Showing 39001 words to 42000 words out of 373688 words
Chapter 14 - A LOKACIN MUKE BOOK BY ZAINAB .I. MAKAWA.txt
suka hau murna.
Nace dasu ba wani bayan kun yadani ba ku zuwa gurina sai kace ba, a gari daya muke daku ba kamar wacce bata da yan uwa.
Nasir yace kiyi hakkuri mama ce ta fadawa baba ranan nan da muka tafi gurin ki shine baba yace kada mu sake zuwa gidan ki.
Lokacn Inna ta shigo dakin inda muke ta samay mu muka kara gaisawa da ita cikin mutunci.
Nan ta zauna a bakin gadon ta ganin Inna ta shigo dakin yasa su zuwaira da muke tare mikewa suna fadin amarya zamu tsaya kofan gida mu jira ki.
Nace haba ku zauna mana suka ce a, a muna dai waje har ki gama mu tafi ai.
Bayan fitan su ne Inna ta nisa take cewa yaran suna da da, a da sanin ya kama ta ne.
Nace cikin shagwaba Inna nikan dai yanzu ba kya sona nice kawai nake can cikin damuwa daku ?
Tace da akai may kuma nace ina ko su Nasir an daina tura min nagan su sai na tara abu don a kawo maku amma babu yaron da zan ba ta kawo nan na ciro wani babban leda daga cikin hijjab dina ina mika mata.
Kallon ledan takeyi tare da tambayan wanan may ne kuma a ciki ledan cike yake fam da tarkace iri iri dana tara don na kawo mata.
Bayan ta gama dan dudubawa ne race yarinya kardai ince kayan mijinkine kika kwaso muna haka na amfanin ki ?
Mijinki fa bai rage ni da komai ba yanzu don inba rashin lafiyan nan da ya kwantar dashi ba kusan duk sati da aiken da yake min daga gurin mamakin mai kuli.
Ni ban san irin godiyan da zanwa wanan bawan Allah ba gashi ya rike min ke da mutunci kullun yana yabawa da halin ki na tarbiya a garesu.
Ga kuma abin alherin da yake kawo muna don kinga yanzu banda talaucin dangin kayan miya sabulun wanka man shafi da sauran su.
Watarana ma har kayan girki kamar shine ya aje mu zai kawo muna da kudi ga hikimar da yayi na bi ta hannun mai kuli ya kai muna ta gurin ta sai dai ta aika nazo ko ta kawo min idan uwar ku tafita daga gidan.
Nisawa nayi nace mama shi Alhajin ne ke kawo maku wanan amma ni bai taba fada min komai ba wallahi.
Tace shine alherin arziki gashi yanayi ke da yakeyi kanki ma baki sani ba sai yanzu.
Nidai ko rike min ke da sukayi da mutunci ya wadatar dani wallahi tun har yau banji wani abin asha ba daga gare ki.
Murmushi nayi nace haba Inna baki koya min yin haka ba aikuma bazaki taba jin shi daga gare ni ba ai.
Nan dai nace Inna su Lawisa yaya nasu zancen auren ne naji shiru har yanzu ?
Tace kin ga yadda baki san komai ba nima haka iyakata dasu ido a gidan nan bana shiga zancen su suma hakan.
Sune ma ganina a wadace yake damun su kin san halin uwar taku da hassada da kyashi ai.
Yadda taso ta kawar dake a gabana taga na wullakanta sai taga sabanin haka ga taimakon da Allah ya jefo mijin ki a rayuwan mu yake muna.
Kedai kikara hakkuri akan wanda kikeyi mai hakkuri baya tabewa ga banza insha Allahu.
Nace insha Allahu ina tace idan ma tayi muna hakane da wani manufa to yanzu mu hakan ya zama muna alheri.
Don ya koma mata ciki kullun zaka ji ta tana sake magana da habaici a gidan nan.
Gashi Allah ba ai mashi wayo ita nata diyan ko tsohon ma Allah bai kawo masu ba sai zaman sa,in sa suke a tsakanin su da ita.
Muryan baba ne daga waje yake kiran Inna ta yana fadin ke Asiya bazaki sake yarinyar nan su tafi ba ga dare yanayi ko anan kike son ta kwana.
Shine ya katse muna hiran mu da inna na mike ina cewa inna zamu tafi zan shiga gurin mama na gaida ita kafin mu tafi.
Tace injin mijin naki yace ki shiga gurin nata don kada ki koyi wanan halin na matan yau da muke daukan hakan ba komai a rayuwan mu hakan ko shine babban koma a gobe kiyama.
Sai kiji mace ta fita da sunan zuwa gida daya sai ta biya gida goma ba da bakin mijin ta ba.
Nace Inna har na fito fa ya kirani yake cewa na, ratse na gaida mama altine din tace to tashi ku tafi kada dare yai maku.
Naba kanne na dari biyar nace su karya dashi da safe suka shiga murna itama inna dubu daya na bata na fita naba babana dubu daya mama dari biyar.
Sai sa min albarka baba da Inna sukeyi mama kan tun ce min da tayi an gode bata kara magana ba.
Gashi ko ranan da haka zata kwana ba ko sisi a hannun ta don yanzu yaranta sunyi wayo suke rike kudin su a hannun su.
Da kyat zata iya karban naira hamsin a gurin su don sai tasha mita kafin su bata wani abu.
Mun shiga gurin mama Altine tai murna kwarai da ganin mu tana ta ina aka saka dani.
Sai tambayana take yaya muke yaya abokan zaman nawa injin dai ba wani matsala ko ?
Tace nayi hakkuri na dage gurin kyautatawa mijina da sauran abokan zamana kamar yadda nakeyi.
Tace hakan da kikeyi shine samun kwanciyan hankalin ki a gidan don da kinje masu a tsaye ne ko shi mijin naku bazaki samu kan sa ba ai.
Bamu jima ba mukai sallama muka koma gida ina jin zuciya na ba dadin rabuwan da zan sake yi dasu sai kuma wani lokaci mai tsawo kila na sake ganin su.
****** ********* ******
Wanan ganin da mama tai min ya matukar tayar mata da hankali sosai gashi don samun guri wai harda kyauta kudi nai masu har dari biyar.
Wa ma yasan abinda nabawa uwata a daki don haka tun da safe tai sammakon barin gidan zuwa gidan aminiyar ta larai bamu da nisa sosai da ita.
Tana shiga suka gaisa larai tana ganin ta tasan akwai abinda ya faru don duk tai mata sakko haka agida da akwai matsala ke nan gare ta.
Tace may kuma ya faru mutumiyar tace bari kedai larai nai wa kaina abinda ya koma min ciki wallahi.
A zato na na hada auren yarinyat nan da garbati don na kawar da ita da uwar ta daga farin cikin da suke ciki .
Ashe ban sani ba na dauko wuka ne na dabawa kaina a ciki dana sani daya daga cikin wa yan nan shashashun yaran na cina mashi.
Kin koga yadda yarinyar nan Rahama ta koma Larai ?
Wai yau har Rahama ce da kanta tabani kyautan dari biyar cas kin gashi gashi nan .
Ta baje tayi kyau ta wani murje ta kara haske da ita kamar mai aure a birni yanzu fa uwarta ma bata cikin matsalan komai a gidan nan don sai bushashan ta takeyi.
Jin tai shiru larai tace da ita to ai baki san wani abuba ne Lauratu idan da yar taki kika bashi sabanin haka zaki gani fa.
Da sauri take kallon Lairai don jin abinda tace tace eh haka nane mana don kinga halin su ba daya ba da ita Rahaman.
Yadda nake jin labari fa ita yarinyar ce ta sai wa kanta zaman lafiya da kowa a gidan.
Don ko sabuwa dake hauka da farko yanzu ta aje shi gefe don mutuncin yarinyar a kan su ta dauke su tankar iyayyen ta ne bata je masu a tsaye ba.
Kin ga kuwa banga dan ki ko daya da zai shiga ya mayar da kanshi kamar bawa ba a gare su don a zauna lafiya.
Dama hakane dan hakin da ka raina sai yazo ya tsone ma ido shiya sa tun farko da kika zo min da maganan wanan hafin nace dake kinyi babban kuskure amma alokacin har haushina kikaji don may na fadi haka.
Kina ganin ke kin cuta masu ne baki san taimakawa rayuwan su kikayi ba ke .
Tace bari larai sabon atamfane ma fa ta daura a jikin ta kuma bana cikin lafen ta ba ne don nasan kayan lefen nata.
Gaskiya yaya sallah ya munafunce ni don da yasan akwai ci a wanan auren shine yaki jona daya daga cikin diyan shi.
Nan dai sukai ta kulle kullen su har take cewa duk yadda zatayi ta goga min bakin jini a gidan nan sai tayi don bazata bari tana kallo ina cikin daula ba dani da uwa ta.
Da tasan hakane da bala mai faci zata hada aurena dashi naje ko abincin ci ya gagare ni.
Kamar yadda ta kulla haka ta samu wata aminiyar sabuwa take fada mata wai suna may suka saka min ido ina yadda naga dama a gidan Alhaji gashi sai dinke dinke yake min kullun kuma yanawa uwata aike ba kakautawa.
Irin zancen da sabuwa ke so ke nan ranan da sakon ya samay ta nan ta haukacewa mutane a gida da masifa inda take shiga ba nan take fita ba ga miji kwance a daki ba lafiya amma ta tayarwa mutane da hankali.
Haka yasa shi daurewa yafito katakata dashi yana cewa ke Sabuwa kin ishe ni da masifa da tashin hankali a gida.
Ke lokacin da kika zo gidan nan haka wa yanda kika sama a gidan su kai maki ne shi ?
Don haka daga yau na sake jin hayaniyar ki a gidan nan kowa yaya ne nai alkawarin sai kin bargidan ko akan waye haba kin ishe ni Sabuwa kin kai min ko ina.
Ba a kan ki aka fara kishiya ba ke ba wasu ne kika zo kika sama a gidan bane wai ko su ba mata bane da basu daga hankalin su ba ga shigowa cikin su.
Duk abinda ke fadan wai nayi wa yarinyar nan nayi mata sabuwa sai kizo ki kwata ke ma in na karfi ne ?
Ya juya zai koma daki ya yanke jiki ya fadi tun take mata da yaran gida aka saka kururuwa a gidan aka kwasa sai asibitin birni
Kwanan shi biyar a ka dawo dashi ba hannu ba kafa tare dashi abu kuma ya koma kasa sabo.
Wanan faduwar ya dawo da ciwo sabo gare shi hawan jini yazo ya shiga ciki kuma da sauran ciwar wukan zamani da ba, a rasawa.
Aiko yaran gida da matan su suka saka ta a gaba sai tabar gidan nan ko suyi mata dan karen dukan tsiya su kora ta.
Ganin zasu iya mata abinda suka furta a kan ta yasa ta sulale ta bar gidan baki alaikum tun basu illanta ta ba.
Haka ya sa suka dan sarara mata don ficewan ta gidan ya dan rage masu zafinta da suke ji a lokacin.
Kusan kwanan kin da tayi bata gidan duk fama da jikin Alhaji akeyi don jikin yaki mai dadi sosai a lokacin.
Haka nan ko yaushe cikin jike jike da dafe dafen magani ake mai wani ai mai tausa wani kuma dafa mai yasha.
Muna faman sintiri yi mai sannu a duk dakin da yake haka za, a kwashe shi tara tara zuwa dakin.
Ranan sai ga Sabuwa ta dawo wai iyayyenta ne suka zo suka bada hakkuri akai.
Washegarin da ta dawo ne ina dakina ina barcin safe misalin karfe sha dayan rana na gama dafawa mama hausatu shimkafa da wanken sana an ta.
Shine na dan kwata don na huta a raina can a cikin barci na nake jin ana sallama a daidai kofan dakina.
Firgigit na falka ina amsa sallaman tare da fadin shigo daga ciki ina kokarin saukowa a saman gado.
Lokacin suka shigo dakin Anty Sa,ade na ce daga birni tayi shigan ta na yan gayu ga kamshi na tashi daga jikin su.
Tana tare da wata yar matashiyar budurwa tare da ita sai diyan ta biyu da take tafe dasu.
Ban san lokacin da na yanka wani uban ihu ba na makale mata a jikin ta ina cewa wai ni Rahama yau ina zan saka kaina.
Sai kuma na fashe da kuka a lokaci daya na durkushe a kasa daidai kafan ta ina rusa kuka gwanin ban tausayi.
Naji tace yau ga tsiya taron da zakiyi min kuma ke nan Ramana daga gani na kuma sai ki saka kuka haka ?
Tace wa budurwan da suke tare maryam tashi mu tafi wanan bata son zamana a nan.
Da sauri cikin kuka nace anty don Allah kiyi hakkuri na daina ina kokarin share hawayen dake fuskana a lokacin.
Nashiga daukan yaran ina cewa kai Fatima kece kika girma haka na taba hannun babban dan ta sai ya jaye daga gare ni.
Nace baka san ni ba ko kokaga na zama wata bakauya dani ko ina fadi ina dariya tare da kallon fuskan yaron.
Nan muka shiga gaisawa dasu cikin murna da jin dadi ina tambayan ta yaushe tazo garin namu ?
Tace ikon Allah Ramana ke ce yau haka a dakin auren ki gaskiya naji mamaki da mama ke fada min wai aure zakiyi sai ko gashi na tabbatar da hakan yau da nazo dakin ki na gani.
Murmushi nayi tare da fita daga dakin da sauri na fita zuwa bakin randan ruwa na na kasa na debo masu run shi a cikin kofin silver mai marfi.
Nakawo masu ba laifin sun karba sun dan kora ruwan suka aje kofin amma yaran su sunki shan ruwan sai turanci suke da uwar su da dayan budurwan da suka shigo da ita gidan.
Tambaya na take ina maigidan naki ne mama tace muna yana fama da jiki wai Allah ya sauwaka ya bashi lafiya.
Mun dan taba hira dasu wanda akan karatuna ne nake mata ina fada mata cewa nawa karatun ya rushe ke nan tunda zaman gidan nan da nakeyi ba fashi a cikin shi.
Tace komai ai na Allah ne baki san ko watarana zai yarda kije gaba ba ai nace cafdi anty bako a gidan nan ba.
Tace muje kikaini na gaidashi da sauran abokan zaman naki ko ?
Ban bata lokaci ba na mike muka nufi dakin mama hauwa inda yake kwance a ranan.
Kwance yake yana ganin mu yake kokarin mikewa zaune sai dai bai iyawa dole ya koma ya kwanta yana masu sannu da zuwa.
Kusa dashi naje ina cewa Alhaji anty na ce ta birni da nake baka labari tazo ganin mu yau.
Hannu yake daga mata alaman yana masu sannu da zuwa yai matukar bamu tausayi gaba dayan mu a dakin.
Gashi dai ya na son yin magana amma babu halin yin haka a gare shi sai in maganan ya zo mai yake samu yayi shi.
Muryan anty ce ke fadin an kaishi asibiti kuwa a hakan da yake kwance a daki ?
Mama tace an kai shi sai dai ba wani babban likita ne suka samu gani ba suka dawo wai akwai tsada ga ganin likitan.
Haba komai tsadan shi ai sai a kashi a ji halin da yake ciki yafi wanan kumshe shin da akayi haka a gida yana wanan wahalan haka.
Tace yana da yara manya ne maza suka ce mata eh tace idan suna kusa ina son magana dasu don Allah.
Daga haka muka fita na kaisu dakin mama hausatu tabata dubu biyar dakin sabuwa ma haka da mama hauwa.
Ai sai aka shiga saka mata albarka kwando kwando a ranan muka koma dakina kafin su yaya Hadi suzo gidan.
Tace gaskiya Ramana mijin ki ya bani tausayi mutum yana wahala haka an kunsheshi a gida ba wani maganin kwarai gare shi.
Kiyi hakkuri kinji duk wanan jerabawa ne daga Allah kici gaba da biyayyan dakike yi Allah ba zai bari ki tabe ga banza ba a rayuwan ki.
Muna cikin maganan ne sai ga yaya Hadi babban dan Alhaji yana sallama daga kofan shiya na.
Na fita naga shine nace mai ya iso itama na fada mata zuwan shi nan tafita daga waje gurin shi suka gaisa.
Take cewa dama tana so ne idan sun yarda sai akaishi asibitin can birni don zata koma ga jibi kunga sai ku isa ina can amma sai abinda kuka gani ga hakan.
Yai godiya yace sun gode zai yi shawara da sauran yan uwan shi takawo dubu hamsin taba shi tace ayi amfani dashi idan zasu zo din.
Da zata tafi tabani dubu ashirin wai na dinga amfani dashi tunda mijina da zai bani baida lafiya yanzu.
Sau mutanen gidan ta basu dubu goma wai su raba haba sai gida ya kaure da bakin albarka kowa na saka mata albarka agidan suka wuce muna kallon su.
Basu ki ba bayan shawaran da sukayi sun yake cewa tunda za, a taimaka masu gara su kaishi su gani kawai zaifi .
Haka su ka yanke shawara bayan kwana biyu da tafiyan ta suma suka take mata baya sai garin kano ganin likita.
Basu sha wahala ba don ta basu lanban wayan ta idan sunzo su kirata don ta sani.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, ,
IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH DON AMANA NE SHIGAN KI GROUP DIN MU, IDAN BAZAKI IYA BA KIYI MAGANA MU BAKI KUDIN KI YAR UWA, , ,
Taro na mutunci suka samu a gurinta ba bata lokaci ta wuce dasu asibiti inda saboda sanin ta gurin ba a dauki lokaci ba suka ga