Showing 324001 words to 327000 words out of 373688 words

Chapter 109 - A LOKACIN MUKE BOOK BY ZAINAB .I. MAKAWA.txt

gida,yake dawowa gaba daya shine ai ake cewa duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau sama baya hango shi.
Yaya sadauki dake gurin Baba tun shigowan mu yana mashi bayani akan tafiyan mu irin nasarorin da yayo a gurin wasu masananta da ya saka hannun jari acikin su a waje.
Yace to ke tashi mu tafi hakana ko mun bar iyya gida ita kadai mama tace yanzu yarinya na zaune tana hira zakace wai ku tashi ku tafi.
Mummy tace yanzun fa ya san dadin iyalin shi bai son zama inda muke kuma .
Yai murmushi yace wallahi mummy ba hakana bane kawai da Iyya Rabi da muka bari a gida ne ga kuma mutane suna zuwa taron mu har yanzu.
Mummy ai da zaku bamu daki a gidan nan sai munfi jin dadin zama a kusa da ku dariya sosai yaba mummy har saida tayi tagaji don kan ta.
Mama ta saki ajiyan zuciya daga inda take zaune bayan mummy ta fita daga falon tace Allah sarki ubana har na rasa farin ciki da jin dadin da zan nuna dana gan ku a gaka wallahi.
Yace kai haba maji falalar adduan ki ne fa yakaimu ga haka baki dayan mu ko Amirah yana takalar Amira da yaga ta cika ta batse da shi.
Mama tace kai amma babana baka da zuciya duk wanan iskancin da take shukawa mutane don taga ta samu guri.
Amma katsaya wani kulata can wallahi Amira da kake gani na kusa fita bayan ta muddin bata fitar da miji tai aure ba mu huta da bakin iya shegen nan nata.
Sadauki ya kwantan da muryan shi kasa cikin sanyi yace maji kiyi hakkuri don Allah nima wanan karon na dawo da wanan kudirin a raina ina son naga tayi aure itama ta kama dakin ta hakana ta huta da fadan ki.
Damu da ita dukkan mu dole ne muyi maku biyayya kada ki damu maji zata fito da miji itama tai aure badadewan nan ba zamu sha buki insha Allahu.
Mama tace Allah ya bada ikon yin hakan ga maryam har tana batun haihuwa ita ko ajikin ta.
Sai wanan lokacin Amira tai magana tace ikon Allah maji gama wanda suka aure basu da komai saini da ko auren banyi ba ake min gori.
Wani iri naji a raina da magansn da tayi nasan ni takewa gori a fakaice naji sadauki na fadin lokaci ne baiyi ba Amirah wata rana sai labari.
Kiyi hakkuri gaskiya ake fada maki ba wai ba,a sonki bane aure shine darajan diya mace zan zo mu zauna dake sai muga may yadace ayi.
Baba ya aiko akira mashi sadauki yafita yakoma dakin baba din ina zaune nai shiru don gaba daya jikina yai sanyi da maganan Amira.
Don na fahinci so take ta jawo min wani sabon matsala a rayuwa na ganin yadda nai shiru cikin damuwa yasa mama kokarin sani magana tace.
Waiko Fatima na kin ko ga yadda kika koma kamar wata diyar larabawa dake can aini da a hanya nagan ki bazan gane ki ba gaskiya babana ya iya kiwo sosai wallahi haka duk uwa ke son ganin diyan ta a cikin farin ciki.
Sai aita hakkuri da rayuwa don hakkurin bawa bai taba tashi a banza insha Allahu.
Amirah ko maganan mama bai mata dadi bane sai mikewa tayi kawai tashige ciki abinta tabar mu inacewa mama.
Mama insha Allahu kuma yaya baida matsalan komai wallahi don duk wanan halaiyar nashi ina gani kamar yanzun duk ya kawu.
Sanan mama irin mutanen da yaya yake zama dasu abune mai wuya mutum bai fada cikin halaka irin tasu ba.
Amma sai naga shi yana kokarin yaga ya kare hakkin addinin shi a cikinnsu da muka je can.
Mama taji dadi tace masha Allahu Allah na gode ma abinda nake matukar son ji ke nan Fatima nan mukaai ta hira iina bata labarin tafiyan mu har haduwan mu da Linda a can da mahaufin ta.
Sadauki yana shiga gurin baba ya samay shi zaune yadda ya,barshi da carbi a hannun shi yana tasbihi jin sallaman dan nashi ya dago kai da sauri ya kalli dan nashi mummy tana daga gefen shi a zaune.
Yace na manta na fada maka cewa muna umurah an shigo dakin nan nawa an min barna wallahi.
Da sauri sadauki yace subbahanallahi baba yace wallahi an kwashe min duk agogaiya na masu tsada dama wasu yan abin amfani na bazan ma iya cewa ga iya abinda aka dauka ba ciki.
Sadauki ya saki ajiyan zuciya yace amma baba sai naga kamar barawon waje zai iya shigowa gidan nan kuwa ashe ?
Babada mummy sukace ba daga waje bane koma,waye a cikin gidan nan yake daya daga cikin yaran nan ne yai min wanan aikin.
Sadauki ya kara ajiyan zuciya yace indon agogo ne aida ka fada min tun muna can da an sayo maka wasu daga can munzo maka dasu ko yanzu naga kamar Fatima ta sayo ma agogo guda biyu a Dubai masu tsada da kudin da abokaina suka bata can.
Baba yai murmushin jin dadi yace ikon Allah kaga hukuncin ubangiji ko ?
Yace Allah yai maku albarka yabaku zuria masu albarka a rayuwanku.
Mummy tace nifa abinda yafi tayar min da hankali shine takardun gidan nan da ba a gani ba har yanzu wallahi.
Sadauki a razane yace subbahanallahi may kuma za,ayi da takardan gida da za,a dauka ?
Baba yace nayi zaton ko suna ganin kamar takardan wani abune suka hada hardashi akwai dai abinda sukazo nema a gidan nan.
Sadauki yace insha Allahu zan sa aimin bincike a tsanake ko za,a gano wanda yai wanan aikin haka.
Sun jima suna maganan shida baba da mummy ya kwantar wa baba da hankali yai masu sallama yadawo dakin mama.
Nan yasamay mu yake cewa mama ashe abinda ya faru ke nan bayan tafiyan mu anshigawa baba dakin shi.
Mama tace ni ina ganin yaran gidan nan ne sukai wanan aiki Allah dai ya shirya ko wanene abin baiyi dadi ba wallahi don ta gurin A C din shine suka shiga yadda ba wanda zai gane an shiga dakin.
Muna hanya yake cewa kai gaskiya ko waye yai wanan abin bai kyauta ba takardun da aka dauka yafi tayar min da hankali wallahi.
Nace Allah ya tsare kada mai shi yayi wa baba bar na da takardan yace nima shine damuwa na wallahi.
Har muka kawo gida ba wanda yai magana a cikin mu kowa da abinda yake tunane a zuciyar shi.

****** ********* ******
Sai bayan kwana hudu kayan mu suka shigo gari nan na fara rabawa kowa tsara ban shi har gida sai da na aika masu kuma nace zan tafi amma sai yaya ya hana yace na bari sai an kwana biyu don zamu koma school lokacin.
Maryam ta gama karatun ta saura ni na rage yanzu don haka na koma ni kadai ce ke moving a makaranta.
Ga idanuwan mutane a kaina duk da ina kokarin kama kaina a matsayina na matar aure kuma musulma.
Amma sai kaji ana gulmana wai suturun danake sawa da motan da nake shiga ya zarta na sauran mutane.
Kullun fa a cikin hijjab nike amma mutane saboda sa ido har suna fahintan may ke cikin jikina.
Dole ne don duk wanda ya sanni a baya babu mai ganina yanzu bai san akwai canji a rayuwana ba.
Banda matsala don ina maida hankalina sosai ga karatuna ba sai na tsaya wani loveying ba akan makin dina.
Na dawo a gajiye daga school da wuri na shigo gida don yau Friday na idar da sallah ina kwance saman sallayan da nai sallah hannuna da carbi ina ja.
Ya shigo dakin nawa yana saye da farar shadda tasha aiki a jikin ta sosai sai maiko take yi.
Na dago kaina a hankali na kalleshi yadda na ganshi na fahinci bai cikin dadin rai a lokacin .
Mikewa zaune nayi da kyau ina mashi barka da jumma,a ya amsa min tare da zama a bakin gadona.
Inda yake zaune na tako na zauna daga gefen shi na kalleshi cikin natsuwa na sakan mai lalausar murmushi don in isar ma zuciyar shi da sako.
Nace wa ya taba min sadaukina kuma yau haka zai bata muna jumma,an haka ?
Ya dan kakaro guntun murmushi tare da dan jan guntun tsuki yana cewa .
Fatima al,amarin yaran gidan mu ne yake bata min rai wallahi yanzun ace duk yadda Baba yai kokarin ganin ya inganta rayuwan mu amma babu wanda ya mayar da hankalin shi ga abinda ya koya muna.
Nace yaya ai yan uwanka duk yan uwan ka ne don haka ni sai naga kaman yanzu abinda ya dace shine ka taimakawa yaya Sagir da yaya Abdul su da ke tasowa yanzu ko Allah zaisa a dace ta gurin su.
Murmushi yayi tace tunanen mu yazo daya danaki ke nan abinda na dade ina kudurtawa a rayuwana ke nan a kan su.
Zan dauko sagir na saka shi a jikina sosai yadda zan samu Allah yasa muna hannu ko za,a samu dama ga al,amarin.
Don kinga yanzu ni nan da wasu shekaru dole na bar zancen buga ball din nan da nakeyi don in girma ya kara kama ni ba zan dawma ga wasan ball ba.
Shiyasa yanzun ma nake ta kokarin ganin na samu inda zan kafu da kafana koda na daina wasa ya kasance ina da wani madogara da zamu ci musha a cikin shi.
Tausayi ya bani don nasan yaba da nauyi da yawa yanzu a kan shi don duk wani lalurar gidan su shine maiyin a yanzu.
Nace bayan duk munyi shiru ba dan lokaci mai dan tsawo kowa na tunane a ran shi.
Yaya yan uwaka ne na jini dukkan su kuma bakai kade suke yan uwanka ba a yanzu nima sun zama yan uwana na jini.
Duk abinda su Umma suke gwada maka kan su,suke gwadawa, abinda basu so su gani yau Allah ya yayi suna gani da idon su.
Kaine kuma mutum mafi daraja a cikin gidan mu a yanzu don haka saka masu da,alheri sai aniyar su ta koma masu.
Nakai kaina saman kafadan shi tare da dan shafo fuskan shi nace sai kai tunanen inda ya dace ka saka su.
Rugumoni yayi zuwa jikin shi tare da sauke ajiyan zuciya yace maganan ki Fatima ya bani kwarin gwiwa a yanzu sosai zanyi yadda ya dace dasu din zuwa wani sati zajiji may muka shirya akai idan naga bashar.
Nace nagode yaya aikin na Alheri allah ya kara daukaka shi akoda yaushe Allah kuma ya tsare muna kai daga duk wani abinnki.
Ba mu sake junan mu ba ina makale a jikin shi ina shakan kamshin jikin shi maidadin amowa.
Sannu a hankali bayan ya dan samu natsuwa naji yai dan gyaran murya a hankali ya soma yi min magana yana cewa ina ta kokari naga kin fara sana,a Fatima.
To amma kuma bazan iya bari kina fita ba akoda yaushe don sana,an mata abune dake yawan dauke masu hankali ga harkokin su na cikin gida.
Bazan so hakan ya kasance dake ba Fatima nafi son kalar sana,an da kina gida kudin ki suna shigo maki ga account din ki kawai.
Wani irin sanyi ya sauka min cikin raina nai maza nace mashi nima yaya ba zanso abinda zai sani na raja,a da bautan Allah na ba ko kadan.
Cikin zuciyana naji kanar nace mai to ko muyi sanan kayan dakin mata show room.kawai sai da ma,aikata maza kawai su zauna a gurin.
Amma sai naji tsoron fadin hakan don ban san irin tanadin da yai min ba a zuciyar shi.
Yana makale dani a jikin shi yake cewa zan kara dubawa nagani idan akwai wani harka mai sauki da zai yiyu.
Amma don Allah koma may nene za,ayi ki yi kokari kiyi adalci tsakanin mu kada ki so kanki da yawa a ciki.
Nace mashi insha Allahu yaya bazan raja,a ba ga son duniya akan ka yaya sai naji yayi murmushi kawai alamar yaji dadin a ran shi.
Sai da ya mike har ya fara tafiya yake cewa yau fa ina ganin mutumiyar ki kamar tana labor ne don nakira wayan Bashar dazun yake ce min wai suna asibiti da ita tun safe.
Da sauri nace anty maryam Allah sarki nan na fara murna da adduan Allah ya raba lafiya .

****** ********* ******
Bai dade da fita ba sai ga wayan ta ta bugo min tana fada min ta sauka lafiya nan na yanka wani ihun murna na nufi falo da zuman fada mai yana zaune ya cin fruit don yanzun ya rage yawan cin abin sosai kamar baya sai dai fruits da yan sauran abubuwan gina jiki kawai.
Murmushine a fuskan shi na iso da murna na nace yaya yace kun zama su mama yau ko nazauna ina fadin wallahi fa.
Nace yaya na tafi asibitin ne na dubo ta yace dauki bai bari ki tsaya mu tafi tare ke nan ko?
Naji kunya nace sorry barin tsaya kagama mu tafi, nasan zolayana yake yana ta shiririnta ci har yagama muka kama hanya zuwa asibitin da ta haihu din.
Nice nai driving din mu yana gefe zaune sai waya yakeyi yana fafin sister shi ta haihu ta samu baby boy.
Muna shiga dakin muka samu yan uwa da abokan arziki harda mummy a gurin don itace tazo daga gidan mu.
Yaron yana nade a cikin showel a,saka mai rigan sanyi sky color mai kyau ta jarirai a jikin shi.
Ita ko maryam tana kwance saman gado sai murmushi takeyi na karbi yaron na mikawa yaya shi ya dan kalle ni yace Fatima ban fa iya daukan yaro ba fa.
Na gyara mai tare da nuna mai yadda za rika yaron ana muna dariya yaya idan naku yazo yaya zakayi inji sister din Bashar nace ai shine fadila
Inda maryam take a kwance ya taka yana ce mata sannu yar gidan maji yau kan kin san kin shigo duniya ko?
Murmushi tayi cikin jin kunya tace kai haba yaya dama ban san nashigo bane yace to yaya jikin naki normal dai kike ko don naga dan nawa so health dashi.
Murmushi kawai tayi tace ummhumm yaya Bintu over to you now ko ni kan na sauke na huta .
Ke ban son Bintun nan na fada maku ku daina kiran ta da aanan sunan kauyawan hakana please mutum da sunan shi mai kyau kuna bata mashi da,wani Bintu can.
Kai malam yayane kuma mutum yayi fitan kutsu haka shine zaka kama min mata da fada tana kwance a gadon asibiti.
Kai dan iska wallahi jawa matar ka kunne duk ranan da naji sunan nan haka a,bakin ta ba hauhuwa tayi ba ko duniya ta haife ranan sai na nashi shegen bakin nan nata.
Aiko da sai fada kawai za,a raba mu dakai donbda sai na rama mata yace ga Fatima zaka ramay ko ankan wa .
Bashar yace akan ka dai kaida kai min laifi ba kaunats da bataji tagani ba yace ko zaka gwada ne yanzu Baba.
Tun da kaga yau ka zama Baba kana gani kamar karfinka yazo ke nan ko yaro.
Yaro fa kace min maye kagani anan kuma ni yanzu ai sai dai baba kawi aka bushe da dariya a gurin.
Naso yaya ya barni gurin Maryam amma yace mu koma gida gobe zai kaini na wuni a can yanzu mutane sunyi yawa sosai.
Haka na tafi gashi muna son kebewa da maryam nasha labarin abinda tasha.
Muna hanya yana waya ina tuki ban yi magana ba saida ya gama waya ya furza iska nace kana can kana fada ga abinda ya dace kaiwa fada akan shi.
Yace may ke nan fa ?
Nace kiran mamana da Majin da kukeyi mana don Allah ua kamata ku canzawa mama suna hakana please.
Kuma fa yaya duk kaine ka saka mata wanan sunan don Iyya ta fada min wai baka iyannkiran ta maijidda da baba ke kiran ta shi ne ka dafa mata wai maji can.
Mirmushi yayi ya shafo kan shi yace na dai ganecwallahi Iyya Rabi tana min tonon silili a gidana .
Nace lah may ye laifin iyya yaya don ta ban kado min sirin baya tafa fada min irin yadda kai ta wahal da su mama wallahi.
Yace hummm yai shiru tare da kwantawa da kyau saman kujeran mota ya rufe fuskan shi da hular kan shi kawai.
Mun kusa shiga kwanan layin mune naji yace Fatima cikin wani irin murya nace na,am yaya yace wallahi yanzun ban san may yasa ba ina matukar son baby nima sosai wallahi tun dai yanzu dana ga na maryam din nan.
Please Fatima will you give my baby too please Fatima ina son naga nima na haihu wallahi.
Idanuwana na lumshe cikin wani irin yanayi da tausayin kan mu don ya fadi ne a baki amma ni na riga shi furta hakanna raina.
To waye mai laifin a cikin ni dashi da muka kasa samo ma kan mu farin ciki irin haka ?




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYABA MUN BARKI GA ALLAH YABI MUNA HAKKIN


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login