Showing 66001 words to 69000 words out of 373688 words
Chapter 23 - A LOKACIN MUKE BOOK BY ZAINAB .I. MAKAWA.txt
barci na, zan samu komai is ready yarinya karama bata jin nauyin jikin ta ko kadan.
Yace kai amma wanan yarinyar ta kyauta min wallahi ki min godiya gurin ta tunda ta kula min da bugun zuciya na.
Dago kai tayi inda nake duke ina zuba mata ruwan miyan a plate tace Ramana kinji ana maki godiyan kula dani ko ?
Murmushi kawai nai mata na fara kokarin zubawa mama nata na mika mata, lokacin kamshi ya tayar da mama dake zaune tana gyangyadi a saman kushin.
Yaran da yake weekend ne na sauko dasu cikin hikima nazuba masu suka zauna ci don abinci bai damuwan su sai dai kayan kwadai kawai shine abincin su.
Ganin Nasir yaki saukowa yasa na diban mai nashi zanje nakai mai murya anty ne dake shan ruwan miya da cibi take tambayana da cewa wanan na waye ?
Cak na ja guri daya na tsaya tare da juyowa gare ta da hannuna dake dauke da kayan plate dana shirya.
Nace anty na Nasir ne yana kwance bai taso ba shine zan kai mai nasa a dakin su.
Tace cikin tabe baki Allah yasa ya karba waban yaron halinsa sai shi wallahi ya faye yawan bakin rai zakace bani na haife shi ba.
Ni dai juyawa kawai nayi zuwa dakin koda na shiga dakin yana kwance rub da ciki da littafi a gaban shi yana rubutu a ciki.
Abincin na aje na dawo gefen shi ta gaban shi na zauna na dan shafo kan shi nace Nasir tashi kaci abinci kaji rana yayi.
Ban ci yace batare da ya dago kai ba nace haba Nasir ka tashi ko kadan ne kaci kaji kada mummy tai muna dariya dama tace min bazaka ci ba nace idan na baka zaka ci don ni abokiyar ka ne.
Dago kai yayi ya kalleni sai ya duka yaci gaba da abinda yake a littafin, nace ni kasan duk cikin ku nafison ka don halinka na da kyau nasir baruwan ka da rigima.
Kaga ko dole na soka na kuma damu dakai gaka yaro mai kirki da kai ko anty ma ta fada min kana da kirki sosai shiyasa take son ka ita da daddy.
Sai ya sake dago kai ya kalle ni nace cikin daga kai hakane yace ba ai kazanta ba ga abincin ?
Banyi magana ba sai bude mai plate din nayi kaman mai tunane sai naga ya mike zaune tare da jawo plate din a gaban shi ya dan diba kadan yakai a bakin shi sai ya fara danci a hankali amma hankalin shi na wurin littafin shi.
Ruwan da nazo dashi na tsiyaya mai na mika mai ya karba ya dan yasha.
Ina zaune tare dashi ban daga ba har sai da ya turo min plate din a gabana a raina nace kai lalai maganan Anty ne wanan yaron akwai miskilanci gare shi.
Na mike tare da kwashe kayan nace dashi na gode Nasir ya bini da kallo har na fice.
Ina fitowa da kayan zan kai kitchen ta bini da kallon tace ai na fada maki ba zaici ba daga inda nake tsaye nake cewa da ita yaci.
Na shige da kayan sai dana wanke su komai da aka bata ina yi ina tuna kalamin Nasir watau kazan ta na cikin abinda bai so ke nan yaro dan kimanin shekara shidda wai yasan kazan ta haka.
Sai da na gyara komai na fito daga kitchen din na nufi daki direct gurin kayan Nasir na nufa na gyara mai komai nashi tsab yanayi yana kallo na.
Na fahinci rashin hayaniya hhalin yaron ne haka hallita ne mai haka Allah yayi shi amma ko ma maye a sannu zan gane komai nasa.
Abincin dare na girka nagama da wuri na sa a kula ganin yaran na waje suna lesson yasa nace da Anty nima ina son zuwa na saurara.
Anty tace kaman kin shiga raina dama ina son magana da lesson teacher din akan ki don nasan karatun kauye ba wani waya ta dauka kafin na fita tai mashi bayani a kaina.
Cikin sati daya na fara fahinta da yake na dan san wasu abubuwa dama don haka ban sha wani wuya ba gurin fahintan karatun.
Gashi dan zamana dasu na fahinci halin ko wani yaro ina kuma jan su a jiki sun sake dani sosai.
Wanda hakan na fahinci yana matukar yiwa anty dadi a ranta niko a guri na naga ba komai ba ne hakan don tafi haka a gurina ni.
Banda abin su na masu hali ni banga wani aiki da take yawan cewa yai min yawa ba amma gashi ita ko wani lokaci sai gode min takeyi.
Sosai yaran suke sake jiki dani gashi har Nasir na dan fahinci halayen shi haka yasa yauma tun dawowan su na fahinci yaron bai jin dadin jikin shi amma ya kasa fadawa kowa sai kwanci yake yana mika.
Mun dawo lesson nake cewa dashi Nasir bari na hada ma ruwa mai zafi ka gasa jikin ka dashi bai ce dani uffan ba har na hada ni da kaina nai mashi wanka na gasa shi da ruwa mai zafi na shirya shi har da robb na shafa mai na rufe shi da bargo.
Na fahinci yaji dadin yadda nai mashi don naji ya sauke ajiyan zuciya dakin anty na nufa don karbo mai magani.
Na tura kofan na shigo da sallama tana zaune saman gadon ta ta baje kanta babu dan kwali akai.
Tana gani na take cewa dani cikin murmushi maman yara kin samu kanki ko kin gama komai.
Nace eh anty yanzu ma nazo ne in da magani ki bani naba Nasir.
May ya samay shi kuma nace ina ganin zazzabine ke dan satan shi amma ba wai ya fada min bane nan dai nai mata bayanin komai.
Tace wanan yaron sai kinyi hakkuri halinsa sai shi wallahi don ni halinsa na rasa ina ya samo shi.
Ta nuna min inda magani yake na miko mata tace Allah yasa yasha don miskili ne wallahi.
Murmushi nayi nace haba anty ba kudai fahince shi bane amma yana da saukin kai ai idan abin shi a sannu.
Tace ai yanzu kunfi kusa dashi Allah yasa dai ya sha maganin don bai son magani sam.
Nashiga dakin na samu yana kwance yadda na barshi da farko na dafa goshin shi jikin ya dan yi sanyi a lokacin ya bude idanuwan shi yana kallona.
Nace Nasir dina tashi ga magani ka sha kada jikin ya matsa ma sai naga ya ya mutsa fuskan shi nace ko na jika mane ?
Sai ya gyada min kai alaman eh yana son haka na dawo da cup da ruwa a hannuna a gaban shi na jika na nasa spoon na juya na bashi sai ya karba yasha yana ya mutse fuskan shi na bashi ruwa yasha.
Ina gyara mai kwanciya sai ga uwar tasu ta shigo dakin tana tambayan yasha ko akai shi asibiti yaga likita nace ya sha anty.
Matsowa tayi ta zauna a bakin gadon da yake kwance sai take bin dakin da kallo komai na dakin tsab dashi.
Tun dai gurin kayan Nasir komai a natse yake tace dani kai ashe ba karamin aiki kisha ba dakin nan ne haka Rama ?
Nace kin san zama da kazanta ba kyau anty gashi yara ne sai anyi hakkuru ana gyara masu dakin nasu.
Kakarin amai yaron keyi yasa hankalin mu ya koma gare shi kama shi nayi amma kafin na dago shi har ya bata min jiki da aman .
Nan uwar ta haushi da fada tana cewa haba Nasir wanan sakaci ne ai zaka batawa Anty jiki da amai kuma ni ba batun kaina nake ba sai kokarin kamashi muka shiga bandaki yai amai sosai a ciki na gyara shi muka fito har lokacin tana zaune inda muka bar ta.
Nace bari na canza mai zanin gado tace haba goge gurin kawai ya kwanta mana.
Nace bari dai na canza mai tunda wanan din ya baci yaron cikin san murya da nuna fushi a fuskan shi yace kai mummy please go now.
Tace cikin dariya dama abinda yake so ke nan shegen tsabta gare shi kaman ba karamin yaro ba.
Sauran yaran ne suka shigo dakin suna cewa anty is time for prayer mun zo muyi sallah ne tare da ke nace tau ayi alwala.
Tace masha Allahu ashe har jam,in sallah ake a dakin lalai an samu ci gaba.
Suka ce anty ta fada muna cewa idan bamu sallah za, a kona mu ne wai da wuta.
Tace gaskiya ta fada maku oya aje zuwa alwala kafin anty tazo nan suka shige bandaki kafin su fito na fitar masu da hijjab din su.
Anty ke cewa idan mun koma wancan gidan zakuji dadin shi don yafi wanan girma sai dai aikin zai karune don haka nace a samo min wata yar dattijuwa mai dan dama don akwai dakuna da yawa sosai a kowani part gidan babbane kwarai.
Nace cikin mamaki anty yakuma fi wanan girma da kuk ciki tace babban gidane sosai Rama sai in kin gani zaki sheda .
Ba karamin kudi ya kashe ba gurin gina gidan don har ginan yaso ya taba mai aikin shi da kasuwan cin shi don mutane nata magana akai.
Nace ashe harda babban gari akwai tsegumi kamar mu kauye tace inane babu gulma yanzu haka duniya ya koma fa.
Ranan itama a dakin mu tai sallah tana kallo yadda muke sallah da yaran sai sun kalla sun ga abinda nayi zasu kwaikwaya suma suyi hakan.
Muna gamawa taji mun fara karatu duk sun haye min jiki na amma haka muke karatun tai mamaki jin har mun kai kulhuwallahu da yaran don tare muke hadda dasu da baki.
Abin yai matukar bata sha, a take cewa lalai munyi kure dole a samo malamin mai koyar da addini koda da dare ne sai yazo a dan taba.
****** ********* ******
Fitina yakai fita don Jatau ya saka mama da baba a gaba daya samu labarin bani garin.
Haka magana har takai gidan maigari dole sai da aka kira mama taje da kanta.
Nan dai ya koro bayani mama tai tsuru tsuru sai kamay kamay takeyi tarasa na cewa gashi babu kudi don har kudin sadakin ta kashe wai tayi sayayya dasu na aure.
An basu sati biyu kacal su kawo mai kudin shi ko su dauki hukunci kan ta nan suka bar gurin kan wanan magana.
Suna dawowa gida ta saka baba a gaba kan sai dai ya tafi birni yazo dani a daura aure akai ma jatau don bata san inda zata samo mai kudin shi ba cikin sati biyu.
Yana gama sauraren ta yace amma kina da wani magana ni ina zanje cikin kano na dauko Rahama ?
Altine ce tasan inda ta kaita kuma suna can tare ban san wanda zan tambaya inda suke ba yanzu don ba wanda yasan gidan yan uwan nata.
Hankalin mama ya kara tashi sosai har gurin Inna ta taje cikin kwantar da murya take cewa a tsaya a fahinci juna kada abin yakai ga bacin rai.
Inna tace rai shi ya dade baici ba ita ko kano bata taba zuwa ba balle ta ce tasan inda muke.
Su dai da suka ci kudin shi sai su tafi can su karata dashi ita babu ruwan ta cikin wanan magana kuma daga yau su fitar da rai ga tinanen zasu hada ni aure da wani jatau a yanzu.
Mama ta bar gidan cikin bacin rai take cewa yadda ba, a so sai ankai ga yin hakan Inna tace to bissimillah kuma tai mata kashedi akan zuwa gurin ta don babu hadin kifi da kaska yanzu.
Haka ta dawo gids cikin tashin hankali ga kwanaki sai matsowa sukeyi tace idan baba ba zai je nemo mu ba ita zata shirya taje kano da kanta ai mai tambaya baya bata sai ta gano inda muke a kano ta dawo dani an mata aure.
Yace bissimillah gaki ga hanya nidai banci komai na Jatau ba balle ya damay ni.
Haka tashirya ita da Larai kawar ta suka tafi kano tun shigan su garin hankalin su ya fara tashi duk wanda suka gani a bakin tasha sai su tsayar dashi suce don Allah ko yasan wata Rahama tare da Altine mai kulli kulli.
Wasu suyi masu daukan mahaukata wasu kuma su tsaya masu tambayan a wani unguwa sukace daku suke ?
Basu sani ba sai a barsu a tafi sun koma kamar mahaukata suka dawo gida cikin dare hankali a tashe.
Ko sannu baba bai mata ba shiya tayar mata da hankali ke nan ta haufada tana cewa munafuki dama ashe tare dashi aka hada baki don aga bayan ta ai tasan zaman ta dashi.
Hankalinsu har baba ba, a kwance yake ba gashi gidan ya fara yi wa baba tsamin har ya fara kewan Innata a lokacin sai dai yana gundu yanuna yaji masifan mama.
Har bakon da mama Altine ta aje gidan ta da iyalinshi sai da mama ta tayar mai da hankali tace yasan inda mama Altine take inba haka ba may zai sa ta aje shi gida bata sanshi ba.
Nan sukayi tas da mutumin ya nuna mata yafita kwaya dole ta fita batun shi ta kyale shi don yace idan ta sake shigowa ta tayar mai da iyalin shi hankali kan abinda bai shafe shi ba sai yai mata tsinanen dukan da sai an kaita asibiti ta kwanta.
Gidan Lairai taje neman shawara nan dai suka kasa kai mafita ga maganan sai larai ne ke cewa nifa ina ganin mafita daya ne a gareki yanzu shine ki daure ki bashi daya daga cikin yaran nan a zauna lafiya.
Cikin mamaki mama tace wa kawar nata Larai yaushe kika fara hassada na a garin nan ban sani ba Jatau ne zan dauki yar cikina naba aure ko may ?
Larai tace to may ye a hakan ba mafita muke nema ba ko kina da jakka dari da tamanin da zaki ba jatau ne kudin shi.
Nu naga haka shine mafita kawai cikin wanan magana ki samu a zauna lafiya don kin san dai Jatau bai daukan kaddara shi.
Aiko mama tai cikin Larai da masifa suka dinga tonon asiri a tsakanin su kaca kaca sukayi tabar gidan Larai a hasale kowa ya kama gaban shi daga ranan.
Duk wanda yaga mama a lokacin yasan tana cikin tashin hankali sosai don ko ba, a fada ba duk ta ramay ta fita hayacin ta fa fitinan yaran ta da yai mata yawa.
Don babu ragowa ko kadan tsakanin ta dasu sai cin mutunci kamar ba uwarsu ba.
Ana cikin haka akace an kama Rukkaiya da mai nama a shagon shi suna lalata wanda dama ba ranan ne farkon yin haka ba a gare su.
Nan wani sabon magana ya bi gari kwaaa ga kauye da iya daukan magana ko karami ne balle irin wanan.
Da labari yaje wa Inna tace ita kan dai ta godewa Allah da yaraba ta salin alin da wanan fitinanen gida a wanan lokacin.
Ranan komawan su gurin maigari yazo dole ba don taso ba ta hada dubu goma da kyat koshi sai da ta sayar da yan kaddarorin ta ta samay su.
Bayan ta gabatar da kudin da tazo dasu ne aiko Jatau ya buga kasa yace bai san da haka ba shi kudi shi minamina yake so don ba zai dauki hasara ba baiga mata baiga kudin shi.
An kai ruwa rana so sai a gurin dole aka bata zabi idan babu kudi a turasu kotun birni ko kuma ta samu mafita ta bashi kudin shi.
Maiunguwa ne ya kebe da ita gefe ya bata shawara ta bashi yarta daya a wuce gurin don idan ta bari aka tafi kotu daure ta za, ayi can babu kuma may sanin inda aka kaita.
Kuka ta saka ma maiunguwa tana cewa ya cece ta yai mata rai ita bazata iya ba Jatau yar ciki ta ba yadda yake din nan gashi kazami fa tsufa ga rowa da cin mutunci.
Maiunguwa yace ni wanan shawaran shine nake gani kawai mafita a gurinki a wuce gurin don gujewa shigan ki gidan yari.
Bata da zabi dole da wanan shawaran suka koma tabarman mai gari nan mai uguwa ya gabatar da shawaran da sukayi da ita.
Baba dake zaune yace idan haka zai kashe maganan shima ya aminta da hakan .
Aka tambayi Jatau idan ya yarda da hakan yace sai dai yayi maneji don dai shi ba cikin su yaso ba.
Mama naji ta dago kai ta kalli Jatau mutum haka a kazance har yake kiran wai maneji zaiyi da yarta.
Muryan mai gari taji yana tambayan su daga cikin diyan wacece zata bayar.
Nan wani sabon tashin hankali yazo mata to ita wa zata bashi don duk yaran nata ba mutunci ne dasu ba ai.
Babu wace zata fahince ta ta fitar da ita wanan kangin da take ciki cikin ruwan sanyi.
Sai bude baki tayi tace kai kai Rahama Allah ya isa tsakani dake da uwar ki da kika jefa ni wanan halin haka.
Maigari ya matsa mata tace a bashi Rukaiyya nan jatau yace wa shi Allah ya sauwaka mai yarinyar da ta zama ba gari dadi zai aura yagane may gurin ta.
Ran mama ya kara baci tai cikin shi da masifa karshe dai da aka kai ruwa akai rana yace sai dai Lawisa dan dama dama zai laba da ita hakana.
Haka a