Showing 45001 words to 48000 words out of 231718 words

Chapter 16 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

28 Feb 2025

14704

zaune a gefen gado, ta saka uniform ɗin Islamiyya, se dai ta takure tana ta uban kuka.

Cikin damuwa Salman ya ajiye Plate ɗin Abincin akan dressing mirror, ya ƙarasa kusa da ita ya zauna, yace "Haba Abbis Fav, why? Dan Allah ki dena kukan nan haka ya isa".

"Faris, Meyasa Mami ba ta sona ne?" Tai maganar kamar za ta shiɗe.

Salman yace "tana sonki mana, kema ba kiga Abbi yafi sonki ba, nima tafi sona ne amma tana sonki kema"

Abra ta girgiza kai tace "No, she hates me, kai meyasa Abbi ba ya maka abunda take min? I so much Love my Mum, i have no one like her, ina son Mamina Faris, but why is she treating me like this? Ni aikin da take sani baya damuna, ta isa ta sani ne, amma meyasa take kyarata, ba ta son inje in da take? I so much Love her, dan Allah in laifi nai mata ka tayani bata haƙuri, amma dan Allah ta din ga sona nima"

Jikin Salman yai sanyi ƙalau, ji yai kamar ya taya Abran kuka, tabbas abunda Mami ke nuna mata ƙiyayya ce, amma shima ya rasa dalilin hakan.

Cikin hikima Salmn ya fara Magana "Haba Yaya, ke fa jaruma ce, kamar yau kika fara jin faɗan Mami, ai idan da sabo ya ci ace mun saba da wannan faɗan nata, watarn ma fa ba mu mu kai laifin ba, amma seta huce a kanmu, Yanzu ma karki raba ɗayan biyu, wani ne ya ɓata mata rai, let's forget about it, muci Abincin nan and hope kin yi shirin screening ɗin nan, dan shi ne na ƙarshe, ko ai sauka da kai ko kuma ka faɗi, ko kuma ai be kamata ma in tambaye ki ba, ku da kuke 'yan gaban goshin sheik Nurain, ai dole kiyi sauka" yai maganar ƙoƙarin basar da waccan Maganar.

Murmushi ta yi lokaci ɗaya fuskarta ɗauke da hawaye tace "Alhamdilillah, ai ni na kammala shiri, se addu'a Allah ya sa muyi nasara, dan Allah Faris kaima ka dage gobe in Allah ya kaimu ku za'ai wa screening ɗin".

Yace "yanzu in ban ci ba ya zaki?" Yai maganar yana kallonta.

Tace "zama ka ci, in baka ci ba haƙura zan da saukar nima" murmushi yai yana jin son yayar ta sa a ransa, tana matuƙar son sa da son ganin cigabansa, shiyasa shima baya son ganin hawayenta.

Da haka ya lallaɓata suka ci Abinci tare, yana yi yana tsokanar ta, wai idan a gidan yawa take, se an dinga cinye Abinci ana barinta saboda ɗan abunda take ci kamar wasan yara.

Suka kammala ci, ta saka hjjabinta suka fice Islamiyya tare.



G.Y Bulama Hospital and Maternity.

Bainu ba kya tsufa, shine kirarin da wasu ka yiwa MD na Asibitin, wato mamallakin Asibitin GY Bulama Hospital and Maternity, babu alamar shekaru a tare shi, kullum cikin gayu da tsafta yake, ga kyawunsa na nan farin bafulatani jawurr da shi, kamar ba ya jin hausa.
  Daga abokan aikinsa zuwa ma'aikatansa mata, da yawa na nuna suna sonsa, sedai ba fuska ga shi ba wanda ba shi da labarin masifar Matarsa da yadda ta kasa ta tsare akan Mijin nata.

Yana zaune a Office ɗin sa, yana aiki a Computer ɗin sa, Nurse Basira ce ta shigo, tace "Sannu da aiki Sir"

Yace "Yawwa Sister, ya aikin"

Tace "Alhamdilillah Sir sai dai...."

Ya ɗago ya kalleta yace 'ina jinki meyafaru?"

"Nace da ma, kaga muna da patient a ward a kwance, ga out patient ga wanda aka ajiye for observation, amma naje pharmacy given set ɗin da za'a saka musu ruwa be fi uku ya rage ba, an tafi kawowa me kawowar haryanzu be dawo ba, wasu sun fara ƙorafi, nace ko gurinka za'a samu? Ko a bawa security yaje Sarauta Pharmacy ya siyo a fara sa musu, tun da duk sun biya kuɗi".

Yai ajiyar zuciya yace "Basira, do you forget this is an business organization, muna aiki ne dan neman kuɗi, Pharmacy sun je siyo abunda babu, and still you are asking for another money a siyo kan su kawo, wannan ai asara ce, wanda ze jira ya jira, wanda ba ze jira ba ya tafi, amma kuɗin mutum baze dawo ba.
And must i teach you everything a Makaranta ba a koya muku use of available resources ba? Ki yi 'yan dabaru ki musu amfani da guda ukun, idan na wannan ya ƙare, sai ki wanke shi ki kuma yiwa wani amfani da shi".

Seda Basira ta buɗe baki sannan tace "Amm Doctor, ai this can be a means of transmission disease, mutane with different health status ai musu using one giving set, is a risky".

"Basira get out of my Office, if you can't do it, i will do it myself".

Cikin girmamawa tace 'am sorry sir" daga haka ta bar Office ɗin ranta a ɓace.

A Nursing station ta tarar da Jamila tana jiranta, Jamila na ganinta tace "yaya ku ka da shi? Ayi a sallami Mutanen can na Emergency, relatives ɗin su sun fara complain"
Basira ta kwashe mata yadda su kai da doctor.
Zare ido Jamila tai tace "ke kuma yanzu yi zaki?"

Basira tace 'idan ban ba to ya zanyi?"

"Caɓ, to gaskiya Wannan rashin gaskiyar ba dani ba, wannan ai zalunci ne, mutum ya biya maƙudan kuɗi dan neman lagiyarsa amma a ƙara masa ciwo, Tiirrr da wannan abu, idan mu kai haka ilimin da mu kai be amfane mu da komai ba"

Basira tace "to ya zan yi, idan ban hakan ba ze iya korata"

Jamila tace "Allah ya temaka, amma ba da hannuna ba kam, ba zan iya wannan gangancin ba".



Cike da farinciki da annashuwa Abra da Salman suka taho gida, sakamakon nasarar da Abra tai, na tsallake screening ɗin sauka, suna tafe ya na zigata yana cewa "dama na san zaki iya, Yayata ba dai hazaƙa ba".

Suna gida a falo suka tarar da Mami, gaba ɗaya har Abra ta manta da abunda Mamin tai mata, Salman ya kalli Mami yace "Mami, Yaya ta ci screening ɗin sauka, a yanzu haka babu me makinta"

Wata uwar harara ta watsa masa tace "to sai me? Kai kuma fa, kana nan kana gayamin taci screening kai kuma fa?"

Abra tace "Mami ai shi ma ya ci zagayen farko zuwa na biyu, gobe in Allah ya kaimu za'a gama yi musu suma, kuma nasan ze ci insha Allah"

"Rufen baki da ke nake?" Tai mata Maganar cikin tsawa.

"Kai kenan kana ɓare ɓare, ita tayi abun arziki a makaranta amma kullum kai ne koma baya"

Salman yace "to Mami ai naga ni da Yaya ɗaya ne, nasararta tawa ce banga.....

"Shut up! Sakarai ba zaka taɓa gane me nake nufi ba, namiji ne kai ita rayuwarta taƙaitacciya ce a gida zata ƙare tata rayuwar, kai ne namiji kai ne ɗan gwagwarmaya, amma kullum ana nuna maka kana shirme"
Abra ba ta kuma tankawa ba, ta wuce ɗakinta rai ba daɗi.


Ƙaton ɗakin taro ne wato event center, cike da manyan mutane, tun daga harabar gurin irin Manyan motocin da akai parking, za ka san taron ya haɗa da Manyan mutane.
Wani sashi na ɗakin taron, ɗalibai ne 'yan makaranta sanye da uniform a jikinsu, kowannen su fuskarsa ɗauke da walwala.
  A dukkan bangon ɗakin taron, ƙatuwar banner ce da tambarin makarantar, daga ƙasa an rubuta speech and prize given day.
Kiɗa ne ya ke tashi, kaɗan kaɗan a cikin manyan speakun da ke ɗakin taron.

Can aka sanar da fara gudanar da taro, in da ɗaliban makarantar za su gabatar, da abubuwa domin nishaɗantarwa da kuma nunawa iyayen su irin ilimin da suke samu a wannan makarantar.
Kasancewar makarantar haɗaka ce ta musulmi da kiristoci, akace za'a gabatar da Addu'a, daga bakin ɗalibai, kan a fara taron.
ABRA KHAMAL KHAMIS, aka fara kira domin buɗe taro da Addu'a.

Cikin nutsuwa ta fito, ta nufi in da zata karɓi mic, gaba ɗaya ido ya koma kanta, saboda farar fatarta da ke ɗaukar ido.

Haushi ne ya kama Salman, ganin yadda aka bi Yayar ta sa da ido, kamar wasu mayu, wasu ko ƙiftawa ba sa yi, komai na ta a nutse.

Abbi kuwa se murmushi yake, yana kallon 'yar ta sa.

Cikin zazzaƙar muryarta ta fara kwararo Addu'a, yayin da hall ɗin ake amsawa da Ameen.

Mami kuwa kamar tai bindiga, dan haushi komai sai dai ace Abra, maimakon Salman.

Bayan ta idar ta koma mazaunin ta, aka kira wani kirista shi ma yai Addu'a, aka saurari jawabin maraba daga bakin shugaban Makaranta, daga nan aka kira debate.
Debate ɗin akan rashin tsaro da ake fama da shi, laifin waye? Gwamnati ko jami'an tsaro?.

Abra na cikin masu kare Jami'an tsaro, yayin da Salman ke cikin masu kare gwamnati.

Masha Allah, yaran sun yi bajinta, yadda suke zubar da turanci, da hujjoji.

Ko da Abra ta fito domin yin nata, Subhanallah, sai da ta sanya idonta a cikin na Abbinta, tai murmushi sannan ta fara kwararo kirari ga jami'an tsaron, ta ƙame tare da sarawa, san nan ta fara sauke sanka-sankar hujjoji, wadda take jin su daga ƙarƙashin zuciyar ta, saboda yadda take jin Abbinta da yadda yake bawa ƙasarsa gudunmawa.

Sai da Abbi yai ƙwalla, yana tafa mata yana jin ƙaunar yarinyar ta sa a cikin ransa.

Ku san duk wani abu da aka gudanar a gurin, akwai Abra ko Salman a ciki, amma Abra ita ce akan gaba a Komai.

A ƙarshen taro da aka fara raba kyaututtuka, Abra ce ke da rinjayen grade a kaf makarantar, sau ɗaya kacal aka taɓa samun wanda ya taɓa samun irin grade ɗin ta, Salman ne na uku, a ɓangaren tsafta sai da ta samu kyauta, haka ladabi da biyayya, sakamakon debate ɗinsu ma su ne na ɗaya.
Abra tafi kowane ɗalibi samun kyaututtuka, duk da Salman ma ya samu sosai, amma ba kamar Abra ba.

Shi kansa Abbi sai da Makarantar ta karrama shi, akan jajircewaesa akan yaransa, aka karrama Familyn su gaba ɗaya, aka gayyace shi dan ya tofa albarkacin bakinsa.

Shima a nan ya dinga koɗa Abra, yana jinjina ƙoƙarinta da jajircewarta.

Salman ko a jikinsa, murmushi ya dinga yi yana tafi, Ammi kuwa ji take da da madoki, sai ta zanewa Salman jikinsa dan sam ba ya kishin kansa.

Daga ƙarshe aka dinga hotuna, ba yadda Hajiya Na'ima ta iya, haka ta dinga yaƙe ana hotuna, sannan suka nufi gida.

Suna tafe a hanya Salman na sake wasa Abra, yana mata kirari tana murmushi, Haka Khamal ma, ya biyewa Salman suna koɗa Abra.

"My favorite, yadda kika dinga wasa jami'an tsaro da gudunmawarsu ga ƙasa, da yadda kika dinga blowing English da points masu kyau, i almost cry".

Abra tace "Abbina, yabon gwani ya zama dole, idan ba'a jinjina muku ba be kamata a zage ku ba, day and night, rain and sun you never off duty,
Tun tasowarmu kuke tsaye akan ganin ƙasarmu ta samu zaman lafiya, Salute to our brave soldiers" ta ƙarasa Maganar tana sarawa Abbin nasu.

Salman wata shewa yai yana tafawa Abra, yayin da Abbi yake ta murmushi yace "Allah ya rayamin ku da imani, haƙiƙa Ku ababen alfahari na ne, ina fatan ku zama wani abu a rayuwa, yadda al'umma da ƙasarku za suyi alfahari da ku, sannan insha Allah zamu shirya walima tayaku murna"

Abra tai farat tace "Abbi, ka manta saukar mu saura sati biyu, kawai a bari semu haɗe kar kashe kuɗin yai maka yawa"

Abbi yace "Masha Allah, Allah ya albarkaci rayuwar ku, ya raya mana ku da imani".

Salman yace "Ameen Abbinmu, maganin kukan mu"

Abbi ya kalli Hajiya Na'ima yace "Madam ba kice komai ba, ba ki ga irin bajintar da yaran naki su kai bane, gaskiya kin iya haihuwa da kika haifa min 'ya'ya masu ƙwazo".

Murmushin dole Na'ima tai kamar be basir, kai da ganin fuskarta ka san be kai zuci ba murmushin tace "Aikam ina jin ku, Allah ya ƙara musu basira"

Haka suka ƙarasa gida, su Salman na ta nishaɗinsu su da Babansu, Hajiya Na'ima kuwa tana tunanin me za taiwa Abra ta huce, saboda yadda take jin tsanar Abra na sake ninkuwa a zuciyarta, kullum Abra ce gaba akan komai, gashi daga Salman har Babansa gaba ɗaya sun maida hankali akan Abra, kamar ba su da sauran abun yi a doron ƙasa sai akan Abra.


"Daddy"
"Na'am Babyn Daddy ya akayi ne?" Cewar GY Bulama, da ke kallon 'tilon yar sa cike da tsananin ƙaunarta.

"Daddy na kusa shakara goma sha takwas fa"

Yace "wow, Masha Allah babyna ta girma, we most celebrate your birthday"

Tai murmushi tace "that's my Dad, amma fa guri za'a kama ai shagali sosai"

Yace "Insha Allah, shagali za mu yi na gaske".

"Kai kam doctor kai ta biyewa wannan yarinyar ta na maka shirme, har Abincin na ka ze sanyi bak ci ba"

Doctor yai murmushi yace "to idan ban biye mata ya kike so a Yi? She's the only daughter i have alive".

Meenal ta kalli Babanta tace "Wai Daddy ni bani da 'yan uwa ne? Nifa ina son in ga nima ina da siblings, I like big family"

Ya ɗan murmusa yace "Babyna kenan, Allah shi ke tsara komai, lokuta da dama ba ma samun abunda muke so, se Abunda Allah ya shirya mana, ke kaɗai Allah ya bamu, ina fatan Allah ya sa ke mu samu jikoki masu yawa daga gareki".

Rufe idonta Meenal tai tace "Ohh Daddy, har ka bani kunya"

Yai murmushi yace "Yau kuma ni ake jin kunya?"

Tace "Ka san wani abu Daddy?"

"A'a sai kin faɗa"

Cikin gaɓunta tace "Wani brother ɗin ƙawata ne ya zo mata visiting, yace ya na so na wai ze kawon ziyara ma"

Yace "Wow, Masha Allah, amma naji daɗi sosai, ɗan ina ne?"

"Nima ban san a unguwar da yake ba, amma dai brother ɗin ƙawata ne"

"Masha Allah, to Allah ya kawo shi lafiya".

Girgiza kai Mummy tai tace "Allah ya kawo ranar da zaki hankali, da babanki kike hirar saurayi?".

Doctor yace "to ya ranki, idan ba tai hira da Daddy ba da wa za tai?"

Mummy tace "lallai 'yar gidan Daddy".





Tsaye yake a gaban dressing mirror yana kallon kansa, lokaci guda kuma yana ɗaura agogo a hannunsa, sanye yake da dogon wandon jeans, da jar riga long slip, ya taje sumar kansa sai ƙyalli take, saboda yadda ta ji mai.
Dogo ne sosai, with Caramel skin complexion, masha Allah balck beauty ne, sedai kallo ɗaya za ka yi masa ka gano yadda yake da matuƙar kwarjini.
Ya gama sanya agogonsa, ya ɗau turare ya dinga fesawa, ya fesa wannan ya fesa wancan, sai da ya gama Sannan ya ɗau mukullin motarsa da wayoyinsa yai waje.

Wata babbar mace zaune a kan ɗaya daga cikin manya manyan kujerun falon, idonta sanye da gilashi ta na duba littafin azkar.

Ƙamshin da ya karaɗe ɗakin ne ya sa ta ɗago ta dube shi, ta ɗanyi tari tace "Kaii Adnan wannan turarukan na ka sun fiye ƙarfi, wannan ai sai Asmata ta tashi"

Yai murmushi yace "Hajiya Mama kenan, ba za su tayar miki da komai ba"

Ta ɗan gyara zama tace "wannan kwalliya haka, hala taɗi za'a je?"

Ya ɗan tsuke fuska yace "taɗi kuma?"

Tace "Eh mana, wato na faɗi maƙiyin naka, shine zaka haɗe rai, haba ɗan Maman, ga kyau, ga kuɗ, ga aiki Alhamdilillah komai kana da shi, sedai haryanzu ba ka cika kamili me kima ba a idon duniya, saboda ba ka da abokiyar Rayuwa, shekaru tafiya suke ba sa jira"

Adnan yace "to Hajiya Mama, za'ai insha Allah, yanzu dai wani ɗan aiki za muje wani guri"

Tace "haka dai, aiki aiki ba hutu, to Allah ya dafa"

Yace "Ameen Maman Adnan" ta bi shi da kallo tana murmushi.


Sannu a hankali yake tuƙin motar, yana tafe sautin waƙar Eminem am not afraid, na tashi daga Radio motar tasa.
A ƙofar wani ƙaton gida yai parking, rage Radio yayi, ya ɗakko wayarsa ya kira wata lamba, sai dai aka ce me layin yana waya. Tsaki yai ya ajiye wayar, ya kashingiɗa da jikin motar, tare da lumshe idonsa.
Can yaji an buɗe gaban motar an shigo, ya buɗe idanunsa ya kalli wanda ya shigo ɗin yace "Wai da wa kake waya ne? Na kira ka amma user busy"

Murmushi wanda ya shigo ɗin yayi yace "Kai dai bari, wato wata new catch na yi, Babyn ta yi Wallahi da ita nake waya, da ƙyar na iya fitowa ma gurinka"

Tsaki Adnan yai yace "Shirme kawai"

"Wallahi ba shirme bane, ai Soyayya duniya ce, wanda yake yinta shi ze gane"

Adnan yace "Please Usman, let's keep this aside, mu je muyi abun da ya kamace mu"

Usman yace "to muje, amma ina gaya maka, Soyayya duniya ce Adnan, kai ba kaga yarinyar ba, ina ga next week insha Allah za ka rakani, muje in kai mata ziyara, da na jewa Ameera Visiting na ga babyn, ba ka ga yadda ta tafi da ni ba"

"Amma ba ni Adnan ɗin ba ko?" Yai maganar ba tare da ya kalli in da Usman yake ba.

Usman yace "Eh ba kai Adnan ɗin ba, aljaninka, ɗan rainin hankali kawai, sai ka rakani".

Adnan be kuma cewa komai ba suka cigaba da tafiya.



Taro yai taro, gidan Khamal ya cika da mutane, domin taya su Abra murnar saukar Alqur'ani me girma, da kuma haddar izufi Arba'in ga kowannensu, ga nasarorin da suka samu, a makarantar boko.
Alhamdilillah, an ci an sha sun samu kyaututtuka daga Manyan mutane, abokan Abbinsu da kuma sauran 'yan uwa da abokan arziki.

Har Bayan sallar isha'i gidan cike yake da mutane, se wajen tara zuwa goma na dare Sannan aka watse.

Tuni Abra ta kwanta bacci, saboda yadda ta gaji tiƙis saboda zirga zirga, da kuma hayaniya.

Mami kanta a gajiye take, tai wanka ta samu tana cin Abinci a ɗakinta, dan ba ta samu ta nutsu ta ci ba.

Wayarta ce ta ɗau ruri, ta miƙa hannu ta ɗauka, ba tare da ta duba me kiran wayar ba.

"Na kira ne domin jin lafiyar 'ya ta, da kuma miƙa saƙon taya murna na saukar Alqur'ani da tai"

"Wace ke? Wai wacece haka ne?" Hajiya Na'ima tai maganar cikin ɗaga murya.

"Meye na ɗaga murya kuma? Uwar Abra ce".

"To in ke uwarta ce ki zo ki ɗauki 'yar ki mana".

"Me ze sa in zo in ɗauketa? Alhalin tana zaune Lafiya a gidan ubanta, Khamal na cigaba da raina miki hankali, amma a zahirin gaskiya Abra 'yar da muka haifa ce ni da Khamal, da ma na gaya miki bariki na ya fi naki, tsayin wannan lokaci ina nan ina bibiyar ki, idan kuma kina musu ki buɗe what's app ɗin ki, na ajiye miki saƙo".

Jiki na rawa Hajiya Na'ima ta katse kiran,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login