doctor." Gyaɗa mata kai kawai ya yi.
"Doctor ɗan gidan Senator shattima aka kawo, asthma ɗinsa ce ta tashi."
Kafin ta gama rufe baki ya miƙe cikin sauri tare da faɗin. "Subhanallahi! Maza-maza akai shi V.l.p room, ki sanar da Doctor Jibril da Lukman su je su ba shi taimakon gaggawa, ga ni nan zuwa yanzun nan."
"Ok Doctor." Ta faɗa tare da juyawa ta fice, zuciyarta cike da tsananin mamakin halin Bulama, yadda yake rawar jiki saboda an ce an kawo ɗan masu hannu da shuni, sai ta tuno jiya bala'in da ya dinga yi mata kamar zai cinye ta ɗanya akan yunƙurin allurar da taso yi wa tsohon da ya rasu, a lokacin ma kuka take yi na tausayin bayin Allan, amma bai damu ba ya dinga zazzaga mata masifa tare da gargaɗin kar ta ƙara yi masa irin haka, ita ba ta ma san wa ya faɗa masa ba.
Tafiyarta, maganarta da yadda ƙwayar idonta ta juye zai saka a kallo ɗaya idan an yi mata a gane cikakkiyar ƴar shaye-shaye ce. Tafiya take cikin rangaji kamar za ta faɗi, Abdul dake cikin Motar yana kallon ta zuciyarsa cike da mamakin yadda cikin lokaci ƙanƙani ta saba da shaye-shaye over, ko wanda yake harkar shekara da shekaru ba zai nuna mata yawan shan abubuwan maye a kullum ba. Domin ta mayar da su tamkar ruwan shanta da abincinta. Yanzu kullum da sassafe take ficewa, ba ta dawowa kuma sai dare. Weekend ne kawai idan Bulama yana nan take takatsantsan. A haka ta shiga part ɗin Hajiya Saudat.
Tana hakimce akan kujera ta miƙe ƙafa ɗaya daga cikin masu aikin gidan tana mammatsa mata, wata kuma na yi mata firfita da mafici na alfarma tamkar wata sarauniya, duk kuwa da air conditioner ɗin dake parlour'n. Sai wata dake yayyanka mata fruits tana ɗauka tana ci kamar ba ta so, idanunta a kan plasma TV tana kallon wani Indian film.
Yadda Meenal ta buɗe ƙofar parlour'n da ƙarfi ya sa su kallon wurin cikin sauri, tana ɗan tangaɗi ta ƙaraso ta zauna a kusa da mahaifiyarta. Wata irin faɗuwar gaba ce ta riski Hajiya Saudat, cikin tsananin kaɗuwa take bin ƴar tata da kallo. A fusace Meenal ta ce wa masu aikin. "Uban me kuke kallo haka a jikina? Kun wani zuzzura mini ido kamar baƙaƙen Mayu? Ku tashi ku bar parlour'n nan!" Ta yi maganar cikin ƙaraji da tsawa. Ko gama rufe baki ba ta yi ba suka miƙe sum-sum suka fice.
"Mene haka Meenal? Warin me nake ji yana tashi a jikinki?" Hajiya Saudat ta tambaya a firgice.
Cikin maye ta ce "Don't worry Mom ba wani abu ba ne, I just......." Ba ta ƙarasa ba Hajiya Saudat ta ɗaga hannu da nufin wanka mata mari, ko me ta tuna sai kuma ta fasa ta yarfar hannun gefe ta shiga girgiza kai tana faɗin. "Na shiga uku! Shaye-shaye kika fara Meenal? Me zan ce wa mahaifinki idan ya gano hakan? Wa ya jefa ki a cikin wannan mummunar rayuwar, ko ma waye ya cuce mu, ki faɗa mini waye? Wallahi sai na yi shari'a da shi tunda ya gurɓata mini rayuwarki." Meenal da ba ta fahimtar abin da take cewa ta miƙe tare da faɗin. "Oh Mom, ya kike faɗa haka kamar haushin kare? Ko Dad ne ya ɓata miki rai? In shi ne kawai ki ɗan mazmazge shi...." Cikin takaici Hajiya Saudat ta lailayo ashar ta ƙunduma tare da fashewa da kuka, tana yiwa wanda ya ɓata mata rayuwar ya Allah ya isa, maimakon ta yi wa ƴar tata addu'ar neman shiriya.
Upstairs Meenal ta nufa, ta zo daidai ƙofar kitchen ta shaƙi ƙamshin farfesun kifin da Hajiya Saudat ta saka a yi mata, da sauri ta toshe hancinta saboda yadda ta ji ƙamshin ya hautsina mata ciki, ta ji ba ta ƙaunar sake shaƙar shi. Lokaci ɗaya ta ji amai ya taho mata, hakan ya sa ta durƙusawa ta fara kelaya shi a nan tsakiyar parlour'n. Da sauri Mommy ta yi kanta ta riƙe ta tare da faɗin. "Ba ki da lafiya ne Daughter? Sorr...." Kasa ƙarasa abin da ta yi niyyar faɗa ta yi, sakamakon lura da wani irin fari da ɗashewa da Meenal ta yi, ƙirjinta ya cika tam kamar zai faso ɗamammiyar rigar jikinta ya fito. Waro ido ta yi tare da faɗin. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un! Na shiga uku ni Saudat! Me yake shirin faruwa da ni ne?"
Zaune take a kan darduma ta ɗaga hannayenta sama idanunta na zubar da hawaye, a fili take faɗin. "Ya Allah kai ne Sarkin kowa da komai, kai ka yi rayuwata a haka, Allah ka sassauta mini ka ba ni ikon cinye dukkan jarabawar dake cikin rayuwata." Ta ƙarashe addu'ar tare da fashewa da kuka, cikin ranta tana hoping a ce duk wannan abubuwan da suke faruwa mafarki take yi, za ta farka ta gan ta a gidan Abbinta sun cigaba da rayuwa da Faris ɗinta cikin farinciki da jin daɗi. Wani irin tuƙuƙi take ji a cikin ranta, a yanda take jin zuciyarta tamkar za ta buga saboda tsananin damuwa da tashin hankali. Ba ta taɓa tunanin za ta riski irin wannan damuwar a cikin rayuwarta ba, ko da wasa aka ce Adnan zai aikata mata haka za ta ƙaryata, duba da tarin soyayya, kulawa da tattalin da ya nuna mata kafin Aurensu. A hankali take jin tsanar shi na maye gurbin tarin ƙaunar da take masa a cikin zuciyarta. Sai a yanzu ta gane tana tsananin so da ƙaunar Faris, so irin na aure ba na ƴan'uwantaka ba. Abin da ya sa ba ta gane hakan ba tun farko saboda rashin sanin Salman ba ɗan'uwanta ba ne na jini.
"Ya Allah!"
Ta furta a fili cikin bugawar zuciya, ta rasa ma tunanin me za ta yi a matsayin abin da yake damun ta. Tabbatar mata da Abbi ya yi ita ba ƴar cikinsa ba ce ba ta da asali kamar yadda Adnan yake yi mata gori kullum ko kuma tunanin rashin masoyi na haƙika da ta yi? "Why Faris? Me ya sa ba ka bayyana mini soyayyar ka ba? Why Bloody? Kai nake so! Kai nake son kasancewa da kai har ƙarshen rayuwata, don Allah ka dawo gare ni Pleaseeeee!" Ta ƙarashe maganar tare da ɗora kanta a kan abin gado ta shiga bubbugawa. A hankali ta dinga furta "Astagfirullah." Saboda tunawa da ta yi da aurenta bai kama ta dinga tunanin wani namijin ba, duk da ta san hakan ƙaddararta ne, kuma har ta koma ga mahaliccinta tunanin Salman ba zai taɓa barin zuciyarta ba.
Rarrafawa ta yi a hankali ta ɗauko alƙur'ani ta buɗe da niyyar karantawa don samun sauƙin damuwar dake cikin zuciyarta. Sai dai babu abin da idanunta suke iya gane mata daga cikin rubutun alƙur'anin, duk yadda taso cizewa ta karanta amma abu ya gagara, wani irin ciwo take ji ƙirjinta yana mata gami da juyawar kai. A dole ta ajiye alƙur'anin ta ɗauki drugs ɗinta ta sha ta kwanta. Ko 30 minutes ba ta yi da kwanciya ba aka buɗo ƙofar ɗakin aka shigo, ko a faɗa mata ta san waye, ƙamshinsa da a yanzu take jin shi tamkar ɗoyin kashin shanu ya ƙara tabbatar mata da haka. Gyara kwanciyarta ta yi tare da ƙara runtse idonta. Cikin taƙama ya ƙaraso gadon ya yaye duvet ɗin da ta lulluɓa, fuska a murtuke ya ce. "Where is my food?" Kamar ta share shi sai kuma ta taɓe-taɓe baki a ranta tana faɗin. 'Acici' Buɗe idonta ta yi da ƙyar ta dube shi, cikin raunin muryar dake nuni da tsantsar damuwar da zuciyarta take ciki ta ce. "Yana kitchen."
"To da kaina zan zuba ko azzalumin ubanki zan kira ya zuba mini?"
"Na faɗa maka ka daina zagin mahaifina a gabana, don ni ko a yaya yake ina son shi a haka, sannan kuma ba zan iya tashi ba saboda bana jin daɗi." Ta yi maganar cikin ƙarfin hali.
A fusace Adnan ya riƙo gashin kanta cikin mugunta tare da faɗin. "Weldone TSINTACCIYA, mara asali da 'yanci, ke har kin isa ina magana kina musa mini, wato kin waye wuyanki ya isa yanka? Who are you? Kin yi kaɗan wallahi!" Fizge kanta ta yi saboda wata irin azaba da ta ji tun daga kanta har tafin ƙafarta, cikin kuka ta ce. "Wanne irin azzalumi ne kai mara imani da tausayi?" Dariyar rainin hankali ya yi ya ce. "Is your father, duk waɗannan abubuwan da kika lissafa halinsa ne ɗabi'arsa ce. Abra Khamal Khamis! Ko kashe ki na yi ban yi kwatankwatan zaluncin da mahaifinki yake aikatawa ba." Za ta kuma magana ya katse ta cikin tsawa da faɗin. "Za ki tashi ki yi abin da na saka ki ko ya?" Cikin kuka ta miƙe jiri na ɗibanta ta fice, har faɗuwa ta yi, amma ko a jikinsa. Bayan ta zuba masa abincin ta ajiye masa ya ce sai ta dafa masa coffee, ba ta yi musu ba ta dafa ta kawo masa cikin matuƙar dauriya da ƙarfin hali. Bayan ta koma ɗaki ta kwanta ta samu bacci ya ɗauke ta da ƙyar, amma Adnan ya zo ya katse mata baccin da buƙatar gangar jikinsa, cikin rashin imani da tausayi kamar yadda ya saba zuwar mata kodayaushe.
Na'ima ce kwance a kan katifa idanunta a lumshe amma ba barci take ba, tunanin yadda za ta shawo kan Khamal ya haƙura ya mayar da ita ɗakinta kawai take. Idan ta tuno yanayinsa a lokacin da suka rabu sai ta ji gabanta ya yanke ya faɗi, saboda sanin da ta yi indai yay irin wannan fushin saukowar shi sai an ci ƙwaƙwa. Ba ta taɓa da na sanin tura Salman China da dagewa akan Auren Abra ba sai yanzu, don da suna nan ta san da yanzu tana gidanta, ko da Khamal ya sake ta ba zai kore ta daga gidansa ba, saboda gudun kar su Abra su shiga cikin damuwa, don idan akwai abin da Khamal ba ya so a duniyar nan bayan fushin iyayensa sai ganin ƴaƴansa a cikin damuwa. Cikin haka Nepa suka yi tsiyar su suka ɗauke wuta, hakan ya sa sauro ya fara shawagi. Tsaki Na'ima ta ja tare da yin juyi tana kore sauron dake yi mata kuka a cikin kunne. Ba ta kai ga sauke hannu ba wani ya millira mata cizo a gefen kunne, hakan ya sa ta tashi zaune ba shiri ta janyo wayarta ta kunna torchlight. Cikin mamakin take kallon Aunty Suwaiba dake baccinta hankali kwance, jinjina kai ta yi don ta san ita kam baccinta a haka ba zai yiyu ba in dai ba Nepa aka dawo da ita ba, ga wani irin zafi da ya rufe ta lokaci ɗaya. Gabaɗaya ta rasa sukuni, ta rasa inda za ta saka ranta. Baƙin ciki kamar ya kashe ta, ga sauraye sai watanda suke yi a jikinta. Ita kuma ba ta son maganin sauro balle ta kunna, mura yake saka ta. Wannan daren dai cikin wahala ta yi shi, sai washegari bayan Sallar Asuba ta samu bacci ya ɗauke ta.
After 2 days
Hajiya Na'ima ce tsugunne a gaban mahaifiyarta tana kuka tare da faɗin. "Kullum sai na kira shi sau ba adadi Mama amma ba ya shiga, na san kuma blocking ɗina ya yi, ko na yi masa text ma ba zai gani ba." Cikin damuwa ta ce. "Lallai ma yaron nan, wato shi ba ya uzuri a rayuwa ko? Bai san kuskure ba, ai ko Ubangijin da ya halicce mu muna saɓa masa kuma ya yafe mana. Amma ba komai, ba ni numbern Mahaifiyarsa mu tafi plan ɗinmu na biyu, in ya san wata ai bai san wata ba. Cikin rawar jiki Na'ima ta lalubo numbern Ammi ta yi dialling ta miƙa wa Mama wayar bayan ta shiga. Don ba ƙaramin gajiya ta yi da zaman gidan nasu ba, kullum cikin faɗa suke da Aunty Suwaiba, ga Faisal dake yi mata rashin kunya son ransa, saboda yana cike da haushin hana shi auren Abra da aka yi. Ga tattalin arziƙinta na neman ƙarewa a ɗan zaman da ta yi na kwana huɗu, ita ce sayan abincin gidan da kuɗin cefene, don Faisal daina bayarwa ya yi, ya ce tunda ta dawo gidan sai ta cigaba ita ma. Har ƙaton Gen. ta siya saboda ba za ta iya rayuwa cikin sauro da zafi ba, ga shi Mama kullum cikin cewa ta yi mata kaza ta saya mata kaza take. Gabaɗaya ta rame ta yi baƙi saboda damuwa da rashin kwanciyar hankali.
Ammi tana ɗakin Baffa tana yi masa tausa a lokacin, kiran Na'ima ya shigo wayarta. Miƙewa ta yi ta ɗauko wayar, ganin Na'ima ce ya sa ta faɗin. "Alhaji ka ga ƴar halak, yanzun nan na gama zancen su ita ƴarta, na ce kwana biyu shiru ba mu gaisa ba, duk da ita Abran Babanta ya ce wayarta ce ta samu matsala." Ta ƙarashe maganar tare da daga wayar ta kara a kunnenta tare da yin sallama. Daga can Mama ta amsa mata, cikin mamaki Ammi ta ce. "Au Hajiya ke ce? Ina Na'iman?"
"Tana nan ƙalau, daga yanda na ji maganarki da alama ba ku san abin yake faruwa ba."
"Me ya faru kuma? Allah ya sa dai lafiya?" Ammi ta tambaya a ruɗe.
Sanar da Ammi sakin Na'iman ta yi. Cikin jimantawa Ammi ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un! Subhanallahi! Baban nawa ne ya aikata haka? Da k'uruciya ma bai yi haka ba sai yanzu da girma ya fara kama su har an kai 'ya ɗakin miji? Wallahi ba mu sani ba bai sanar mana ba."
"To dai yau kwananta huɗu a gida, abin dai ba daɗin ji."
"Ku yi haƙuri Hajiya, insha Allahu za a daidaita tunda saki ɗaya ne, bari in kira shi yanzu."
"Tom shikenan Hajiya mun gode, sai na ji ki."
Bayan sun gama wayar Ammi ta kira layin Abbi, ta yi masa har 2 missed call amma bai ɗaga ba. Baffa dake sauraren duk abin da suka tattauna ya ce. "May be yana wani uzurin ne, idan ya gama na san zai kira, sai mu ji gaskiyar abin da yake faruwa." Ammi ta ce. "Haka ne, amma wannan abu bai daɗi ba ko kaɗan."
"Allah ya kyauta kawai." Cewar Baffa cikin jimantawa.
Kwance take a kan gado ta lulluɓe jikinta da bargo, fuskarta ce kawai a waje ta ƙura wa wuri ɗaya ido, ga dukkan alamu sana'ar tata take yi wato tunani. A haka Adnan ya shigo ɗakin ya same ta ba tare da ya yi sallama ba, uniform ɗinsa na police guda biyu ya watsa mata a jikinta, cikin ba da umarni ya ce. "Gashi nan ki wanke mini su yanzu-yanzu." Kallon kayan ta yi ta kalle shi ba ta ce komai ba, don ko magana ba ta son yi, saboda tarin damuwar dake cikin ranta, ga shi yau ta tashi ba ta jin daɗin jikinta, gaɓoɓin jikinta duka ciwo suke mata, ga ciwon kai da idan ana sabo da shi ta saba da shi, ga wata irin kasala da take ji.
"I'm talking to you Madam!" Adnan ya faɗa cikin tsawa tare yin kanta.
Cikin ɗaga murya gami da kuka ta ce. "Ba zan yi ba, idan ka tashi ka kashe ni, haba! Na gaji da wannan azabtarwar taka Adnan, ka yi mini duk abin da ka ga dama!" Ta ƙarashe maganar tare da tashi zaune ta ɗauki uniform ɗin nasa da niyyar ta cillar da shi, hakan ya sa ƙamshinsa dake manne a kayan bugar hancinta, da sauri ta saki kayan tare da toshe hancinta, don wani irin hautsinawa ta ji jikinta ya yi mata lokaci ɗaya. Dama tunda ya shigo ta shaƙi ƙamshin ta ji kamar za ta yi amai. Cikin masifa ya buɗe baki da nufin zazzage mata kwandon bala'i, miƙewar da ta yi cikin sauri kamar wadda aka tsikara ya hana shi abin da ya yi niyya, sakamakon ganin ta nufi toilet a guje ta fara kelaya amai kamar za ta amayar da kayan cikinta.
It's not for free, contact us for more information. 09047871750
[10/24, 12:28 PM] Abk: Ta daɗe tana aman, sannan ta fito gaba ɗaya gaɓoɓinta sun saki, saboda yunƙurin amai. Ko da yake ba sabon abu bane a gurinta, dan haka kan faru da ita lokacin period ɗin ta.
Ba ta ko kalli Adnan ba, ta wuce ta fara ƙoƙarin hayewa kan gado.
"Wai me kika