Showing 69001 words to 72000 words out of 373688 words
Chapter 24 - A LOKACIN MUKE BOOK BY ZAINAB .I. MAKAWA.txt
kawatse kan za a daura aure nan da sati daya ta tare dakin ta mama ta dawo gida cikin bacin rai ta isa gida har da suma sai da tayi hankalinta ya tashi baci ba sha ta shiga wani hali na tashin hankali.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,
IDAN KIN BIYA KI RIKE AMANA DON NAUYI GARE SHI YAR UWA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYA BA DON GIRMAN ALLAH, , , ,
Muna nan jikin yaron yaki dadi dole anty ta kira mahaifin shi a waya take sheda mai yau Nasir jikin ba dadi don har da amai yayi sau biyu
Yace yanzu zai turo hamza driver yazo yakai shi asibiti amma ni yanzu na sha magani ba zan iya fita ba gsskiya.
Yace ko da mama ce ta kai shi mana asibitin tace ba damuwa tana gama wayan lokacin ina tsaye na rike hannun shi sai cewa tayi ki shirya shi ku tafi asibiti yanzu driver zai zo.
Da sauri na dan kalle ta nace asibiti gabana ta fadi na farko ga dare yayi na biyu ban taba shiga ko asibitin garin mu ba balle na birni irin kano san nan ma ni a wurina dan wanan ciwon ne za, a kai har asibiti.
Ganin nayi shiru tace dani ko akwai matsalane naga kaman kina tunane akai ?
Dan dariyan yake nayi da bai kai ciki ba, kawai nake cewa da ita ba komai anty.
Amma gabana sai faduwa yakeyi sosai haka na shirya driver na zuwa muka fito don tafiya asibitin.
Can naji tana cewa da driver ya tabbatar da bai barmu mu kadai ba don ni ba kuwa ce ban san gariba sai lokacin nadan ji sanyi a raina.
Tafiya mukeyi yayin da Nasir yake kwance a jikina jikin shi yai zafi radau.
Amma ni sai faman kallon yanayin garin nakeyi ga kwan haske wutan lantarki ya haske ko ina na garin.
Wani katon guri muka shiga naga motoci an parker iri iri a gurin nan ya samu guri shima ya parker tamu motar.
Ya bude don ni ban iya bude motan ba ma muka fita ina rike da yaron shine ya karbo family file din su muka bi layin ganin likita.
Sai baza ido nakeyi ina kallon yanayin mutanen birni yadda suke harkokin su ba ruwan wani da wani na lura ba mai ko gaida wani sai dan wanan yabi can wancan yabi nan.
A haka har aka kira mu Hamza driver yace na shiga da yaron ciki shigan mu office din ya dawo mun da burina na son zama likita ko nurse.
Komai na office din a tsare yake nan ya nuna min kujera muka zauna yai muna yan tambayoyi akan ciwon yaro na bashi amsa.
Bayan ya gama yan rubutun da zaiyi a cikin takardan ne ya miko min tare da cewa muje lab da yaron.
Nafito Hamza ne ya kai mu akai koma suka gane maleria ne kawai ya kama shi nan akai mai allurai muka juyo zuwa gida.
Sosai yaron ya samu kulawa a gare ni haka shine ya jawo mun shakuwa dashi fiye da duk sauran yaran da nake dawai niya dasu nata.
Shakuwan da yaron da bai yarda koda iyayyen shi yasa anty matukar mamaki take cewa lalai Rahama kinci sunan ki wanan mara yardan ne har yake manne dake haka ko yaushe.
Ai Nasir da kike gani tun yana goye baya da yarda sam da kowa ko yaushe yana like dani.
Da ya fara wayo ne kuma koni din baruwan shi dani kullun yana make gefe daya shi kadai.
Nace anti baku fahince shi bane akwai abubuwan da baya so kuma hallitan shine hakan.
Na fahinci ita anty irin rayuwan turawa gare su nabawa kowa freedom din shi don har yaran sai abinda suke so ake masu.
Ni kan ai a gare ni ya kwana gidan sauki dama ina da son yara don haka sai nabiye masu amma cikin hikima nake gyara mata tarbiyan su.
Ganin yadda ta ya mutse ne a yadda na san ta yar gayu a baya ranan nake cewa da ita Ina son nayi kitso kaina yana damuna.
Tace kinga sai mu tafi tare a gyara muna kai ni dai ba kitso zanyi ba sai dai a wanke min kaina kawai.
Tace shirya da azahar mu fita mu leka saloon din don kiga guri.
Ni dai ban san ina ne saloon ba na dai ce da ita to ne kawai na shirya kamar yadda tace din muka fita.
Ita da kanta take jan motan ina ta kallon ikon Allah ashe dama ta iya tukin mota mace da ita.
Wani katon shago naga mun tsaya sai mata ke shige da fice a gurin an rubuta a gurin saman wani katon abu da rubutu mai launi tare da hoton mace da gashi dogo da akaja.
ASSAMA,U SALOON waje ne dake cike da manyan mata masu fada aji yanayin masu aikin gurin ba namu bane don shigan matan kasan larabawa ke jikin su.
Na kara ganin wani guri an rubuta haka PEDICURE & MANICURE Anty tace zo mu fara shiga nan muna shiga na fahinci ba bakuwa take a gurin ba don naji suna cewa a hajiya kwana biyu baki leko mu ba ko lafiya ?
Ta dan yi murmushi tace kin san jikin ne sai a hankali yanzu ni tace a fara yiwa ina ta faman kalle kallen abinda akeyi a gurin.
Gaba daya naji yan gurin nata faman yaba kyauna da dadawa ni dai bangani ba sunce na kalli mirro amma na kasa don kunya.
Har kai na sai da aka yarfa min kitso masu kyau kanana nai mamakin irin saurin mutanen
Da akai wa anty sai naga gaba daya ta canza min ta koma kamar wata yar karamar budurwa da ita sai ka rantse da Allah ba itace muka shigo ba a ya mutse.
Haka muka dawo gida shar damu tun shigiwan mu mama ke fadi kai kai kai wai ko Rahama ce nake gani ko gizo idona ke yi min.
Falo muka zauna sai naga ta baje rigunan da muka sayo a kusa da ita tana fitarwa daya bayan daya ta sake duba su tare da yaba kyawon su.
Gaba daya ta miko min su gaba na tana cewa a kashe lafiya sai na samu lokaci akwa wanda zan kara duba maki a cikin kayana sai ki kara.
Daga yau bani son ki kara saka komai da kikazo dashi daga kauye don matan gidan nan yan rainin wayo ki dinga kwalliya kamar kowa a nan kina gyara jikin ki a kai akai.
Kafin nakai ga godiya ta daga min hannu alaman a, a bata son haka shigowan yaran da suka dawo ne yasa muka mai da hankalin mu gare su baki dayan mu.
Yau da kuka Amira ta shigo wai Nasir ne ya buge ta a mota anty tace oya kije gun anty Rama ta cire maki uniform.
Kallon mamaki naga yaran na min ai dayan yar gurin zulfa take cewa wanan anty Rahama ce mummy.
Gaba daya dariya akasa anty ce a to sunga yau kin sake masu kin zama wata yar birni dake haka nake son kowa yaga yar kauna nawa ya yaba maki don badai kyau ba kan sai dai wani abin kuma.
Muka kwasa dani da kayana dasu muka shige ciki a tare gaba dayan mu.
Bayan shiga na ne mama ke cewa ikon Allah watau gyara shine mutum mutumin kauye da ta gyara akafi watau.
****** ********* ****** ******
Yau tun safe dana tashi banji duriyan ta ba sai ni da mama ne ke faman dawainiya da yaran har suka gama shiriritan su suka wuce school.
Lokacin ne nake cewa mama yau ban ga anty ta fito ba don takan fito su gaisa da mama wani lokaci ma a falo zata dan zauna har sai yaran sun fice daga gidan amma yau shiru banji duriyan ta ba.
Dakin nata na nufa a hankali na tura kofan dakin don na dubata na hangota rufe a cikin bargo tana rawan sanyi.
Da sauri na karasa gurin ta ina cewa anty lafiya kike kuwa maganan ta baya fita don haka na bude bargon da take rufe a cikin sa.
Gabana ne yai mugun faduwa don duk ta fita yacin ta cikin murya mai makyarkyata nake cewa anty jikin ne ?
Da kyat ta iya cewa Rama taimaka min miko min wancan abin maganin nawa kibani na sha, ga wani irin numfashi da takeyi kamar zata shude a lokacin.
Da sauri na dauko abin maganin tana nuna min na juya zuwa waje don na dauko goran ruwa tasha.
Hankali tashe nake fadawa mama halin da Anty ke ciki naga hankalin ta yai matukar tashi sosai tabi muka koma dakin tare.
Na bata maganin tasha da kyat ganin yadda jikin nata yake nace da ita ko akwai taimakon da zan iya maki anty ?
Na tambaye ta cikin dukawa kanta ina son inji may zata ce dani sai alama taimin na rufa mata bargo a jikin ta.
Haka muke a kanta cikin tashin hankali yadda naga tana shan wahala yasa na fita daga dakin dakin mu na koma na takure kaina ina faman kuka.
Ba abinda nake tunane sai irin taimakon da boyar Allah nan take min yanzu idan wani abu ya faru da ita aiko diyan ta sai na fisu shiga uku.
Muryan mama ne naji tana kiran sunana shi yasa ni fitowa daga dakin da sauri da kaga idanuwa baisai amfadawa mutum na darji kuka bane.
Mama take tambayana ina kika shige ne tundazu kije Saade na neman ki a dakin ta da sauri na karasa dakin ba laifi na samu ta yaye bargon dana rufa mata a jikin ta.
Ba laifi don tabar rawan sanyin da take yi da farko murya a wahale take magana dani.
Ramana don Allah taimaka min ki matsa min kafafuwan nan ko zan samu ya sauka min gaba daya.
Ba musu na gyara yaye bargon a kafanta na shiga tausa mata kafan ta a hankali ina jin yadda take sauke ajiyan zuciya a hankali.
Sai ce min takeyi ta gode jin banyi magana ba yadda muka saba da ita yasa ta dago kai ta kalle ni.
Yanayin idanuwa na ne ya nuna mata kukan da sha tace subbahanallahi Rama kuka kikayi ne ?
Allah sarki ai wanan ba komai bane don yazo min ma da sauki ai don Allah ya kawo min ke da wuri kin bani magani nasha.
Dan fitan nan da mukayi jiyane nasan ya tayar min da ciwon haka amma ya kwana biyu bai motsa min ba da yake na samu hutu yadda ya dace.
Tun dare ya fara min gashi ban iya tashi na dauko magani inda yake ke kuma baki da waya a hannun ki.
Yakama ta nasai maki waya ki rike don irin haka idan ya taso kina sani nace waya anty tace eh nace ban san yadda ake amfani dashi ba ai.
Zaki sani ai baida wuya da ankoya maki zaki gane yadda yake tun ban gani ba nace da ita na gode.
Babu wanda ya sake magana cikin mu sai zuwa can a zatona ma ta samu barci ne sai take cewa.
Gobe baban su Nasir zai dawo don munyi waya dashi yanzu yake fada min haka.
Don haka ina son ki gyara gida da kyau kamar yadda kika saba sai kiyi abincin da zamu tare shi.
Amma shi yafi son yaci abinci mai nau,in gargajiya idan zai samu sai ki duba kiga wani yafi maki saukin girkawa a tanadi abinyi.
Taci gaba da cewa sai dai idan ya dawo fitinan gidan nan zai dan karu don matan shi zasu dawo don a matse suke ya dawo din daga su har iyayyen su.
Don haka abinda nake so dake a gidan nan ki tsaya a inda na aje ki don ba mutunci ne dasu ba.
Gabana ya fadi don jin may tace dani tace ina ga ai shike nan zaki iya tafiya ki huta kafin yan rigima su dawo.
Sai yamma lis ta samu tafito falo ta zauna har lokacin alama ya nuna bata jin dadin jikin ta sosai ga yanayin ta duk ya dan sauya ko don gyaran jikin da akai mata ne nake ganin canji a jikin ta haka.
Aiki nake amma tunane nake a raina don gaskiya ina ganin za, a takurawa rayuwan mu ne idan sauran masu gidan sun dawo.
Tunda yadda na fahinta sam babu zaman lafiya a gidan da sauran mata ga alama ya nuna maigidan kamar fitanane yadda yai karfin halin tura mata biyu gidan iyayyen haka kai tsaye kuma aka tsaya ga sai yadda yace za, ayi.
Ni dai komai mugun halin su mudfin ina gidan nan bazan bari su kawowa Anty na rashin mutunci ba a gabana ina gani na kyalesu sai dai ayi wanda za, ayi din.
Tuwon farar shinkafa na tuka mai da miyan kuka yaji kayan yaji kamshin dadawa yakeyi sosai sai kassan maman rago da nai amfani dashi cikin miyan.
Nai ferfesu kayan cikin rago da ban shima hadin hausa nai mai don ban sa kayan an gayun su ba ga miyan.
Daga gidan har abinci na kammala gyaran su tsab na koma gurin anty dake daki a kwance na samayta nake fada mata na kammala komai yadda ya dace take cewa kin gama a cikin sa,a don yanzu ya bugo min waya wai sun sauka garin.
Su ma matan nashi ina ganin yau zasu dawo gidan don naji yana tambayana ko sun shigo.
Nace to anty ki tashi mana ki dan shirya kada a amay ki haka ko ?
Murmushi tayi tace kai kaji Rama da wani zance waye bako na a cikin su idan sun samay ni a hakan ?
Nace su duka ai tunda sun kwana biyu basu gidan ya kamata su samay ki a shiri ke ma.
To yanzu yaya kike son ayi na ce bari na duba maki mai saukin sawa sai ki saka.
Duk wanda na ciro sai tace yai mata nauyi da yawa ga kaya shake a wadrove amma bata damu da sakawa ba ita.
Sai wani dogon riga light blue mai shara shara baida nauyi tace na miko mata shi ta saka.
Rigan yai mata matukar kyau a jikinta sosai gashi dama ta yi gyaran jikin ta sai kyaunta na asali ya fito sosai.
Falo ta koma ta zauna nace mata ina zuwa na shige ban dade da shiga ba naji hayaniya a falon amma hakan bai sa na fito ba a lokacin don ba, a nemay ni ba in ba gulma ba may zan fito yi kuma.
Duk da dai ina so ganin waye mijin na anty mai irin wanan dukiyan haka mai yawa haka da yai sa, an samun mace ta gari mai halarci irin Anty Sa,ade.
Daga kitchen nake jin muryan wata dadtijiya yana tashi da alama fada takeyi don sai na kasa kunne na dakyau naji tana cewa.
A kan wanan tsohuwar da ka aje a gida zaka kwaso diyan mutane kuna cuta masu sai abinda tace shine akeyi don ta mai she ka bi can.
Dakai da ita Sa, ade duk zan yi maganin ku ne kwanan nan yadda ta hure maka kunne ka tunkuda keyan yaran gidajen su itama haka za, a tunkuda ta tafi nasu gidan.
May ma wai kagane ga auren wanan wannan mutu kwakwai rai kwakwai ne wai ni banga abinda kagani jikin wanan maikama da kyankyaso din.
Wanan wanan da kake gani bani mussu idan ance ta girmay maka don kana ganin ta haka a fige ne kake mata daukan yarinya karama.
Ni dai daga inda nake ba na jin muryan mijin nasu amma matar dake fada naji tana cewa in har tace bata zama da yaran nan don bakin kishin tsiyan ta sai dai ita ta fita tabar masu gidan mai bakin halin tsiya.
Yau ko kinki ko kin so duk zasu dawodakun nan su kuma su kwana a gidan nan jarababban baza kawai mai bakin kunatan tsiya.
Zuwa can na bar jin hayanitan su haka yasa na fahinci masu fada kila sun tafi ne don naji shiru kamar babu kowa falon.
To amma kuma wacexe mai ma anty wanan mugun zagin haka har take kiran ta da tsohowa na ji dai tana fadin wai ta girmi mijin nata shi mijin wani iri ne wai badai yaro ne zai iya tara wanan abinda nake gani ba haka ?
Har nagama abinda nakeyi ban ji duriyan kowa ba na koma daki na shige sai da yara suka shigo muyi sallah ne naji suna cewa wai sun raka daddy su sharada gidan su grandma.
Ina shirin kwanciya don yau ba fita falo kallo gare mu tunda mai gidan yana gari suna falo da iyalin shi mama kuma har tayi barci a inda tai sallah.
Sai ga Nasir ya shigo inda nake yana cewa anty wai mummy kizo ku gaisa da daddy.
Nace to tsaya mu tafi tare kaji Nasir na jawo hijjab dina da nai sallah har na nade shi na saka akaina.
Nabi bayan yaron muka fita zuwa falon inda iyayyen nasu suke zaune tare da sauran yaran gida baki dayan su.
Da sallama na na shigo falon yana zaune saman dan karamin carpet din dake tsakiyan falon nasu,
Ya mike kafafuwan