Showing 102001 words to 105000 words out of 231718 words

Chapter 35 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14710

Salman ɗinki."

Cikin farinciki ta ce. "Dagaske?"

"Eh mana, mene a ciki, duk abun da zai saka ki farinciki kome ne zan yi miki, kin wuce haka a gurina."

Ajiyar zuciya ta sauke cikin jin daɗi, cikin murna ta ce. "Thank you."

"Don't mind Dear, bari na saka kaya, fitowata kenan daga wanka kika kira ni, i will call you later."

"Okay sai ka gama."

Cikin shagwaɓa ya ce. "Ki zo ki shirya ni my love, I'm tried."

Murmurshi ta yi mai sauti cikin kunya ba ta ce komai ba, shi ma murmushin ya yi ya ce. "Bye, Sarkin kunya, soon zan cire miki duk wannan kunyar taki, wuyarta a kawo ki gidana mu kwana tar...." Bai ƙarasa ba ta kashe wayar still tana murmurshi, wani irin son Adnan na ƙara mamaye zuciyarta, wayar da suka yi yanzu ta sa ta fara jin sauƙin damuwar tafiyar Faris da kewar shi.



Cikin takunta na ɗaukar hankali mai cike da izza ta shiga parlour'n part ɗin Momy. A shagwab'e take kiran sunan, "Mommy, Mommy."

"Na'am Daughter har kin dawo?"

"Na dawo Mommy."

"Welcome" Hajiya Saudat ta faɗa tare da rungume Meenal."

"Thank you Mom, I want to take Bath, ki saka wata a cikin baƙaƙen yaran nan ta haɗa mini ruwa a toilet yanzu."

Shafa kanta Mommy ta yi ta ce. "Yanzu kuwa."


Around 11pm Meenal tana online tana chat mutumin da suka haɗu ɗazu ya yi mata magana, babu bata lokaci ta yi masa reply. Introducing kansa ya yi mata ya sanar mata sunansa Abdul. Daga nan suka fara hira, Abdul ya iya tsara mace, hakan ya sa a cikin daren ya sace zuciyar Meenal. Dama 2 days ta rasa gane kan Usman, ya canza mata gaba-d'aya.

Har 2 na dare suka kai suna chat ɗin, wanda rabi duk stickers ne da emoji na love da hug da kisses Abdul ya cika ta da shi.


Cikin lokacin ƙanƙani Meenal suka saba da Abdul sosai, kodayaushe cikin chat da waya suke, video call kam kusan raba dare suke suna yi. 1 week da haɗuwarsu ya zo gidansu, aka sauke shi a parlour'n saukar baƙin Bulama. Abdul Saɓanin Usman yake, sun banbanta a halayya, dan shi Meenal tana zuwa ya rungume ta tare da kissing ɗinta. Hakan ko a jikin Meenal, ta biye masa sukai ta shashanci.



Shirye-shiryen biki ya kankama ta kowanne ɓangare, su Hajiya Na'ima ba zama, ana ta shirye-shiryen yanda abubuwa za su kasance. Yanda Na'ima take murna da rawar ƙafa akan bakin ba ƙaramin mamaki ya ba wa su Aunty Iman ba, sanadiyyar ƙin Abra da suka san Na'ima tana yi.

A ɓangaren Amarya kuwa tana cikin tashin hankali da damuwa, sakamakon kewar Salman dake addabar ta. Kullum sai ta ɓuya a ɗaki ta ci kuka ta ƙoshi. Ko kuma ta zauna ta saka hoton shi a gaba tay ta kallo tana hawaye, ko ta faki ikon Mami ta shiga ɗakinsa ta kwanta tana shaƙar ƙamshinsa da har lokacin bai bar ɗakin ba. Babbar damuwarta rashin ji daga Salman tun da ya tafi, komai take yi wayarta na hannunta cikin tsammanin kiran shi ko ganin text ɗinsa amma shiru. Ta karɓi sabuwar Numbernsa ta ƙasar Chinan a gurin Abbi, amma idan ta kira ba ta shiga, ta duba kuma numbern ba a WhatsApp da ita. Abun da yake rage mata damuwa Adnan, saboda wata irin kulawa da ƙauna gami da tattali na musamman yake nuna mata. Damuwar rashin Salman a kusa da ita ya sa duk ta rame.


Meenal ce tsaye a gaban mudubi tana shiryawa, sanye take cikin wasu matsatstsun kaya riga da wando, wanda suka bayyana surar jikinta. Wani yalolon mayafi net ɗan ƙarami ta saka akanta, rabin gashinta daga gaba duk a waje, mayafin kuma iya ƙasan wuyanta ya tsaya.

Cikin takunta na ƙasaita da ji da kai ta fice ta sauka ƙasa. Hajiya Saudat na zaune ita da wata k'anwar BULAMA da ta kawo mata ziyara suna hira, takun saukowar Meenal daga kan step ya sa su ɗaga ido suna kallon ta. Tun kafin ta ƙaraso ƙamshinta ya gama cika parlour'n. Baki buɗe Aunty Murja take kallon ta cikin ɗaurewar kai. Hajiya Saudat kuwa murmurshi ta saki ta ce. "Wow, Daughter irin wannan kyau haka? You look so beautiful!" Murmurshi Meenal ta yi cikin jin daɗi tare da juya ido ta ce. "Thank you Mom." Sannan ta dubi Aunty Murja daga tsayen da take ta ce. "Ina Yini Aunty?" Numfashi Aunty Murja ta sauke ta ce. "Lafiya ƙalau Meenal." Duban Hajiya Saudat ta yi ta ce. "Bye Mommy sai na dawo, Abdul na jira na tun ɗazu."

"To a dawo lafiya, Allah ya kiyaye ya tsare."

Bayan Meenal ta fita cike da al'ajabi Aunty Murja ta ce. "Aunty Saudat! Yanzu da wannan shigar kamar ta ƴaƴan turai kika bar Meenal ta fita?"

Ɓata fuska Hajiya Saudat ta yi ta ce. "Ban gane ba? Me ne laifin shigar jikin Meenal?"

"Haba Aunty Murja, ƴar taki guda ɗaya tal a duniya kikewa irin wannan tarbiyyar? Gaskiya wannan al'amarin naki da sake, kamar ba ki ga yanayin shigar tata ba ne? Kuma idan na ji da kyau kamar wani ta ce yana jiran ta."

"To sai me? Kawai sai in hana yarinya sakewa ta yi abun da take so? Mene a ciki dan sun fita da saurayi? Kuma ba wani gurin za ta je ba birthdayn ƙawarta zai raka ta."


"Taɓdi can! To ko ma ina zai raka ta ai bai dace ba, yaran yanzu ka yi iya yinka ma ya aka ƙare balle ka yi musu irin wannan riƙon sakainar kashin."


Haɗe rai Hajiya Saudat ta yi ta ce. "Me kike nufi Murja? Wacce irin magana ce wannan? Ni fa ba na son irin wannan sa idon, haba daga yarinya ta fita sai ki fara wani zancen mara tushe?"

"Zancen nawa ne mara tushe Aunty Saudat? Shikenan Allah ya kyauta ya kare."



Tunda ta fito ya ƙura mata ido ta cikin glass ɗin Motarsa, lips ɗinsa na ƙasa ya lasa cikin duniyanci.


"Oh My God! Irin wannan kyau haka Baby na?" Abdul ya faɗa lokacin da Meenal ta buɗe Motar ta shiga.

Murmurshi ta yi tare da yin fari da ido ba ta ce komai ba. Hugging ɗinta ya yi suka fara shashancinsu. Bayan wasu mintuna ya kunna Motar suka tafi. Wani ɗan ƙaramin gida mai kyau suka je, babu kowa a gidan, shi ya fita ma ya buɗe gate suka shiga. Bayan sun shiga ya fita ya buɗe wa Meenal Motor tare da faɗin. "I want to show you a special love today my Baby." Ya ƙarashe maganar tare da kashe mata ido.

"Mee too." Ta ba shi amsa tare da kwanciya a jikinsa. Kissing forehead ɗinta ya yi sannan ya kama hannunta suka shiga cikin gidan. Direct wani bedroom suka shiga suka faɗa kan gado rungume da juna, shaiɗan na kaɗa musu ganga a tsakiyar kai.


Har bayan Magriba Meenal tana gidan Abdul, wanda ya yi nasarar raba ta da budurcinta a yau. Da farko Meenal ta ɗan damu bayan komai ya kammala, amma Abdul ya kalailame ta da daɗin baki, ya nuna mata hakan ba wani abu ba ne tunda shi zai aure ta. Ba tare da fargabar komai ko damuwa ba ta kimtsa ya mayar da ita gida. Abdul sai soyayya da ƙauna da tarairaya yake nuna mata.


Jiki babu ƙwari ta shiga gida saboda yanda take ji ko'ina na jikinta na yi mata ciwo saboda rashin sabo, yanayin tafiyarta kaɗai zai saka duk wani mai hankali da ya san me yake yi ya gane abun da ya faru. Amma Meenal tana cewa Hajiya Saudat ciwon mararta ne ya tashi ta yarda.

Tun daga wannan rana Abdul da Meenal suka zamto tamkar mata da miji, kodayaushe cikin sheƙe ayarsu suke.




Yau Lahadi, wanda ya kama saura sati Uku a fara shagalin biki, yau ne kuma za a kawo lefen Abra daga gidansu Adnan. Tun da safe driver ya kai ta gidan Aunty Iman, kasancewar Maza ne za su kawo kayan.


Tana kwance a bedroom ɗin Aunty Iman, idanunta a lumshe hawaye na fita daga cikinsu yana bi ta gefen idonta ya sauka akan pillow'n da take kai. A haka Aunty Iman ta shigo ta same ta. Cikin mamaki ta ce. "Subhanallahi, kukan me kike yi Abra? Ko auren ne ba kya so?" Buɗe idonta ta yi tare da taune lips ɗinta na ƙasa, cikin muryar kuka ta ce. "Ina so Aunty, kuma ina son Adnan sosai, damuwata kawai Salman ne."

"Me ya samu Salman ɗin?"

"Ban san me na yi masa ba Aunty, tunda ya tafi ko kira na bai yi ba, kuma ya san ina cikin tsananin kewar shi."


"Ki yi haƙuri, may be sha'anin karatu ne."

Girgiza kai ta yi ta ce. "Ba karatu ba ne na sani, tunda yanzu bai isa fara karatun ba, sai ya fara koyon yaren ƙasar na 1 Year fa, idan ma karatun ne ai ko text ne ya turo mini."


Lallaɓa Abra Aunty Iman ta yi ta samu ta bar kukan da take da ƙyar. Amma a cikin zuciyarta ba ta daina ba, saboda ita kaɗai ta san halin da take ciki, gabaɗaya babu wani karsashi ko ɗokin bikinta da take yi, saboda rashin Salman a kusa da ita.


Da yamma Abban Adnan suna zaune a parlour shi da Yayansa suna tattaunawa akan lamarin bikin mutanen da suka kai lefe suka dawo. Uncle Kabir ƙanin Abba shi ya fara shigowa cikin wani irin yanayi, da kallo su Abba suka bi shi har ya zauna. Yayan Abba mai suna Alh. Mustapha ya dube shi ya ce. "Yaya Kabir? lafiya kuwa?"

"Akwai matsala Yaya."

"Subhanallahi? matsala kuma? ta mece ce?" Abba ya tambaya cikin ruɗu.

"Yarinyar da Adnan zai aura, Major Khamal ba shi ne ainihin Mahaifinta ba, tsinto ta ya yi a daji."

"Kai kuwa a ina ka jiyo wannan maganar mara daɗin ji?" Cewar Alhaji Mustapha cikin tsananin mamaki.

"Daga majiya mai ƙarfi, dan haka da sake wai an bai wa mai kaza kai da ƙafafuwa, tunda Allah ya sa kafin a ɗaura Aure muka samu wannan labarin dole a fasa abun nan, dan ba za mu haɗa iri da Yarinyar da ba a san asalinta ba!"




Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423  Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ta account ne ɗari uku kacal.


Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750.
[10/7, 2:28 PM] Abk: "Sunan zuri'armu zai ɓaci muddin muka bari Adnan ya auri yarinyar nan wacce babu wanda ya san Asalinta balle iyayen da suka haife ta, We want a girl with originality and roots" Cewar Uncle Khabir ya faɗa yana mai girgiza kansa, alamar abinda ya ke faɗa tun da ga ƙasan zuciyarsa ya ke fitowa.
"this is not a problem, and Adnan must marry this girl as he intended, ni baga wani aibun Auren ta ba gaskiya, kowa akwai yadda Ubangiji ke tsara masa rayuwa" Kallon Alhj Mustapha Uncle Khabir ya yi fuska babu walwala ya ce.

"Yaya mara asalin kake so yaronmu ya aura? Kada ka manta yadda jama'a ke mutun ta familynmu, ta yaya zamu zuba idanu Adnan ya aure ta, bayan mun san abinda hakan ke nufi? Our dignity is seen, we have money, education. Mun fito daga cikin Ahhali mai kyau da nagarta, auren Adnan da wannan yarinyar na nufin zubewar Alhhalin Matawalle I don't want that to happen"
Da Mamaki Alhj Mustapha ke kallon Uncle Khabir, he just thinking ina ilimin Khabir ya tafi haka? numfashi ya sauke cikin tarin nutsuwa da nuni d cewa shi ɗin he's educated ya ce.

"Idan Abra Khamal Khamis ta kasance Shegiya ko mara tushe da asali kamar yadda kake ta ɗaga murya kana faɗa, ina tunanin cewa ba ita ta tsarawa kanta yadda za tazo duniya ba. Kuma bada yardar ta abinda ya kasance ya kasance ɗin ba, God determines everything that happens, and He determines how a person will come to earth. Ka ɗauka hakan zai iya kasancewa da wani namu, ɗa kuma na kowa ne so please ka bar wannan maganar"
Jinjina kai Uncle Khabir ya yi cikin girmamawa kuma ya ce "Shi kenan yaya, Allah ya basu zama lafiya"
"Amin, Amin" Alhj Mustapha ya faɗa yana sakin Murmushin jin daɗi na amincewar ɗan uwan nasa.

"Do me a favor, please."
Professor Aliyu Matawalle ya faɗa yana gyara zamansa kana kallon su kasan cewa, kuɗi ya gama yin kuka a jikinsu, ga tarin ilimi komai nasu a waye ya ke kuma cike da tsari.
"Muna jinka idan har bai gagara ba"
"Ba zai gagara ba Insha Allah" Abba ya faɗa idanunsa akan Uncle Khabir kafin ya ce.

"Maganar nan ta tsaya iya mu, bana son Sp Adnan yaji wannan maganar, balle wata rana ya goranta mata, I know he loves her, but the heart can decide for him one day. Even Hajiya bana son ta san haka balle ya fita zuwa Matawalle Family please brother's"
Murmushi Alhj Mustapha ya ƙara saki ya ce.
"U don't have to be worried about, babu wanda zai ji haka Insha Allah. Adnan nada hankali da tausayi ba zai taɓa aikata hakan ba koda yaji haka, nasan kuma Barrister ba zata ce komai ba"

"Bar sha'anin mata yaya, bana son Hajiya ta san zan can wallahi kasan abin surutu da yayatawa baya yi musu yawa, zata iya hana auren wanda kan janyo matsala ga Adnan. Bana son komai ya samu Adnan"
Uncle Khabir ya ce.
"Extly. Mace taji zance ka tabbatar kowa ya sani more Especially irin wannan, Allah dai ya ki yaye"
Rufe zan can sukai tare da fara tattaunawa akan sabon Companyn da zasu buɗe ƙarƙashin Matawalle Family.

Bayan Magrib Sp Adnan ne zaune shi da Usman cikin wani ƙaramin garden dake gidan, ba zaka taɓa cewa duhun dare ya fara kawo kai ba, sbd yadda wajan ya ƙayatu haske ko ina.
A hankali Sp ke sipping tea ɗin da ke kusa da shi, yana lumshe fararen idanunsa gaba ɗaya gajiya ta saukar masa a karo na farko na rayuwarsa damuwa ta bayyana akan fuskarsa.
"Gaskiya gidan ka ya haɗu Sp duk wanda ya yi maka zanan gidan ya iya, anya ba za'ai min irinsa ba"
Harara Sp ya watsawa Usman ba tare da ya ce komai ba. Usman ya gyara zama ya ce "U looks so worried what's up?" Watsa hannun Sp ya yi a hankali ya ce.
"Time ɗin bikina nake gani kamar baya zuwa"

"Are you serious? Maganar 3weeks ake shi ne baya sauri this is wonderful yau Sp ke son kasancewa da mace"
Idanunsa dake a rufe ya buɗe tare da kai hannunsa ya ja zip ɗin gaban rigarsa surar jikinsa ta bayyana.

"Ina jinta a nan"
Ya faɗa yana nuna saitin zuciyarsa da hannunsa "komai ƙwace min ya ke idan naji muryar ta, i can't control myself idan nai tozali da Fuskar ta, kamar nai ta kasancewa da ita har gaban Abada"

"The day I've been waiting for has come. Allah ya nuna min Annabi kamar yadda naga wannan ranar, yau Adnan ke sambatu akan wata"

"Ba wata bace, she's my wife mother of my children my life partner"
Sai kuma ya gyara zamansa sosai jikinsa na fidda Ƙamshin Pur oud ya ce.

"My wife is different from other women, firstly sanyin halinta ke ƙara sawa na sota, uwa uba haƙuri da biyayya, she never lie to me" baya ya yi kaɗan yana lilo jikin Kujera da ya ke zaune tare da rufe idanunsa a hankali ya saki lallausan murmushi wanda ya sanya fararen haƙoransa bayyana cikin husky voice ya ce.

"A beautiful woman, with big white eyes and a small mouth with a sweet voice and a lot of religious knowledge. Wow Sp Adnan Aliyu Matawalle I'm lucky ni mai sa'a ne"

Dariya Usman ya yi sosai yana ɗaukan bottle of water tare da ɓalle murfin gorar ya tsiyaya wa Adnan ya ce.
"You have to drink this ko ka samu nutsuwa" tashi Adnan ya yi yana shafa kansa bai ƙara cewa komai ba ya nufi cikin gida saboda kiran sallar issha da ya ji.
Miƙewa Usman ya yi ya ce.

"Amma da ga ɗan iska sai kai, ka kirani akan tsara Invitation na ɗaurin aure, But you didn't tell me anything about it,We don't have time, we don't have anything planned for the ceremony"

"Karka min ihu akan I.v ko da shi ko babu dole a ɗaura min aure kuma a kawo min Angle gidana" dry kawai Usman ya yi yana ƙara mamakin yadda idanun Sp ya rufe akan Abra, ga shi ko a photo ya hana ya ganta Maybe shi da ganinta sai kuma biki idan Allah ya kaimu da rai da lafiya.

Bayan sallar issha Sp da Abba da Hajiya Mama duk suna zaune a dining area suna yin dinner, rabin cin abincin Abba ne da Hajiya, Sp tea kawai ya ke sha a hankali, sai fried indomie wacce akai masa ta sha hanta sai Ƙamshin ta ke, bayan sun kammala ne Hajiya ta kalli Sp ta ce.
"Ya kamata a kawo min Daughter-in-law" ɗago kansa ya yi a hankali ya zubawa mahaifiyar tasa ba tare da ya ce komai ba.

"Ka tsare ni da idanunka ko baka gane bane?"
Ɗan marairaicewa ya yi ya ce "Haba Hajiyata idan ban gane ba to maganar wa zan gane?" Abba ya kalli Adnan ya ce.
"Rigima ce kawai ta Barrister amma tun daga Kano ya ɗakko ƴar mutane har Kaduna, ai iyayen ta ba zasu amince ba"
Jinjina Kai Sp ya yi kafin ya ɗauki wayarsa ya ce "Ina laifi a haɗaku V.c amma is too par from kano to Kaduna"

"I knw, na matso naga Daughter-in-law ɗita nima kafin Allah ya kawo mana Grandchildren"
Shafa kansa ya yi zuwa Fuskarsa yana sakin Murmushi "I'm so anger to see my wife kusa dani"

"Me kace?"
Hajiya Mama ta watso masa tambayar domin kusan a fili ya yi maganar bawai a zuciya ba kamar yadda yai niyya. Miƙewa ya yi idanunsa akan wayarsa ganin notification.

"Abba, Hajiyata good night" da idanu suka bisa sai da ya ɓacewa idanunsa Hajiya Mama ta ce "A wanne part zai saka Amaryar ne naga baya magana hakan?"


"A gidan sa zai sakata" nan da nan Mama ta ɓata fuska domin har zuciyata ta ke son zaman Abra kusa da ita, ko Adnan baya nan sai su zauna tare. Haƙuri Abba ya bata akan ta rabo da shi yanzu yana kan giyyar soyayya ba zai fahimta ba.

Misalin 11:00 na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login