Showing 15001 words to 18000 words out of 373688 words

Chapter 6 - A LOKACIN MUKE BOOK BY ZAINAB .I. MAKAWA.txt

gurin mama again take cewa wai maza nake tarawa a kofan gidan mu ana abinda bai dace ba.
Shima baba yai fadan shi har yagaji baida yadda zaiyi ya hanani talla ne da yahana ni yadda ya sha zugi gurin mama din.
Ina aji hudu akai min jumping a school din mu don kokarina don munyi debet na sa school din mu tayi nasara na samu wanan daukakan haka.
Nan ma mama tace ai inba ina tare da malaiman ba babu yadda za, ai min hakan ni kadai don banfi kowa a school din ba.
Nan ma baba ya hau ya zauna akan zance haka ya jawo mama tasawa karatun nawa kahon zuka sai da a ka dakatar dani daga karatun boko na ga baki daya hankalinta ya kwanta.
Tsayawa fadin irin bakin cikin da naji alokacin bata bakine gurin fada.
A makarantan mu sun samu labarin babana ya fitar dani daga makaranta haka yasa suka tausaya min sukazo har gida suka samay shi kan zancen.
Amma yace suyi hakkuri abar zancen da suka matsa mai yace a bari sai yayi shawara tukun.
Badakowa zaiyi shawara ba nasan da mamacd idon itace kuma babu yi ke nan na sani.
Daya tunkare ta da zancen cewa malam mu ne sukazo akan zancen dakatar dani daga kararu sai cewa mama tayi dama may na fada maka ?
Tare take dasu yanzu sunga basu samun ganin ta su kwakwaleta shine suka biyo sawun ta har gida.
Nan baba ya kara turjewa bazan koma karatu ba idan mana samu miji aure zai min kowa ya huta.
Jifa ga Lawisa ga Rukaiyya da Naja wai amma nice baba ke maganan aure na.
Ganin za, a cuta min a gida yasa shugaban makarantar kai karan babana a gidan maigari.
Kan zasu cutawa rayuwana kasancewa ta yarinya mai kwazo ga karatu ya kamata ace ko dai secondry din ne na gama ai.
Da kyat baba ya yarda koshi sai da maigari yai mai jan ido ya yarda don yasan idan yadawo gida akwai matsala tsakanin shi da mama idan taji zan karasa karatuna a shekaran nan.
Haka kuwa akayi don ranan ba karamin tashin hankali akayi ba tsakanin baba da mama.
Take cewa ai dama har dashi cikin cin kudin da mazan dake lalata dani suke bani.
Idan bashi ba don may zaice sai na karasa karatuna may ye amfanin karatun diya mace na boko da za, a kare shi a gidan miji.
Tana kurin tana karatun boko watafi kyau da za, a nace kan sai nayi boko nakai wasu can daban
Ni dai tunda naji baba yace na shirya gobe na koma makaranta nake cikin farin ciki da zumudi don ina gani kila ina da rabo ne a duniya.
Washe gari tun da safe na bar gidan duk da na saba idan zan tafi sai na sallami kowa na gidan kafin na fita.
Yau ma dana shirya munyi sallama da inna na nufi kofan mama tun ban karaso ba tana hangoni take cewa za, a yawon tazubar din ko akuyan daure ta samu saki.
Duniya ce dai ayi ta a sannu don maza ba abin goyo bane da sun gama yayin ka su ka hango wata kai kuma ka tashi aiki ke nan.
Ni dai ban biye taba nace mama ni na tafi kafin ma naji amsan da zata bani har na fice daga gidan ko.
A kofa na hadu da babana da zai shigo gida na dan rabe gefe nai mashi ina kwana yabini da harara yana cewa har zaki tafi ke nan ?
Nace eh baba yace Rahama ki kula da rayuwan ki kada ki ja min abin kunya a garin nan.
Duk dai har yau babu wanda ya taba kawo min karan ki na assha amma dai kuma maganan maman ku abin dubawa ne.
Don diya mace ba, a saka mata ido tayi yadda take so dole sai da tsawatawa akai.
Nace nagode baba insha Allahu zan fake na tafi ina tunanen halin baba idan mama bata kusa zakaji ya dan sanyaya ma al, amarin mu .
Amma da zaran yaga idon mama damu da makiyan shi duk daya muke gare shi kamar zai yanka mu da ran mu.
Bani ba har yan kanne na biyu hakan ya shafa don dai kawai su maza ne basu zama gida su.
Ina isa makaran ta ban tsaya ba sai office din malam Mudi don nasan shine kadai zai iya min wanan kokarin.
Na samay shi yana shirin fita na duka nagaida shi cikin ladabi nake cewa kuma malam nazo ne nai ma godiya don nasan kaine da wanan kokarin.
Yace hakane Rahama don haka kema ki kula da rayuwan ki don ban san dalilin yin hakan ba ga mahaifinki.
Ko da yake mun samu labarin cewa takurawan kishiyar mahaifiyan ki ne akan ku ya shafe ki.
Ki kula ki mayar da hankalin ki wata rana sai labari idan kin dage Allah zai kawo maki mafita da yardan ubangiji.
Nai mashi godiya tare da sallama na koma class sai sheri yan uwana dalibai suke min wai ta fudu ta dawo.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, ,


IDAN KIN BIYA KI KA BAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YAR UWA, , , ,


A haka na juya zuwa cikin gida jiki a sabule min ina dauke da ledan da suka bani a hannu na.
Har lokacin Inna suna gurin zaune da babana nazo na wuce su zuwa cikin dakin mu.
Tafe nake ina tunane a zuciyata sam bana cikin natsuwa ko kadan a lokacin zuciya bata kwanta ba da wanan hadin da ake son yi min.
Sam garbati bai min ba gashi dai dattijo a gurina na ni yar sha biyar tsoho kutuf nake ganin shi,
Koma da ace lokacin kuruciyar shi yake nidai bai mun ba don bakine wulluk kakaura dashi sai dai ba can kwarai ba.
Ga fuskan shi duk ya bar gemu a ciki baje baje wai shi sunnan kauye babu dai wani abin armashi a cikin sa ko kadan.
Sai dai ban da wani zabi ga gakan tunda ba zan iya bijirewa hukuncin mahaifina ba akaina.
Duk da har lokacin ba wai ma na fahinci may ye zaman aure ba tunda a gidan mu ba wani zaman auren dadi naga anayi ba ma balle na koya.
Nasan irin rayuwan da inna ta tayi na zaman bakin cikin rayuwa ni ma dai din shi zan je naitayi gidan nawa auren ke nan.
Ban da wani zabi a hakan don ban isa na bijirewa zabin mahaifina ba haka zan ta kokarin tursawa zuciya na kaunan shi koda kuwa zuciyan nawa na barazanan kamuwa sa ciwo ne.
Ganin yanayin da na dawo gidan yasa bayan na dan shiga da yan mintoci Inna ta mike daga inda take zaune ta biyo ni dakin mu.
Nan ta samay ni nayi zaune nayi tagumi ga ledan da nashigo dashi na tasa a gabana.
Tocilan hannun ta ta haska ledan da shi sabulai ne sai clean manya biyu sai turare fesawa na passition da turmi zani guda biyu sai kudi wai kudin dinki dubu uku.
Baki Inna ta ta rike tana cewa kai anya Alhaji garbati bai dauko hanyan riya ba ga alamarin nan kuwa ?
Yanzu ace duk yawan iyalinshi zai iya binsu da makamancin kayan nan haka ne ?
Gaskiya ni ban son abinda tun ba, aje ko ina ba zai shafa maki bakin jini akai .
Duk wani abinda zaiyi a gidan nan tamfar a kunnen iyalin shi ne don dai yaya tana hurda da sabuwa da can baya.
Daukan ledan tayi wai zata kai wa babana da mama dake waje da sauri na tura hannu ciki na kwashe kudin don nasan idan ankaisu mamace zata kwashe su da wani dadin bakin ta.
Inna dai bata ce min komai ba ta juya ta fice daga dakin ina jin su baba yana cewa kai kaya haka kamar za, a kai lefe ?
Mama sai faman binciken ledan take da sauri nasan kudi ne take nema a ciki gashi ta wani tsuke fuskan ta tamau da ganin kayan.
Can taja tsuki tare da tura kayan a gaban babana tana fadin kaiyya sai dai tsiyan abin duk wanan gatan tsoho ne.
Da yaro ne shine za ai farin ciki da nuna rawan kai amma tsoho ga karamin yaro may za, a gane ciki haka.
A, a lauratu inji babana kon san da haka kikace nai maki alfarma na bada ita gare shi tunda da dan uwanki akazo neman ta ?
Idan kin san haka ne may yasa kika sakani gaba saida na furta na bada ita yanzu zaki zo min da wanan sabon zance kuma ?
A, a ni yanzu may nace kuma ai gaskiya na fada yanzu ba ga abin arziki ya fara sauka maka ba har kuna murna.
Cikin mamaki yace murna kuma kamar yaya lauratu akan wanan kayan ne zanyi murna da rayuwan da yata zata shiga ?
Nifa don ki na yarda naba Rahama ga wanan mutumin may naci nasa da zanji nauyi shi a baya ?
Ashe ke nan ke da wata manufa kika sa na bada Rahama gare shi ke nan ?
Manufar may kuma malam banda abin arzikin da na hada ni idan bashi din ba akwai wanda ka taba jin yazo ya sallama akanta ne a gidan nan bayan duk ta gama zubar da mutuncinta ga samarin gari.
Daga inda nake ina sauraren su na hade wasu yawun bakinciki a raina tare da hawayen da yazubo min.
Koma may zan tarar a gidan gara na tafi na huta da kullin sherin mama da yaranta hakana nida inna ta akaina.
Jin hayaniyar tasu zai yi karfi ne yasa na fito waje inda suke don mama ba komai bane hassada ta nuna min karara .
Tayi min hakane don ta jefa rayuwana dana mahaifiyata a kunci ne kawai.
Basuyi aune ba sai ganina sukayi a waje durkushe a gaban su ina cewa baba don Allah kabar wanan magana haka.
Indon nice na yarda da kaddaran da Allah ya kawo min na auren garbati bazan bari kayi kunya ba a kaina insha Allahu.
Tausayi na bashi yai shiru tare da yi min wani irin kallo na ban tausayi yagane manufata bazan bari yai magana biyu ba yace eh yadawo yace kuma a, a daga baya.
Yace shike nan Rahama Ubangiji ya tsare mun ke a duk halin da zaki riski kan ki a gidan shi nace amin baba na share kwallan da suka zubo min na mike na koma dakin mu.
Ina jin mama bayan sun gama hayaniya ta juya dakin ta bata dade ba ta rufo kofan ta hakan ya nuna ranan bazata yarda na kwana a dakin ta ba ke nan.
Inajin Innata bata shigo daki ba da taga haka dakin da suke aje shirgin su har bunun dakin ya zabbace ta gefe daya don wahala ta dan gyara min gefe daya tace na kwana a can ko naje gidan mai kuli na kwana.
Nace dare yayi Inna bari kawai na koma can na kwanta yanzu mama ta rufe gidan ta nasani.
Baba tana ganin haka ya nufi dakin mama ya na bugawa tace daga ciki wai lafiya kake dukan min kofa haka kuma may kuma zan maka ?
Yace ki bude Rahama ta shigo ta kwanta tace ai kaba uwar ta daki ka bani don haka ku kwanta tare da ita mana tunda ta zama yar gwal matar Alhaji yanzu.
Dole ya juya ya barta zuciyar shi na tir da Allah waddai da halin mace ba haguwa irin ta.
Sai ta kaika ta baro kuma ta tsira ma sabon fitina dama wanda ya kaucewa Allah dole ya fuskanci kalubali irin haka a rayuwan shi.
Hakana na kwana dakin ga sauro ga beraye suna ta hawa min jikina ba dadi ko kadan dakin don yawan shirgin kayan aikin su dake cikin dakin.
Kwana biyun girkin Inna haka tayi shi a cikin kunci a gidan rai a bace mata duk nabi na damu ga bacin ran da mahaifiya ta take ciki ga zancen auren da ake son yi min na dole.
Haka nake zaune a takure ga mama ta saka mu gaba da gori ita da diyan ta duk mun kasa sukuni a tare da mu.
Na dai yanke shawara zuwa yamma na shiga gurin mama altine ko zan dan sarara a tare da ni.
Nan samu mama tana dan aikace aikacen marance na shigo da sallama na na karbi tsintsiyan da take shara a hannun ta na karasa mata sharan.
Na dawo gurin da take zaune tana gyara geron da zatayi birbisco dashi na abincin dare na karba ina gyara mata.
Kallon yanayi na tayi abinka da babban mace ta fahinci babu dadin rai a tare da ni lokacin.
Take cewa lafiya kuwa yar gidan anty na gan ki yau wata iri dake haka ?
Maimakon nayi magana sai hawaye ne suka biyo baya tace subbahanallahi may ke faruwa ne Rahama ?
Sai da nayi kuka mai isata nake cewa mama baki ji kaddaran daya fada akaina bane halan innata bata samu shigowa ta fada maki komai ba ?
Tace Asiya ta kwana biyu bata shigo gidan nan ba gaskiya may ya faru.
Ina kuka nw nake labarta mata komai da ya faru a gidan mu akaina cikin kuka tace waye shi wanda aka baki din ne ?
Nace Garbati cikin rike kirjin ta tace wani garbatin ba dai Alhaji garbatin dan bida ba dana sani ?
Nace a sanyaye shi mama.
Tace subbahanallahi yanzu shi mahaifinki da ranshi da lafiyan shi zau dauki ya kamar ki ya mika wanan gidan na sa, an nin kakan nin ki ko may ?
Nan ta haufada tana cewa idan Salihu bai yi hankali ba sai Lauratu ta kona shi tun a cikin duniyan nan wallahi ko.
Fada sosai mama tayi tare da kara kwantar min da hankali take cewa zan tafi gurin anty ki ance min ita ma bata jin dadi ga abokan zaman ta ba kirki ne dasu ba.
Kin san kishin yan birni ba irin namu ne ba na kauye kishi suke suna hadawa da yahudanci aciki.
Rayuwan ne na kowa tasa ta fishe shi akeyi wai suna ganin su wayewa ne a gare su.
Inbashi ba dan uwan ka baida lafiya ina zaka kawar da kai gareshi haka kana tsabagan gaban ka.
Nace mama Anty na bata da lafiya ne ?.
Tace ina fa taga lafiya tunda tazo din nan take fada min wai bata da lafiya ajikin ta har zasu tafi kasan waje da maigidan a dubata.
Allah yaba anty na lafiya nace tace amin Rahama ita nake gani ta tuna min da mahaifiyar ta don dan uwan ta shi namijine baidamu damu ba kamar yadda ita take kula mu.
Na sake cewa mama dama anty tana da abokan zama ne tace tana dasu mana har biyu ma.
Ai anyi aurenta ba a kokai shekara ba uwar mijin tasa ya auro yar uwarta shima mahaifin shi wai akwai yar abokin shi da yake son hada shi dashi tun farko shima yasa ya auri yarinyar.
Zoki ga irin yadda suka saka min yarinya a gaba da fitina suna ganin itace bare a cikin su sai abinda suka ga dama suke mata a gidan .
Allah dai yasa shi mijin yana son abin shi haka yasa basu samu yadda suke so ba akanta.
Yanzu ga ciwo yazo ya sakata agaba haka wama yasani ko ije ne aikai mata ya hanata jin dafin rayuwan ta.
Nace mama ije kuma may nene ije ?
Tace baka ji maganan ba keda zaki shiga kishi cikin tsofon mata Rahama baki san ije ba kuma sai may.
Nan tashiga yi min irin kissan ije da dalilin da ke sa aiwa mutum asiri idan anga hankalin miji nagareshi da yaran shi.
Nan nai mutuwan zaune nace na shiga uku mama koma don ai min ne yasa mama ta tura baba ya kaini wanan gidan akashe ni kowa ya huta dani kamar yadda take fadi.
Har na dawo gida duk yadda mama taso ta fahintar dani hakan bai samu ba daga gare don na kasa fahintar dongon sharfin da take min akan ije wai shirin kishiya .
Ko da na dawo gida na samu ranan har baba ya dawo daga kasuwa ko suna zaune da mama yake tambayana daga ina nace na shiga gurin mama altine ne na taya ta aiki .
Bai yi magana ba sai bina da yayi da harara har na shige dakin mu ban dade da shiga ba Inna ta kamala abinda takeyi sai ji kawai nayi ta rufo kofan dakin ta garam.
Nace ashe yau akwai tsiya a gidan nan ke nan don Inna zata rama abinda akai min ne kwana biyu na barina na kwana dakin shirgi ni kadai sai bera ye.
Lawisa ce tashigo gidan daga gurin hira ta fara zuwa dakin mu don ta kwanta taji shi a kargamay.
Ina jin ta lokacin data juya zuwa inda iyayyenta suke tana fadin wai Asiya ta rufe kofan ta don haka suke kiran Inna da sunan ta gazatsau ba sayawa.
Mama tace kamar yaya ta rufe kofan ta a ina take son ku kwana yau din ?
Nace a raina jifa mama da son kai ta manta abinda tai min ni .
Ban dai ji baba ya tanka masu ba har lokacin tasowa mama tayi ta shiga dukan kofan mu da karfi amma ko motsi Inna batayi ba ga wani katon dutse da tasa ta kare kofan dashi.
Ranan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login