Showing 33001 words to 36000 words out of 231718 words
Chapter 12 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
je ta bashi ba, baza ta faɗa mata yanda za ta yi Abra ta bar gidan cikin sauƙi ba, ba tare da an yi tunanin da saka hannunta ba. Ita kuma Na'ima gani take Aunty Suwaiba ba za ta gane halin da ta ciki ba ne, a ganinta ita aka cuce ta, kuma an hana ta kuka. Aunty Suwaiba ba kuwa tsoron kar Auren Na'ima ya mutu su shiga uku take, dan ita suka dogara ita da sauran ƴan'uwansu. Domin ta fuskanci babu abun da Khamal ba zai iya ba akan Abra.
"Amma fa Aunty daƙyar in zai hak'ura, dan yanda ya hasala ko su Ammi na zaga sai saka."
"Zai hak'ura mana, kamar kin manta halinsa ne, yana da zafi amma kuma yana da sauƙin kai wani lokacin, ki nuna kin damu kin yi nadamar maganganun da kika faɗa masa, duk taurin ransa zai hak'ura. Su Maza suna san ka yi musu laifi ka amsa ka yi, kuma kar ki bari sai gobe, da zafi_zafi ake dukan ƙarfe, ki je yanzu yanda zai gane da gaske kin yi nadamar, in ya so cikin nutsuwa sai ki faɗa masa komai na kiran wayar da aka yi miki."
Numfashi Na'ima ta sauke ba don son ranta ba ta ce. "Shikenan Aunty, zan yi duk yanda kika ce."
"Yawwa, ki fa yin fa, dan na san halinki sai ki amsa ki kuma ƙi yi."
"Zan yi fa da gaske."
"Shikenan, sai mun yi waya da safe, ki kwantar da hankalinki, na miki alƙawarin zaman Shegiyar yarinyar can a gidanki ya zo ƙarshe."
Duk yanda take jin tsananin zafi da k'una da baƙin ciki gami da takaici a cikin ranta, haka ta taushi zuciyarta ta miƙe tana goge hawayen fuskarta bayan sun gama wayar ta nufi ɗakin da Khamal yake.
A hankali ta tura ƙofar ɗakin, ta yi sa'a ƙofar a buɗe take, a zaune ta tarar da shi akan bedside drawer ya riƙe kansa da hannayensa, alamun ransa ya kai ƙololuwar ɓaci. Jin ƙamshinta ya saka shi ɗago kansa da sauri tare da miƙewa yana kallon ta.
Kafin ta ce uffan ya nuna mata ƙofa da hannunsa cikin ɗaga murya ya ce. "Get out!"
Marairaicewa ta yi ta buɗe baki za ta yi magana amma ya ƙi ba ta damar hakan.
"I said get out from this room." Ya faɗa a tsawace kyakkyawan idanunsa da suka rine zuwa ja duka a waje.
Jikinta ne ya ɗauki ƙyarma, ba ta yi tunanin ya ɗauki zafi haka ba, tsugunnawa ta yi akan ƙafafuwanta ta fashe da kuka ta ce. "Please My Man listen to me, ka saurari abun da zan faɗa maka."
"Me kuma ya rage baki faɗa mun ba Na'ima? Me zaki ce mun? Duk yanda nake danne zuciyata akan kar mu matsala amma ba kya gani? To tunda haka kika zaɓa mu zuba ni da ke a gidan."
"I'm sorry, dan Allah ka saurare Ni, wallahi na yi nadamar maganganun da na faɗa maka, amma ka mun uzuri raina ne a matuƙar ɓace a lokacin."
Numfashi ya sauke ganin yanda take kuka sosai sai zuciyarsa ta fara karyewa, ya yi tunanin da gaske ta yi nadamar ne har cikin zuciyarta.
Fuska a ɗaure ya ce. "Ba na son jin komai daga gare ki a yanzu, maganganun da kika faɗa mun ɗazu ma sun ishe ni."
Wani yawu ta haɗiye mai ɗaci ta shiga girgiza masa kai.
"Dan Allah Khamal ka saurare ni ka ji bayanin da zan yi maka."
Zama ya yi a gefen gado ya ce. "Ina jin ki."
Ajiyar zuciya ta sauke ta bashi labarin kiran wayar da aka yi mata. Kallon ta kawai yake har ta miƙo masa wayarta tana nuna masa kiran da aka yi mata da Private Number. Karɓa ya yi ya duba amma bai ce komai ba, ita ma ba ta ce komai ba sai idanu da ta zuba masa, imagine kawai take yi a cikin ranta ƙaramin yaƙin da za'a yi idan ya amsa laifinsa.
"Ba zance k'arya kike yi ba, amma gaskiya ban yarda da wannan abun ba, babu wanda zai kira ki ya faɗa miki haka, because ban da Family na da naki da wasu daga cikin abokan aikina, babu wanda ya san ta yanda muka samu Abra da matsayinta a gidan nan."
Wani malolon baƙin ciki ne ya ƙara cika zuciyarta, wato ma maƙaryaciya ya mayar da ita? Ita ta shirya hakan nufinsa ko kuma cigaba da raina mata hankalin da yake yi tun lokacin da ya kawo Abra zai yi? Ji take kamar ta tsinka masa mari dan baƙin ciki, amma dai ta daure ta yi kalar tausayi ta ce. "Wallahi da gaske nake, akan me zan ƙirƙiri wannan abun? Kar ka manta tun lokacin kawo Abra gidan nan na yiwa abun mummunar fahimta har muka samu saɓani ban ƙara tayar da hankalina ba, na cigaba da rainon ta cikin kulawa da zuciya ɗaya, to me zai saka yanzu kuma in yi haka?"
"Duk da haka, amma ko da hakan ne, daga kiran ki an faɗa miki wannan maganar sai ki zo ki dinga jifa na da waɗannan miyagun kalaman? Why Na'ima? Idan rai ya ɓaci sai kuma hankali ya gushe?"
Shiru ta yi ba ta ce komai ba, cigaba da magana ya yi idanunsa a cikin nata.
"Baki yarda da kanki ba, ba kuma ki yarda da ikon Allah ba, da kin yarda da baza ki dinga wannan abubuwan kamar wata illiteracy ba, ki saka a ranki Ubangiji ne ke yin komai, kuma shi ya nufa sai Abra ta yi rayuwa a gidanmu. Sannan kuma k'arya fure take ba ta ƴaƴa, ki saka a ranta komai daren dad'ewa gaskiya za ta bayyana, idan ma ƙarya nake miki Ubangiji ba zai barni ba, dole watarana sai ya toni asirina."
Na'ima ta kwantar da kanta ta dinga nuna masa ta yi nadama, sharrin shaiɗan ne da kuma tsananin kishin sa da take yi, amma Insha Allahu haka baza ta kuma faruwa. Ganin yanda take kuka da kalar tausayin da ta yi yasa Khamal ya janyo ta jikinsa ya ce. "Shikenan Wifey komai ya wuce, amma kar ki ƙara mun irin haka, ban ji daɗi ba, raina ya ɓaci sosai, yanzu fa ba da ba ne, mun girma mun zama iyaye, ya kamata irin wannan abubuwan duk mu daina su."
"Insha Allahu bazan kuma ba."
Ta yi maganar cikin sanyi tana ƙare shigewa jikinsa kamar ba Uwar ɗan saurayi Salman ba.
Bayanta ya shafa ya ce. "Allah yasa, bana son muna samun saɓani, musamman akan Abra, dan watarana yaran nan za su iya ji su gane halin da ake ciki. Ke Mace ce mai daraja a idona, ko dan yanda kika riƙe mun Abra da amana ba zan so wani abu na ba dai-dai ya shiga tsakaninmu ba."
Ƙwafa ta yi a cikin ranta tsanar Abra na ƙara cika mata zuciya, wato saboda ita ne ma yake ragwanta mata? Lallai dole ta san abun yi, dan gaba zai iya cewa ma saboda Abran yake zaune da ita. A fili kuwa murmurshin yaƙe ta yi ta ce. "Na gode Mijina, Abra kuma she is my Daughter, ka daina danganta ni da mariƙiya a gare ta, ni mahaifiya ce a gurinta, dan kallo ɗaya nake yi musu ita da Salman, matsayinsu ɗaya a cikin raina."
Murmurshi ya yi yana jin ɓacin ransa fiye da rabi ya tafi.
Washegari Bayan an idar da Sallar Asuba Abra ta yi lazimi da karatun Alƙur'ani kamar yadda, ta saba kullum ta nufi kitchen dan haɗa breakfast. Sai da ta fara tsaftace kitchen ɗin duk da ba ya tare da wani datti sannan ta fara aikin.
Around 6:40 Salman ya shigo kitchen ɗin fuskarsa na nuna alamun tashin sa kenan daga bacci.
"Sleeping sickness, an tashi kenan?" Abra ta faɗa tana kallon sa.
Yamutsa fuska ya yi ya ce. "Baccin ma ko isa ta bai yi ba, na tashi ne kawai saboda school."
"Ba dole ba, tunda jiya ka raba dare kana ta aikin kallon Ball."
"Baza ki gane daɗin kallon Ball ba ne Yaya, na ce ki zauna muna yi tare amma ƙin ki."
"Wannan sai ku, ni ina zan iya."
Irish ɗin da take soyawa ya ɗauki yanka ɗaya ya ci ya ce. "Sannu da aiki, ke kullum ba kya gajiya da yi mana daɗaɗan abinci masu motsa kunnen mutum, kuma gashi ke ba ci kike yi sosai ba."
Murmurshi ta yi ta ce. "Yanda kake da cin nan Salman idan ban zage na yi girki ba a gidan nan ai sai a samu matsala."
Murmurshin ya yi shi ma ya ce. "To Allah ya biya ki, bari na taya ki mu samu ladan tare."
Da sauri ta ce. "A'a ban ce ba, ka je ka shirya school kar mu yi late, nima na kusa gamawa." Ƙi ya yi ya ce shi dai sai ya taya ta, ita kuma ba ƙi take ba, tsoron kar Mami ta zo ta gan shi ne, duk da Abbi yana nan baza ta ce komai ba a yanzu, amma yana tafiya duk sai ta fanshe mata masifarta.
Tare suka kammala aikin suka kai komai dinning, suna aikin suna hira cikin nishaɗi da ƙaunar junansu. Bayan sun gama kowa ya nufi ɗakinsa dan yin wanka tare da shiryawa.
Salman ya riga ta fitowa, dan dama ita yanda take da sanyi haka take yin komai a sanyaye. 5 minutes da zaman shi ita ma ta fito sanye cikin uniform ɗinta mai kyau riga da skirt gami da ɗan ƙaramin hijab iya ƙirji. Salman ya bi ta da kallo. Tana duban sa ta ce. "What are you waiting for? ka zauna kana kallo na baza ka zuba abinci ka ci ba."
"Ke nake jira mana Yayata, kin san ai ba zan iya cin abinci ni kaɗai ba kya nan ba." Ya yi ƙarashe zancen tare da jan kujerar kusa da ita ya zauna. Dai-dai nan su Khamal suka yi sallama a parlour'n, Hajiya Na'ima ta ci kwalliya sai ƙamshi take zubawa, kamar babu wani abu na ɓacin rai dake damun ta, Salman ya bi ta da kallo yanayin da ya gan ta jiya ya faɗo masa a cikin rai.
"Good Morning Abbi and Mami" Abra ta faɗa fuskarta ɗauke da murmurshi.
"Morning Daughter, da fatan kin tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau Abbina."
Cikin murmushin munafurci Na'ima ta ce, "Uhm, ƴar gidan Abbi, wato shi kaɗai kika gani ko?"
Sunkuyar da kai kawai Abra ta yi, mamakin halin mahaifiyarsu na yanda take nuna mata a gaban Abbi yana cika mata zuciya. Khamal ne ya bawa Na'ima amsa da faɗin.
"Me kuma ya faru? Yau ma zaki ce ta nuna bambancin ne? Na ga dai a tare ta gaishe mu."
"Amma ai sunanka ta fara kira kafin ni."
Murmurshi ya yi ya ce. "Mr Jealousy, ga naki ɗan nan ai kema, yanda yake kallon ki na san ke zai fara gaisarwa. Salman ya murmusa sannan ya gaishe su a tare. Bayan sun zauna Abra ta yi serving ɗinsu, Khamal sai saka mata albarka yake yi tare da yaba mata. Hakan ba ƙaramin ƙona ran Na'ima yake yi ba, ji take kamar ta ɗauki ruwan tea ɗin dake tururi ta sheƙa mata a fuska, ƙarin abun takaicin Salman sai taya shi yabon Abra yake yi. Babu yadda ta iya ita ma haka ta dinga yaƙe tana taya su.
Bayan sun gama suka ɗauko school bags ɗinsu suka yiwa iyayen nasu sallama suka fice. Kafin su ƙarasa parking space Salman ya ɓata fuska ya ce, "Uniform ɗin nan kamar ya matse ki sosai Yaya."
"Ba bu abun da ya mun, me ka gani?"
"Kawai ni dai haka nake gani, haushi ma nake ji kina yawo a school a haka."
Cikin mamaki Abra ta ce, "Me yasa? Duk sauran students ɗin dake yawo a haka fa?"
"Ni ke kaɗai na sani, gaskiya zan cewa Abbi duk ya sauya miki uniform ɗinki, ba na son ganin ki da waɗannan."
Tace "Sannu Yaya."
"Ai dama ni ne Yayan ko ba ki faɗa ba." Dai-dai nan suka ƙarasa parking space inda direban sojan da zai kai su yake jiran su, hakan yasa Abra ba ta kuma magana ba.
Masha Allah, an samu sauyin gwamnati, bayan shafe dogon lokaci waccan jami'iyya ta na mulki, duk ta yi iyakar bakin ƙoƙarin ta, gurin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro, amma abun ya ci tura, a wannan karon sabuwar gwamnatin ta zo da sabbin tsare tsare, ciki har da yiwa harkar tsaro garan bawul, aka kawo sauye sauye da dama.
Sauyin gwamnati da aka samu ya sa da yawa daga cikin iyayen gidan General Ibrahim da suke harƙallar su tare ba su koma ba, sedai a hakan gwamnatin ta sake ɗibar kara da kiyashi a tafiyar, dan an kuma kitso da kwarkwata gurin zaɓen muƙarraban gwamnati, dan akwai sauran ire iren wanda su ka yiwa waccan gwamnati aiki, suka hanata cigaba suka hana ƙasa cigaba.
Amma duk da haka a wannan karon, jami'an tsaro ma su cike da son ganin zaman lafiya ya wanzu a ƙasa, suna cike da farincikin sauye sauyen da aka samu a harkar tsaro, kuma suka sa ran cewar alamu sun nuna ƙarshen harkar ta'addanci a ƙasa yana kusantowa.
Sabon shugaban ƙasar ta bakin me magana da yawunsa, ya fitar da sanarwar cewar babu yafiya ga duk wani wanda aka kama da laifin ta'addanci ko yi wa harkar tsaro zagon ƙasa.
Sannan duk wanda aka kama da laifin mallakar makami ba bisa ƙa'ida ba musanman bindiga, to hukuncinsa ki sa ne, ba tare da wata Shari'a ba.
Haka zalika duk wanda aka samu da fitar da sirrin rundunar tsaro, shi ma ze zama a cikin 'yan ta'adda kuma hukunci ɗaya za su karɓa da 'yan ta'addan.
Se dai an kai ruwa rana akan wannan ƙuduri na gwamnati kan majalissa su amince, kasancewar shugaban ƙasa a tsaye yake, ya sanya shi tsayawa kai da fata akan dokokin, tare da ba da umarnin bincikar duk wani ɗan majalisa da ya soki wannan ƙudurin.
Da yawa cikin marasa gaskiya ya ɗuri ruwa, dan wannan gwamnati da gaske ta ke, irinsu General Ibrahim kuwa, ciki ya ɗuri ruwa gashi akwai yiwuwar ai musu retire, kuma shugaban ƙasa ya kafa kwamiti na musamman, dan bincikar yadda akai da maƙudan kuɗaɗen da aka dinga sawa a harkar tsaro, gwamnatin baya.
Yau ta kama Saturday, da rana bayan su Abra sun dawo daga Tahfiz suna zaune a parlour suna game ita da Salman, Na'ima tana kallon wani program a tv, Khamal kuma yana karanta News paper.
A shagwaɓe ta ɗago fuskarta tana kallon Salman dake ƙunshe dariyarsa, dungurar masa da Game ɗin ta yi ta ce. "Ni dai ban yarda ba wayo kawai kake mun."
Dariyar da yake ƙunshewa ya saki ya ce. "Akan me zan miki wayo, ki yarda kawai na fiki iyawa."
Turo ɗan ƙaramin bakinta ta yi tare da kawar da kanta gefe. Murmurshi ya yi ya ce. "Shikenan mu sake yin wani, ke zaki ci insha Allahu."
"Ba zan yi ba ɗin, girki ma zan tafi in ɗora."
"Haba ƴar ƙanwata ki tsaya mu ƙara ɗaya Please, ƙara koya miki nake son yi yanda gobe zaki winning a kaina."
Na'ima dake sauraren su ta harare shi ta ce, "Ka bar ta, ta je yi aikinta, kai tunda ba ka da abun yi sai zama a cikin gida tare da mace sai ka yi ta yi ai." A hankali ta yi maganar yanda Khamal ba zai ji ba, kasancewar ta fi shi kusa da su.
Jiki a sanyaye Abra ta miƙe da niyyar zuwa kitchen.
"Daughter ku shirya ku je ku gaishe da su Mama yanzu."
Muryar Abbinta da ya faɗi haka yasa ta tsayawa cak ƙirjinta ya faru dukan uku_uku, domin ko kaɗan ba ta ƙaunar abun da zai kai ta gidansu Mahaifiyarsu ko gidan wani nata, saboda tsana ƙarara da suke nuna mata.
Salman da shi ma ba son su je yake ba saboda kar a ɓata ran Yayarsa ya ce. "Abbi akwai Islamiyya fa, ƙarfe huɗu za mu koma."
Khalmal ya ce, "Za ku iya zuwa ai ku gaishe su kafin time ɗin, tunda yanzu ko 1:30 ba ta yi ba, weekend ɗin nan shi kaɗai time ɗin da kuke da shi na ziyara, dama suna ta complain ba kwa zuwa sosai." Jiya Mama ta kira Na'ima a waya ta bawa Khamal dan su gaisa, shine bayan sun gaisa ɗin cikin kissa take ce masa su Abra ba sa zuwar musu sosai, shi yasa ya ce su je yau su gaishe ta.
"Abbi to ai girki Yaya Abra za ta yi."
"Salman! Gidan namu ne ba ka san ku je ko me? Dan girki idan kun tafi ba sai in yi ba?" Cewar Na'ima cikin haɗe rai.
"Allah ya baki haƙuri Mami, ba haka nake nufi ba." Ya yi maganar tare da miƙewa tsaye.
Numfashi Abra ta sauke ta ce. "Bari mu shirya sai mu je yanzu Abbi."
"Yawwa ƴaƴan albarka, Allah ya albarkaci rayuwarku."
"Amin." Suka amsa gaba-ɗaya.
Salman yana duban Abra ya ce. "Ki yi sauri ki shirya kar ki tsayar da ni, dan na san hali."
Murguɗa masa baki ta yi ba ta ce komai ba ta shige ɗaki.
Kasancewar sun yi wanka kafin su tafi Tahfiz, kaya kawai ta sauya ta saka wata doguwar rigar abaya mai kyau da tsada purple colour, ta yi kyau sosai dan rigar ba ƙaramin haskakata ta yi ba. Ta fashe jikinta da turaruka masu sanyin ƙamshi sannan ta ɗauki handbag ɗinta ta fito parlour. Sallama ta yiwa iyayen nata ta fice bayan Abbi ya ba ta kuɗi ya ce su tsaya a hanya su siyawa su Fruits, tare da addu'ar Allah ya tsare. Na'ima ta bi ta da wani irin kallo tare da sakin wani munafukin murmushi.
Suna tafe Salman na yaba kyawun da ta yi kamar yadda ya saba yi mata kullum idan ta yi kwalliya, murmushin yaƙe kawai take yi masa amma ta gaza cewa komai, saboda tsoro da fargabar abun da za ta tarar a gidansu Mama na cin mutuncin kamar yadda suka yi mata kodayaushe. Duk yadda ta kai ga ɓoye damurta sai da Salman ya gane halin da take ciki, tausayin ƴar'uwar tasa ne ya cika masa zuciya. Ya rasa laifin da ta yi da ya saka Mami da danginta ba sa ƙaunar ta.
Mintuna goma sha biyar ne ya kai su Unguwarsu Mama, kasancewar ƙaramin gida ne a ƙofar gida Driver ya yi parking Motar. Salman dake gaba ne