Showing 162001 words to 165000 words out of 231718 words
Chapter 55 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
karan ba zai kuskuren da ya yi a baya ba, dole ne samu mafita, wacce zata yaye masa ciwon dake cin zuciyarsa na tsayin shekaru masu yawa. At this time dole ne idan Abra ta samu lafiya ya aiwatar da burin zuciyarsa duk da yana tunanin hakan abune mai wahalar gaske.
Zuwan Dr wajan shi ne ya katse masa tunanin da yake, a hankali ya juya idanunsa da ya yi jajur ya kafe likitan dashi kamar yadda shima yake kallonsa. Likitan yaja numfashi bayan ya gama ƙare musu kallo, amma bai ga wanda yake nema ba cikin ƙasa da murya ya ce.
"Where is Adnan Aliyu Matawalle?" Ya faɗa idanunsa akan Abban Adnan. Abba ya juya baya kaɗan ya ce " There he is behind you" Abba ya faɗa yana mai ɗaga murya "Adnan, Adnan" ya kira sunansa da ƙarfi kiran da babu wanda Adnan yaji ya tafi can duniyar tunani gaba ɗaya baya cikin hayyacinsa. Sai a kira na huɗu sannan ya miƙe a firgice yana dafe kansa dake barazanar tarwatsewa a haka ya ƙaraso wajan.
Girgiza kai kawai Likitan yai kafin ya kalli Adnan sosai cikin tausayawa ya ce "Your wife wants to see you"
Gaba ɗaya wajan suka miƙe tsaye kusan a tare suka ce "She woke up from the surgery?" "Sure. But yanzu mijinta take son gani, daga shi sai Abbi, who is he? Yana ina? ba a son mutane da yawa 1 by 1 ok" Adnan bai tsaya jin bayanin likitan ba, jiki na rawa ya nufi room ɗin da Abra ke ciki. A nutse Abbi ya ce. "See me here Dr. Ni ne Abbi" Dr ya jinjina kai ya ce "that's good after Adnan ya fito zaka iya shiga" jinjina kai kawai Abbi yai ba tare da yace komai ba, domin shi kaɗai yasan abin da yake masa yawo a cikin zuciyarsa dauriya kawai yake, ba iya Abra ce damuwarsa ba a yanzu haka kurum yaji tunanin Salman ya faɗo masa.
Hannunsa na rawa ya murɗa handle ɗin room ɗin tare da turawa a hankali without making any sounds wanda zai iya damunta ba. Idanunsa akanta ya maida ƙofar ya rufe, ban san meke masa daɗi ba, amma wata mummunar faɗuwar gaba ce ta dirar masa, a lokacin daya daidai ƙwayar idanunsa akan fuskar Abra. Gani yai tai haske sosai kamar bata da jini sai kuma cikuwar da tayi wanda hakan baya rasa nasaba da ƙarin ruwan da ake mata akai akai. Ji yai kamar an zare masa lakar dake sarrafa ganganar jikinsa da ƙyar ya iya jan ƙafarsa zuwa bakin gadon daidai kanta ya nemi waje ya zauna.
Ajjiyar zuciya ta sauke a hankali lokacin da Adnan ya zauna kusa da ita, idanunta rufe amma ta ɗan motsa kaɗan tana gyara kwanciyarta, ganin yadda take ƙoƙarin Zamewa ya sanya Adnan ɗagota baki ɗaya tare da kwantar da ita a jikinsa. "Oh sorry, sorry" ya faɗa in a very low voice ganin yadda ta cije bakinta. "Ya jikin Angel? kinji sauƙi ko, meke maki ciwo yanzu?" Adnan yai tambayar ajere cike da tashin hankali musamman da yaji jikinta zafi zau.
Slowly ta shiga buɗe idanunta wanda suka fara juyewa kamar mai shirin sumewa, Adnan ta kalla ba tare da tace komai ba sai binsa da take da idanun kamar wanda bata sani ba, yau ta zama ranar farko da tayi arba da fuskarsa. "Why are: you silent Angel? Talk say something" tana jan numfashi da ƙyar ta ce "It's too late to cry Adnan" a ruɗe ya ce "kamarya? bana son irin haka, ki tashi mu tafi gida i knw kin samu lafiya Madam" ya faɗa yana tallafota gaba ɗaya zuwa jikinsa yama mance da batun ƙurajen da yake tsantsami ya rufeta ruf a jikinsa. A hankali ta kwantar da kanta a ƙirjinsa domin bata da wani kuzari ga C.s ga kuma ciwon da yaci ƙarfinta, a karo na farko tun bayan aurensu ta sakar masa wani irin sanyayyan murmushi wanda ya sanya kyunta bayyana muryarta na rawa tace "Me kake tsoro? Ina tunanin za kafi kowa farin ciki Adnan? Why are so worried? zakai rayuwa free yanzu burinka ya cika, na tabbatar da cewa kuma baka sona" da sauri ya rufe mata baki da tafin hannunsa yana riƙeta sosai a jikinsa ya ce "Na tuba, na tuba, na tuba ki yafe mini Abra,nabi Allah na biki kada ki tarwatsa mini zuciya da wannan maganganun naki, bana da kalmomin yi maki bayanin da zaki fahimta amma kece rayuwata ki sanya haka a ranki" jan numfashi tayi tana riƙe hannunsa sosai fuskarta cike da Murmushi kafin ta ce "Kada ka damu, nasan an maka ba daidai ba, kamar yadda ka ke faɗa. Sai dai kayi kuskuren ɗaukan fansar abun a kaina, bana da laifi bana laifi ban san me aka akaita maka har haka ba, ka cutar dani cuta mai yawa, ka yaudareni yaudarar da banyi tunaninta daga gareka ba, ka sanya na amince da kai,na guji Salman akan ka ka nuna mini SO da ƘAUNA, a wannan lokacin bana da wanda nake so nake da muradin kasancewa da shi kamar kai Adnan Aliyu Matawalle, but why why?" Ta faɗa murya shaƙe numfashinta na sama tuni hawaye suka cika idanun Adnan bai taɓa jin akwai abin da yake ladamar aikwata kamar yadda ya cutar da Abra ba, bai taɓa zaton abin da ya aikata ba daidai bane ba sai yanzu. Kafin yai mgn Abra ta zabura tare da ƙanƙamesa jikinta na rawa ta ce "mene laifna? yanzu burinka zai cika zan barka tare da mahaifin nawa wanda ban san shi ba, daman ka faɗa ka shaida masa cewa ina tsananin son sa da ƙaunarsa ina mafarkin haɗuwa dashi amma Ubangiji bai nufa ba" girgiza mata kai yai ya yi ya ce "No Abra, stop saying that yanzu a kuma yau za kiga mahaifinki na janye ƙudirana na zubar da dukkan makamaina na ɗaukan fansa, nima soyayya da kuma haushin abin da aka aikata a gareni ya sanya nai miki haka, an rabani da farin cikina, jin daɗina, kwanciyar hankalina, garkuwata, an rabani da abu mai muhimmanci a lokacin da nake tsananin so da ƙaunar kasancewa da abun" girgiza kai kawai tayi ba tare da tace komai ba, a hankali ta zame daga jikinsa ta koma saman pillow idanunta na zubar da hawaye. Sun jima a haka kafin ta ce "Me aka ciro a cikina?" Da sauri Adnan ya ce "It's a baby girl mai kama dake sak" ya faɗa yana kama hannunta tare da riƙesa cikin nasa hannun. Murmushi tai while hawaye na zuba daga idanunta ta ce "Kama dani? Uhm ka faɗa mata cewa ina sonta fiye da komai na duniya, idan babu damuwa kayi mini alfarma" jikinsa na rawa ya ce "faɗi komai kike so Abra, ko rayuwata kikeso zan baki wallahi Allah" "ka samawa yarinyar suna Aishatul-humaira" Hawayen idanunsa ya goge "Insha Allah, daga yanzu ma na raɗa mata suna da haka, Ubangiji ya raya mana Little Aishatul-humaira zamu reneta tare mu nuna mata zallar so da ƙauna irin na iyaye wanda duk daga ni harke bamu samu ba"
Shiru tai masa idanunta rufe "Angel, Angel.. Abra! Abra".... "I'm still alive me kake tsoro" juyawa tai gaba ɗaya ta kallesa a hankali ta ce "Adnan" "na'am Angel" hannunta ya kama yana shafa raguwar sumar da tai saura a kanta ta ce "Ka yafe mini, banyi maka biyayya ba, na mayar maka da martani wanda mai dace da macen ƙwarai ba, kuma.....," Katse ta yai da faɗin "Baki mini komai ba, har wajan Ubangiji baki da laifi, idan ma Kinyi mini na yafe maki duniya da lahira don Allah ki yafe mini, na maki Al'ƙawari a lokaci na biyu zaki koma cikin gidana cike da jin daɗi da kwanciyar hankali, zan nuna maki soyayya wacce babu wanda ya taɓa samun irinta Abra, kiyi hqr ki zama mai yafiya" ita da bata zaton akwai wanda zai nuna mata soyayyar da Salman yai mata, har abada ba za'a samu ba. Murmushi tai masa a hankali fuskarta mai fidda annuri ta ce "Na yafe maka, amma zan barka ina mai jin tsanarka a zuciyata bana sonka Adnan, bana ƙaunar ganinka ina jin zafi da raɗaɗi a duk sanda na tuna abin da kai mini" a kiɗime Adnan zufa na yanko masa ya ce "No Abra kina so na, U love's me kada ki sanya zuciyarki cikin shakku akan soyayyata" hannunta ta miƙ tare da kama fuskarsa sosai ta ce "I hate you, wallahi bana ƙaunarka Adnan, kawai na san cewa na yafe maka, ina fatan ba zaka cutar da Aishatul-humaira kamar yadda ka cutar dani ba kaje abin ka, ka matsa daka kusa dani Mahaifina nake son gani" ta faɗa da ƙarfi ƙirjinta na ɗagawa sosai.
Durƙushewa Adnan yai tare da fashewa da kuka sosai ya ce "Ina Son ki Abra, wallahi Allah ina son ki matata. Since the time I've met you, I cry a little less, laugh a little harder, and smile all the more, just because I have you, my life is a better place, naji dama ban aureki ba aduk sanda na azabtar dake, a kullum cikin kunci nake kwana, Every day with you is a wonderful addition to my life's journey, ki yafe mini ina tsananin buƙatar ki...."
"Get out Adnan,I only want to see my father ka fita ka bani waje bana son ganinka wlh...," Fisgar da numfashinta yai ya sanya ta kasa magana sai rawa da jikinta ya fara. Da sauri Adnan ya miƙe yana faɗin "Bani 10 minutes Angel yanzu zan zo da Real father ɗinki I promise to you" yana faɗin hakan ya miƙe da sauri tare da nufar waje. "Adnan..." Ta kira sunansa a hankali juyawa yai suka haɗa idanu gani yai ta miƙa masa hannayenta a hankali ta ce "Come closer" kasa ƙara sawa yai murmushi ta saki tana jinjina masa kanta alamar yanzo ɗin, da ƙyar yaja ƙafarsa ya Ƙarasa wajanta yana zuwa ya zauna gefen gadon hannunta tasa ta jawosa jikinta holding nata back yai a tare suka saki ajjiyar zuciya tare da rungome juna. "I think I'm going now" hawaye na zuba daga cikin idanunta, shima kukan yake. Adnan dai bai fahimta riƙon da Abra tai masa ya shige na tunani kamar zata ɓallasa gida biyu "Am sorry Abra,.am sorry" ya faɗa yana sumbatar goshinta idanunta rufe bata ce komai ba, zare jikinsa yai da ƙyar ya jima yana kallonta kafin ya juya da sauri ya bar room ɗin.
A haukace Adnan ya fito hankalinsa baya jikinsa Abbi da Abba a tare suka ce "Lafiya mene ya samu Abra meke faruwa" bai tsaya saurararsu ba ya fita da gudu zuwa reception kai tsaye ya nufi harabar asibiti mota ya shiga kamar zai tashi daga sama haka yabar cikin asibiti.
Bayan Adnan Abba yabi, Abbi kuma da gudu ya shige room ɗin yana zuwa ya nufi kan Abra tare da kiran sunanta "Daughter" idanunta ta buɗe ta ce "Abbina?" "Na'am Daughter ya jikin?" "Naji sauƙi babu inda yake mini ciwo, Abbina ka kira min Salman ka kirasa shi kawai nake son gani Abbi ka taimaka mini don Allah" a rikice Abbi ya ce "zan kirasa ki kwantar da hankalinki zai zo insha Allah" jinjina kai tai tana ɗora kanta saman cinyar Abbi. "Abbi" ta kira sunansa kasa amsata yai sai Kallonta da yai ta ce "Allah ya saka maka da Alkairi Abbi, Ubangiji ya biya maka buƙa tunka na duniya da lahira, Allah yai maka kwatankwacin alherin da kai mini Abbi" "ya isa bana son magana irin haka, you'll be fine daughter" murmushi kawai tai domin a jikinta take jin cewa ta samu lafiya. "Abbi kada a bawa Adnan Aishatul-humaira, don Allah Abbi kada a bashi ƴata zai cutar da ita kamar yadda ya cutar dani kayi mini wannan alfarmar don Allah Abbina ka bawa Mami Aishatul-humaira na bar mata ita" Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kawai Abbi yake faɗa kafin da ƙarfi ya ce "Dr...!!!!!!".
A hankali jirgin ya sauka a airport ɗin kaduna, wajan 10 minutes da saukarsa passenger's suka fara sauka daga cikin jirgin fuskarsu ɗauke da farin ciki. Kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki haka ya sakkowa daga cikin jirgin fuskarsa babu walwala hannunsa zube cikin Aljihu, farar fatarsa sai sheƙi take ya ƙara haske sosai da ƙiba ya zama saurayi sosai sai rashin kwanciyar hankali. Farar shadda ce a jikinsa wacce ta ƙara fito da kyansa na fulani sumar kansa tai kwance gwanin sha'awa. Salmanun-faris kenan yaro mai kyau da tsarin halitta. Yana sakkowa daga cikin jirgin kai tsaye wajan texsi ya nufa ya faɗa masa sunan unguwar da zai kaisa a nan Kaduna, har suka isa ƙofar gidan kansa a kife yake hannunsa dafe da saitin zuciyarsa dake harbawa da ƙarfi, fargaba ganinta a karo na biyu bayan tafiyarsa ta riski zuciyar Salman. "Saurayi waka ke nema?" Idanunsa ya ɗaga da ƙyar ya kalli Gatekeeper ɗin kafin a nutse kamar dole ya ce "Matar gidan" "wayyooo, Allah sarki baiwar Allah ko yaya jikin nata?" Da sauri Salman ya ce "what? Waye babu lafiya mene ya samu Angel?" Gatekeeper ɗin ya ce "Ayya yaro matar gidan babu lafiya suna asibiti kwana guda kenan da yini" dafe bango Salman yai sbd jirin dake neman yarda shi kafin ya ce "Wanne asibitin?" "Tana na wani private hospital amma yarinyar na jin jiki da....," "Shut up" Salman ya faɗa a hargitse yama manta tsoho ne mutumin. Jikinsa na rawa ya shiga mota Allah yasa mai texsi ɗin bai tafi ba. A haka suka bar wajan bayan an faɗa musu sunan asibitin mai texsi ɗin kuma yace ya san wajan.
Gudu kawai Adnan yake shararawa a mota ikon Allah ya kai sa cikin wajan, ko kashe motar bai ba ya nufi ciki da gudu mutanan da suke cikin reception ne sukayo kan Adnan "Malam lafiya ka faɗo mana kamar wani sabon kamo kana neman taka mana patients?" Wani irin banzan kallo ya watsawa mai mgn ɗin kafin ya nufi ciki kai tsaye kuma wani office ya nufa.
Yana zaune saman chair yana duba wani files kamar daga sama yaji an shaƙo wuyansa tare miƙar dashi tsaye. Kallon Adnan mutumin yai sosai kafin ya ce "who are you? How dare you come to my office without my permission eh? Mene matsalarka ba zan taɓa ko wanne mara lafiya ba sai an bada kuɗi cash, shi talaka wani lokacin bashi da lissafi gaba ɗaya" a hargitse cike da zafin zuciya Adnan ya ƙara shaƙe mutumin cikin zafin da ƙonar zuciya ya ce "Waye ni kake tambaya?" Mutumin ya ce "E, waye kai kuma da izinin wa ka shigo mini office" idanun Adnan cike da hawaye ya ce "Think.."
"I don't have much time to think just explain Malam ko na kira securities" ƙara shaƙe masa wuya Adnan yai har sai da idanunsa ya fito waje kafin cikin ƙaraji kamar zaki Adnan ya ce "I Adnan Aliyu Matawalle, Yanzu ka tuna ko?" A wahale Mutumin ya ce "No, i can't ka sakeni Malam" girgiza kai Adnan yai kafin ya zaro Wayarsa daga cikin Aljihu ya shiga photos folder da aka saka _Life partner_ photon Abra ya fito dashi ya nunawa mutumin ya ce "Itama son zuciyarka ya sanya zaka kashe ta? Ya sanya zaka rabani da ita kamar yadda ka rabani da Mahaifiyata shekaru kusan 30 da suka shige? Ramin mugunta daman ance ka gina shi daidai kanka, ƙaiƙayi mai komawa kan masheƙiyya" mutumin ya kalli photon Abra sosai gabansa na faɗuwa ya ce "Wacece ita? Me nayi mata? Yaushe na aikata mata wani laifi?" Wani wawan kallo Adnan yai masa cikin ɗaga murya ya ce.
"Ƴarka ce, wacce ka haifa da cikinka Abra Yusuf Garba Bulama.. duk abin da ya sameta dalilin G.Y Bulama hospital ne, wallahi idan na rasa matata kamar yadda na rasa mahaifiyata a sanadin wannan matsiyacin asibitin sai nayi Shari'a dakai, a wannan karan ba a matsayin talaka nazo ba, ba kuma a matsayin wanda ya kawo mara lafiya nazo ba, nazo tafiya dakai ne dalilin matata kuma ƴarka wacce ta buƙaci ganinka, kaje kaga halin da take ciki dalilin wulaƙanta ta da kayi asibitin ka, ka sanya anyi mata Allurar da sam bai dace da ciwonta ba" yana faɗin hakan yai cilli da Dr G.y wanda tunda Sp Adnan Aliyu Matawalle yake Masifa babu inda yake kallo sai fuskar wayar Adnan ɗin, zallar kamarsa yake kalla a fuskar Abra, wace ƴarsa? Yaushe ya samu yarinya kamar Abra? Duk duniya Yarinyarsa ɗaya Meenal, sai kuma wanda suka mutu bada haka ina ya samu wata yarinya? Zallar kamannin da suke da Abra ya ƙara sanya Dr G.y cikin ruɗu da kuma tashin hankali, ya kasa fahimtar komai shi kansa Adnan bai gama fahimtar wanne laifi ya aikatawa yaron ba, balle kuma ya samu zarafin tunani akan Abra?.
Wayar Adnan ce ta fara ƙara ganin sunan Abba ya sanya ya ɗaga kiran da sauri yana faɗin "Abba ya jikin Angel?" Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Abba ya sauke kamar ba zai mgn ba sai kuma ya ce "Duk inda kake kazo asibiti yanzu Adnan" jikin Adnan na rawa ya ce "Mene ya samu Abra Abba? Don Allah kada ka faɗa mini abin da zai iya tarwatsa mini zuciya" Abba ya ce "No lafiya lou take, infact ita ke nemanka" ajjiyar zuciya ya sauke ya ce "ok I'll be there yanzu Abba".
Hajiya Mama ce ta riƙe Mami sosai wacce take rusa kuka tana neman kwacewa, Ammi na zaune ta kifa fuskarta a cinyarta tana salati da ƙarfi, Abbi kam yana jingine da jikin bango idanunsa sunyi jajir waya riƙe a hannunsa sai trying number Salman yake amma babu. Abba sai safa da marwa yake. Kamar daga Sama haka Abbi yaji saukar Muryar Salman cikin kunnansa yana faɗin "Abbi" da sauri Abbi ya juya domin ya ɗauka kunnansa ne kawai yaji haka, ganin Salman ya sanya Abbi sakin numfashi da sauri yaje ya rungomesa yana faɗin "Allhamdulillah" "Abbi Abra?" Kafin Abbi ya bawa Salman amsa wani Dr ya fito da sauri yana faɗin "waye Salman?" Da sauri Salman ya ƙarasa yana faɗin "I am" "Abra..." Kafin ya Ƙarasa Salman ya kwasa da gudu