Showing 36001 words to 39000 words out of 373688 words

Chapter 13 - A LOKACIN MUKE BOOK BY ZAINAB .I. MAKAWA.txt

yarinyar za, a ce wai ta samu ciki da mutum irin Alhaji wanda kewa iyalin shi ikirarin baida lafiya bai iya komai da mace amma ya takure a gidin yarinya karama to ga abin boye ya fito fili ai kowa ya gani yanzu gaskiya ya baiyyana.

****** ********** ******
Tun lokacin da na fara period naga gaba daya na sauya wani girma ya zo min ga kayan dadin da nake samu ina ci iri iri gwagwadon halin yan kauye irin dadin su na kauye.
Wani lokaci sai nayi kyauta da wani abin ma na rabawa yaran cikin gida su ci don ban iya ci ni don ban saba da yawan ciye ciye ba a rayuwana.
Zaune nake a saman kujeran dakina nayi tagumi da hannuna na hagu na zurfafa ga tunane.
Sai ganin shi nayi ya shigo dakin na bishi da idanu kamar shima yadda ya bini da kallo don ganin yanayi na a cikin damuwa.
Guri ya samu ya zauna a bakin gado yana kokarin cire babban rigar dake jikin shi.
Yace may kuma ya faru na gan ki haka amarya, murmushin kake nayi wanda bai kai ciki ba a fuska na.
Yake cewa wai may ke faruwa ne ko anyi wani abin ne kuma bayan fita na ?
Nace babu komai tashi yayi daga inda yake ya dawo kusa dani ya zauna saman kujera two seater dani kai a zaune.
Yake cewa fada min mana may akayi ne wai naga yanayin ki ya nuna min kina a cikin damuwa.
Nace ba komai Alhaji tunane Inna ta kawai nakeyi.
Yace wani abu ya samu inna din ne kuma ?
Kai na girgiza mai alaman a, a.
Murmushi yayi tare da riko min hannuwa na wani irin yar naji har cikin zuciyana tare da jin nauyin shi na ganin ya taba min jikina karo na farko zamana dashi.
Ban kai ga karasa mamakina na ba naji ni ya kwantar dani a saman jikin shi yana dan shafana a hankali.
A take naji yanayina na neman gagarana zama a gurin da nake zaman tsara dashi.
Yace ki kwantar da hankalinki insha Allahu akwai shawaran da nakeyi akan ki idan har nakai karshe wata kila ma zaki koma gurin Inna din da zama na dindindin.
Da sauri na dago kai ina duban shi yace ki dai kara hakkuri kinji Rahama dan bani lokaci kadan.
Nace ni ban son komawa gidan mu gurin inna ta, zama na nan yafi muna komawa gidan su Inna yanzu hankalin ta a kwance yake don mama bata gani na balle ta tayarwa Inna da hankalinta .
Ni nan zan zauna gurin ka kana kula dani fiye da Inna ta da baba na ban cikin matsin mama kuma yanzu.
Dukar da kan shi naga yayi a kasa sai naga hawaye suna zubo mai sannu a hankali.
Cikin mamaki nai zubur na mike daga inda nake a zaune tare da dawowa gaban shi na tsugun na ina cewa .
Don Allah Alhaji idan har na fadi wani abinda ba daidai bane kayi hakkuri kayafe min naji zan koma gidan mu gurin Innata muyi ta hakkuri da rayuwan da zamu tsunta agurin mama.
Ji nayi ya tallafo ni daga gurin da nake a tsugune zuwa jikin shi ya rugumay ni yana dan shafa min bayana tare da fadin ya isa haka kiyi shiru babu inda zaki tafi kina nan tare da mu insha Allahu.
Wanan ranan ne muka fara kwanciya saman gado daya da Alhaji sai dai yana gefe ina gefe a kwance har gari ya waye .
Abinda ban sani ba ranan shi gare shi ko runtsawa bai yi ba sai faman tunanen duniya yakeyi.
Ya so it a mayar dani gidan mu gurin iyayyena don yana ganin yana kuntatawa rayuwa na sosai, amma kuma sai gashi ni da bakina nake fadin wanan zaman yafiye min zaman gidan iyayyena dadi.
Haka yasa ya fahinci daga ni har innata muna wani rayuwa ne na zaman ukuba a gidan.
Dole yabar wanan yarinyar yaga abinda Allah zaiyi akai don Allah kadai yasan dalilin wanan auren don shi baki sa,ata ba ko wace tafini shekaru bai da nufin karawa a rayuwan shi.
Sai gashi a lokaci daya Allah ya jarabce shi da kara aurena auren kuma yazo da kaddaran rayuwa gare shi.
Yadda na samu kwanciyan hankali na mirje nai kyau dani haka yasa Sabuwa tayar da hankalin ta duk ta fige tayi wani baki da ita.
Gashi ta sa a ranta cewa cikine a jikina yasa na koma haka dani lokaci daya.
Akwana a tashi hasaran mai rai yau nakai wata takwas da aure har lokacin ban sheda nayi aure ba a rayuwa na.
Iyakata naci na sha na kwanta nai kwana idan naso na shiga na taya matan gidan aikin su.
Ba mama da mama hauwa ba kawai nake tayawa aiki har sarakan su idan aiki yai yawa nakan kama masu.
Ban hakkura da zancen zuwa islamiya ba na kara tunawa Alhaji da kyat na samu ya yarda na tafi sai gashi ya sawo min hijjab har uku maya har kasa da nikaf na rufe fuskana.
Ranan da zan fara fita nasha sheri gurin matan gidan wai ni yar izzala ce shiyasa nake da mugun tsabta ashe.
Na dai yi murmushi nai masu sai na dawo nafice daga gidan dama Alhaji ya riga yai min register komai a school din.
Don haka ban sha wani wahala ba na gane ajina gwajin farko ya fahinci na dan yi nisa aka mayar dani ajin manya.
Sosaina dage ga karatu na ba wasako a gida nake banda abinyi sai karatu da yan aiyuka na.

****** ********* ******
A bangare Alhaji ya samu sauki sosai don tsare dokokin da yayi na likita har anfasa zancen yi mashi aikin da akace za, ayi da farko.
Hakan da yake ji yasa yake ganin ya samu sauki ya shiga kokarin gwada sa,anshi ya gani .
Ranan a cikin barci na dinga jin wani bakon al,amari ya na ziyarta na idan dai ba mafalki nakeyi ba to zan iya cewa kirjina, watau dukiyan fulani na ne kejin ana taba min a lokacin.
A hankali na zubura zubur daga mafalki kamar zan fasa ihu sai jin muryan shi nayi yana ce min kamar rada yi shiru amarya nine Alhaji ba kowa bane.
Na gyada kaina alaman na gamsu sai naji yana sauke ajiyan zuciya naji yana ci gaba da saukewa a hankali.
Bai kuma fasa abinda da hannayen shi keyi a saman kirjina ba har lokacin.
Sai faman rintse idanuwa na nakeyi don irin bakon yanayi da nake ji a lokacin.
Kama an fisge shi naji ya juya da sauri tare da rike maran shi da hannayen shi yana wani irin nishi kamar kugi a hankali.
Shiru nayi ina sauraren yadda yake fitar da sauti daga bakin shi cikin yanayin ban tausayi .
Can a kasan makogwaron shi naji yana kiran suna na a hankali da kyat sautin maganan shi ke fitowa a lokacin yana fadin naje na dauko mai ledan maganin shi da ya bari a dakin sabuwa.
Ban ki ba haka na daure cikin wanan Uban daren hana na wucw gurin mama hausatu na buga mata kofan dakin ta tare da cewa maganin shi yace na karbo mai a gurin mama Suwaiba.
Ita da kanta ta tafi dakin ta buga mata take cewa miko min ledan maganin Alhaji da ya bari a nan ta tambaya da sauri injin dai lafiya yaya ?
Lafiya kalau ya manta bai sha bane yace a dauko mashi ya sha ta karbo ta mika min na juya na bar dakin simi simi dani.
Nakai mai sai da ya hada ya sha zuwa can ya dan samu relief sai barci mai nauyi ya dauke shi nima na koma na kwanta zuciya na fam da tunanen abinda ya faru yan mintina da suka wuce a tsakanin mu.
Wanda har lokacin ina dan jin dan matashin kirjina yana dan min radadi.
Washe gari na tashi ina matukar jin nauyin shi da kunya akan abinda yai min a daren jiya gashi alama ya nuna yana dan jin jikin shi .
Amma haka ya daure yafita daga gidan zuwa gurin neman kudin shi daya saba yi.
Bai jima ba a waje jikin ya tsanan ta mai ya dawo gida ya kwanta min a daki gashi kunya da nauyi nake ji har lokacin ban iya hada ido dashi.
Haka yasa shi fahinta halin da nake ciki daga inda yake kwance na shigo dakin ne naji ya kira sunana.
Na amsa sai naji yace na gode daren jiya fa ko ba komai na dan more daga ni,iman da Allah yai maki ya fadi hakan cikin dan lumshe idanuwan agi a hankali.
Shi kadai yasan irin halin da ya tsinci kan shi a daren jiya sai dai yana gap da biyan bukatan shi a gare ni ne yaji maran shi ya rike mai sosai a lokacin.
Hakan ne yasa shi dole neman magani ya hadiye don samun saukin abinda yake ji.
Tambayan kan shi yake a zuciyar shi yayin da idanuwan shi suke a rufe yaushe ne zai samu ya more niiman da Allah ya hallata mai ga wanan yarinyar ?
Irin yanayin da ya tsinci kan shi da ace shi mai lafiya ne yasan cewa a daren jiya din Allah ne kadai zai kare bai kai ga mayar da ni cikakkan mace ba kamar yadda yake gurin yin haka a gareni a kullun.
Ganin da nayi jikin shi ya matsa mai yasa naje na fadawa sauran matan nashi halin da yake ciki.
Ba bata lokaci dakin nawa ya shiga ganin yan zuwa yi mashi sannu da jikin shi.
Nan sabuwa ke cewa Alhaji kana son matsawa rayuwan ka akan sai kaga ka burge wanan yarinyar a koda yaushe.
Idan baka bi sannu ba zaka halaka kanka da kan ka furin budurwan zuciya.
Sai ka dinga farwa yar karamar yarinya akoda yaushe yaushi zaka ganewa lafiyan ka tunda kaki na tsuwa da girman ka a koma ana taratara da kai kamar karamin yaro har may kake nema ne gareta wanda baka samu ba a baya.
Yana jin ta sai dai halinda yake ciki bai iya bata amsa a lokacin don jin zuciyar shi yake yana mai tafasa .
Ga zancen ta na kara kona mashi zuciyar shi akoda yaushe.
Shima laifi ne ga maganan sabuwa da take yawan nanata yana yawan kusantar Amaryan shi ne yasa matsalan shi ke yawan tashi koda yaushe.
Shi dai a gare shi yadauka kawai wanan wani jerabawa ne daga Allah kawai.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,


IDAN KIN BIYA KIKA BAWA WACCE BATA BIYA BA ALLAHNA GANIN KI DON AMANA NE A GARE KI YAR UWA, , ,


Sannu sannu sai gashi lokaci yana ja a wanan lokacin duk wani dan matashin yaro dake gidan idan dare yayi muma shiyana muna karatu, wanda suke jin dadin hakqn anan zamuyi ta shirmay har dare kowaya watse.
Bayani nake masu sosai yadda zasu fahinta gakaratun da suke dan tsinta a gurina.
Wani lokaci kuma novel zan samu mai dadi da ma,ana da koyar da wani abinda ya shafi fannin rayuwan dan adam.
Zan dafa abinci na zuba a babban tire nan zamu taru muna ci muna hira muna dariya abin dai na kurciya zallah kawai.
Har zuwa wanan lokacin zama na da maigidan kamar kullun ne ya kan yi iya bakin kokarin shi don yaga yadda zai yi ya dan samu gamsuwa.
Sai dai hakan bai yuyu ba a gare shi don da alama matsalar shi tana nan mai bai gushe daga gare shi ba.
Don idan yaso ya kai gare ni sai naji yana zufa yana wani irin kugi mai fitar da wani sauti na ban tausayi.
Ni kaina nakan matukar jin tausayin shi idan ya shiga wanan halin don haka zai wayi gari ya wuni a wahalce dashi dashi.
Na fara fahintar wasu abubuwa duk da dai wayo na baikai na fahinta ba a lokacin amma sai nake fahintar ba gani kadai hakan ke faruwa ba har ga sauran matan shi musanman ma dai sabuwa.
Idan ya kwana a dakin ta zanga ya tashi wani lokaci ba dadi har aka fara dan rade radi a gidan abinka da gidan yawa.
Ranan mama da kanta take bugun cikina akan zancen take cewa dani wai amarya kuna dai biyewa wa maigidan yaki natsuwa har ta samu lafiya komai ya zama daidai ko ?
Nace mama na daina zama ne idan yana daki kike nufi?
Ta kama baki tace wane ni da fadar haka amarya rufa min asiri tace ni dama cewa nayi kawai ki dan kaurace mai ga shimfida irin ki dan rika ba da lokaci din nan .
Kin san shi namiji kullun a bukace yake da mace ba ruwan su da lafiyan su koda hakan kuwa zai masu illa ne.
Nace mama kina dai nufi idan yana daki na fito waje na barshi ya huta ya samu hutu sosai ko.
Nan dai ta gane shirmay na bai bari na fahince ta sai ta fito min fili tai min bayanin komai a baiyyane.
Cikin canza fuska nake ce mata gaskiya mama ni Alhaji bai taba nuna min wanan abin ba a tsakani na dashi sai mutunci kawai.
Kan ta ya daure ba don ta yarda ba don tasan hakan ma ba zai faru ba koda kuwa ace ni ba yarinya bace yaya zan zauna har wanan lokacin.
Karshe dai sai cewa tayi dani ki daiyi a hankali kinji kada ki yarda ace an samu wani matsala a kan ki kinji ya ta.
Nace to mama nagode Insha Allahu zan kula kamar yadda kikace din.
Sai gurin karima sarakuwan tane ranan take kara fayyace min yawan hasashen da ake mun a gidan kan lafiyan Alhaji.
Muna hanyan makarata ne take fada min komai tare da jamin kunne akan na kara kulawa sosai.
Tun ranan ban yarda ko dan tabanin da yake ya samu relief din da yake yi na daina bari yanzu.
Har abin ya fara dan damun shi da yai min magana ban boye mai komai ba na fara kuka ina fada mai abinda akace ina yi mai.
Ya gane anja min kunne ne akan haka yasa ya daina kada ya jamin bakin jini ga iyalin shi don su a ganin su nice ban bari ya samu sauki.
Ranan dakin mama hauwa yake ciwo ya murtuke shi a cikin dare aka kwasa sai asibiti.
Nan suka fara fahintar cewa ciwon ne dai bai bar jikin shi ba ba yadda suke hasashe bane.
Koda aka dawo dashi gida wanan karon andai dawo ne amma yana matukar jin jikin shi sosai.
Don yakai idan zaiyi fitsari ma kusan zakaji yadda yake faman nishi da kugi kafin fitsari yazo mai.
Wasa wasa ciwo sai gaba gaba yake mai ya ramay yai baki sai dan wuya takai ma yanzu bai fita kamar yadda yakeyi a baya.
Cikin haka ne ranan aka aiko babana yai faduwan mashi a hanyan shi na dawowa daga kasuwan kauye da yake zuwa.
Alhaji ya samu labari don haka yana dakin sabuwa yasa a kirani nazo na dan rusunna daga kofan dakin nata don ban yarda na shiga daga ciki ba don ta cikin dakn zaune a lokacin.
Yake cewa dani yanzu nake jin labarin abinda ya faru da mahaifin ki jiya shiyasa na kira ki.
Ki shirya sai zuwa ta rakaki ki dubo shi amma kada ku wuce goma ku dawo gida.
Nace na gode cikin murana wanan ne karo na biyu bayan aure na da naje gaida mahaifana.
Na farko tare dashi muka tafi ban ko kai minti talatin ba baba ya matsa min nafito muka koma gida.
Sai wanan daya bani bako mu tafi da zuwaira na dubo jikin mahaifina ko shi nasan don baya jin dadi ne da tare zamu tafi dashi.
Tsab na shirya cikin katon hijjab sai nikaf dana dora akai duk d dare ne amma na saka nikaf din na tare fuskana da shi.
Har mu uku muka tafi don Aisha ta biyo mu da taga zamu fita tare da zuwaira din.
Da sallama muka shiga gidan a tsakar gida muka samay su suna shan iska tare da baba.
Nan muka durkusa muka gaida su tare da mai yaya jikin shi da Allah ya sauwaka ya tsare gaba.
Sai can yake cewa wai Rahama ke ce ai ban gane kiba ikon Allah ya kuke ya gidan duk kuna lafiya ?
Yaya shi maigidan naku da na sa jikin dafatan ya samu sauki ko don ance jikin nasa ba dadi kuma ?
Bayan mun gama gaisawa da baba ne da tambayoyin da ya jero min na juya inda mama take tayi tsit tare da kura min ido.
Ko may take kallo hakana ban sani ba daga jikina na daiga duk da dare ta kura min idanuwan ta a kaina.
Nace mama mun samay ku lafiya yaya gida ashe baba kuma wani kaddarane ya samay shi haka?
A cikin basarwa take amsa min gaisuwa na a tsatsaye na gaida Inna ta dake zaune a gefe tana motsa kunu mai zafi data dama ina ga na baba ne.
Can na mike na leka dakin mama gurin su Lawisa suma ba wani karban arziki ne na samu a gurin su ba.
Na fito na shiga dakin Inna ta na samu kannena zaune suna dan hiran su, suna gani na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login