Showing 45001 words to 48000 words out of 373688 words
Chapter 16 - A LOKACIN MUKE BOOK BY ZAINAB .I. MAKAWA.txt
ta dawo gida ko ?
Baba yace kaji haukan ki ke nan ke wallahi yanzu don duniya su zage ni lauratu yarinyar nan jiya jiya da dawowan ta ace wai yau da safe har ta fara fita diban ruwa a rijiya.
Ki tuna fa mijin ta mutuwa yayi ba wai rabuwan dadin rai sukayi ba dashi da har haka zai kasance da ita.
Ya tako har kofan inna yana cew ke kama min bakinki ruwa dai ne nace bazaki diba ba su zauna haka ba ruwa in sai kin fita diban masu shi.
Maganan baba yasa na dan sasauta kukan da nakeyi tare da share hawaye na zuciyata yai min wani kololon bakin ciki dashi.
Mama tace aiko zaku ga tsiya a gidan nan don wallahi daga ita har uwarta ba yaron da zai debo min ruwa su taba shi.
Can bayan ta dan lafa fadan ta naji sallama a kofan dakin mu take na sheda muryan mai shi nace wa nake gani kamar habib.
Yace nice Anty naje can gidan shine akace min wai kin dawo nan yakarasa shigowa dakin yana zama tare da dan share hawayen shi dake zubo mai.
Nima kukan nake sai da mukayi mai isar mu wanda kowa da abinda ke damuwan zuciyar shi wanda idan mun hada damuwa guri daya zai dawo akan sanadin rashin Alhaji a tsakanin mu.
Nice na fara kawar da shirun da cewa yau habib ka tashi ka fita idan ka samu mai ruwa ka kira min na saya ina son nai wanka yace bari dai na debo maku anty.
Wanan randunan ne za, a cika ko na waje ?
Nace zaka iya kuwa Habib don rijiyan na da zurfi fa sosai yace zan iya mana anty ai kayan ba yawa ya dauki abin diban ruwa yafita daga gidan.
Lokacin mama tana nan ta hake ruwan da aka debo mata mayawa uku tana jiran mu taba tai muna cin mutunci akan shi.
Don daren jiya bata bar komai ba a randunan Inna ta don tsaban mugunta dama gadan zare ne ta shirya muna.
Sai ganin Habib tayi yana cika muna kayan ruwan mu gashi da kwazo nan dana ya cika komai na kofan Inna ta da ruwa.
Naje nai wanka nafito na shirya naji shi muka fice zuwa gidan mama Altine don bazan iya zama gidan mu na wuni tare da Mama ba a gidan.
Tana ganina ta shiga nuna jin dadinta na ganina sai dai kallo daya tai min ta fahinci nayi kuka a ranan .
Take cewa haba yar nan yanzu har yau baki daina wanan kukan ba gaki da manyan idanuwa kada kijawa kanki illa fa.
Na kai zaune ina murmushi nake cewa mama ba kukan Alhaji nayi ba.
Nan dai na kwashe yadda mukayi da mama da safe na fada mata komai take cewa kai amma anyi mutumiyar banza wallahi.
Yanzu ita bata tausaya ma halin da kike ciki sai ma nina halin ko in kula zatayi ,
Da tasan ciwon kan ta da ta tausaya maki don itama ai uwace tunda tana da yaya mata mata zaune a daki.
Habib dake jin mu yace anty kada ki damu nai maki alkawari kullun safe da yamma zanzo na cika maku randunan ku na ruwa insha Allahu.
Mama tace kinga ma Allah ya kawo maku sauki ta wanan hanyan kuma ba.
Can muka ci muka sha sai lokacin zuwa makaranta yace min zai tafi sai ya dawo.
Ban shigo gidan mu ba sai da akai kiran magariba ashe wai mama takiba su Inna abincin rana a gida sai dan dabara mama tayi tabawa kanne na sukaci.
Kamar wace ke jiran shigowa na sai ta hau bakin ta tana cewa ni dama nasan ai asoye da mutum wanan mutuwar don gashi har an fara yawon zawaeci ko.
Bamu kulata ba muka shige daki sai da dare ya dan yi na kwanta abina na barsu nan suna harkokin su.
Washe gari ban shiga gidan mama ba sai da na hada kayan Innata dana kanne na na wanke su fes na shaya na bar gidan.
Ganin har kwana biyu mama ta hana ma inna ta abinci yasa na fito da kudi dake hannuna na aiki habib ya sayo muna kayan abinci a kasuwa.
Nai sa,a mama bata gida muka shige da abin mu daki muka boye nace wa inna ta daga yau basai kin tsaya jiran na gida ba ki girka abinki kuci ke da yara kada yunwa ya illanta ku.
Da yake mama bata da kunya da inna tai abincin ta ta kwashe bata tsaya tambayan na gida ba ranan.
Don gurin mama Inna ta take karban komai na girki kamar yadda wasu matan hausawa sukeyi komai sai dai mace ta karba a hannun uwar gida idan zatai girki.
Haka ranan mama ta hake mama tazo karban kayan girki tai mata wullakanci yadda ta saba yi mata.
Amma sai taji shiru bata zo ba kuma gashi tayi girki kamshi ya bure ta ko ina dama kuka ne da dadddawa sai magi take karba gurin mama din .
Amma yau mama kamshin lafiyayyen girki take ji tana mamakin haka ba dama kuma ta tambaya don tasan akwai magana jiran baba ya dawo takeyi.
Inna ta sa yaran ta daki tabasu abinci suka ci suka koshi tai masu wanka suka shige ciki.
Itako bata girka ba wai ala dole Inna ce da girkin gida itace zata girka masu suci ita da yaran ta takwas.
Shigowa na gida daga gidan mama Altine dana taya ta aikin kuli kulin ta yai daidai da dawowan babana daga kasuwa.
Yake tambayana Rahama daga ina haka da wanan magariban nace ina gidan mama altine muna aikin kuli kuli da ita.
Yace hakan yana da kyau don zai rage maki kewa ai da zaman gidan da zakiyi na kwana biyu kafin Allah ya kawo maki mijin aure.
Muna nan zaune inna tana labarta min yadda mama take ta leken ta da take girki sai muryan baba mukaji yana kiranta ta kawo mai abinci.
Ba bata lokaci ta dauki tuwon masaran da tayi da miyan danyen karkashi ciki takai mai.
Ya zauna ke nan zai fara ci sai ga mama ta uso gurin tana zuwa ta jaye kwanukan abincin a gaban shi cikin hasala ya dago kai yana cewa yaya haka kuma ?
Tace ni za, a kawowa barkado a gida anshirya makirci ni na dama mutum na shanye indai gurin barkado ne.
Yace da akayi may tace wanan makiran matar taja bata girka tabamu ba duka gida shine kai zata girka ta baka daga kai sai diyan ta kawai iya bakin ku.
Mu may take nufi damu da bata bamu namu abincin da zamuci ba sai kai.
Kafin baba yai magana Inna ta take cewa kamar yadda kwana biyu kika hana min ni da yara na muci musha a gidan nan don kina bakin ciki da zaman mu cikin ku haka nima yau na girka na hana maki.
Lauratu may yai zafi haka da har zaki hana masu abinci a gidan nan ita da diyan ta.
Sai mama tace saboda ba yar aikin su nake ba nan ruwa a debi ka daurewa karya gindi wai Rahama bazata dibo ruwa ba waye dan aikin su.
Tsaki yaja yace amma anyi babban kwabo ke kan baki san girman ki ba wallahi ko .
Ashe ke kika fara an maki kuma kice kinji zafi tace zafin may abinci dai ne idan bamu ci baka cin shi kai ma indon ka akayi shi dama.
Inna tace idan kin hana mijin ki ci ki bani abinci na na mayar daki don kada ki fara ki ce zaki taba min abinci ko yanzu duk a rikice a gidan nan.
Tasan bata in ma Inna ta kuma tunda taji ta fadi akwai tsiya ke nan ranan don Inna ta hau.
Tace sai dai ki dauke shi amma bai cin shi Inna tace ai tunda yaci naki wanan ma kamar ya gama cin sa ai.
Ina daki ina sauraren draman su nace oh ni ko yaushe iyayyena zasu daina wanan kishin kauyen nasu haka ?
Gidan Alhaji da nai zama sabuwa ce kawai mai irin wanan matsalan a gidan ita kuma anfi karfinta bata samun yadda take so tayi a gidan.
Nan naji Inna ta tana cewa indai ni zan girka kuci keda diyan ki a gidan nan daga yau na kashe yi sai dai mu zauna da yuwan idan Allah ya bani abinda zamuci sai muci.
To, wooo yanzu nagane da kyau watau makiran diyar ki ta dawo gida irin mulkin da taje gidan Garbati ta kafa tasa aka raba talle shine tadawo muna dashi nan kuma yanzu ko.?.
Don kuji dadin cin karen ku ba babbaka ko ta baki isa ba wallahi Asiya.
Inna tace idan ma na usa ko ban usa ba ai yanzu ki gani na gaji da wulakancin ki gidan nan abu ba abu ba sai kice zaki horani da yara da yunwa to nagaji wallahi.
Baba yace ku dakata ni kan banda karfin raba maku tukunya nakawowa wanan nakaiwa waccan idan zaku gyara ku gyara yafi maku sauki.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, ,
IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH DON CIN AMANA NE YIN HAKA, , ,
Sanye take a cikin kayan sanyi irin na kasan turawa rigan yakai kusan gwiwan ta hakanne ga mijin nata kamar yadda tasaka kayan tare tsananin sanyin da akeyi a garin.
Yana rike da ita a kafadan shi suke saukowa daga matakalar benen gidan nasu wayan shi ce dake aljihun shi ta ruri a lokacin yadan tura hannun shi cikin aljihun shi ya ciro ganin wacce ke kiran shi a layin yasa shi daukan wayan nata.
Sai da ya sauke wani irin ajiyan zuciya yake cewa yaya akayi ne zulfa ?
Jin sunan wacce ya ambata yasata zare jikin ta daga nashi a hankali, tafara tafiya tako biyu zuwa bakin dayan kujeran dake falon.
Ta zauna tare da tsura mai ido daga inda take a zaune daga jin yadda yake magana ta tsigan lalashi ta san fitina ne ake da shi ga wayan.
Can taga yayi dan murmushi a fuskan yana cewa ke ma ai uwarsu ce zulfa don haka kiyi yadda ya kamata dasu mana.
Kofa likita bamu samu gani ba tukun ki ke wanan zance haka idan mun gama ai zamu dawo ne ko.
Bataji may tace dashi ba sai dai murmushin da taga yayi a fuskan yake cewa wata rana kema ai zaki bar naki a gurin ta ko ?
Don haka ki yi hakkuri kifitar da komai a ranki ina diyana diyan ki ne kema koda ba, a gida kike ba.
Can taji yace kwarai da gaske zulfa aiko ita kun san dalilin zuwan namu wannan lokacin ko.
Shiru ya dan ratsa falon yana sauraren mai maganan ta waya har ta taji shi yana cewa ok shike nan sai mun yi waya anjima ke nan.
Ya kashe wayan tare da dago kai yana kallon inda take zaune, ya dan yi murmushi .
Ya zauna gap da ita yana cewa yaya tafi mana ko kin kuma zauna anan ?
Ta dago idanuwan ta fuskan shi a cikin damuwa take cewa dashi akan yaran take magana ko ?
Bai bata amsa ba don yasan ranta zai kara baci ne ga banza yace tashi mu tafi ko ?
Da kyat ta mike tsaye ga dan matashin cikin dake a jikin ta ya turo a cikin rigan dake jikin ta.
Rai bace take magana tana fadin kaga abinda nake gudu ke nan tun farko nace ka bari na kai su gurin hibba su zauna har mu dawo amma kace wai a barsu su zauna agida tunda akwai mutane.
Ya jawo hannun ta yana fadin ke ma dai kin san bazan lamunci ina da gida da iyalina a ciki kuma na dauki diya na zuwa wani gurin ba.
Tace idan baka yarda an kaisu wani wurin ba ai gashi kana shan korafi akai ni dai tsorona kada a cutawa yaran da basuci ba basu sha ba kan zancen mu.
Haba Sa,ade Zulfa ce zata cutawa yarana kuma kada ki manta fa a matsayin yar uwa take a gareni fa.
Tace a da ke nan yanzu kan ai a matsayin diyan kishiya take daukan diyan ka gare ta.
Kofa ya bude masu suka fito daga gidan wani sanyi ne ya daki fuskan ta amma ba yadda ta iya dole haka zasu fita duk da tsananin sanyin da akeyi a garin
Don fitan ya zama masu dole sai sunyi shine dole zai sata fita a hakan.
Bayan sun gama da asibiti ne suka wuce zuwa wani shago nan ta dan yo sayayan abubuwan da ya dace ta tsinta har da tufafin yaran ta dana yaran abokan zaman nata.
Ko da suka dawo gida a gajiye take don bata da kuzarin da zata dinga tafiya haka mai nisa a jikin ta.
Zama yayi kasa a daidai kafan ta ya dan fara matsa mata su a hankali tana jin dadi hakan har cikin ranta ta dan fara lumahe idanuwan ta a hankali.
Haka yasa ta samu saukin yadda take ji a ran ta a lokacin sai bata samu wani matsala komai ba ga yadda take zato.
Washe gari ta riga shi sauko wa kasa don ta karya saboda yace yana son ya dan kara barci.
Har sai bayan ta gama ne sai gashi yau sauko kasan a lokacin har yai wanka yana saye a cikin kananan kaya a jikin shi.
Sau daya ta daga kai ta kalleshi taci gaba da duban wayan ta da takeyi tana murmushi a fuskan ta.
Da alama hiran da takeyi yana mata dadi a ran ta lokacin ya iso inda take yana cewa madam yaya jikin naki ?
Ta dan dago kan ta a hankali ta dube shi tana cewa Alhamdullahi ya kokari bai amsa mata ba sai da yakai zaune yace kokarin yiwa kaine ai nidai gurina naga Alllah ya rabaki da wanan cikin na jikin ki lafiya.
Sai lokacin tabar abinda take a wayan ta ta dago kan ta ta dube shi inda ya zauna sai suka hada ido dashi tayi saurin kawar da idon ta cikin nasa .
Yace No no no kada ki soma yi min wanan kukan naki dake tayar min da hankalina please ?
Yace cikin kamo hannun ta zuwa na shi cikin girgiza mata kai yake fadin ki dinga sakawa zuciyar ki dangana Allah daya baki ciki a cikin wanan halin da kike yasan dalilin yin haka a gare ki.
Don haka ki zamo cikin bayi masu rugumar kaddaran ubangijin su ako da yaushe.
Wanan tayar da hankalin da kikeyi zai iya kara jefa ki a cikin wani sabon tashin hankali kuma har mu dake tare dake abin ya shafi zukatan mu.
Ajiyan zuciya ta sauke tace dole na daga hankalina idan na tuna da lalurar dake tare dani sai ga shi kuma wanan cikin yazo ya shiga again.
Murmushi yayi tare da jawo ta ajikin shi yana dan shafa bayan ta yake cewa lafiya lau zaki haihu insha Allah ai ciwo ba mutuwa bane.
A hankali tace dashi abin ne ke bani tsoro sosai sai yake hanani sukuni a raina.
Ya girgiza mata kai yace ai abin bada ga nan bane heartbeat ke dai Allah ya kawo muna sauki ga al,amarin.
Sai da ya tabbatar ta kwantar da hankalin ta ya mike yana cewa zai dan fita amma ba zai dade ba indan ya fita.
Nan ya fice ya barta zaune zuciyan ta cike da tunanen yan diyan ta biyu dake gida Nigeria gurin kishiyan ta.
Tun ba akai ko ina ba gashi ta fara jin Zulfa din ta bugo waya tana korafi akan rikon yaran nata gashi zasu iya share wata uku basu koma gida ba.
Shine dalilin da tun farko taso zuwa da yaran ta ko tabar su gurin yar uwarta amma sai ya nuna mata rashin yardan shi ga hakan .
Don shi mutum ne mai matukar son iyalin shi a kusa dashi akoda yaushe haka ne yasa akwai shakuwa sosai tsakanin shi da italin shi don yana fitarwa kowa da hakkin shi yadda ya dace.
Wanan zuwan da sukayi dashi ba itace ya dace tabiyo shi ba amma saboda dalilin rashin lafiyan ta yazo da ita din.
Wanda kafin su zo saida akakai ruwa rana da sauran kishiyoyin nata akan basu yarda da hakan ba don acewa su yafi nuna kulawan shi akan Sa,ade da yaran ta bisa gasu.
Don har kara suka kai shi gurin iyayyen su kan abinda yake shirin yi masu.
Ita bata da ko labari sai dai ta fahinci ya dauki zafi da sauran matan nashi a lokacin.
Ita da ake abin akan ta sai daga baya ta fahinci rigiman akan tafiyan su ne akeyin sa.
Haka ne ya dan haifar mata da rashin natsuwa a tare da ita don haka ta bukaci da ajaye tafiya sai taga likitan ta na nan gida Nigeria.
Amma amma mijin tana yaki janye zancen ba irin rokon da bata mashi ba kan ya barta amma sai yaki yarda da bukatan ta.
Karshe ma cewa yayi da ita idan ke lafiyan ki bai damay ki ba ni ya damay ni tunda bake ce keda hasara ba ai .
Hakkuru ta bashi don yadda taga ya hau tasan itama zata iya samun nata rabon fitina a ciki don haka taja bakin ta