Showing 186001 words to 189000 words out of 373688 words
Chapter 63 - A LOKACIN MUKE BOOK BY ZAINAB .I. MAKAWA.txt
dan gishikin dakin da hannun shi daya.
Batai mashi magana ba ta shige dakin ta kawai,ran ta a bace tana mamakin irin wanan halin na uwargidan su.
Bai shiga ba juyawa yayi ya fita daga gidan ran shi a bace don wanan cin zarafi da akewa mahaifiyan su yana matukar damun shi a rayuwan shi.
Tun da safe yabar garin don bai iya tsayawa yana ganin irin wanan takaicin haka a rayuwan shi.
****** ********* ******
Zaman shi a turai yasa ya manta da bakin cikin da ya baro a gida.
Sai dai kusan kullun zai kira mahaifiyan shi su gaisa yakuma tambaye ta yaya suke da sauran kannen shi.
Yana kiran mahaifin shi shima suna gaisawa har su dan taba dan hira a tsakanin su.
Bangaren Bashar kuma komai yana tafiya masu daidai don yana da rikon Amana sosai .
Gashi kuma sadauki ya yarda da Bashar din don tun suna kana suke tare dashi, lokacin mahaifin Bashar na da rai yafi mahaifin su sadauki kudi sosai shine ke yi masu komai.
Koda sadauki ya fara shaye shaye bai hana bashar yai mu,amula dashi ba duk da hanashi da mahaifiyar shi tayi da farko.
Amma da taga alakarsu abin daga Allah ne sai takawo ido ta samasu kawai don tasan shakuwar su daga Allah ne.
Hankali shi sosai yake a kwance yana sha har yanzu sai dai ba irin na can farko ba irin shan kauyanci da kurciyan da yayi a baya.
Don yanzu ko mutum yafi aula dubara ba zai iya gane cewa ya sha wani abuba.
Haka yasa mutane ke ganin ya daina sha ne kwatakwata a rayuwan shi.
Wani yammaci ya bugowa mahaifin shi waya a yanayin da yaji muryan shi sai baji dadi ba.
Yake cewa Baba lafiya kake kuwa murmushin manya Alhaji yace lafiyata kalau sadauki sai dai dan zazzabin da ba,a rasa ba kawai.
Yace to Allah ya sawaka basuyi wani dogon hiraba yai mai sallama ya kashe wayan.
Washegari tun da safe sai yaji bari ya kira Baban yaji lafiyan shi saboda jiya, yana jin jiki.
Sai dai yana kira hjy Kubura ce ta dauki wayan suka gaisa take ce mai sadauki Alhaji ba lafiya amma gamu asibiti dashi don jiya anan muka kwana.
Hankalin shi ya tashi cikin rudewa yake tambayan ta komay ya sami mahaifin nasu.
Tace mai hawan jini ne akace kuma har ya fadi jiyan sai dai da sauki don yanzun ma ya bude idon shi amma dai har yanzu akwai jikin.
Hankalin shi yai matukar tashi yace mata don Allah ayi duk abinda ya dace dashi kafin ya iso garin.
Sukai sallama da ita hankalin shi a tashe tun a lokacin ne yafara shirin tafiya dawowa gida don ganin halin da mahaifin shi yake ciki.
Washegari Sai dare ya shigo garin don nisan inda yafito a lokacin.
Kai tsaye bai yo gida ba yace Bashar ya,wuce dashi asibiti nan ya samu yan gidan su gaba daya a gurin mahaifin shi.
Umma tana zaune a bakin gadon da Alhaji yake kwance ya shigo dakin daga cikin su wasu sunyi mashi sannu da zuwa.
Wasu ko sai harara shi kawai sukeyi yana saye cikin swoth na maza baki mai guntun hannu daga ciki yar rigace itama pink mai guntun hannu.
Sai dai bai sa aninin rigan saman ba haka yasa za,a hango tacikin sosai a fili.
Ganin Umma ta babake gaban gadon ba wanda ya isa ya matsa bakin gadon bai hana shi karasawa gaban mahaifin nashi ba.
Tare da rage tsawon shi ya duka gap da kan mahaifin nashi ya dan rike hannun shi yana fadin Sannu baba ya jikin naka yanzu.
Alhaji Abubakar ya dan juyo tare da bude idon shi da suke mai a lumshe yace,
Alhamdullahi na samu sauki sadauki ya ya hanya har ka iso ne ?
Yace eh Baba,
Likita yace kada a damay shi da surutu abarshi ya huta kawai, Umma ce ke fadawa sadauki hakan.
Yasan nufin ta bai biye mata ba yace wa mahaifin nashi Baba amma ya kamata a fita dakai zuwa wani kasan a dubaka sosai zaifi zama haka anan.
Murmushi yayi tare da rike hannun yaron yace kada ka damu Faruku ai naji sauki sosai.
Kana dai jin abinda nake fadi likita yace kada asa shi yawan magana ko ?
A hankali ya dago kai ya dan kali inda take zaune tana shimfidawa sauran iyali ikon ta.
Daga bayan ta hjy Kubura tace haba ki barsu su gana mana yanzun fa ya iso shi.
Kada ki fada min magana Kubura don ke ba kunya ne dake ba yaya zan kyale shi yana sashi magana bayan likita yaba da doka.
Hannu Alhaji ya daga masu yace don Allah ya isa hakana please,
Idan shi zakuyi min ku koma gida gaba dayan ku,
Sadauki dai yana duke ya kurawa mahaifin nashi ido dake cikin wani hali gwanin ban tausayi.
Can ya mike ya juya gurin hajiya Kubura yana fadin wani likitane mai duba shi mummy ?
Tace tau kasan likitocin yawa gare su amma dai doctor Ango shine yake shigowa akai, akai gurin shi.
Man let's go yace wa Bashar dake tsaye daga can kofan shigowa dakin.
Ajima kadan sai gashi da likitan sun shigo dakin tare nan likita ya bukaci kowa ya fita daga dakin a lokacin.
Umma kaman zatai magana sai tai shiru tamike ranta a bace suka bar dakin yaran ta suka bi bayan ta.
Har an rufe kofan sai gashi an leko akace hjy kubura ta shigo.
Wanan abin yai matukar harzuka ran Umma sosai take ganin shi sadauki da hjy kubura sun fitane ga Alhajin da za,ace ita ta fita daga dakin.
Mikewa tayi ta nufi kofan ta tura da sauri likitan dake duke kan Alhaji ya dago kan shi hjy kubura tana kokari kamashi a daura mai abin gwaji.
Likita yace haba mama munce ku dan tsaya a waje har mu gama abinda zamuyi mashi ko.
Wani haushi ya kumay ta ta buga kofan ta wucd fuuu tana cewa yaranta su zo su tafi tunda basu da amfani a gurin.
Dan ta Sagir yace haba Umma yaya zamu wuce don kawai ana mashi gwaji ance mu fito.
Sagir kai dama nasan baka da zuciya wallahi, baka san ciwon kanka ba ko kadan a gidan nan.
Sagir yace ni dai ba zan tafi ba gaskiya tace zauna wanan mashayin ya gwada maku iko anan.
Mama ma mikewa tayi tabi bayan Umma suka bar asibitin cikin fushi suna sake bakar magana kai kishi ho.
Likita yace mai nan da kwana biyu idan ya kara jin sauki zasu iya fita dashi din don dai yanzu yana jin jiki tukun na.
Sai dare sosai Sadauki ya bar asibitin don yazo gida yacewa Sagir da Mustapha zai je ya gaida maji ya dawo idan basuyi barci ba.
Ya samu har mun rufe kofa don mama bata zuwa asibitin da dare don habaici da gori ne idan taje suna nan.
Wanka yayi yajuya sai asibitin a can ya kwana gurin mahaifin shi a zaune tare da kannen shi biyu.
Cikin dare Alhaji ya falka ya gan shi zaune saman kujera a gaban shi yana barci yake cewa a ranshi Allah sarki .
Ya Allah ka kara shirya min wanan bawa naka Allah ka shirya min duk zuria ta baki daya.
Jin kaman motsin Alhaji yasa shi saurin bude idon shi ya mike yana cewa Baba yaya ne may ke damun ka ne?
Uban yai dan guntun murmushi yace Umar Faruk Allah yai maka albarka Allah ya kara shirya min kai.
Jinkin sadauki yai sanyi zuciyan shi ta fara bugawa don hankalin shi yai matukar tashi sosai a lokacin.
Nishi ya fara guda guda alaman yana jin jiki shi sosai a lokacin da sauri sadauki ya ke kiran Sagir yana cewa.
Yi sauri kira min nurse a waje sagir ya mike da sauri ya fita shiko yana tsaye sai sannu yake wa mahaifin cikin damuwa.
Nurse yashigo da sauri yana cewa bari akwai Alluran da dama za,ai mashi yanzu zai samu sauki insha Allahu.
Bayan anyi alluran da yan mintoci ne, sai ya samu barci sukan yaran basu barci ba suna tsaye a kan uban nasu har safe.
Jin kiran sallah yace su sagir su fara zuwa suyi sallah in sun dawo sai shi ya tafi.
Sagir yace yaya ku tafi kawai idan kun dawo ni sai na tafi haka sukayi suna dawowa sagir ya fita yai sallah.
Can Alhajin ya bude idon shi lokacin gari ya dan fara haske yace ba,ai sallah bane sukace mashi anyi Baba.
Yace ku taimaka min kuyi min alwala sai nayi sallah da taimakon diyan nashi su kai mai alwala yai sallah daga kwance inda yake.
Sai kuma ya koma barci suna gurin zazzaune ba wanda ya gusa daga cikin su har lokacin.
A gida kuma tun da asuba muka tashi muka hada abin breakfast don mune da girkin gidan.
Ni da anty maryam ne muka dauka zuwa asibiti don mukai wa wan yan da suka kwana dashi abin karyawa.
Muna shiga dakin da,sallama yana tsaye yaba da baya jin sallaman mu yasa shi juyowa.
Sai da gabana ya fadi danaga yadda ya sake min muka karasa muna masu ina kwana ya amsa da kyat cikin yanayin damuwa.
Yaya yaushe ka dawo yace mata jiya da dare daga inda nake tsaye ina kallon yadda Baba yake a kwance na dan dago kai nace mai,
Sannu da dawowa yaya sai lokacin ya dago kai ya dan kalle ni da sauri ya kawar da kanshi tare da cewa yauwa.
Yace ya maji suna lafiya jiya na shiga na samu kun rufe kofa ai.
Maryam tace yaya shine baka buga ba mun kai sha biyu bamuyi barci ba ni da Bintu ai.
Bai bata amsa ba yake cewa sagir su tashi su karya ga abin karyawa nan.
Sagir yace kaifa yaya naga alaman baka ci komai ba tunda kazo fa?
Yace No don't mind zan tafi gida yanzu na dawo sai karya a can idan na dawo sai ku tafi kuma kuyi wanka ku dan huta.
Bashar ya kira yace yazo ya kaishi gida yanzu, ba a dauki lokaci ba nacewa maryam mu tafi,
Tace zamu koma idan Baba ya tashi muna gaidashi don Allah.
Batare da ya juyo ba yake cewa, No ku tsaya Bashar yazo mu tafi tare ko kunzo da mota ne ?
Dariya tayi tace kai haba yaya wani mota kuma ina muka gan shi sai dai mu tare Napeo mu hau.
Dan dariya ciki ciki yai mata ba,adauki lokaci ba saiga bashar cikin jallabiya ya shigo suka gaisa yana tambayan jikin mahaifin nasu yace Not bad gaskiya.
Mukai masu sallama muka fara fita daga dakin kafin su fito mu tafi.
Muna fita maryam tace tau dada ga dodon maza ya dawo yanzu za,a fara ke nan ko ?
Nace ni gida zan tafi sai ya tafi na dawo ban iya zama mugun nan yana gari wallahi.
Ganin sun fito yasa nai shiru ba don na tashi ba yana cewa mutafin ku ko?
Nan muka bisu a baya suna gaba muna biye dasu magana suke akan jikin baba.
Baya muke Bashar na jan motar shi kuma yana gaba yana waya yadda naji wayan da abokin shi yake wayan.
Har muka kai uguwar mu waya yake cikin wani yanayi nikan mota na tsayawa na bude na fita abina ban tsaya ba.
Na shiga na samu mama tana zaune suna magana da Amira tana cewa ko sai yaushe zai shigo garin yazo yaga mahaifin nashi .
Na zauna sunacewa mun dawo nace eh tare suke tambaya yaya jikin Baba nace da sauki mun samu yana barci ne.
Tace Alhamdullahi ai barci alaman sauki ne ga mai jinya.
Maryam tashigo da ledan da ya bata a hannu n ta daganin ledojin na kasar waje ne shi ya mayar da hankalin su mama a kan ta lokacin.
Tace Maji kina da bako fa ashe yaya ya dawo tun jiya wai yazo ya samu mun rufe kofan mu.
Sai gashi ya shigo nan suka fara murna suna mashi sannu da zuwa, suka gaisa da shi.
Nan suka zauna ana magana akan rashin lafiya Baba da halin da yake ciki.
Maji tace akwai abinda ke damun shi don tun ranan da ya dawo daga kasuwa rai a bace washe gari yace ba zai iya fita ba shine har abin ya kai shi kwance haka.
Amirah tace wallahi yaya na zaci ko Baba ba zai tashi ba yadda aka kai shi asibiti rai a hannun Allah wallahi.
Sadauki yace to may Baba yake tunane haka har ya ja mashi wanan matsala kai tsaye.
Maji tace tau ana raba dan adam da damuwane ko al,amarin iyalin shi ai ya ishe shi abinne dai bai faduwa kawai.
Maryam tace ni dai nasan akwai wani abu mama don ranan mun fita da Bintu zamu tafi makaranta naga yan sanda da yan hisbah a kofan gidan nan.
Suna magana dashi kuma wallahi baba sai rantsuwa yakeyi bai zuwa ko ina shi.
Akwai dai gaskiya amma ko may ye ai muji idan yai wari.
Ka karya ne uwar take tambayan shi yace No sai nai wanka zan karya na koma asibitin na duba Baba.
Bai jima ba ya fita daga falon yabar mu nan a zaune can yafito cikin shirin shi yana fadin.
Abashi abin karyawan shi inda nake mama ta dan juyo tana fadin Fatima ba yayan ku, abin karyawa kinji.
Har na fara tafiya na juya inda yake ina cewa na hado ma da indomei ne ?
Yace see you may zanyi da indomie ni kaman wani karamin yaro can?
Kayan tea nafara kawo mashi na juya na dauko mashi kwai da irish su yaci bai sha tea din ba sai ga kira yazo likita ya shigo.
A hanya ya hadu su Umma suna jiran napep su tafi asibitin nan ya tsaya ya dauke su a tare suka tafi dashi sai wani shan kamshi Umma take a bayan mota.
Sun zasu Alhaji a zaune likita yana dubashi suka gaidashi tare suka fita da likitan yana fada mashi yadda suka kwana jiya dashi.
Maganin da aka rubuta da irin abincin da za,a bashi ya tafi ya sayo a nan ya samu da hajiya kubura da maji sun dawo suna sauka da Napep mamaki ya faea wai ina motan Baban sune ?
Zai iya cewa tun wancan karon ya fara ganin kaman arzikin mahaifin su ya fara ja baya sosai.
An bashi maganin da abinci yacu sosai ya kwanta barci don maganin da yasha.
Sadauki ganin su gaba daya yasa shi cewa dama ina son nai magana da ku don ina son nasan da,wa za,a tafi da Baba India ?
Umma tai farat tace kaman yaya dawa za,a tafi dani mana za,a ?
Hjy Kubura tace wanan ma ba magana bane wanan zance ne na jinya babu son kai a cikin shi.
Mama Asiya tace to may kike nufi ke zaki tafi ke nan ko kuwa?
Dama aikin sani,
Wallahi baki isa ba don baki kai muna can ba ni din dai da baki son a tafi dani da ni za,a tafi.
Fitayayi ya bar su dakin cikin dan hatsaniyan su da suka saba har suka falkan da Alhaji daga barcin da yake yi.
Nan yake jin abindaya hadasu fadan yace dama kun bari don ni bazan tafi India ba dan dama dama da saudiya ne ?
Sadauki ya shigo da abokan shi suka gaida Baba nan yake cewa kace za,a kaini India ?.
Yace eh Baba,
Yace to ba zan yafi ba inda dai saudiya ne zan iya zuwa ko don na sauke farali a can nai Umurah.
Yace tau Baba idan can kake son a tafi sai a tafi din ai yace dawa za,a tafi don mu shirya passport din tafiyan.
Gaddama ya kara kaure tsakanin matan sai cacan baki sukeyi a tsakanin su.
Maji na zaune tun fara magana bace uffan ba a zance duk kuyi min shiru ban zuwa da kowan ku, da Hawau zan tafi.
Tsit sukayi don jin furucin shi, yace tun da abin naku rashin hankali ne baku damu da halin da nake ciki ba.
Dama haka zakace don ka gyara mata rai tunda dantane ya biya.
Sai dai dadin abin kowa ma dai ya hafa a gidan balle yanzu don ana ganin kaman danta ya kawo karfi, za ai muna cin fuska.
Umma na fadin haka tamike tana daukan jakkan hannun ta zata fice daga dakin.
Sadauki yace ba matsala sai aiwa kowan ku passport a tafi ai umuran can sai a dubi lafiyan ka.
Hjy Kubura tace Allah yai maka albarka sadauki wanan dawai niyan haka tace tau sai a mayar da yuka a kube, don dan albarka ya yanke hukunci.
Wani kallon banza ta watso ma hjy kubura tace yanzu ke ake ji mara kunyan yarinya kawai ni ba sa,an yinki bane,
Yaushe kuma muka zama daya tunda bori guda mukewa tsafi ni dake yanzu.
Maji dai mikewa tayi tana fadin ni zan koma Allah ya sauwa Alhaji hjy kubura tace tsaya mu tafi tare anjima nadawo.
A waje suka samu sadauki shi ya dauke su zuwa gida,