Showing 189001 words to 192000 words out of 231718 words
Chapter 64 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
ke".
"Me kake nufi?".
"Twin sister ɗinki da na aura, Allah ya yi mata rasuwa kwanakin baya, ta rasu ta bar mini 'yar jaririya mace" yayi Maganar hawaye na zubowa daga idonsa.
Zubewa ta yi a wurin ta ɗora hannu a kanta ta ce "Na shiga uku!"
₦300 NE DAN ALLAH KU SIYA KAN KU KARANTA MANA
08081012143
[11/12, 3:38 PM] Abk: Ƙasa Adnan ya yi da kansa cikin ƙoƙarin tsayar da hawayen idonsa amma ya ƙi tsayawa, ganin yadda yake kuka sai jikin ƴar Baba ya yi sanyi. Idanunta cike da hawaye ta ce. "Ka daina kuka, ba a son yi wa wanda ya mutu kuka, haka Inna take ce mini idan ina kukan rashin Baba." Bai ce komai ba sai da ya share hawayen fuskarsa duka, cikin raunin murya ya ce. "Ai za ki maye mini gurbin ta ko?" Turo baki ta yi ta ce. "Huh'um, wallahi ni ba na son ka, kalle ka fa baƙi." Duk da halin da yake ciki na tuna Abra sai da ya murmusa saboda yanda ta yi maganar.
"Shikenan, tunda kin fi so na auro wata ta riƙe mini ƴata, in ma muguwa ce ta cutar da ita idan bana nan."
Shiru ta yi kamar mai nazari tana kallon shi na wasu sakanni, taɓe baki ta yi ta ce. "Ina son ƴar taka, tunda ka ce ƴar'uwata ce ta haife ta, yaushe za ka kawo mini ita ko kai ni na gan ta?"
"Ranar da kika fara so na." Ya faɗa idanunsa a cikin nata.
Janye idanunta ta yi da sauri, cikin raunin murya ta ce. "Amma ka san iyayenmu? Me ya sa suka yarda da mu?"
"Ban sani ba, amma ina nan ina bincike akan hakan, ni da wanda ya riƙi Abra."
"Abra."
Ta maimaita sunan kamar mai tunanin wani abu a cikinsa. Kallon yadda rana ta fito Adnan ya yi ya ce. "Lokaci yana tafiya, mu je ki raka ni gidan Sadin."
"Gaskiya ba zan iya zuwa ba, ni roro na zan tafi, na san yanzu ana can ana ta yi, an kusa rore gyaɗar ma duka ni ban je ba."
"Mu je na taya ki."
Kallon shi ta yi cikin mamaki ta ce. "Ai ba ka iya ba."
"Sai ki koya mini."
"Tom shikenan mu je."
Suna tafe yana tsokanar ta har suka ƙarasa gonar, wani irin farinciki da nishaɗi yake ji na kasancewa da ƴar Baba, ji yake tamkar Abransa ce ta dawo. Yara da manya damƙam a gonar, sun zagaye tumin gyaɗar kowa na roro. Cikin takaici Ƴar Baba ta dubi Adnan ta ce. "Ka ga har an cika ban zo ba, ni da nake riga kowa zuwa, kuma alƙur'an sai ka taya ni." Bai ce komai ba sai idanunsa da yake ba wa abinci yana kallon yadda ake roron gyaɗar. Ƴar Baba na ƙarasawa gurin aka fara kiran sunanta, ta kula wanda ta ga dama ta share waɗanda take jin haushi. Su kuwa ƴan ƙauyen sai kallon Adnan suke, cikin mamakin ganin shi tare da ƴar Baba, suna son su tambaye ta wane ne shi, amma yadda ta yi kicin-kicin da fuska ya sa kowa ya haɗiye gulmarsa bai fito da ita ba.
"Ka zo ka taya ni, ka tsaya kana kallo na." Ta yi maganar cikin sangartar ta.
Ƙarasowa ya yi ya tsugunna a kusa da ita ya ɗauki ganye ɗaya ya fara cire gyaɗar yadda ya ga suna yi cikin yamutsa fuska, a ransa yana tambayar kansa ko mene ne amfanin wannan abun?
Wasa-wasa sai ga SP Adnan ɗan gayu mai ji da kansa ya wuni a gona yana roron gyaɗa, don hana shi tafiya 'yar Baba ta yi da rigimar ta, Sallah ce kawai take tayar da shi, rashin sabo ya sa duk ya galabaita, kayansa suka yi futu-futu da ƙura da ƙasa. Ƴar Baba kuwa sai murna take gyaɗarta ta fi ta kowa yawa, saboda taya ta da Adnan ya yi. Sai da mai gonar ya zo ya rarraba ya ba wa kowa ladan roronsa sannan suka tafi, lokacin Magriba ta kawo kai.
Suna cikin tafiya 'yar Baba ta dube shi ta tuntsure da dariya, saboda yadda ya yi wani kalar tausayi, ga shi ya taka ƙaya a gonar da ɗingishi yake tafiya, ɓata fuska ya yi bai yi ce komai ba.
"Gaskiya kai rago ne, kana namiji amma ɗan wannan aikin ya wahalar da kai, ba ni kwanon abincina da robar ruwan idan ba za ka iya riƙewa ba."
Hararar ta ya yi tare da faɗin. "Idan na ba ki da wanne hannun za ki riƙe?"
"A kai nake ɗora buhun gyaɗata, sai na riƙe kwanon a hannu, haka nake yi kullum."
Jinjina kai ya yi, a ransa yana jinjina yadda mutan ƙauye suke shan wahalar rayuwa. Har ƙofar gida ya raka ta, har ta wuce za ta shiga gida ta dawo ta ce. "Yawwa na tuna, jiya na tafi kiran Inna shi ne ka gudu ko?"
Cikin gajiyar dake addabar jikinsa ya ce. "I'm sorry."
"Ba zan haƙura ba gaskiya, sai dai in ka yarda in kira Innar ta gan ka yanzu."
"Ki bari sai gobe, zan zo na gaishe ta my Angel, yanzu duk a gajiye nake, kin ji ma an fara kiran Sallah, ko da yake na ga ke duk wunin da muka yi a gona ba ki yi Sallar ba."
Murguɗa baki ta yi ta ce. "Ina ruwanka, dama saka mini ido kake yi." Murmushi ya yi tare da kama hannunta ya riƙe, idanunsa a cikin nata yana jifan ta da wani irin kallo.
"Na shiga uku! Don Allah ka cika ni, kar Inna ta leƙo ta gan ni ko Yaya Musa ya zo wucewa." Ta yi maganar cikin tsantsar tsoro da fargaba, idanunta duka a waje tana kallon zauren gidansu.
"Have a nice night, good bye, I love you."
Ajiyar zuciya ta sauke jin ya sakar mata hannu ta rarumi bugun gyaɗarta ta yi cikin gida da gudu a ranta tana gulmar Adnan. Inna dake alwala ta saki salati tare da faɗin. "Wai ƴar Baba kanki ɗaya kuwa? Da magaribar ma ba za kina tafiya cikin nutsuwa ba? Wunin yau bakina shiru amma yanzu daga dawowar ki zaki fara sa ni magana, me yake damun ki ne wai?" Ba ta ce komai ba sai da ta koma ta ɗauko kwanonta ta dawo, bayan ta zauna a kan kujera yar tsugunne ta ce. "Inna daga dawowa ta maimakon ki tarɓe ni da ruwan sanyi na randa da abinci amma sai ki fara da faɗa? Na je na gaji na wahala amma ko ki mini sannu."
"Ba zan yi ba, tunda ke yin abin da aka ce ki yi kike yi, yarinya kina girma amma kullum jiya i yau, ai ta maimaita magana ba kya ɗauka, sai dai ta shiga ta dama ta fita ta hagu, to in ma wani motsin ne a kanki gobe zan kai ki a miki roƙiyya a fitar."
"Taɓ, wallahi ba zan biki a zane mini jikina ba haka kawai." Ta yi maganar tare da miƙewa ta shige ɗaki.
A matuƙar gajiye ya ƙarasa gidan Hakimi, bai zauna ba sai da ya rage kayan jikinsa ya yi wanka ya shirya cikin ɓaddakama ta shiga irin ta matasan garin da kayan wani ɗan Hakimi da ya aro, bayan ya yi Sallah ya naɗe ƙafarsa da hanky, ya ci cakes ɗin da ya zo da su da lemo ya ɗauki torchlight da kuɗi ya fita. Da ƙyar yake iya tafiya saboda yadda ƙafar tasa ta ɗaure, ba ƙaramin cakar shi ƙatuwar ƙayar ta yi ba don da ƙyar ya iya zare ta saboda zugi da raɗaɗin da gurin yake masa a lokacin. Ba don dole ba da kwanciya zai yi a yanzu ya huta, amma aikin da ya zo yi ƙauyen ba na wasa ba ne, ga IG kullum sai ya tambaye shi akan ina aka kwana? Haɗuwa da ƴar Baba duk shi ya ɗauke masa hankali. Da ƙyar ya iya gano layin su Sadi ɗan kunama, yana shiga karnuka suka fara yi masa welcome da haushi..
"Kai, waye a nan?"
Muryar wani ɗan tauri cikin shaye-shaye ta doki kunnensa.
Cikin ƙwarewa a aiki ya sauya muryarsa zuwa ta yan yawa ya ce. "Ni ne, abin zuƙa nake buƙata, an ce mini babu inda zan samu sai nan."
Haske shi aka yi da fitila mai haske ba tare da ya san waye ba, sai da suka ƙare masa kallo sannan wanda ya yi magana da farko ya ce. "Kawo silalla a baka abun duniya Baba." Bai ce komai ba ya zaro kuɗi ba tare da ya ƙirga ba ya ba su. Wiwi suka ba shi da wani abu a kwalba wanda ya tabbatar giya ce, karɓa ya yi ya zauna ɗan nesa da su yana kallon gurin cikin nazari, wani ƙaton gida da ya banbanta da ginin gidajen garin ya ƙurawa ido, ko tantanma ba ya yi nan ne gidan Sadi ɗan kunama.
Mami ce zaune a main parlour tana ba wa little abincinta, bayan ta ƙoshi ta kwantar da ita akan carpet ta shiga kitchen don ɗauraye bowl. Kafin ta fito amarya Salima ta shigo parlour'n cikin wasu matsatstsun kaya riga da wando, sai baza ƙamshi take. Ganin little a kwance ita kaɗai ya sa ta ɗauke ta cikin sauri ta fara yi mata wasa tana shilla ta tare da yi mata waƙa.
"Mamana kin fi ta kowa, ƴar fara kyakkywa, mai kama da mamanta."
"Malama ya za ki ɗaukar mini yarinya kina ciccilla ta sama a daren nan? Mene haka?" Na'ima ta faɗa lokacin da ta dawo parlour'n tare da ƙwace little a fusace.
"Ki yi haƙuri kar ki karya mata haƙarƙari."
"In na karya kina da asara ne? Haba, bana son maita, na ce bana son ana ɗaukar mini yarinya amma don naci da rashin zuciya sai an ɗauka."
"A'a, hayaniyar me nake jiyowa tun daga baranda? Lafiya?"
Abbi da ya shigo gidan ya tambaya idonsa akan Nai'ma.
Hawaye Salima ta ƙaƙaro cikin kissa ta ce. "Ban san me ya sa ba ta son na ɗauki little ba, ko na yi mata wani lefin ne ban sani ba, ni kuma ina da son yara, shi ya sa bana zuciya na ƙi ɗaukar tata." Duban Na'ima dake huci ya yi ya ce. "Na'ima ke kika haifi yarinyar nan ne ko ke kaɗai aka haifawa ita? Abra is my daughter, ke da Salima kuma duk matana ne, don haka yadda kike da iko da abin da Abra ta haifa ita ma haka, don haka kar na ƙara jin wata rigima ta tashi don ta ɗauki little."
"Wallahi ba zai yiyu ba, Abran ai ni na riƙe ta ba wata can ba, don haka nike da iko da abin da ta haifa."
"Okay, abin da na faɗa ne ba za ki bi kenan? To cigaba kar ki fasa, kar ki ɗauka wai na sauya ne daga Khamal ɗin da kika san ni saboda kwana biyu ina ɗaga miki ƙafa, fitina ce kawai bana so." Ya yi maganar cikin fusata.
Miƙewa Salima ta yi ta kama hannun Abbi tare da kwantar da kanta a jikinsa, cikin muryar rarrashi mai cike da salo da shagwaɓa ta ce. "Honey please ka bar maganar, in dai little ce ba zan ƙara ɗaukar ta ba." Bai ce komai ba sai gefen fuskarta da ya shafa cikin ƙauna.
Tsaki Nai'ma ta ja ta yi wucewar ta part ɗinta, zuciyarta cike da tuƙuƙin baƙin ciki da kishi. Tana shiga ɗaki ta goye A'isha Humairah sannan ta ɗauki wayarta ta kira Aunty Wasila, bayan ta ɗaga ta fashe mata da kuka.
"To uwar kuka, yau kuma me ya faru?"
"Na gaji Aunty wasila, na gaji da zaman baƙin ciki da ganin takaici, wallahi zuciyata ba za ta iya ɗauka ba, idan aka cigaba da haka watarana sai dai ku zo ku tarar da gawata."
"Yanzu dai faɗa mini mene ya faru."
Cikin gunjin kuka Mami ta ce. "A gabana fa Khamal yake nuna wa yarinyar nan k'auna, ya rungume ta ko ya ba ta abinci a gabana ba komai ba ne a gurin shi, washegarin da aka kawo ta da yamma har da fitowa main parlour tana tafiya ƙafa a tale, a dole sai ta nuna mini an ɓurma ta, iskanci dai kala-kala."
"Ke ma sai ki tsuro da naki salon, mijinki ne fa, kin fi kowa sanin shi, ai kowa ya iya allonsa ya wanke kawai, amma kya zauna kina wani koke-koke, har yanzu ba ki bar shashancin nan ba Na'ima? Sai ka ce a kanki aka fara kishiya? Duk kin fice daga hayyacinki."
Shiru Mami ta yi ba ta ce komai ba, ita kaɗai ta san halin zafin kishin Mijinta da zuciyarta take ciki, idan ta ga Abbi tare da Salima sai ta ji tamkar ta shaƙe su saboda tsananin baƙin ciki, ga yarinyar da shegiyar kissa da iyayi da firirita.
Washegari da safe Nai'ma ta fito don haɗa wa kanta breakfast ta tarar da Abbi da Salima zaune akan dinning suna cin abinci a cikin plate ɗaya, Salima sai nanaƙe shi take tamkar za ta koma cikinsa, shi kuma sai jifan ta yake da wani irin kallo ƙasa-ƙasa. Wani irin abu mai kaifi da zafi ne ya soki zuciyar Mami, mijinta abin son ta wanda suka shafe fiye da 20 Years tare amma yau shi ne yake soyayya da wata macen da ba ta fi Yar cikinsa ba a gabanta, ji ta yi tamkar ta juya ta koma part ɗinta, amma dai ta ɗaure saboda kar a gane halin da take ciki ta nufi kitchen, cikin yaƙi da hawayen dake ƙoƙarin fita daga cikin idonta. Kamar yadda ta yi tamkar ba ta gan su ba haka su ma suka yi, sai Salima ce ta bi ta da kallon gefen ido tare da sakin wani munafukin murmushi.
Rasa abin da za ta girka ta yi, yunwar da take ji ma nemar ta ta yi ta rasa saboda mugun ganin da ta yi, tana hawaye ta dafa noodles guda ɗaya ta juye ta a plate ta fito bayan ta goge hawayen fuskarta. Kakarin aman da Salima ta fara ne ya sa ta tsayawa cak ganin ta tashi ta shiga toilet ɗin dake parlour'n da sauri, a ruɗe Abbi ya bi bayan ta yana faɗin "Lafiya Baby? Me ya faru?" Ba ta ba shi amsa ba sai da ta gama aman, kamo ta ya yi suka fito yana yi mata sannu, har lokacin Nai'ma tana parlour'n a tsaye ta kasa tafiya.
"Baby ko na ɗauko key ɗin Mota mu tafi asibiti ne?" Ya yi maganar yana shafa bayanta.
Ƙara lafewa ta yi a jikinsa tana kallon Mami cikin yamutsa fuska ta ce. "A'a Honey ba wani abu ba ne, kawai ƙamshin turaren da Maman Salman ta fesa ne bai mini ba, tunda ta fito cikina ya fara hautsinawa, da ta dawo kuma sai na ji abin ya tsananta." Duban Mami Abbi ya yi cikin ko in kula ya ce. "Please ki daina saka turaren da kika sa, kin ga ya sa Baby amai, ko kuma idan kin san ki daina fitowa parlour idan tana nan." Ya ƙarashe maganar tare da kama hannun Salima dake ta toshe hanci suka bar parlour'n. Tsananin baƙin ciki da takaicin da Mami ta ji ba zai misaltu ba, ba ta san lokacin da ta saki plate ɗin hannunta ba indomien ta baje a ƙasa ba, cikin kuka mai cin rai ta yi part ɗinta da gudu.
"Doctor magana fa nake maka ka mini shiru, haba, I'm tired da wannan sabon halin da ka tsiro da shi, gaskiya."
"Na miki dole ki zauna da ni a hakan da nake ko kuma na ɗaure miki ƙafarki ne na hana ki tafiya? Idan ba za ki iya ba you are free to go."
Cikin tsantsar mamaki da shock Hajiya Saudat ta ce. "Yusuf! Yau ni kake fadawa ba ka ɗaure wa ƙafa ka hana ni tafiya daga gidanka ba?"
"Uwata ce ke da ba zan faɗa miki haka ba?" Ya yi maganar yana jifan ta da wani mugun kallo, kasa magana ta yi saboda tsananin al'ajabi. Dogon tsaki ya ja ya ɗauki coat ɗinsa da briefcase ya bar mata ɗakin. A wahalce ta yi zaman ƴan bori a ƙasan ɗakin jin kanta na juya mata, wata irin mummunar faɗuwa gaba ce ta ziyarce ta, lokacin da wani tunani ya ɗarsu a ranta.
Daga yanayin yadda ya shigo asibitin ma'aikatan suka san babu lafiya, dama kwana biyu zuciyoyinsu cike suke da mamakin rashin zuwan shi Asibitin, kasancewar wannan ne karon farko da hakan ta taɓa faruwa. Suna gaishe shi amma ba ya amsawa, fuskarsa a cukule ya ƙara office ɗinsa. After 30 minutes ya aiko a kira masa Nurses and doctors ɗin dake asibitin. Bayan sun hallara ya dinga kiran su ɗaya bayan yana ba su wani envelope. Fuskokinsu cike da mamaki suke baro office ɗin.
"Na shiga uku! Takardar sallama fa na gani." Cewar Nurse Basira cikin tashin hankali.
"Ni ma haka." Sauran Nurses ɗin gurin suka haɗa baki gurin faɗar haka.
Kafin su ƙara magana wani likita ya fito daga office ɗinsa fuskarsa ɗauke da tashin hankali, yana share zufa ya ce. "Don Allah ko kun san laifin da na aikata da na cancanci kora a asibitin nan? A sani na ni dai ban yi komai ba."
"Ai ba kai kaɗai aka kora ba, mu ma nan duk korarraru ne."
"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, to me yake damun Doctor Bulama? Me aka yi masa da lokaci ɗaya zai kori fiye da rabin ma'aikatan shi? Anya lafiya kuwa?"
"Ƴar Baba ki je ki ɗebo mana ruwan nan, ko na shiga banɗaki fa babu a gidan nan."
Diddire ƙafa ta fara yi tare da faɗin. "Wai don Allah Inna da girmana zan fita ɗiban ruwa? Salan a raina ni."
"Ni zan fita in ɗebo kenan? Don yau ɗaya mai ɗebowar ba ya jin daɗi shi ne ba za ki fanshe shi ba? Shi ba mutum ba ne kenan da kullum yake ɗebowa kike facakar ki da shi."
Ba ta kuma magana ba ta figi mayafinta ta ɗauki botikan ɗiban ruwan da guga ta fice kamar za ta tashi sama.
"Budurwar ƙauye."
Ta tsinkayi muryar Adnan a kanta yana kiran ta. Tsayawa ta yi amma ta ƙi juyawa ta kalle shi, sai cuno baki take kamar zai taɓo sama.
"Ni fa ba sunana budurwar ƙauye ba, ba haka Babana ya raɗa mini ba gaskiya."
Murmushi ya yi ya ce. "Ina zuwa da wannan botukan?" Ya soso mata inda yake mata ƙaiƙayi,