Showing 42001 words to 45000 words out of 373688 words
Chapter 15 - A LOKACIN MUKE BOOK BY ZAINAB .I. MAKAWA.txt
likita.
Nan likita yai ta fada don may zasu aje shi a gida haka har tsawon wanan lokacin basu zo dashi asibiti ba.
Hakkuri suka shiga bashi ya duba shi aka bashi gado har na tsawon sati biyu .
Duk anty Sa, ade ce ke kokarin haka dasu gashi tana yawan zuwa duba su akai akai har zuwa lokacin da ya samu sallama daga asibitin.
Sunyi da likita nan da wata hudu zasu dawo dashi lokacin ya kara murmurewa za, a ai mashi aiki a gaban shi.
Itace taba da mota aka dawo dashi gida cikin iyalin shi da abinci masu gina jiki da zai dinga ci don lafiyan shi.
Muna nan muka ji dirin mota sai ganin su mukayi yana tafiya da kan shi ba kamar yadda aka tafi dashi ba da farko alaman sauki ya samu ke nan gare shi.
Mun ga yan zuwa gaida shi daga ko ina na muna barka da arziki suko su yaya hadi sai labarin irin karamcin anty sukeyi baki sake.
Suna fadin sunga inda daula ya yanke saka a gidan su sai kace ba a kasan nan ba mutum yake sun yaba da halarcin ta kwarai da gaske.
Sosai yake samun kulawa yadda ya dace abashi nan kuma aka koma yawon bin daki dashi duk wace keda girki za a kawo shi dakin ta yai kwana biyu kafin ta fita daga girki ya koma wani dakin kuma.
Ranan ina zaune ina kwalliya yana dakina nikan na mayar da hankalina ga shafan mai da nakeyi .
Ashe yana daga bayana ya falka ya kura min ido yana kallona a cikin tausayawa.
Shi kadai yasan abinda yake ji a ran shi a lokacin gamay dani yana ganin ya kuntatawa rayuwa na ya zama wajibi idan ya dan kara samun sauki ya sallamay ni naje na auri yaro wanda ya dace da ni.
Ban ankara ba sai jin sautin kukan shi nayi daga bayana yana tashi a hankali.
Ban lokacin da na shuri da kayan shafan nawa ba na isa gurin shi cikin tashin hankali nake tambayan shi ko jikin ne na kira mutanen gida suzo.
Yace dawo ki zauna Amarya lafiya na kalau wallahi tausayin ki ne kawai ya kamani ni san ban maki adalci ba a rayuwan ki.
Bazan iya biya maki bukatan ki ba amma na ajeki a hakana ina kallon ki gashi sai kara cikowa kikeyi shine nake ganin anya ban shiga hakkin ki da yawa ba kuwa nan da wani dan lokaci dole tun baki fahinta har kizo ki fahinci maynene sirin aure ke da kanki zaki fara son hakan a rayuwan ki.
Kinga duk halin da kika fada ciki nine da alhakin hakan a kaina ba wani ba don nine na ajeki batare da biya maki bukatunki ba.
Nace haba Alhaji bayan wanan kokarin da kake min may na rasa a gidan nan ni wallahi nagode kuma har gobe ina gode ma sai idan ban nufashi zan daina gode ma.
Na sa hannu na dan share mai hawaye nace kayi hakkuri Allah zai baka lafiya kamar kowa da yadda Allah.
Ajiyan zuciya naji ya sauke yake cewa ba komai zan dai san yadda za, a yi akan wanan ala, amarin naki nan gaba.
Haka yai min kwana biyu na ya koma wani dakin wasa wasa sai wanan halin ya zama mai jiki duk yake dakina da wuta bai zubar da kwalla ba a kaina wanda ni ban san ko na may ye ba.
Haka muka zauna dashi watan shi uku da dawo asibiti yaji sauki sosai ya murje har ya dan fara fita kofan gida yana shan iska waje tare da jama,a.
Ranan ya dawo dakina naga yana muku mukun ciro abu daga Aljihun shi na taimaka na ciro mai sai naga kudi ne masu yawa a ciki ya kira da yawa yace min yaki nan .
Nazo kamar yadda yace kusa dashi na durkusa yace ungo wanan kikai wa Innan ki asamu wani sana, a a dinga juya maki kudi suna dan shigo maki kina samun na kashi.
Don kinga yanzu ni ba fahita nake ba balle na dan dinga samo maki dan abin kwallam kina tabawa.
Gashi duk wani motsina idon mutane yana akaina ba halin nai maki wani alheri mai tsoka a gani.
Har lokacin da yake bayanin kudin suna a hannun shi ban karba ba sai da ya kara cewa cikin daure fuska karbi mana nace maki.
Nasa hannu na karba tare da godiya yace gobe sai ki shirya idan nabar dakin ki kije gida kikaiwa Inna ki ayi shawaran abinda za, ai maki dasu nace nagode.
Nan na duka gefen shi nai kuka mai isata tare da fatan Allah ya bashi lafiya.
Washe gari kamar yadda yace na shirya sai gidan mu na kebe da Inna ta nai mata bayanin komai kamar yadda yace min.
Tace to sai dai naga mamanki Altine don tafini dubura sai na barmata ta dinga juya maki su don nasan gurin ta sisin kwabo bai ciwon kai a cikin kudin nan.
Da haka na dawo gida na shige dakina ita kuma taga mama Altine tai mata bayanin komai suka yanke shawaran yadda za, a dinga juya min su
Mai hali baya barin halin shi ranan ya bamu dubu biyu biyu yace mu rike a hannun mu muyi amfani dashi.
Nan Sabuwa ta shiga fadawa wai ba, a adalci don may damay iyali da wanda baida za, a basu komai daidai.
Sau daya ya iya cewa ke Sabuwa daga haka kuma sai maganan ya tsaya mai ya dan dukar da kan shi.
Wasa wasa yana fadin yana jin kamar masasara ya kama shi nan suka kira wani nurse yazo yai mashi yan allurai a gida.
Sati biyu da yin wanan a tsakanin mu ina barci tsakar dare naji an fasa wani irin kuwa a gidan.
Duk wanda yaji wanan kuwan yasan muryan Sabuwa ce gaba daya mukayo waje sai ihu take tana fadin Alhaji Alhaji babu shi.
May kikace Sabuwa tace wallahi Alhaji ne daga yace na bashi ruwa yasha sai kawai naji ya sarke shike nan sai naji shiru.
Nan aka fada dakin amma ina yariga da ya tafi sai addua kuma din rai yayi halinsa ko a gare shi.
Hadi ya shiga yafito ya fasa wani irin kuka yace baba ya riga mu mama baya yarasu ko .
Daga inda nake tsaye nace da karfi Alhaji ya rasu yaya ?
Ban kara sanin inda nake ba sai dai na falka naga mama Altine da mama Asabe makwabciyar mu a kaina ina kwance saman gado dakina.
Ina iya jiyo hayaniyan mutane suna koke koke a tsakar gidan na tunkura zan tashi mama ta rike ni tace haba Rahama.
Kiyi hakkuri ki dangana Allah daya hada ki da Alhaji ya karbi abinshi sai hakkuri kawai.
Wani sabon kuka na fasa ina fadin mama da gaske Alhaji ya rasu shike nan bazan sake ganin shi ba.
Tace ya tafi Rahama adduan mu kawai yanzu yake bukata tashi takare shi yau ya koma ga mahaliccin mu sarki Allah.
Kuka sosai nakeyi haka gari ya waye muna cikin tashin hankali a gidan kafin wani lokaci har an hada shi za, a kaishi gidan shi na gaskiya.
Aka ce muzo muyi ban kwana dashi kafin afita dashi daga gidan mama tace min ki daure kada ki fara kiyi mashi kuka Rahama.
Ina rike ga hannunta muka shiga dakin da yake kwance an shirya shi cikin fararen kayan shi na tafiya kayan da kowa ke jiran ranan sawan shi tazo mai.
Nan mukai mai addua muna waje aka fito dashi aka fice dashi daga gidan nan gida ya barke da sabon kuka kuma.
Daga ranan muka shiga takaba sai tambayana ake zuwa yi wai banda komai tare dani ko ?
Sai dai nai masu murmushi kawai ba amsa don ban san may zan ce dasu ba ni don mama tai min dalla dalla akan tambayan da ake min.
Sai da aka watse an tafi sallah nake cewa da ita mama nifa ba wa abin da ya taba shiga tsakanina dashi irin haka.
Tace ke don Allah rufe muna baki da wautan ki keda kwanaki akewa radw radin ciki sabuwa har da yaji tayi kan haka zakice wai ke ba abinda ya taba shiga tsakanin ki dashi.
Kada na kara jin wanan zancen ko ga wani balle ai maki daukan mahaukaciya.
Haka dole naja bakina muka shiga takaba ni da sauran matan shi a gidan inda nake zama da mama Altine da wata tsohuwa cikin yan uwan Inna ta.
****** ********* ******
Tunanen makoma na yadda zan koma gidan mu cikin ukubar mama ya fara damun zuciya na.
Har nakaiga furtawa ga mama tace to yaya za, ayi ya zama dole yanzu kan ki koma gidan ku gaban iyayyen ki tunda nan baki da kwai baki da dunge a gidan to zaman may zakiyi masu a gida kuma ?
Hakana muke wankan a dadafe ranan da ya cika sati biyu ne yar gurin sabuwa ta zo ta kwashe min ruwan randana nai mata magana cewa bata ganin yanzu sai na sayi ruwan tunda banda mai debo min.
Daga can kofan uwarta ke cewa ke ma dai baki jin magana wallahi may yakai ki gurin wanan mai farar kafan ki debo min tsiya.
Ga uban ku nan tun ranan da ya tsiri auren wanan matsiyaciyar yarinyar bai kara lafiya ba sai da ya kwanta daman shi.
Shine ni zakije ki debo min tsiya kikawo min har ana maki kwakwazo akai kan ruwa.
Mama Altine ce tafi ban ko sani ba tace boyar Allah maida yukan ki kube yau ina wanda kuke fadan a kan shi ya kwanta daman shi.
Ke har wani dadi kikaji kina cikin wanka kike sababi haka kamar wacce abin bai dama ba.
Aiko ta juya kan mama da masifa wai mama ta kama girman ta kada yanzu ajisu da ita.
Karya ta fadi banice na jawo masu masifan rayuwa ba kala kala don iyayyena suna makwadaita aka cinna mai karfen kafa.
Allah yasa yaya Hadi yana shigiwa lokacin ya taka mata waigi da cewa ke sabuwa kin fa ishe mu a gidan nan dama don baba nake daga maki kafa.
Yanzu ke ba, ace kin kashe muna mahaifi ba sai wanan yarinyar da kullun baba cikin saka mata albarka yake har ta bar duniya keko fa daidai da rana daya banji makamancin wanan kalman ba daga gareshi a kanki.
Don mu har wasiya ya bar muna akan yarinyar nan kan ko bayan ranshi mu kula mashi da rayuwan ta kada mu bari ta shiga wani hali na wahala.
In ma kashe baba ne badon kada mu bata mai gawan shi ba ai sai muce kece kika kashe muna uba.
Don matsalanki ya kara jefashi ga ciwon da yayi na ajali karshe ma bamu san may kikai mai ba sai gawan shi muka gani a dakin ki.
Cikin wani irin tashin hankali take cewa yanzu Hadi ashe sherin da kuke kulla min agidan nan ke nan ku da muna fukan uwayen ku ban sani ba.
Tsofin dake gidan suka fito sukai mata caaa akai suka ce fitinan ta ya ishe su idan kin matsa zamu mayar dake gidan ku ne.
Tace wani gida ga gidan mijina da dakina da ya mutu ya barni a cikin sa ai yanzu kuma sai ido don jini ya riga ya gauraya da ruwa ko.
Fitinan sabuwa ne yasa diyan shi suka hadu kan a hada gadon daya bari a raba aba kowa nashi kowa ya kama gaban shi gashi ita yaran ta duk yan mata ne har su bakwai ras gare ta a gidan.
Nan akai kasafi basu yarda sun barta a cikin gidan su ba aka bata wani gida na Alhaji karami ita da yaran ta ranan sukace bazata kwana masu gida ba sai ta fice ta basu gurin su.
Da kyat aka lalashe su su bari a gyara gidan tafice masu daga gidan su.
Ban san Alhaji na da arziki haka ba sai wanan ranan nima na samu gida daga kason na na wanka da gona sai dai ba babba ga shanaye dana samu a ciki da kudi tare da sauran tarkace.
Iyayena suna ganin yadda aka kwashe da sabuwa suka roka abasu ni su tafi dani gida na karasa wanka a can amma aka hana.
Suka ce idan sun min hakana basu rike amanan da mahaufisu yabasu ba nawa ayi hakkuri kwana nawa in ga rai ga lafiya zan gama wanka na koma gida.
Mama Altine kwana arbain tai min ta barni cikin su banda wani matsala tare dasu sai na kewan Alhaji kawai wanda bani kadai ba har yaro karami dake gidan yana yi don halin shi na alheri ga iyalin shi.
Ban da rashin komai in ban da na maigidan don komai suna wadatar min dashi duk da an raba an ba kowa kason shi amma su yaya Hadi basu barina haka na cikin su.
A dadafe na gama wanka a gidan ranan da muka fita tun safe sai ga su Rukaiyya wai mama tace suzo su fara rage min kayana zuwa gida.
Mama hausatu ne tace haba sai kace zaman da akayi cikin bacin rai aiko zata koma a bari har a dan natsu sai ta koma gidan ko ?
Haka suka juya suka koma suna fada mata ta haufada wai ko ni nafi kowa son gidan miji yanzu ai dole na dawo gidan ubana tun da dadi ya kare anga guri anbaje ana cin dadi yanzu ko dole na dawowa turke na mai cabo yana nan yana jirana karya ya kare da sallon auren mai kudin gari gare ni.
Ban dawo gida ba sai da na cika sati biyu ranan mutuwan ta sake dawo muna sabo a gidan .
Ina kuka sunayi aka kwashe min kayana zuwa gidan mu su mama ne suka raka ni har gida da dare sai fadin alherina sukeyi suna fadin zasu sha kewa dai kan a gidan.
Yarinya karama amma bata san zafin jikin ta ba ko kyashi irin na yaran yau komai da zuciya daya zatai maka shi.
Mama jin su kawai take tana fadi a ranta ai dole kuce haka tunda kun samu boya to muma nan mun fiku bukatan ta ai yanzu.
Suka tafi suka barni ina kukan bakin cikin rabuwa dasu danayi na shige dakin Inna ta na kwanta a saman gadon ta na lafe.
****** ********* ******
Ban fito ba tunda na kwanta haka gari ya wayw min sai juyi nake ina tunane banyi barci ba mai dadi.
Sai bayan nayi sallah ne na samu barci ya dan dauke ni mai dadi har ban san inda nake ba a lokacin.
Can cikin barci naji muryan Inna ta tana tayar dani wai na tashi mama tana kira na a waje.
Nai mika tare da juyawa
na mike na sauko saman gadon tare da jan hijjab dina na saka a jikina.
Na nufi waje inda nake jin mama tana kwada min kira harshe sama na amsa da na,am mama .
Tace to kin shige daki kin mimike kafa wa kike jira ya debo maki ruwa da za, ai aiki da shi.
A hankali na dago kai na kalle ta nace ruwa mama ?
Tace eh ruwa ko kinfi karfin diban ruwan ne ke da bazaki ba kike nufi ko may , don ban san uban da kika aje da kike son yaje maki rijiya ba ai.
Ko har yanzu mulkin auren gidan mai kudin ne a saman kan ki muji ?
Ban yi magana ba sai juyawan da nayi zuwa dakin mu na koma na zauna a bakin gadon dana tashi.
Inna dai tana jin mu batai magana ba sai aikin ta takeyi kawai a tsakar gida.
Can dai taji ni shiru ban fito ba ta kara kwala min kira karo na biyu daga dakin na leko kaina ina fadin mama ni ba zan fita ba gaskiya don kunya nake ji wallahi.
Eyya su kunya manya ke nan ke gaki matar Alhaji ko to Alhajin ma ina yake yau ko diyan shi da matan shi na kwarai sun kama kan su yanzu haka.
Balle ke da ba kowan kowa ba a gari kice wai ke kina jin kunya anganki a bakin rijiya.
Nace ciki ciki gaskiya mama ba zan je ba fa don wallahi ban san yadda zan kalli mutane ba da idona.
Eh lalai kuwa kin kai Rahama aure dadi idon ki ya bude don yanzu abinda na sani kin riga kin san shi shiya har nake fadi kina fadi ko ?
Nan ko ta hau fada ban san lokacin da wani kukan bakin ciki yazo min ba atake na shiga rera kuka.
Sai ga baba gidan kamar an jefoshi yayi mantuwa ya dawo gidan.
Tun daga kofan shigowa gidan yake jin muryan mama sai kuma sautin kukana dake fitowa daga cikin dakin mu.
Kai kai wai yaya hakane kuma may ke faruwa ne wai kuma yanzu fa na bar gidan nan na fita shine har zan dawo na samu gida ya rude may ke faruwa ne wai tambaya fa nakeyi ?
Tace isashiyar yar ka mana wai taje ta debo ruwa shine ba kunya wai har yarinyar nan ta kalli idona tace min ita bazata ba kunya take ji.
Baba yace haba lauratu wai har yaushe yarinyar nan ta dawo gidan nan da za, a fara jin ku da ita.
Yanzu koke ce kikaga ta dauki abin diban ruwa ai ki mata fada lauratu don haka bai dace ba gaskiya.
Tau ashe abin naku dama hadin bakine kukayi kun riga da kun shirya yar lele