Showing 30001 words to 33000 words out of 373688 words
Chapter 11 - A LOKACIN MUKE BOOK BY ZAINAB .I. MAKAWA.txt
Zuwa can naji anyi sallama ya amsa wata budurwa ce daga cikin diyan shi dauke da kwanon kunu da kosai taje cewa baba ga abin karyawa inji mama akawo maku.
Yace kice ana gaida ita da aiki ko inda nake bata kalla ba tafita daga dakin har takai kofa naji ya kirata yace suwaiba kun gaisa ne da sabuwar umman taki ?
Tace baba ai ban gan ta bane tabashi amsa murmushi tayi tace ina kwana .
Nace mun tashi lafiya yaya gida bata tsaya ba tabar dakin yace taso ki dibi kunun da kosan mai isar ki kisha.
Nace sai zuwa anjima bani karyawa da safe haka ai yace to injin ku yan boko ne ?.
Da naji alaman suna aiki na fito na samu ashe kowa ce ta fito tana aikin sana, anta da takeyi a gidan .
Na kama wa mama dama kokon da takeyi za, a fita mata dashi nan da nan muka gama.
Sai mai bi mata dake dafa shinkafa da wake itama na karbi wanke shinkafan na wanke mata tas na zuba tare da gyara wutan da icce ya jaye na hura wutan sai gashi ya kama.
Ban koma daki ba sai dana kwashe mata shi a kwano na gyara yadda za, a fice dashi na koma daki na.
Na samu maigidan ya shirya zai fita yace ina kika shige ne Amarya nace ina gurin da ake aiki ne.
Yace to ni zan fita sai na dawo zan dan leka waje nagani ko akwai abinda zan iya yi a can na neman kudi.
Kin san angon naki dan bida ne ba mai zaman gida bane ni.
Na durkusa nace Allah yasa a dace Allah yaba da nasara a dawo lafiya baba.
Yace kai ni fa wanan baban ba son jin shi nake a bakinki ba da dai za, a canza min suna ko Alhajina akirani dayafi min alheri.
Nace to Alhaji Allah yaba da sa, a yasa a fita a nasara yace amin yar amarya ta yaushe rabon da naji anmin fatan alheri haka a rayuna.
Nan yasa kai yafice ni gyara dakin na dan zauna sai barci ya kwashe ni afurin mai nauyi ban sani ba.
Muryan yan gidan mu ne da suka shigo ganin kwanana ya tayar dani daga barci.
Na mike zubur ina masu sannu da zuwa idanuwan su fes a kaina suna kallona ban san may suke son fahinta ba daga gare ni.
Na gaidasu daya bayan daya tare da tambayan sauran mutanen gida.
Da yake iya yan uwan inna ne sai kadan daga dangin babana sai cewa sukayi kowa lafiya sai maman ku ne dai da ta saka muna hauka wai sai baban ku ya fada mata inda ya samo kudin da yai maki hidima haka na fita kunya.
Duk rantsuwan da yai mata ba yarda dashi ba wai idan bashi ya yi ba mijinkine yaba da kudin aka boye mata.
Nace cikin murmushi tare da zama kan makarin kujera na kai mama ho yaushe zata bar wanan halin nata ne na hassada da bakin ciki.
Ita da tace da tabar za, a kawo ni yanzu da taga sabanin haka shine kuma ta tayar da hankalinta.
Rabu da mahaukaci wacce bata son azauna lafiya iji kauna babana ta fadi hakan.
To yaya kuka kwashe da matan gidan naku yau da safe da fatan babu wani matsala dai ko daga gurin su.
Nai dan murmushi nace babu komai mama batare da na fada masu abinda ya faruba da safe akaina a gidan.
Sai dayan mama tawa tace ai ina ganin indan dai ta iya binsu zata samu sauki ga biyun mata wanan dai da take biwa ce matsala nake gani sai yaran su kuma don naga yaran a tsaye suke suma.
Nan dai sukaci ga ba da yi min nasihohi na in zauna da zuciya daya dakowa na basu girman su tunda duk sun haifeni baki dayan su.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, ,
IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WASU MUN BARKI GA ALLAH YA BI MUNA HAKIN MU A KANKI YAR UWA DA FATAN ZAMU JI TSORON ALLAH MU RIKE AMANA DON AMANA GIRMA GARE SHI.
Dawowan Sabuwa gidan yasa yanzu na rage fita gidin darbejiyan da matan gidan suke fita hira ko yaushe.
Idan ma na dan fita bani daukan lokaci a gurin don gujewa shiga tarkon ta don ko yaushe ita a cikin fitina take.
Gata irin figagan matan nan ne marasa jiki komai nata dan kyamn, ne a fige sai bakin fitina da mita ga yawan haihuwa a yadda naji matan gidan suna fadi wai bata yayewa take samun ciki.
Ganin na rage fitowa ne yasa ranan mama hausatu take tambayana dalilin kumshewa na daki yanzu murmushi kawai nai mata batare da na bata amsa ba.
Sai cewa tayi Allah ya kyauta halin sabuwa sai ita don mai hali baya barin halinsa komu nan ba barin mu tayi ba ai da girman mu gaban diyan mu da sarakan mu sai taci muna mutunci ba komai bane a gurin ta.
Jin da nayi yarona abokin hirana dan makwabbcin mu habib yana da kwazo ga karatu addini gashi karami amma Allah yai mai baiwa gurin garatu.
Yasa na ke zama dashi muna karatun mu a shiyana muyi karatu idan mun gama muyi ta shiriritan mu kamar yada kauna muke dashi.
Don dan abinda yake samu a gurina gashi na rike shi da zuciya daya shima hakan nake gani a gare shi don bai taba min abu sai ya roke ni .
Wasa wasa sai na fahinci ba karamin karuwa nakeyi ba da karatun da nakeyi a gurin habib din.
Hakane ya bani daman tunanen na roki Alhaji idan zai yarda na rika zuwa makarantan islamiyan dake kusa da gidan mu.
Don akwai daya daga cikin sarakan gidan da kullun ita sai tafita zuwa daukan karatu.
Da naiwa Alhaji magana yace haba amarya kofa wata uku baki kai ba da zakice zaki fara fita ?
Dole na hakkura naci gaba da karatuna tare da habib din amma abin yana a raina.
Dama nayi nisa tun a gida haka yasa na samu saukin karatun a yanzu wani lokaci kuma littafaina na boko na kan dauko nai tabi ina dubawa ni kadai a daki na.
Mama Hauwa tana aikin fura sai dai ba kullun takeyi ba daga shiyana nake jin harshen ta tana fada da yarta mai mata talla wai sunyi rana ga aikin kuma yarinyar ta tsaya tana shiririta ga aikin.
Na mike tare da shiga daki na sauya zanin jikina na jawo kofan dakin da kuma kofan shiga shiyan nawa don akuyoyin gidan masu bakin barna.
Na samu ga gari aje ga aikin gida da yasha mata kai don ita ce da girki ranan.
Ina zuwa nai mata sannu na karbi rariyan dake hannun ta na shiga tankade da gyaran garin.
Na fahinci su kamar mama lauratu na gidan mu suke don basu damu da koyawa yaro aiki ba a gida.
Yar ta Amina tana fitowa ta ganni a zaune ina tankade tace wai har naji dadi amarya dana ganki don yanzu dana fita tunda kin saka hannu ga aikin nan zaki ga na sayar da furar nan a take.
Kai ji wani batu daga can kofan mama hausatu Zuwaira tace mama ai ba karya ta fada ba mun gane idan amarya ta taba kayan sana an mu a take muke saidawa idan mun fita.
Hannun ta yana da albarka sosai wallahi a kaji min yara da sabon surukulle kuma ?
Inji mama hauwa take fadi tana dariya tace muma wallahi zuwaira ta fara lurar damu haka dakuma muka duba muka ga ai hakan gaskiya ne.
Nan dai sauran matan gidan aka taru ana wanan zancen ana dariya ni dai akina nake ban yi magana ba.
Daga can kofan ta sabuwa ce ke cewa daurewa karya gindi ke nan ita waye da zaku ce haka ko watafi sa, a kuke kara zugata tana ganin ta kai wata aba a cikin mutane ji wani sabon tsurkun da kuma kuka camfa mata don taji dadin iya shege.
Ni dai wanan aikin jagwalgwalen badani balle a camfani ni kishiya bata fini ba balle na sa a kaina.
Wanan abar ce zaku tsaya kunawa wanan camfin kamar wata babban mace can da ita.
Nan daya da kacin sarakan mama ta cafe da cewa ai ba camfi bane dama can a garin nan kowa yasan irin sa, an dake ga Rahama ai gurin talla don komai ta dauka sai kudin shi.
Eh hakane dama tunda tana da tsifin dake mata juye subata kudi ta kaiwa uwarta ana cewa sa, a ne yanzu ai gaskiya ya tabbata don mungani koshi Alhajin ba ragowa ne ya kwaso muna ba Allah mudai ya cece mu da daukan ciwon sanyi wallahi.
Shiru gurin yayi don jin inda ta biyo da zancen can mama hauwa tace wanan kuma sabon kake ne don ban taba ji bani kan abin garin nan da ba a boye yake ba.
Tace kece baki sani ba kuma dole ne sai kin sani ba tunda idon ku ya rufe don kawai ai min sheri a hada min kai a gidan nan aga bayana nida Alhaji ko mutu ka raba.
Sai lokacin mama hausatu uwargida tai magana tace kai haba sabuwa in an girma asan an girma mana yanzu wanan yarinyar dako hankalin kanta bata gama mallaka ba zaiyi wanan sheri a matsayin ki na uwa.
Ke ma fa gakin nan dasu a gaban ki indai yaran ne ai ba uwar da zata so aiwa yarta sheri haka ?
Au to yaya abin yakai can baki zakiyi wa yarana kuma?
Ai dama ba yau ba nasan sun kai maku ko ina a gidan nan saboda hassada aiko tashiga bakin ta harshen ta har waje ana jin ta.
Daidai lokacin ne mukaji gyaran muryan maigida yana tafe tare da dan shi babba a baya da mai bi mashi.
Tun a kofa yake fadin wai yaya ne kuma may kuma ya faru haka da rana tsaka.
Ledan dake rike a hannun shi na vaco na je na karbo da sauri yayin da sauran matan ma suka karbi na hannun mazajen su idan ta akan ledan dana karbo take fada.
Na nufi dakin mama hausatu da ledan don itace ranan da girki sai yamma zata fita sabuwa ta karba don girkin namu a jere yake muna.
Ina nufin shigewa dashi dakin ta yace dawo dashi nan mikawa hausatu a raba abakowa nata ta shiga dashi ya juya yana fadin tambaya nakeyi mai ya faru wai ake wanan fada murya har kofan gida.
Shiru kowa yayi babu ma magana a cikin su sai Amina yar shi ce ta shiga koro mai da zancen abinda ya kawo rigiman haka.
Ya kalli inda sabuwa take yace kai amma dai sabuwa ke mutumiyar banza ce wallahi.
Kina zaton yadda kike watsatsa haka kowa ma yake a rayuwan shi tashinki a garin nan aike ce kika so bata tarbiyan yaran garin nan kaf don ke kka zo da wanan halin ko don su nan basu sani ba har kika samu bakin yiwa wata sheri kuma ?
Haba nan ta juye bala,in ta kan shi sai da yai saurin saka mata waigi ta dakata don tasan abin da yake nufi zai iya aikata shi da gasken a kan ta.
Malam wanan kuma Yaya za, a yi dashi tana kokarin fitar da gorunan man shanu daga cikin ledan tana jerawa a kasa.
Ya dan juyo gare ta yana tsuki abinda ya dakatar da su daga fitinan da suka dauko yi da sabuwa ke nan.
Yace ai gora hudu ne ko kibawa kowa nata ke Amarya ya duban gurin da nake ina gyara wutan huran da muka nasa yana zabarbaka daga tukunya.
Jeki ki karbi gorunan ki bawa kowa nata kason ta dauka da sauri na nufi gurin mama hauwa din na fara kaiwa mama hausatu ta zaba na mikawa mama hauwa na ta,na dauki daya zuwa gurin yaya sabuwa da nata goran .
Tun kafin na karaso na ji tace may kike nufi wai ke yar wayo ko kin zabi mai kauri kn kawo min mai ruwa ko ?
Da sauri na juya inda dayan goran yake na dauka na kai mata ta zaba sai da ta karba ta jijiga ta kara juyawa sama da kasa sai ta miko min wanda na aje da farkon na juya don duk a tsorace na ke a gaban ta kada ta make ni.
Kaiyya inji mijin su daga gurin da yake zaune saman wani dutse dake tsakar gidan.
Yana na kallon yadda muke kwasa da ita kan man shanun da ya sayo muna daga kauyen da suka tafi.
Tace ana dai rabon son kai a gidan nan ace da may iyali da mara iyali duk kaso daidai za,ayi shi wai haba wanan ai dul cikin zalumci ne wallahi Allah ko.
Zaki soma ko ?
Wai ke Sabuwa baki ba kanki lafiya ne ki rufawa kanki asiri ne haka wai ?.
Kin manta da yadda aka kwasa a baya ko da kyat fa na samu malam shehu yai bugun gaba yaje ya dawo dake .
Au to kina son fada min cewa kece kika tura biko na ko may ?
Daga inda yake zaune yace ke dama kina daukan cewa zata canza halinta ne ai mai hali baya barin halin sa.
Yace ke hausatu dauko min tsimayn nan nawa na dan sha don banjin alaman dadin jikin nan.
Nan dai kowa ya watse ya kama gaban shi muma muka gama hura kusan nice nai aikin huran don na iya dama tun a gida.
****** ********* ******
Kamar yadda mata idan sun taru sai zancen mazan su hakane ke kasancewa yanzu a gurin maza.
Taron da akeyi na fadanci a kofan gidan na Alhaji garbati wanan karon ma sun hadu ana fadanci don dan abin da suke samu daga gare
shi.
Baba salla ne ya fara cewa aikai Alhaji sanyin babana lafiya lau kake ga amarya ga sanyi .
Ko ba a fada ma jikin ka ya nuna ka samu lafiya ga hakan nima dai kukewa zanyi naga na samu koda bazawara ce mai dan dama na kawo gida ko zan samu dan gurin hutawa bana.
Jin zancen su kawai yake amma zancen yana tsuma shi sosai haka yasa ya yanke cewa zai gwada ya gani dai ko ya samu lafiya shima ya fara murzan amarci da yar amaryan shi.
Ranan da akai wanan zancen a dakin sabuwa yake dama ta ishe shi da mitan ita a bukace take fa.
Bayan ya shigo gurin ta ya kokarta yaga ya samu gamsuwa amma ya kasa hakan gashi ta isheshi da minta wai ai da amarya ce inda yake kare karfin shi gurin yar karamar yarinya dan yai bajinta ta gani.
Shiko ya na samun kanshi daga gareta ya fara wani irin nishi yana jin kamar ranshi zai fice mai a lokacin.
Da kyat yaga safiya sabuwa ce ta tayar da mutanen gidan don neman taimako a kan shi.
Ba,a bata lokaci ba da safen nan aka nufi asibiti dashi hankali a tashe duk kowa gidan ya koma jigun, jigun abin babban gida take a kashiga tsegumi ga Sabuwa.
Wasu suce kila wani mugun abin tai mashi har taso halaka shi, wasu kuma suce dama ba lafiya gare shi ba kila bakar jarabanta da ta sabane ta matsa mashi har ta so halaka shi.
Nidai da yake akwai kurciya a tare dani ba fahintar zancen su nakeyi sosai ba amma na shiga halin damuwa don ance sabo turken wawa ne.
Dan zama na gidan ko ba komai yana bani kulawa yana tattalina yadda ya dace ayi.
Sai zuwa karfe biyu suka dawo tare dashi yaji sauki sosai kamar ba shine aka fita dashi gidan da taratara ba..
Sun tara mu duk kan mu matan shi a dakin mama hausatu sun muna bayani cewa likita yaba da doka kan cewa mahaifin su har yanzu bawai yaji saukin lalurar shi bane don haka akula don Allah kada a dinga matsa mai kancewa lalai sai yayi wani abu da watan mu a bishi a hankali.
Ni dai na fahinci suna magana suna yawan kallon inda nake zaune ni da sabuwa ne amma ba wai na gane manufan su bane.
Sai da yai mata kwana biyun ta ya dawo dakina kamar kullun idan nice zanyi girki na kammala komai da nakeyi wanda ba sai na fita tsakar gida nayi shi ba.
Don ni ai fadan sabuwa zance gaba ya kaini don Allah ya rabani da tuwon taro komai a dan karamin shiya na da aka kebe min nake abina wanda hakan yakaiwa Sabuwa ko ina.
Tayi mita akan itama sai ya kebe mata nata shiyan daban kamar yadda ya ke be min nawa ni kadai nake kwamacala na ba wanda ke ganina sai wanda ya shigo inda nake.
Girki dai Alhamdullahi don tun a gida nakeyin abina tun mama nacewa wai Innata tana sa ina masu jagwalgwale har ta gaji ta sa ido ranan girkin inna ta idan na dawo tallah da wuri kafin naje diban ruwa zan tsaya na taya ta aikin girki da gyaran gida.
Haka yasa yanzu ban sha wani wahala ba a gidan auren nawa da na tsinci kaina a ciki da rana tsaka.
Yau da yake ba fita hira yakeyi ba sai gashi ya dawo gurina tunda magariba, anan yai sallolin shi kofan daki inda yasa nai mashi shimfida.
Nakawo mai abinci na koma daki na zauna ina ciki naji ya kirani yana cewa fito mana Amarya ki