Showing 183001 words to 186000 words out of 231718 words
Chapter 62 - Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt
kan cikakkiyar sumar kan A'isha Humairah.
"Wifey."
Ya kira sunanta cikin wata irin murya. Duk yadda ta so daurewa kasawa ta yi ta fashe da kuka, cikin kukan ta ce. "Da gaske Khamal kishiya za ka yo mini? Ni ce fa Na'iman ka uwar Ƴaƴanka, me na yi maka ka zaɓi hukunta ni da abin da zuciyata ba za ta dauka ba, ka san ba zan juri ganin ka tare da wata ba.
"Babu abin da kika mini Na'ima." Ya yi maganar yana ɗauke A'isha daga kan cinyarta ya kwantar da ita a gefe. Cikin ƙauna da kulawa ya rungume ta tare da faɗin. "I'm sorry, Ina son ki sosai matata, kuma duk wata mace da zan so a bayan ki take." Rarrashin ta ya yi sosai da daddaɗan kalamai har ya samu ta yi shiru, bai bar ɗakin ba sai da ya tabbatar ya sanyaya mata rai, ya yi musu pictures a wayarsa tare da A'isha Humairah, yana fita ta ƙara fashewa da kuka, a haka su Hajira suka dawo suka same ta.
"Mene haka? Kukan na mene kuma? Sai kin ɓata kwalliyar? Haba Nai'ma sai ka ce wata yarinya, jama'a sun fara taruwa ke kuma kina nan kina kuka? Haka za a kawo amaryar kina wannan sakarcin? To wallahi idan ba kya danne kishin ki za ta samu lagon ki tana ƙunsa miki baƙin ciki, ki je ki yi tunda ke ba kya jin magana."
"To ni Aunty Wasila ya kuke so in yi? Ko don ba ku san me nake ji ba ne a cikin raina?"
Ganin yadda take kuka kamar za ta shiɗe sai suka shiga lallaɓa ta, har ta haƙura ta yi shiru ta shiga hada-hada da jama'a. Biki ya ƙayatar sosai, Nai'ma ta saki ranta ana ta hidima da ita, duk da ba ƙaramin dauriya take ba, don ji take tamkar ana rura mata garwashin wuta a cikin zuciyarta. Bayan Magriba aka kawo amarya, kafin ƙarfe tara kowa ya tafi, gidan ya rage daga Na'ima da Humairah sai amarya a part ɗinta, sai mai gadi da sauran masu aiki dake waje. Na'ima tana zaune tana ta trying numbern Salman amma ta ƙi tafiya Abbi ya shigo gidan. Part ɗinta ya zarce direct ya ajiye mata yoghurt da kazar ta, sannan ya sanar mata yana son ganin su a main parlour. Ba ta yi musu ba ta ce masa ga ta nan zuwa. Sai da ta kwantar da A'isha Humairah a cikin net ɗinta sannan ta yafa mayafi ta fita. Shigar ta parlour'n ya yi daidai da ɗago kai da amarya ta yi tana gyara mayafin jikinta. Turus Nai'ma ta ja ta tsaya cikin tsananin ƙaduwa da mamaki, lokaci ɗaya gabanta ya yi mummunar faɗuwa, sakamakon tozali da fuskar amaryar.
Littafin kuɗi ne, don neman ƙarin bayani ku tuntuɓe mu a wannan lambar. 09047871750
[11/9, 8:06 PM] Abk: Da mamaki Na'ima ta din ga bin amaryar Abbi da kallo,dan abin da take gani ya saɓa zatonta, a tunaninta zata ga Salima, tsinanniyyar karuwar data maƙalewa mijinta Khamal Khamis. Matar data tsani jin ko sunanta balle kuma ta yi tozali da mummunar fuskarta wacce take ƙara harzuƙa Mami. Amma sai taga akasin haka dan kuwa wannan Salimar baƙa ce sannan yarinya ce ɗaya shakaf.
Danne mamakinta ta yi tare da ƙarasowa ta nemi kujera can gefe da su ta zauna ba tare da tace musu komai ba.
Gyara zama Abbi ya yi, yana ƙarewa matan nasa kallo cike da Soyayyar ko wacce a zuciyarsa,sai dai son wata ya rinjayi na wata. Sauke numfashi ya yi kafin yai gyaran murya yana kallonsu duka, a hankali ya fara magana yana ɗan satan kallon Na'ima da yaga ta sunkuyar da kanta tana kallon ƙasa,kwata-kwata taƙi kallon inda yake zaune bare kuma amarya tasa Salima.
Nasiha ya yi musu sosai akan yadda zasu zauna da juna lafiya, su mutunta juna sannan ya juya ga Salima yana faɗin.
"Salima ga yayarki nan, bana so ki ɗauke ta a matsayin kishiyarki ina so ki ɗauke ta a matsayin ƴar uwarki,wanda zaki iya tunkarar ta idan abu ya shige miki duhu, sannan ina so in sake jaddada miki ban aureki dan bana son Na'ima ba, ina son matata, bata taɓa nuna gazawa akan kulani da kuma iyalina ba, kada ki sawa ranki cewa don bana son matata na aureki ba, na aureki me sbd Ubangiji ya bani damar hakan. Allah ya ƙaddara ni acikin mutanen da zasu ƙara aure sannan su zauna da mata sama da ɗaya, saboda haka ina so ki girmamata ki mutunta ki bata girmanta a matsayinta na wacce take gaba da ke"
Ita dai Na'ima har lokacin kanta a sunkuye yake tana yaƙi da hawayen dake son zubowa kan fuskarta amma taƙi bashi daman hakan, cikin kulawa Abbi ya juyo ga Na'ima ya ce.
"Uwargida sarautar mata, Mrs Khamal ga ƙanwarki nan na kawo miki ita, please Na'ima bana so ki ɗauke ta less than a sister, ki gyara mata inda tayi kuskure ku taru ku bani farinciki, sannan bawai nayi aurennan bane dan kin gaza a wani guri ba,nayi aure ne dan Allah ya bani dama kuma ya hore mini arziƙin da zan zauna daga mace ɗaya har zuwa huɗu, saboda haka ina so ki karɓeta hannu bibbiyu ku zauna lafiya hakan zai sanya ni cikin farin ciki"
Ƙala Na'ima bata ce ba, sai ma amarya Salima ce tayi gyaran murya tare da soma magana cikin kissa
"Insha Allah zaka same mu masu maka biyayya, kuma daga yau wallahi na ɗauke ta kamar ƴar uwa kuma ina fatan nima zata ɗauke ni haka, Insha Allah babu abin da zaka samu daga garemu sai tarin farin ciki mara yankewa mijinmu"
Murmushi kawai Abbi yayi kafin yace "Na gode"Sake kallon Na'ima yayi
"Baki da abin faɗa ne uwargidan Khamal?"
"Eh" kawai ta faɗa tare da miƙewa tana gyara mayafinta.
"zan iya tafiya?"
"Eh kije sai da safe"
Bata jira komai ba tayi wucewarta ɗakinta, a hankali ta mayar da ƙofan ta rufe tana sauƙe ajiyar zuciya tare da bin ledojin da ya ajiye mata a bedside da kallo, ƙarasawa tayi ta buɗe, kaza ce guda uku sai fresh milk da sauran tarkacen su fruit da sauransu, tsaki tayi tare da sunkutar ledan ta fito falo, ganin Abbi shi kaɗai yasa ta ƙarasa ba tare da tace masa komai ba ta ajiye ledan akan table ɗin gabansa kafin ta juya zata bar wajen.
"Na'ima" ya kira sunanta a hankali
Daka tawa tayi da tafiyar da take ba tare da ta juyo ba, tana ƙoƙarin mai da hawayen idanunta.
"Please ki kawo min Aishatul-humaira , i want to say goodnight"
Juyowa tayi a fusace kamar za ta yi magana sai kuma ta fasa kallonsa kawai take hawaye na bin fuskarta, cikin sauri Abbi yace
"Sorry Allah ya baki haƙuri, kije ki kwanta sai da safe we will meet in the morning, ki shafa min kan Aishatul-humaira bye"
Daga haka ya miƙe ya nufi ɗakin Salima ba tare da ya sake cewa komai ba, ɗan juyowa ya yi yaga har lokacin tana tsaye ta ƙura masa idanu tana kallonsa ɗan murmushi Abbi yayi cikin tsokana yace.
"Ko zaki rakani ɗakin amarya?"
Kukan da take dannewa ne ya ƙwace mata kawai ta fashe da kuka tare da rugawa da gudu ta shige ɗakinta ta rufo ƙofar tana ci-gaba da kukanta.
Murmushi kawai yayi kafin ya kakkashe komai ya wuce ɗakin amarya Salima.
Washegari ma dai Na'ima ƙin tashi tayi bare tayi musu breakfast kamar yadda yawanci uwargida ce ke yi, sai ma Salimar ce tayi girkin, da tazo kiranta ma ko kallo bata ishe ta ba, cikin jin haushi Salima ta juya ta bar ɗakin tana faɗin
"Mtsww cikin ki ko cikina kar ma ki ci mana" ita kaɗai tayi breakfast ɗinta kasancewar da ma Abbi baya fitowa da wuri, tana cikin karyawar Abbi ya fito kujera ya ja ya zauna yana murmushi tare da faɗin
" Amarya bakya laifi" sunnar da kai tayi tana murmushi itama kafin ta miƙe tana tambayarsa mai zaici tayi serving ɗinsa, ganin Na'ima bata wajen ya sashi faɗin
"Ina antyn taki kuma kike cin abinci ke kaɗai?"
Cikin kissa da kisisina ta shiga faɗin
"Wallahi nayi nayi ta zo muci abincin amma ko kallo ban isheta ba,kuma dama da naga ba tayi girkin ba na shiga kitchen nayi da kaina, shi ne naje part ɗin nata atleast tazo muci amma ban san ko mane yake damunta ba ko zaka kirata?"
Miƙewa kawai Abbi yayi ba tare da ya karɓi plate ɗin soyayyen dankalin da take miƙa masa ba ya wuce ɗakin Na'ima
A kwance ya sameta ta bawa ƙofan baya, jingina yayi da ƙofan kafin yace
"Morning wifey"
Bata juyo ba bare ya sa ran zata kula shi,
"Me yasa kika ƙi fitowa muci abinci?"
"Bana ra'ayi a ƙoshe nake"Ta faɗa ba tare da ta juyo ba.
"Okay to, shikenan" ya faɗa tare da ƙarasawa ya ɗauki Aishatul-humaira dake ta wasan ta abin ta, zama yayi a gefen gadon yana mata wasa yana ɗan satan kallon Na'ima har dai ya gaji ya miƙe ya fice a ɗakin nata.
Shima kaɗan yaci abincin kafin ya miƙe ya fice a gidan ma gaba ɗaya.
Gidansu Ammi ya wuce ya gaishe su tare da sanar dasu dama yanaso ya koma bakin aikinsa cikin satinnan, babu wanda yace masa komai sai fatan alkhairi da suka masa tare da tambayar lafiyar su Na'imar.
A kishingiɗe yake akan kujerun da ke gaban beach ɗin yana kallon yanda ruwa ke gudu akan surface ɗin, yana sanye cikin kayan shan iska guntun wando ne da ya wuce gwuiwarsa da kaɗan sai riga short sleeve, idanunsa da sunglasses sai cup na soft drink dake hannunsa.
Faris kenan, wanda zuwa yanzu ya ƙara wani irin kyau da girma na ban mamaki, duk da har zuwa yanzu tunanin Abra ya kasa barin zuciya da gangar jikinsa, ya riga ya san ya rasa yayarsa har abada amma bai san me yasa ya kasa daina tunaninta ba.
A hankali ya ajiye cup ɗin a gefensa yana ɗaukar wayarsa ta ke ta ruri tun ɗazun, ganin Mami ce mai kiran ya sashi saurin ɗagawa tare da yin sallama.
Na'ima da har ta sadaƙar Faris bazai ɗauki wayar ba jin ya ɗauka ya sata fashewa da kuka.
"Faris ina son ganinka urgently please ka dawo gida, akwai matsala ka dawo ina buƙatarka a kusa dani"
Da sauri ya miƙe zaune hankali a tashe yake faɗin
"Mami, lafiya?me ya faru?me aka yi miki sanar dani"
Bata sake cewa komai ba sai ji yayi ta kashe wayar.
Cikin sauri ya lalubo number Abbi, bugu ɗaya ana biyun ya ɗauka yana faɗin
"Faris ya akayi? "
"Me ya sami Mami?"
"Da akayi me ?"
"Yanzu ta kirani tace in dawo tana buƙatata kuma naji tana kuka me ya faru Abbi"
"Kana jina Faris, kar ka damu da Maminka ta kasa daina tunanin Abra ne, maybe ta tuna ta ne shiyasa take kuka, ka kwantar da hankalinka, ka dage da karatunka duk da nasan bazaka iya dainawa ga baki ɗaya ba but please ka rage tunani more especially akan Abra kaji?"
"Na ji Abbi but please you should be there for Mami, kaga yanzu bata da kowa bana nan yaya bata nan"
"I will, karka damu"
Daga haka suka yi sallama, ajiye wayar Faris yayi yana sauƙe numfashi, ya zai yi ya kasa hana kansa tunanin Abra, be couldnt stop himself but zai yi ƙoƙari yaga bai shafi studies ɗinsa ba insha Allah.
Ƴar Baba na kwance a daɗi tai shiru idanunta rufe amma ta lula duniyar tunani, waye wannan ɗan gayon da yake ta damunta ne? Wace kuma Babur take kowa. Ko dai Aljani ne?.
Da sauri ta girgiza kanta kafin a fili ta ce "Allah ya sauwaƙe na zama matarsa, ɗan Iska ne" da sauri ta ja iska tana shaƙar Ƙamshi ta ce "Kuma turarensa mai daɗi ne, amma baƙiƙƙirin dashi".
"Wai Meke damunki ne ƴar baba? Ki yi ta kwanciya a ɗaki kamar ruwa, maza tashi kafin na dokeki" turo baki tayi cikin taɓara wacce ta zama ɗibi'arta ta ce.
"Ni kam Inna idan kin tsaneni ne kawai ki faɗa mini na sani, bani da lafiya fa? Ba kiga na rame nai zuru-zuru ba, sai ki tayin mita da faɗa"
Inna ta shiga tafa hannu sosai tana faɗin "Na shiga uku, yau naga abin da yafi ƙarfina,wai wacce irin yarinya ce ke ƴar baba? Ace ba zaki hankali ba kisan Annabi ya faku kalli sa'aninki fa duk suna ɗakin mazajansu amma ke jiya iyau" "Inna kina nufin nafi ƙarfi kenan? Gudana nawa nake gaba ɗaya da zanfi ƙarfin fisabilillahi" sai ta fashe da kuka tana kifa kanta a cinya.
Zama Inna tayi tare da yin ƙasa da murya ta ce "Haba ƴar baba shallen Inna, ƴar gatan yayanta Musa, daina kukan kinji share hawayen ki saurare ni"
"Ba dole nayi kuka ba Inna, tunda Baba ya rasu mitar yau daban ta gobe daban, daman shike so na" Inna ta kamata ta ce "Ba haka bane, ai ni uwa ce ba zan so ki lalace ko kuma ki sangarce a aikin banza ba, shi ya sa nake tsawatar dake amma babu abin da nake so sama dake" Ƴar Baba na dry sosai ta ce "Inna kinfi so na fiye da Yaya Musa ko?" Inna ta ɗaga kai ta ce "Sosai ma, ina ruwana da wani Musa, yanzu dai tashi ki shirya ki amso mini gyaɗa tun safe ake sallama a nema" turo baki tayi tace "Ke Inna wai babu wata sana'a sai gyaɗa ni banga wata riba a ciki ba" Inna ta riƙe haɓa ta ce "Oh! To aini na gani maza tashi tunda mun shirya idan ba mitar kike so ba, saura kije ki yi ta tsokana kina ja mana bada hqr ana zama lafiya"
"Ni dai Inna ba zan kulaki ba, ki barni kawai da tunanin da nake shi kaɗai ya isheni" Inna ta ce "Meke damunki ƴar baba?" Shiru Ƴar baba tai tana mirginawa tare da juyawa Inna baya. Inna ta taɓe baki tai waje tana faɗin "Allah ya kyauta,ya shirya mini ke".
Inna na fita ƴar Baba ta miƙe ta cire kaya tare da nufar banɗaki wanka tai, ta shirya cikin wata atamfa mai kyau, duk da cewa a ƙauye take amma bata zama cikin mummunar kama, Baba kafin ya rasu yana iya ƙoƙarinsa ganin ya kyautata mata, komai ya gani ƴar Baba haka Yaya Musa. Hakan yasa take da komai na buƙatun rayuwa kaf ƙawayenta ta fisu suttura mai kyau.
Ƴar Baba na gyara zaman mayafin jikinta, ba wata kwalliyya a fuskarta dai kwalli da man leɓe hakan yasa fuskar tai sharr gwanin sha'awa, ga ɗan jikin nan nata ba auki wanda yake ƙara ɓoye shekarunta. "Allah ya a tsare, ki kula banda shirme banda....," Kafin Inna ta Ƙarasa Ƴar Baba ta ce "Banda tsona da kula samari, haka zaki ce ko? Ni fa duk na hadda ce wannan sai dai wani abun" girgiza kai kawai Inna tai. Ƴar Baba ta fita zuwa karɓar gyaɗa.
A hankali take tafiya duk wanda ta gani sai ta murguɗa masa baki "Ƴar Baba an fito ne?" Cewar wani saurayi riƙe ƙugunta ta yi tana murguɗa baki ta ce "Wai kai sani mene matsalar ka dani ne? Ko baƙin ciki naka baban baya son ka?" Sani ya ware ido ya ce "Wai ni na isa na haɗa kai na dake ne? Ai ke ce sarauniyar ƙauyen nan kawai ki bani dama na nuna bajinta ta" tsaki tai ta ce "Allah ya sauwaƙe me zan dake, jibi ƙaton baki da ido ƴan mitsi mitsi ka fita a harkata wallahi" tana faɗin haka tai gaba Sani ya bita da idanu. A haka ta Ƙarasa gidan amsar gyaɗar mai maimakon ta amsa kamar yadda Inna taso sai ta nemi waje ta zauna suka kafa hira.
Adnan na jingine a jikin wata bishiya ya harɗe hannayensa a ƙirji, yana sanye da wasu manyan kaya masu kyau, wanda suka haskaka baƙar fatarsa, fitowar sa kenan daga gidan da yake zaune sbd ya gaji da zama, honestly ma ba zai iya zama ba tare daya ƙara tozali da Yarinyar nan ma wacce yake jinta tamkar matarsa Abra. Lokacin guda so da ƙaunar Ƴar Baba ya gama ratsa zuciyarsa har yana jin babu abin da zai hana ya mayeta da gurbin murgayiya Abra Khamal Khamis. Ita ce zata goge masa tabon dake maƙale a zuciyarsa. Numfashi ya sauke yana duba agogon hannunsa ganin rana na shirin faɗuwa.
Yana ƙoƙarin juyawa idanunsa ya sauka akan ta tana tafe farantin gyaɗa na kanta sai fari dake da idanun. Wani sanyayyan murmushi ya yi yana dubanta frm head to toe. Buwayi gagara misali. Al-hakkamu mai tsara komai a lokacin da ya so. Yana ganin identical twins masu tsananin kama da juna, amma bai taɓa ganin mutane masu kama da juna irin ƴar Baba da Abra ba. "Something fishy" ya faɗa cikin ransa.
Ƴar Baba har ta shige ta gabansa bata lura da shi ba, kamar daga sama taji ya ce "Mai gyaɗa a bani gyaɗa" da sauri ta juya tana faɗin "Auzubillahi wayyo Allah Inna na shiga uku" ta faɗa tana dafe ƙirjinta da hannu ɗaya. Adnan ya ware manyan idanunsa waje cike da mmki yake binta da kallo ya ce "Kamar kinga aljani?" Murguɗa baki ta yi "Malam ɗan baƙi ka fita daga sabgata, Wlh kuma aniyyarka ta bika, idan kaci gaba da bina sai na kai ƙarar ka wajan Mai Gari"
"Yanzu ko dai anjima, ko gobe?" Adnan ya tambaya "Kai baka jin tsoran Mai gari ne?" Ya watsa hannu ya ce "For what reason zan ji tsoron sa? Bayan ke ɗin matata ce ina nufin zaki zama matata kiyi ta haifa mini fitsararrun yara irinki" Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un bata taɓa jin rashin kuka da batsa irin wannan ba, ita yake cewa zata haihu iskanci fa kenan? "Wallahi ni ba ƴar iska bace, Allah ya sauwaƙe na zama matar ɗan baƙi wallahi bari kaji ba zan taɓa son ka ba, daka ganinka mugu ne" Murmushi kawai ya yi yana faɗin "Kinga kuma ni ɗan iska ɗin ne, kuma dole na aureki" banza tai masa zata juya ya yi saurin kama hannunta ya ce "Wait don tsaya sbd darajar iyayenki" jin ya ce iyaye ya sa ta tsaya ta ce "Sake ni, shi ya sa kwana biyu Inna ke ta caje ni kamar wata