Showing 54001 words to 57000 words out of 373688 words

Chapter 19 - A LOKACIN MUKE BOOK BY ZAINAB .I. MAKAWA.txt

matukar tashi sosai don idan akwai abinda dan kauye yaki jini shine kiran maigari.
Yashigo gida hankali a tashe yana fadin zashi gurin mai gari yanzu yaron mai unguwa yazo yace ana neman shi gidan mai gari shida mai unguwa.
Mama hankali tashe take cewa to may kuma ya faru ko anyi wani abin ne kuma.
Bai tsaya bata lokaci ba yafita gurin amsa kiran inda mai uguwan mu yai mashi jagora har gidan.
Bayan an gaisawa ne maigari ya gabatar mai da zancen karan shi da aka kawo kan yana son yiwa yar shi kuma bazawara auren dole da Jatau.
Sai da wani uban zufa ya karyowa baba yana gyara zaman shi cikin kwantar da murya yake cewa.
Rankaidade ba haka na bane ba wai auren dole nake son yi mata ba ita da uwarta ne dai basu fahince ni ba.
Take dattawan fada suka katse shi da cewa shin yarinya ta yarda ko bata amince ba akan auren.
Sai baba ya dukar da kan shi kasa yace a gaskiya ba ra, ayinta bane nawane dana iyayyen ta hakan.
Iyayyen ta uwar da ta haife ta ko wa kokai da yan uwan ka ke da wanan danyen hukuncin akan ta haka ?
Shiru baba yayi don ba amsa sai lokacin maigari ya karba dacewa ko wancen auren na farko dakai mata mun so mu hukunta ku amma sai muka duba shi garbati mutumin kirki ne zai iya rike maka ita amana.
Amma Jatau ko mutumin banza mutumin da bai san darajan kowa ba a garin nan sai kansa.
Babu wanan zancen yarinua dai bazawara ce abarta ta yi zabinta da kan ta dan doka yanuna yanzu ko budurwa ce idan bata son aure kada ai mata dole balle bazawara da tasan ciwon kan ta ko.
Fada sosai akai wa baba ya baro fada sai dai maigari ya boye mai cewa Inna ne da kan ta ta kawo karan shi yadai ce makwabtane suka zo suka fada mai wanan labarin .
Shiko a matsayin shi na maigari yana da ikon karewa yaro da babba hakin su idan za, a cuta masu.
Wanki nake yi kafin na shiga gidan mama Altine ina dan rarage kayan daudan mu ni da kanne na da Inna baba yadawo.
Kana ganin shi kasan babu lafiya tare dashi lokacin Inna ko har ta shirya tana jiran cin mutuncin da baba zai dawo mata dashi daga gidan mai gari.
Yana shigowa mama najin sallaman shi tai but tafito daga daki tana fadin malam lafiya dai ko wanan kira haka tunda sassafe haka ?
Yace lokacin da yake zama saman dutsen dake tsakar ana alwala a saman shi bari ke dai Lauratu munafunci baiyi ba wallahi.
Wai yanzu aka samu munafuki a cikin uguwan nan yakai karana kan auren yarinyar nan da Jatau gurin maigari.
Gaban mama yai mugun faduwa tace kara malam wake da wanan aikin haka yace wayasani yadai ce daga uguwar nan namu ne akai karana gurin shi.
Affan malam wa zaiyi karan ta inba ita da uwarta ba kaiwa kake tsamanin zaiyi haka waya damu da damuwan su anan balle ya kula al, amarin su.
Umm, umm lauratu daga nan ne dai aka fadawa maigari amma ai mace bata ganin mai gari kai tsaye wane ita nan.
Nan suka shiga dura ashar har mama na ikirarin ai ba maigari ne ya haifa mashi ya ba da zai mai iko akan gidan shi.
Baba yace Lauratu na rabaki da wanan zancen kada ki dauko min wani sabon rigima kuma don ni yanzu tsoron mutane nake ji su labe ta baya suna sauran ki.
Mama tace duk mai fadi yaje ya fadi amma aure ba fashi sai anyi shi tunda bashine ya haifa muna diya ba ba kuma cin shi a gidan mu.
Baba ya katse ta da cewa kina da kudin biyan taran da za ai min ke nan ko da kuma dauri kan na shiga hakkin diyata bada son ran ta ba.
Cikin mama ya duri ruwa sai da ta kewaya ban daki tafito ta samu baba a gurin yana fada har lokacin.
Nidai ina wanki na tare da hamdalla a cikin rai na don maigari da mama Altine sun ceci rayuwana ko ba komai sun kwato ni da shiga bani.
Inda nake ina buga zanin da zan shaya mama ta kalla tare da cewa tir dake Rahama kinyi hasara wallahi tunda akan yi yau akai karan mahaifin ki har gurin mai gari sukutum.
In yar arziki kike kin haihu cikun malam yau kije kice wa maigari da miyau bakikin ki za ai wanan auren.
Ban kula ta ba illa idon da suka sako min daga ita har baba din a lokaci daya.
Ganin bazan taka masu ba ne baba yace ai in taki wanan auren nikan ba dai gida na ba wallahi don ba zan zauna da ita ba haka ina ganin bakin ciki a raina.
Fat naji muryan Inna a bayan mu tana fadin a hayye nanaye wanan hukuncin yau yafi nono fari a gare mu don na dade ina jiran anan ranan dama.
Idan baka zauna da ita ba a gida don tana bazawara ai zaka zauna da gandan gadan din yan mata suna maka manne da dare a bayan katanga da samari.
Aure dai ne Allah ya kawo muna saukin shi cikin dadin rai Allah kuma yaiwa wanda yakai kara albarka.
Ikon Allah zamani yanzu Asiya bakiji kunyan wanan maganan ba a duniya ana jinki kina guda akan yar farinki don baki da kunya ga idon ki.
Kunya kunya fa kace malam ai kunya ya kaura ba yau ba ga idon Asiya don ka sani don baku so haka ba.
Gida kuma in kace yarinya bata zama maka gida sai dai dani da ita mubar maka gidan ka a tare don ni ban san zaman da zanyi ba kuma ?
Lalai Asiya kin haihu cikin fulani yau kin sheda min kun bar rugga da dadewa tun da idon ki ya kyakyashe haka kan yar farin ki.
Mu zuba dake a gidan duk inda zaku tafi ku tafi badai gidan Audi ba wallahi ba mai min gori kan abinda na fi karfi yazo yafi karfina a gida na.
Inna tace haka yafi nono fari wallahi yanzu kuwa ba sai anjima ba zamu bar maka gidan ka sai ka zauna da wa yanda kake so kajika kasha.
Magana har takai ga makwabta sun shigo gidan namu suna tambayan ba, asi nan baba ya shiga zagin mu dasu yana cewa wai duk munafukaine mu dasu afice a bar mashi gidan shi.
Hijjab dina na jawo daya bushe na saka nafice daga gidan inajin mama nace indai baki auren Jatau daga wanan fitan kin fice daga cikin mu ke nan.
Nasa kai abina na fice ko waigen ta ban tsaya yi ba sai gidan mama Altine ina shiga take cewa dani Allah mun godema da ya kawo muna saukin al, amarin nan.
Ni yanzu damuwa na shine wanan rantsuwan da mahaifanki ke yi sai kinbar maigidan shi ita kuma Inna ki ta rantse kina barin gidan itama ta bari ke nan.
Nace mama nima shine ke damuna wallahi don bazan so ace saboda ni Inna ta bar dakin auren ta ba akaina.
Zafin raine ke damun su dukan su daga ita har malam Audi din suna cikin bacin rai ne.
Muna nan muna magana sai jin hayaniya mukayi ya kaure a kofan gidan mu da sauri mama ta yafa tafita daga gidan.
Jatau ne yazo ya zauna yana cin mutunci wai kamar shi za, a tozarta a gari ai karan shi don yace yana son .
Indai har ban son shi nafito na bashi kayan shi da naci don shi bai gaji hasara ba akan shi.
But nafito daga gidan mama nace dashi dakata malam ga mutane sun taru wasu har a zanan gida matan aure ke lekowa ta kafan zanan gidan su don gulma.
Nace tsakani na dakai ko uwa ta ka taba ba mu ko kwandalan ka a hannun mu idan dai ka taba ka fada min yanzu na biya ka abinka.
Sai yadan washe baki yace ni da zaki yarda ki amince ai da babu zancen biya a tsakanin mu.
Amma ace ba a bani mata kuma a ci min dukiya na ga banza shine ba zan lamunta ba gaskiya.
Nace to kayi da wanda kaba kudin ka don ni ban san ka raba bani komai ba, muryan mama Lauratu naji daga ta cikin gida tana cewa tau mara kunya idan ke baki ci ba ai mu iyayyen ki munci don nai amfani dashi gida kowa yaci.
Nace kin dai ci ni tundana dawo kin taba girka abincin ki kika bani a gidan nan ko kiba kanne na sai naji tayi shiru nan mutane suka saka salati yan gulma suka hau bakin su.
Aka shiga zuga shi na shige cikun gida abina na barshi nan yana haukan shi shida yan kallin shi.
Nasa kafa zan karasa ciki naji muryan mahaifina cikin kakausar murya yace dakata nan Rahama badai gidana ba wallahi nai maki itaka da gida na daga yau duk inda zaki kije nayafe ki.
Inna dake daki tagama hada kayan ta naga tana fitowa da buhuhuwan data dura kayan ta a ciki.
Nan na duka nafara rusa wani sabin kuka zuciyata tana raya min nace kawai na amince da wanan sabon kaddararen auren akaina kada uwa ra ta shiga wani hali saboda ni.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,


IDAN KIN BIYA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYA BA KI TUNA DA AMANA NE HAKAN A TSAKANIN MU , , , ,


Ina duke a gurin naji an dafa ni mama altine ce a bayana take fadin taso daina kuka haka zo mu shiga gida wanan tonon asirin haka da may yai kamane wai ?
Ban kiba namike na bita sai ga yara na shigo da kayan inna ta gidan buhu har uku duk na komatsen ta ta hada ciki.
Ba a jima ba tashigo gidan ran ta abace sai dai kana ganin idon ta kasan ranan ba sauki sai na Allah.
Nan mama ta shiga bata hakkuri akan ta zauna amma tace indai ba zai barni gidan shi itama may zata zauna yi a gidan.
Dama don ni da kanne take zama badon wani abuba don haka bazata koma ba sai idan nima ya mayar dani gidan.
Nan dai abu ya yamutse daddatawan unguwa duk sun taru suna ba baba na baki amma ya kyakyshe kasa yace bai san zancen ba tunda mama da tai jagoran ci muke son tozartawa.
Magana zabban kunya yadda baba ke magana kai daji kasan an fi katfin shi.
Shi dai jatau anbashi hakkuri akan cewa ya bari a sulhunta maganan nan da sati daya za, a nemay shi insha Allahu.
Sai dare Inna ta nufi gidan su can taiwa mutanen gidan su bayani suka ce ta zauna suma halin gidan ya ishe su haka na.
Magana har gurin maigari ya koma kan fitinan gidan mu aka kira babana aka bikon Innata amma yace shi ba zai tafi ba kuma zancen Rahama ya yafe ta cikin zurian shi.
Ba, a watse gurin ba sai ga Jatau yazo kan zancen kudin shi yace yai lissafi har sadakin shi dubu sittin yaba mama din.
Akace wa babana to kai kaji abinda ya fadi sai da baba ya share zufan dake karyo mashi yake cewa baida wanan labarin .
Amma abari yaje gida ya tambayi mai dakin shi yadda akayi haka don shi dai bai san komai ba akai.
Sadaki kawai ta nuna mai kuma suna hannun ta tace zataiwa yarinya sayaya da su ne ya bar mata a gurin ta .
Nan yabar fada maimakon suji haushin shi sai tausaya mashi sukayi don sun san baida tacewa a gidan shi don mama tafi karfin shi.
In bashi sadaki da maza ke karba ina mace ina karba sadaki hannun mijin yarta.
Washe gari da aka sake tuntuban shi kan zancen Inna sai cewa yayi suje ya sauwaka mata .
Wanan labarin yai matukar tayar muna da hankali sosai dayazo muna kowa na ma baba kaico da rabuwa da Inna dayi.
Don yayi hasaran macen rufin asirin shi a duniya gashi tana haifa mai diya kyawawa masu tarbiya yace ta tafi da kanne na maza biyu duk ya yafe mata don mama tace bata rika su.
Sabon tashin hankali na shirya ni da mama sai gidan su Inna ta a yadda nai tsanmanin na samay ta cikin damuwa sai naga sabanin haka don dan kwana biyun da tayi har ta dan murmure sosai abinta.
Nan hankalina ya dan kwanta muka ba juna magana take ce min indai naga zaman bai min gurin mama na dawo nan na zauna tare da ita a gidan su.
Nace inna banda matsala gurin mama ko kadan tabkar a furin ki nake zaune a gidan ta don haka zan zauna gurin ta kusa da babana watakila idan yana gani na ya sauko ga fushin shi a samu ku shirya dashi.
Tace Allah sarki yarinya idan har kina hasashen komawa na wanan gidan to kina kaunan mutuwa na ke nan.
May zai mayar dani gidan Audi kuma indai ba wani ikon Allah ba kuma ai na bar gidan shi har abada insha Allahu.
Banji dadin hukuncin Inna ba nashiga damuwa take cewa dani na kwantar da hankalina gurin mama in Allah yakawo min manemin da hankalina ya kwanta dashi a daura min aure na nima na huta.
Cabdijam ni zawarci uwata zawarci dawani ido mutanen gari zasu kalle ni dashi ace auren uwata ya mutu akaina ko may.
Cikin tashin hankalin da na wuni ke nan a gidan su innata ina lalashinta ko zata sauko in baba ya huce ya aiko bikon ta ta koma dakin ta amma fir inna tace badai ita ba kan.
Haka na dawo gida da dare gidan mama ban gane komai ba a gurin Inna sai hakkuri da kwantar min da hankali da tayi.
Ina shigowa gida na samu mama tana waya ga alwal mai wayan sadawa tsaye kofan gida uana jiran tagama abashi kudin shi ya tafi.
Ko ban tambaya ba nasan da yarta take waya a lokacin don yadda naji suna magana na fahinci hakan.
Don naji tana cewa yanzu haka ma rikicin auren ta ake a gari don uban ta ya kara jajibo mata wani tsohon wai ta aura har kai tashin hankalin daya sauwaka wa uwarta tabar gidan nasu.
Banji may tace ba sai cewa tayi abani waya naji mama tana ce min karbi wayan anty ki ce daga birni ke magana dake.
Nakarba muka gaisa da inta take ce min ashe abinda ya faru ke nan Ramana ?
Sai na sa kuka take cewa nayi shiru na saurareta zata dawo wani sati in Allah ya yarda da tadawo zata turo a dauki mama sai mu taho tare da mama na huta da kauyen nan idan ba a ganni ba aibabu mai saka ido a kaina kuma.
Nan dai tai ta bani magana har na gamsu da maganan ta mukai sallama muka awal wayan shi da kudin shi yatafi yana godiya.
Mama tace min kin dawo a lalace na amsa mata tare da neman guri na zauna ina cewa ehmama.
Tace ga abincin ki can dauko kici nace da ita mama na koshi kunu kawai nake son na dan sha na kwanta.
Ina cire kayan jikina ne naji mama nace kinji abinda yar uwar ki ta fada ko akan ki.
Nace naji mama amma ai al, amarin babane da wuya don nasan mama bazata bari ba idan taji tace nima hasashen da na keyi ke nan Allah dai ya haushe mu kan ta.
Mun bar zancen don ko inna ta ban fadawa maganan ba kada hankalin ta ya tashi sai in abin ya tabbata zataji.


****** ********* ******
Bai fadawa kowa dawowan su kasar ba bayan sun gama ganin likita haka ita ma yace bai son ta bugawa kowa waya zasu dawo.
Taja bakin ta tai shiru bata fada ga ranan da zasu dawo ba gidan har suka shigo b Nageria ba wanda yasan da zuwan su.
Karfe goma sha biyun rana suka sauka gida kano ya daukan masu shatan taxi din airport sai gida.
Alama ya nuna matan gidan basu gida a lokacin duk da weekend ne ranan hutu don motocin su baya gida.
A can kan hawa step din gidan ne ya hango Nasir a zaune yayi tagumi sai Amira dake tsaye bayan dan uwan nata tana wasa tsaletsalle akan steps.
Tun hango yaran ya sauke ajiyan zuciya yaran basu damu da tsayawan mota ba a haraban gidan nasu sai harkan gaban su sukeyi kawai.
Muryan mahaifiyar su ne sukaji tace Sweethearts da sauri yaran suka yo kan su cikin murna da jin dadi nan ta durkusa tare da rungumay su zuwa jikin ta sai kuma ta sake kuka.
Ya gama sallaman mai taxes yazo inda suke shima suka rungumay shi cikin murna yake tambayan su ina anty ta tafi yaran sukace tun safe bata tare da mu sunfita da yasmin a mota.
Ciki suka shige da kayan su wanka ta fara yiwa yaran tare da canza masu kayan jikin su tabasu abinci sukaci don sunce yunwa suke ji a lokacin.
Har tagama abinda takeyi bata ga shigowan shi ba gurin su haka yasa ta tsamani ko ya kwanta ne a lokacin don


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login