Showing 48001 words to 51000 words out of 373688 words
Chapter 17 - A LOKACIN MUKE BOOK BY ZAINAB .I. MAKAWA.txt
ta tsuke tai shiru har lokacin tafiya yayi suka wuce.
Don makaran ta ne kawai yasa ta bar yaran ta a hannun kishiyoyin ta ba don taso ba don tana nan ma yaya aka kwashe da su balle bata kusa.
Ko ita Zulfa ba don Allah ta rike yaran ba don sai daya zube mata kudi masu yawa ta yarda zata zauna dasu din.
****** ********* ******
Na gama aikin da nake taya mama altine na kwashi kayan na aiki tare da kaisu bakin kwata na wanke komai fes na mayar na kife mama na zaune ta zuba min ido daga inda take zaune ta motsa furan data dama ta sha.
Ina yarfar da ruwan dakw hannu na bayan na dauraye kafana take cewa sannu Rahama ai kin huta ke bakajin kiyuyan aiki ko kadan.
Da ace uwarki lauratu ta gane haka ta nemi zaman lafiya dake a gidan dan wanan zaman da zakiyi a gida aida ta more maki sosai.
Na dago kai da sauri ina kallon mama nace kai mama matar da tun ina yar kankanuwa na fahinci bata kaunana yaya zan zauna da ita ta more min haka.
Ni fa yadda mama bata kaunana a sannu nima haka kiyayyan ta ya shiga har kasan raina wallahi.
Mutumin da zai iya maka sheri da kazafi aiko kasheka yana iyayi mama.
Bata kashe ki sai dai sherin ta ya koma mata baga diyan ta nan ba babu mashinshini a tare da su duk fa cikun mugun halin ta ne amma ita bata ganewa ne kawai.
Ki debi abinci kici kada yai sanyi gashi da zafin shi nace ba yanzu ba mama sai anjima kafin na kwanta don tunda na dawo gida idan Innata ce da girki a gidan mama altine nake kwanci na don nasan Mama bazata yarda da na kwana a dakin ta ba yadda muke din nan yanzu kamar annabi da kafiri ni da ita.
Muna nan muka ji sallaman dan wurin mama yana cewa Rahama wai kizo inji baba .
Nace yau baba lafiya ya dawo gida haka da wuri don nasa sai yamma lis da magariba yake dawowa gida.
Ban bata lokaci ba na figi hijjab dina zuwa kiran baban nawa da yake min ko da na shiga yana alwala zaiyi sallah na nufi inda yake zaune saman dutse na gaishe shi da dawowa.
Na samu guri daga gefen shi na tsugunna ina fadin baba gani .
Yace dan dajan ta min na rarage alwala na mike na koma gefe ina jiran idarwan shi har lokacin daya gama ya mike tsaye.
Sai naji yana kiran Lauratu lauratu, lauratu fa da dan karfi ta amsa daga daki da saurin ta tafito tana gyara daurin zanin ta.
Tana cewa lafiya dai malam wanan kira haka kamar zaka tsaga min kunne dashi.
Yace to ke ce din idan ba haka aka kiraki ba sai ki kyale mutum tsaye wani zubin.
Yace ina ita Asiya take inna dake bakin murhu tana kashe wutan da tai girki tace gani.
Yace to dama ba wani abu bane yasa nai kiran ku ku duka ukun sai akan Rahama gata nan.
Allah ya kawo mata mai nema a cikin sauki ba ko wani bane sai Malam Jatau na hayi dotse abokin maigidan ta marigayi.
Shine ya aiki min yau da safen nan akan yana son ta da aure ya hada ta cikin iyalin shi.
Don ya yaba da zaman ta gidan aminin nashi da tayi kwadayin hakan yasa yake sha, awan auren ta.
Wani irin dariya gami da guda mama ta ranga tare da cewa yarinyar tayi tagomashi ga tsofin gari.
Wani irin dam dam naji kirjina yaba da a lokaci guda cikin raina nace wani malam Jatau kuma can ai gara ma Alhaji garbati marigayi din shi a tsaye yake kyam ba irin malam Jatau ba dake tafiya a duke.
Gashi da dan banzan kazanta da rowa ko kiyashin gidan shi sun san shi da rowa da mugun halin.
Mama sai da ta gaji don kanta san nan ta tsagaita dariyan ta tana cewa injin ka bashi dai.
Yace ban amsa mai ba sai naji shawaran ku tukun akan zancen kafin na basu amsa ta.
Lalai ma malam yo may zaka tsaya jira da ita Allah ya kawo mata mai so da wuri haka ?
Yace ai komai sai a hankali akeyin sa tunda yanzu ita ba budurwa bace kin ga zama dan bata zabi ai ko?
Zabin may har nawa Rahama take da za, a tsaya neman wani zabin ta kudine dai akwaishi kaga sai taje taciwo muna nashi kasuwan kuma.
Ban san lokacin da bakina ya kufce ba nace ai kina da tan mata zuka zuka har uku a dakin ki kibashi mana.
Salati ta saka tare da saka kuka wai naci mutuncin ta a gaban uwaye na ai ba ita bace tasamin farin jinin tsofi balle naci mutuncin ta bakin halina ne dani da uwata ke bibiyan mu.
Da kyat baba ya lalashe ta ta koma dakin ta nikuma yai min fadan haka kaca kaca ya fice gidan.
Dakin Inna ta muka shiga kowan mu bakin ciki yana cin sa a rai da wanan sabon fitinan dake neman bullo muna kuma.
Nace wa Inna ta ni wallahi wanan karon ko kashe ni baba zaiyi ba zan yi auren nan ba ai bani kadai ce diya ba a gidan da zaita badani ga tsufin gari haka.
Inba tace kidai bi sannu ke ma kin san idan uwarku ta kafe sai ya bayar dake ko bakya so hakan.
Daga daki muna jin mama da yaran ta suna bidirin su cikin jin dadi har da shewan su.
Don su burin su dama shine suga bakin cikin mu nida uwata a gidan ga kuma wani dama ya sake samuwa gare su again.
Washegari koda na je gidan mama na kasa fada mata komai sai dai ta fahinci ina cikin yar damuwa a lokacin.
Ta tambaye ni nai mata yake kawai da cewa ba komai mama don ba ko wani sirin gidan mune zan dinga fada mata ba din yanzu girma yazo min na san wasu abu ba kowane zaka fadawa ba.
A kai sallama a kofan gidan mu lokacin baba ya fice zuwa kasuwa ba yara gida mama ta yafa ta fita.
Malam Jatau ne a cikin wani tsohon babban rigan shi daya takure don tsufa ga dauda taf ga kayan sai tsohon hular dake kan shi don tsufa har zaren hullan ya fara zarewa daga jikin shi sai shafin dauda daya kwanta akai.
Suka gaisa tana washe baki take cewa , a, a Alhaji Jatau ne sannu da zuwa .
Ai kuwa ba kunya mama take cewa har an fara zuwa zance ne gashi maigidan ya fita amma ba matsala bari a kira ma yarinyar ai tunda ina nan.
Ya washe bakin da duk goro ya bata shi yake cewa ikon Allah ashe kun san da zancen ke nan wallahi yabawa da halaiyar yarinyar don marigayi yana yaba hankalin ta.
Hakan yasa nai kwadayin saka ta a cikin nawa iyalin ko banza na taimakawa shi marigayin ga nauyin da ya bari ai.
Mama take cewa gaskiya ka kyauta muna sosai ga wanan jahadin don kaga dama yanzu auren ta sai mai dan hannu da shuni tunda ta saba da daula a can.
Ya kara washe bakin shi yana dariya tare da fadin kada aji komai zan rike ta amana yadda shima ya rike ta a gidan shi.
Mama ta wuce shi zuwa gidan mama Altine inda nake ina dakin mama na dan kwanta don ranan bamu aikin komai.
Sai muryan mama Lauratu muke ji yana tashi tun kafin ta kawo kwanan shigowa cikin gidan.
Rahama Rahama wai ina mara kunyar yarinyar nan ta shiga ne haka ana kira kamar bata ji.
Daga inda nake kwance ina jinta sai mama Altine ce kecewa injin dai lafiya wanan kiran irin haka ?
Cikin takaici take cewa ina wanan yarinyar take ne wai ana kira tana kyale mutane to ki fito ga bazawarin ki yazo gurin ki.
Bazawari kuma mama Altine ta tambaya cikin mamaki tana kallon mama lauratun dake wani haki.
Tace basu fada maki zancen malam Jatau na hayin dutse dake son auren ta bane ko may ?
Takara cewa ai kinga matsalan su basu bar kowa ba a gurin kilibibi har dake uwar dakin nasu sai sun gwadawa halin su.
Daidai lokacin na fito daga dakin mama ina mata kallon takaici nace.
Mama ina tun ranan na fada maki ra, ayina akai ke ma may yan mata uku a daki da basu taba aure ba ai su gwada sa, an su sugani gareshi ko don naga sunfi dacewa dashi bani Rahama ba.
Daga haka na shige daki abina na kwanta na barta nan waje tana sallami da zagina sai inda ta tsaya ta fita tana cewa Jatau din kyale jairan yarinyan nan sai an fito mata tabayan gida.
Koshi Alhaji marigayin ai ba kasafai ya samay ta hakana ba sai da muka hada kai dashi komai yazo daidai gareshi.
Kokai sai mun kai ga hakan in har kana son ta da gaskiya dole sai kayi wani abu don na shiga na fita a samo maka kan ta.
Ya gyara tsugun ni shi yace to wo hakane abin yake to yanzu kina ganin kamar nawa zamu kashe ke nan.?
Mama ta samu yadda take so takara dan matsowa kusa dashi ta kashe murya tana dan kuskus tare da shi cikin rada.
Badon abinda yake muradin samu bane da babu yadda mama zata iya cin naira guda nashi daga aljihun shi komai dabaran shi kuwa.
Nan dai sukai sallama da ita tai mashi alkawarin zata san yadda ta shiga tafita aka samu kaina a cikin sauki.
Bayan fitan ta gidan mama Altine ne ta saka ni gaba da tambaya ina kuka ina sharan hawayen bakin ciki da takaicin dake cina ne ina fada mata kan maganan.
Tace amma ko halin malam baiyi ba wallahi don dai wanan karon in har da adalci bai kamata yai maki haka ba.
Abune dai na sunw iyayyen ki ban da iko akan ki da sun ga tsiya wanan karon.
Kuma ai ba karya kika fada ma tana da yara dakin ta in har yarinya yake son aure ta bashi daya.
Mama ko tana shiga gida sai zagin Jatau takeyi tana cewa kaga matsiyaci ko kudin share kasa wanan yana isa ne balle na wani aiki can a haka dai komai rowan ka sai naci abin ka ta wannan fannin.
Baba na dawo wa gida ina jinta tana mayar mai da yadda mukayi da Jatau da ita.
Daga can naji yana kirana babu tsoro ko kadan a raina na fito amsa mai kiran.
Nan ya hauni da fada inda yake shiga banan yake shiga ba yana fadin ba zai lamunci ina wa mama rashin mutunci ba a gidan shi in har nace ban auren Jatau to nafito da wanda nake so yai min aure don shi ba ai mai dogon zawarci a gidan shi.
Inna tana daki tana jin duk yadda muke kwasa da babana a tsakar gida na shigo daki ina kuka ina cewa ban san abinda naiwa baba da mata suka tsaneni ba haka ?
Inna tace bake suka tsana ba yarinya nice suka tsana a gidan nan har ya shafe ki an riga an dasa mashi kiyayyan mu a ran shi tuntuni.
Nace Inna irin wanan abinda baba yake min wani lokaci har tunane nakan yi nace anya kuwa shine mahaifina kuwa ?
Tayi shiru ranta a bace yana mata suya da takaici cikin bacin rai tace dani idan bashi bane uban ki waye yarinya ?
Tsaban rashin tsoron Allah da makoma ne dai ke damun su daga shi har ita din.
Karasa wacce zaka dinga kuntatawa sai yar cikin ka ko yaushe ita yaya nata haukan kishine ya rufe mata ido take haka akan mu.
Don kullun burinta shine taga bacin raina a gidan nan idan taga haka shine farin cikin ta a gidan nan.
Ki dai yi hakkuri ko yaya yake mahaifin ki ne daga su har mu bamu isa muja da ikon Allah ba idan kuma Allah ya kaddara shima wanan din mijin ki ne babu tsimi babu dabara sai kin aure shi.
Yanzu abinda nake so dake shine ki daina wanan rashin kunyan da kika dauko mata kici da yi mata biyayya a matsayin ta na uwa a gare ki don matar uban ki ce kullun ina fada maki haka.
Ina zaune ina jin duk nasihan da Inna ta take min naso na daure amma kuma kukan da nake dan newa ya tsanan ta min zuciyana ya kasa daurewa ita kanta Inna ganin yadda nake kuka gwanin ban tausayi bata san sanda kukan ya kwabce mata ba.
Can dau inna ta daure take ce min yarinya yanzu ba kuka ne abin yi ba gare mu dole ne musan mafita ga wanan zancen naki.
Muryan baba ne mukaji yana cewa duk abinda zakuyi sai dai kuyi dana ai nasan kece mai daure mata gindi tanayiwa mutane iya shige a gidan nan.
Inna tana jin haka tamike tafito daga dakin tana cewa ai dama nasan duk maganan yarinya idan ya taso akaina yake karewa a gidan nan don rashin adalcin da ba ai muna.
Idan bani da ita ba wa ake wa wanan ikon haka a gidan nan ya kyale sai dai mu da aka raina muna kuran mu kawai.
Baba ya dinga kallon Inna da mamaki yasan duk lokacin da ta va da ansa ga zance a gidan to abin yakai karo ke nan ba dadi.
Ido kawai ya tsura mata ya kasa tabuka komai a kan ta sai muryan mama ne daga bayan su take cewa ai har da daurin gindin ka da suke samu suke ganin kamar wuyan su ya isa yaka yanzu a gidan
In bashi har yau Rahama take da zatace wai ga zabinta bayan wanda kai mata don ta samu dauri daga uwarta ko ?
****** ********* ******
Da sassafe sai ga Larai kawar mama ta shigo gidan wurin mama lokacin Inna tana dama muna koko da zamu karya dashi don ina daki dun kule har lokacin bana jin dadin jikina.
Da dariyan ta suka gaisa da mama take cewa a, a lauratu kice min kuma yar ki ta kara maku babban kamu ne agidan kuma ?
Lalai kun iya jefa fatsa a ruwa ko yaushe sai manyan kifin garin kuke kamawa, yarinya ta zama ma uwarta jari a gari don ko shi wanan din kada ku bari ya sullube maku.
Don nasan yo Allah na tuba ai kaman wancan din za, ayi tunda shima sai a hankali kinga kun kara samun wani gadon kuma ku haye ai.
Da farko Inna taso tai banza da su da suka taba ita da mama sai kuma taga indan tai shiru ta kyale su sun sha da ita.
Don ko gobe dawowa zatayi ta kara gasa mata wani don taci riban na farko din da tazo tayi.
Inna ta dago kai inda suke ta dube su tana murmushi ace hakane fa kedai Larai.
Kuma kin sab jahili shike gagawan yanke hukunci amma shi mai ilimi kullun yana kyautata zaton sa gurin ubangijin sa ne domin shine mai azurta bawan sa a duk lokacin da yaso hakan.
Tunda fatsar mu ya iya kama babban kifi ko yaushe idan kamu banza ne wasu sukama koda karami ne mugani .
Don ita killa wanan karon kifin da zata kama ba irinsa a wanan ruwan sai na gaba zata kamo.
San nan ku sani shi sheri kare ne don mai shi yake bi hassada ga mai robo ko yaushe ai taki ne da ace ko wancan din ansan haka zai zama muna alheri da wasu sun kai nasu sunci.
Amma daya abin rabone daga Allah sai sheri ya juye muna alheri a rayuwan mu.
Sai gashi a filin Allah an dawo ana hassada akan mu kinga ko ai bamu ga kaico ga kamun manyan kifi don isa ne wani ko uwar ruwa yajefa fatsan shi ko kwai bazai kamo ba.
Take suka hasala matuka gaba dayan su don sun fahinci inda maganan Inna ya dosa gare su don kowa na da manyan yan mata a dakin shi.
Don idan baki yasan abin fadi baisan ansan da zai samo ba sai suke ji kamar Inna ta watsa masu ruwan zafi ne da safen nan.
Nan suka kama masifa da kumfan baki gareta sai ashar da mugun kalamai suke watsowa ita dai inna ta shige daki abinta tana dariya.
Bata san baba na gida ba sai muryan shi taji yana cewa haba haba Laira wanan ba girman ku bane kizo har gidan mutane kina masu shagube.
Idan ma an kaiki gurin maigari baki da gaskiya anan din babu ruwanki cikin zancen kishin su.
Nan suka juya kan baba da fadan suna fadin dama ai baka taba ganin laifin su kamar Asiya ce har zatai muna gori wai namu diyan ko samarin kirki basu dashi.
Dama ai nasan duk munafunci ne kokai baka kaunan wanan zancen akan ta sai in yai dadi ne kake fin kowa cinyewa.
Idan ma asirin su ne da suka iya yaka ma ka sai dai ya tsaya a kan ka don ni bazasu iya komai dani ba.
Yace maza Larai ta fice mai a gidan shi tunda ba alheri ne ke kawo ta ba gidan sai hadin hasumi a tsakanin iyalin shi.
Simi simi