Showing 3001 words to 6000 words out of 373688 words

Chapter 2 - A LOKACIN MUKE BOOK BY ZAINAB .I. MAKAWA.txt

ba da nakeyi.
Takarba da mamaki tare da kirgawa ta dago da sauri tana cewa ke yar nan har jakka hamsi ne fa tabaki ?
Nace ban kirga ba ta daice na kawo maki kiyi amfani dasu kafin ta wuce na fara talla.
Take cewa ikon Allah ita din aikin may takeyi haka har ta samu wanan kudin masu yawa take kyauta dasu ?
Nace Inna ba, a birni take ba ance kudi abirni banza ne duk wanda yaje fa sai yai kudi a can.
Tace ke rufa min baki da maganan wautar ki can a ina kika samu wanan labarin karyan haka ?
Idan da banza ne may zaisa wasu suje su dawo tsula yadda suka tafi ?
Mahaifinku sau nawa yake zuwa birni bai samo ba da zaki fadi hakan.
Nace to inna kin sani ko baiso ne shi yafi son zaman mu haka ?
Kallon takaici tai min tace ke kan ban san ranan da zakiyi wayau ba wallahi.
Nace killa sai na girma ko Inna ?
Wani irin takaici na kara bata tace to ai sai ki tsaya har ki girma din sai kiyi wayon.
Sai dan shiru da ya biyo baya a dakin can tace ki saurare ni da kyau kiji abinda zan fada maki.
Na gyara zama ina fuskantar Inna na tace banda kwadai banda roko don yafi komai zubar da mutuncin mutum da sauri.
Ki kawar da idon ki ga abin duniya sai ki zauna da kowa lafiya a duniyan nan.
Allah ne ya hada ki da ita jinin ku ya hadu haka don haka ni bazan hanaki hurda da ita ba don ban taba jin wani abin assha daga gare ta ba banda alherin ta da nake ji a gurin uwarta ko yaushe.
Don haka ki kama mutuncin kan ki don Allah ki rufa min asiri ni da mahaifin ki.
Inda sabo na saba jin nasiha irin haka ko yaushe a bakin Inna ta don haka wanan ba bakona bane sai ma cewan da nayi.
Ai ina dazun da mama altine ta dafa mata kaza tace nazo naci nace da ita na koshi.
Tace kin daiji na fada maki don ke har yanzu naga ba wayo ne dake ba.
Haka ya kasance tsakanina da Inna ta har mahaigin mu ya dawo daga kasuwan kauye da yake zuwa tallan buhun shi na saka kayan masarufi aciki.
Lokacin Inna ta fita don itace da girki ranan idan tana girki dakin mama laure nake kwana haka ma idan mama laure ce da girki dasu Lawisa muke kwana a dakin Inna ta.
Ba zancen awara da safe don haka na fito daga dakin Inna ina gaida baba da dawowa.
Yace a, a Rahama yau ba atafi kai nikan bane nace baba ai bazan yi tallah ba har kwana biyu.
Yace ikon Allah damay ya faru kuma sarkin tallah ?
Nace baba Anty Sa,ade ta zo na gidan mama altine itace ma tace na zauna gida har sai ta koma.
Yace a, a kice min uwar dakinnki ko uwar goyon ki har yanzu ashe ana tare ke nan ?
Mama na zama take cewa kai kwadai bayi ba wallahi yanzu kaida kan ka kake koya mata harkan kwadayi ?
Ashe bari nabar ganin laifin uwarta ita kadai abin ruwan dare ne ashe Allah ya kyauta.
Muna nan maji magani wai an bizzine tsohuwa da ranta.
Yanzu may ye abin kwadai a furin nan ina dai jinin sune ya hadu da yarinyar nan tun tana karama suke tare ?
So kike nace ta daina kulata ko may kike son nayi Allah ne fa ya hada jinin su.
Yara nawa ke garin nan wakikaga ta mama idan ba ita ba da Allah ya hada jinin su.
Yanzu dai ni may nace kuma wanan ai koyawa yaro kwadaiyin abin duniya ne ba akidar alheri bane .
Baba bai kara mata magana ba yajawo turen abincin shi kawai ya soma ci ranshi a bace

Da dare na shiga kwanciya har na kwanta a saman dan keson tabar da nake zuwa kwana dashi naji mama laure tana tashina tace ke Rahama tashi muyi magana.
Wallahi idan naji kin fadawa sokuwar uwarki ko nawa aka bani gidan Altine sai rayuwan ki ya baci a gidan nan kin dai san halina wallahi ko.
Nace ni mama ai ban san ma ko nawa tabaki ba balle na fadi tace munafuka kece baki san kudi ba ?
Kin dai ji abinda na fada maki saina lahira yafiki jin dadi wallahi ko.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
MARICCIN KAN DUTSE, , ,

WANAN LITTAFIN NA KUDI NE CIGABAN SHI SAI DAI ZAKI FARA KARANTA FREE PAGE DINA A KYAUTA YAR UWA IDAN KINA DA RAAYIN HAKAN.


Yau da sauri na shirya zuwa makaranta tunda ba tallan safe gareni ban tafi ba sai da na leka gidan mama Altine tukun.
Ita kadai ce a tsakar gida tana yan aikace aikacen ta muka gaisa nace ina baki tace wai ke ma kin san ai basu tashi da wuri haka.
Tace yau da wuri haka za, a bokon ?
Nace mama kin manta anty ta saye tallen nawa sai hutu yanzu tace humm hakane fa na shafa sam.
Duk da ance suna barci bai hanani lekawa ba dakin nasu suna kwance saman gadon mama da yasha shimfidan sabon zanin gado.
Barci suke hankalinsu a kwance na dan dade tsaye a kan su ina kallon su cikin sha, awa komai nasu gwanin ban sha, awa dashi.
Najuya nafito mukaci karo da mama zata shigo dakin tace ai har ina batun shiga na samay ki kada ki tayar dasu da ga barci.
Nace kai haba mama, may zai sa na tayar dasu suna hutun gaji tare da su.
Nace zan tafi mama sai na dawo muryan ta ne naji tana cewa yaki Rahama.
Najuyo zuwa inda take tsaye tana kokarin kwance haban zanin ta data kulle kudi a cikin sa .
Naira ashirin ta miko min tana cewa karbi wanan kyaci tara dashi indan kin tafi can.
Take fuska na ya sauya nace cikin marairaicewa mama da kibar shi wallahi yau ai Inna ta tabani Naira biyar zai isheni na sha ruwa a can.
Tace ruwa kawai Rahama bayan nasan ko karyawa bakiyi ba kika fito daga gida?
Nace dimamay mama laure tace baida yawa don haka su dake gida zasu ci abinsu wai idan naje can ban rasa abinda zanci.
Mama Altine tace shine kuma ita Inna ki ta baki Naira biyar kacal ki sai mai da naira biyar din.
Muryana na tausa kada wani yaji ni nace mama kin san idan tabani da yawa mama fada take mata wai tana lalatani da yawa shiyasa mama ta kafa doka wai Naira biyar kawai za, a dinga bani ya isheni .
Kai amma dai laure takai muguwa wallahi nace mama barin tafi kada na makara yau ina son naga assymbly don na manta yaushe rabo da ayi shi dani.
Najuya ba tare da na karbi ashirin din hannun nata ba nafice daga gidan da sauri tana kirana amma bai sa na tsaya ba .
Koda na isa makaran ta nayi dace da abinda nake son gani ina shiga ana kada kararawan assymbly yau ba duka gare ni zan kuma ga assymbly din mu.
Kowa ya ganni sai mamaki daga dalibai har malamai suna cewa, sarkin late yau lafiya kuwa ?
Sai dai nayi masu murmushi kawai na wuce haka muka zauna nai matukar jin dadin samun darasin safen da nayi yau.
Allah Allah nakeyi a tashi daga makaranta na koma gida na samu anty na yar birni don ni gaskiya ban gajiya da kallon ta ita da yarta mai kyawo.
Har zuwa lokacin tashi ranan saurin da nayi har yafi wanda nakeyi zuwa daukan talla na a kullun.
Na shigo gidan mu da hakki alaman nayi gudu ko sauri a lokacin sai dai may na samu a gidan mu mama lauratu na sana,an fadan ta da ta saba yi idan fitinan ya motso mata.
Duk da har taci ta sude babu mai biye mata indon ta inna tace zata iya kwana tanayi bata tanka mata ko uffan.
Sai dai idan baba yana gida ne wani lokacin zaibi ta kanta suyi ta tonon asiri a junan su.
Wanan haushin da naji tayi yayi dalilin da na fasa shiga cikin gidan namu na dan daka ta ina sauraren ta don naji akan may take fada kuma.
Daga inda nake sauraren fadan nata na fahinci fitina take da Inna na wai akan kudin da aka bani inna bata nuna mata ba taba babana ya dan kara jarin shi.
Sai zuwa can naji muryan Inna tana cewa yaya kiyi hakkuri dan Allah ni bawai na nuna bakece kika haifi Yarinyar nan ba .
Naga kin san da zancen ne tunda boyar Allah nan a gaban ki ta furta cewa ta dauke ma yarinyar nan yin sana,an ta.
Ai fa yanzu sai kiyi kwana nawa ne idan bakin ciki kikeyi dani akan ki zai kare Asiya don wucewa yar gidan Altine mai kuli zatayi.
Kuma kowa komawa zaiyi ga turken shi mai cabo ai har kudin nawa ne da suka rufe maki ido haka ?
Maimakon na shiga yadda nai niyar yi da farko sai kawai naja na juya zuwa gidan mama altine mai kuli.
Tafiya nake kamar banda lakka a jiki Allah ya taimake ni naga kanina zai shiga gida na mika mai jakkar makaranta na nace ya kai min dakin mu.
Da sallama na shiga gidan suna zaune su biyu ga kwanon dan wake da mai da yaji tana ci cikin irin cin abincin su na yan gayu.
Mama altine ne tace a, a yar gidan anty har andawo bokon ke nan nace eh mama cikin kada kaina.
Zama nayi tare da gaishe su naci gaba da tunane a cikin raina wai yaushe ne Inna ta zata samu saukin rayuwa ne agidan mu?
Duk abinda tayi batayi daidai ba gurin mama, damu da ita duk bamu da wani yancin kan mu sai abinda mama laure tace.
Na sauke ajiyan zuciya ina fadi a raina yaushe ne wai muma zamukai ga namu yancin kan ne agidan mu , ?
Jin ajiyan zuciyar dana sauke karama dani yasa hankalin su ya dawo gare ni mama altine da anty sa,ade har suna hada baki ita mama na cewa may kuma ya faru yar gidan anty ita kuma nacewa Rama na duk gajiyan ce haka wai ?
Nace a hankali mama ni halin mama laure ne yake min ciwo ace kullun duk abinda Inna tayi ita a gurin ta ba daidai bane ?
May kuma ya faru yanzu?
Nace mama bakiji haushinta bane har nan gidan wai akan kudin da anty ta bani shi ne Inna nasan tabawa baba kudin ne ga Mama can ta saka inna a gaba da masifa akan may tabashi kufin bata bata ba.
Ikon Allah waiko laure na da hankali kuwa mama altine ne ta fadi hakan.
Nace mama akullun wanan halin na mama ya damu na inna sam bata da sukuni a gidan mu.
Wanda kinga abin har muma ya shafe mu muda ita bamu da incin kan mu ko kadan.
Nan kata tunanen yaushe ne wai muma zamu zauna kamar kowa agidan.
Nace mama fa har ikirari takanyi da cewa sai dai mu zauna a haka mu da uwar mu don bazata zauna tana ganin ita da mijin ta ba wasu banza can suzo su shige mata gaba.
Duk da Inna tana hakkuri da ita kalamanta badu damunta nake gani amma baisa mama ta watsar da wanan halin nata ba har zuwa wanan lokacin.
Wai mama kin kuwa san duk saba, an da nakeyi kudin mama laure ce ke karbe su a gurin Inna da sunan wai zatai min tari ko kuma tace wai ta ara.
Kuma bawai zata biya bane sannan ni har yau banga wani tari da ake min ba agidan.
Wani lokaci idan tace abata kudin na hana don sai yakai ma bamu da jarin da zamu juya awataran.
Data gane ina hanawa yanzu shine take cewa idan ina ganin nai wayo ne na kama kaina don dagani har uwana da uban nawa bamu fi karfin ta ba don haka in ina shiga hankalina mu zauna da ita lafiya nayi .
Idan bazan iya ba wallahi ko yaushe kofa a bude yake mina dagani har Inna muyi gaba.
Anty ce tace kai ashe haka take ina ganin ta a hakan ?
Mama tace wa laure da kike gani bata da dama komu makwabta sai munkai zuciyar mu nisa da ita ake zaunawa lafiya.
Nace muma hakan muke zaman takura da tsangwama a tare da ita kullun sai ta kirkiri sabon jidalin da ta dora akan Inna don dai ayi fitina kawai.
Anty tace kuma shi mahaifin naku duk yasan da haka Rama ?
Nace cikin kada kai kamar wata babba dani yasani mana anty may zaice tunda baya iyayin musu kullun da ita baya kuma jayayya da ita sai abinda tace don azauna lafiya.
Sai idan abin ya ishe shine yake magana kuma maganan ba amfani zaiyi ba ai.
Balle ma yanzu nagane baba yana matukar gudun bacin ran mama sosai sai abinda takeso akeyi agidan mu.
Don kinga kan tallah mu ba yadda baba baiso mu bari mu kama boko da islamiya ba amma mama ta hana.
Don dai kawaiba zauna lafiya a gidan da ita ko kwanaki an kawo karan Lawisa amma mama ra hana yayi magana dole yai shiru ya kyale ta hakana.
Anty tace Allah ya kyauta ni dama zai ban ke mu tafi birni muyi zaman can ki shiga bokon ki yadda kike so daya kyauta min.
Nace wai anty idan na tafi birni na zauna waye zai kulla min da Inna ta ko kudin sayen sabulu kawai ya isheta ai.
Mama tace balle ma laure bazats bari ba dakike ganin ta na tunda ba yayan tane zaki dauka ba.
Ai duk wanan fitinan da kikaji tanayi da ace tare da yarta kike da baza, a ji shi ba sam.
Halin Laure sai ita dubi yadda Asiya ta koma kamar ba ita bace ta tashi a garin nan abin sha, awa ga kowa.
Amma mahaifinta ya hana ta zabi yacs sai malam Abubakar zaiba don zumuncin dake tsakanin shi da mahaifan ta.
Yarinya da gatan ta amma dubi yadda duk ta zuke takoma kamar ba Asiya ba, lokacin da tai yan matancin ta babu wanda zai ganta bai kyasa mata ba.
Yanzu gashi tun auren ts gidan nan dubi duk yadda ta tsiyaye babu komai gajikin ta sai tarin hakkuri da zaman sunnu kawai.
Anty tace mama ashe mahaifiyan ta takwaso gurin kyau ke nan ?
Kai wane ita da kyaun Asiya wanan da bata gyara kai zaikai wata biyu ba kitso kafa ba lalle kamar ba matashiyar budurwa ba da ita ?
Nace kai mama duk wanan gyaran da nakeyi zakice haka ina wanka fa sau uku ko biyu a sati 😆
Dariya ne sosai ya kumshe anty tace kai Rama na wankan ma har sai an kidaya kwanakin yin shi kuma ?
Nace anty ai nayi kokari bakiji har ana yaba tsabtana ba don fa ina da tsabata wasu ke sayen sana, ata sosai.
Dukan su dariya suke min akan maganata niko ko ajikina ban damu ba sai mama ce tace nidai bari na zubo maki abinci kici da wanan bakin surutun naki haka ?
Na gyara zama ina ta kawo min dan wake ranan har da ruwan goran da anty ke sha nasha azatona yana da zaki amma sai naji shi salaf kamar ruwan rijiya.
Ina gamawa na gyatse dama nasan ko naje gida tuwo ne zai tare ni don haka ban rage komai ba harda sude kwanon nayi.
Anty tana ganin haka tace dani ko a karo maki ne idan baki koshi ba nace sai zuwa anjima Anty yanzun kan Alhamdullahi.
Tace oya zo na banye maki kanki nai maki kitson shi duk da take na manta ko yaushe rabona da yin kitso a duniya.
Ina bude kaina saida tai wani irin ihu tace Rama subbahanallahi kanki ne haka nace shine anty yayi yawa ko ?
Tsuki naji taja tace haba Rama kamarki kuma kinkai har secondary ace baki gyara jikin ki sai yaushe zaki koyi gyaran jiki kuma ?
Haka zaki dingayi agidan mijin ki idan kinyi aure ki dinga zama da kazanta yace kina wari.
Kunya maganan ta yabani na tsune kaina akafa nace aure Anty ina nai aure wazai zauna da inna ta yana taimaka mata da diban ruwa da tallah kuma ?
Kinaji na idan kina son mu shirya dake daga yau duk sati ki dinga kitso da kunshin da mama tace idan ba haka ba wallahi wanan kazantan zai sa mu bata dake.
Nace insha Allahu anty zan dinga kitso bani son mu bata dake ko kadan a rayuwana.
Tace dakin kyautawa kanki haka taci gaba da sance kan har wani gari ke zuba a cikin don dankarewan dayayi.
Dama asalin haduwan mu da ita shine yawan gashin da nake dashi.
Watarana tazo garin inna takaini an min kitso ya sauko har bayana taga mun shigo gidan mama Altine sayen mangyada take cewa kai wake wanan fine girl din a kauyen ga kyawon yarinyar na ace a birni kika fito da kinsha gyara yarinya.
Tace zo nan ban mata kiuya ba nazo ta rugumay tana cewa kina so na na kada mata kai alaman eh.
Tun rana muka shaku da ita da zan koma ta saya min biscuit da sweet naje


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login