Showing 72001 words to 75000 words out of 373688 words

Chapter 25 - A LOKACIN MUKE BOOK BY ZAINAB .I. MAKAWA.txt

shi tare da dora daya akan daya yana rike da wayan shi yana dubawa.
Da alama abinda yake a wayan yai matukar dauke mai hankalin shi sosai a lokacin
Anty ce na hango ta kishingide a saman dayan kujeran da yake zaune jingine akai.
Tana amfani da remote a hannun ta gurin canza channels din tv dake aiki shi kadai a falon da alama tagaji da inda yakai ana news .
Kallo daya nai ma inda yake zaune ban iya kara daga kai na koma kallon shi ba, saboda tsaban kwarjin da yai min a idona ga kuma hallita mai cikar zati a tare dashi.
Zaka rantse da Allah kace shi din ko saurayine bai ma taba aure ba balle har tara mata har uku haka a gidan shi.
Jin na shgo falon yasa anty dago kai tana murmushi take cewa Ramana ga baban su ku gaisa ko.
Tun dazu da ya dawo bai samu zama ba sai yanzu ya samu kan shi, gashi yaci abinci sai faman satin tuwon ki yake yi wai ya dade bai ci tuwo mai dadi haka ba.
Murmushi nayi nace kai anty kila ma bai yi dadi bane kike zolayana ko ?
Fuskan shi a dake duke ya dago kai yana murmushi tare da kallon inda nake lokacin har na kai durkushe ina fadin sannu da dawowa daddy.
Yace cikin murmushi yaya na samay ku ? sannu da fama fa ina tajin labarin ki ta waya wurin yara kullun idan muna gaisawa dasu.
Sunce yanzu anty tana masu sallah kullun kuma kuna hadda a tare da su don sun karanta kuma na gamsu sosai da karatun su.
Na murmusa tare da dukar da kaina kasa ina wasa da yan yatsun hannuna a hankali nace Alhamdullahi.
Yace ban da abinda zance dake sai godiya don kinyi matukar kokari gurin taimakawa iyalina da bana nan.
Cikin murmushi nace ai yiwa kai ne balle ma ai ba wani aiki don yaran na da saukin kai sosai.
Ya dan murmurmusa karo na biyu tare da juyawa inda matar shi take zaune yace lalai wanan anty kan akwai sa,a ance harda nasir ta san yadda take zama dashi ai kinyi kokari.
Na mike tare da cewa Allah ya hutar da gajiya yace Allah yasa na juya tare da fara tafiya zuwa ciki.
Muryan anty ne kewa dani Rama dawo ki kwashe kayan nan ki shiga dasu ciki cup ne da goran ruwa da akasha.
Muryan shi naji yana fadin ashe ba wata babba bace yadda na dauka wanan ta ma kai 18 kuwa ?
Tace yanzu dai take seventh don ko da ta gama makaranta kasan irin karatun su na kauye ne ai pushing din mutun din nan don kokarin shi.
Ni dai nai simi simi na kwashe kayan zuwa cikin kitchen na barsu nan suna magana a kaina.
Yace wa matar nashi yanzu yar wanan abar ce kike nufi an tabawa aure ?
Tace sosai kuwa mutuwa mijin yayi don ba yaro bane zai haifi sa, ata ma gaskiya.
Ikon Allah wani magana sai kauye ba tausayi ba sanin human right ko kadan a kauye.
Anty tace ina son na mayar da ita makaranta taci gaba da karatun ta don tana son karatu a rayuwan ta.
Yace dakin kyauta gaskiya don yarinyar na da hankali na gani tace ai Rama akwai hankali sosai wallahi.
Sai da safe dana shiga gaida anty bayan tafiyan yara take fada min wai matan gidan ai sun dawo jiya cikin dare.
Da maki na ce da ita ashe sun dawo gidan ya cika kake nan yanzu?
Tace kin san su da naci kamar masu jiran saukan shi sai ga kowace an dawo da ita daga gidan su a cikin dare.
Har uwar yesmin tazo cikin dare don fitina wai a bata yarta a gurin ta zata kwana sai da maigidan ya tsawata mata.
Ni dama ya bari na bata yar ta tun daren kowa ya huta haka ko kwasa fitsari ai ya ishi mutane ma.
Ni ba don Allah ya kawo min ke ba da ban san yadda zan kwashe da rigiman yaran nan da ya bar min ba.
Yasan kuma ba lafiya ke gareni ba gashi fitinan su ya hana ko yar aiki a bar muna a gidan ko mutum yaji dan sanyi.
Don haka don Allah Rama kafin su dawo ki hadawa kowa na ta ya na ta su koma wurin iyayyen su kema kya huta ai, da wanan wahala tunda su basu san wahala suka barwa mutane ba ma.
Inda sune ai ba zasu dibawa mutum nashi ba kamar yadda yaran ke samu kulawa a nan yanzu.
Nan take bani labarin tafiyan ta da yadda ta dawo ta samu yaran ta hannun su tace shine take ganin dalilin barin su gidan da sukayi.
Ta tabe baki tare da komawa ta kwanta tana cewa nasan shine dalilin jin haushin da yasa tazo cikin dare wai a bata yar ta ta tafi da ita gurin ta.
Nace ai da abari ta tafi da abinta ba shike nan ba kowa ma ya rike nasa a zauna lafiya.
Tace wallahi fa kedai Rama ba su da mutunci fiye da tsanmanin ki don sun samu daurin gindi a gurin sarakkan mu ne.
Dazu bakiji yadda hajiya tazo tai min tas ba a gidan nan saboda sune kuma tai min haka.
Ai indai kina gidan nan zaki gani don kullun aikin ke nan su basu laifi sai nice bare a cikin su nice mai laifin don Allah ya jefani cikin su.
Nace anty dama yan uwan shi ne yake aure ? tace eh kusan hakane don ita hindatu yar uwan hajiyan shi ce.
Ita kuma zulfa diyan amininahaifin shi ne da suka dade suna tare tun kurciya suke tare kinga ke nan ai sai ace duk yan uwan shi su biyu din.
Nace cabdi amma kina fama gaskiya anty tace bari ke dai to yaya na iya da raina Rama ?
Ganin ta kwanta na juya zan fice dakin take cewa dawo kiji, da sauri na juyo ban tafi ba tace daga yau wanan girkin wahalan ya kare koda yake ma ina ganin nan da two days zamu bar gidan nan kowa ta kama part din ta daga ita sai nata babu mai ganin wani cikin mu
Amma dai duk da haka yau abinda zamu ci kawai anan ni daku zaki girka muna yau din.
Nace to anty na juya na fita tare da rufo mata kofan dakin don nasan barci zatayi kila.

****** ********* ****** ******
Mama Lauratu ne zaune da yaran ta dukkan su uku sai baba da ke gefe daya zaune saman tabar ma yana sauraren abinda zata fadi.
Can ta sauke ajiyan zuciya tare da cewa ina son ku saurare ku fahinci may nake son fada maku a gurin nan.
Bawani magana ba sai maganan kaddaran da ya samay mu a gidan nan wanda ba kowa ne ya jawo muna shi ba sai Rahama da uwarta don sune suka cuce mu haka?
Haba mama in zaki magana da kika tara mu kiyi muna amma ki bar kawo muna zancen mutanen da basu san arziki ba a rayuwan su.
Rukaiyya ce ke wanan magana cikin hasala tana kokarin dakatar da uwar tasu da ta fara masu dogon sharhi.
Mama tace cikin sanyin murya na dauko maganan ne yadda zaku fahince ni da kyau amna tunda baku so bari naje kan maganan da nake son fada maku.
Ke Lawisa dai yau Allah ya nufi auren ki da Jatau na hayin dutse don haka Allah ya kadda, , , ,
Kafin ta karasa Lawisa tai but tace wata Lawisan mama ba dai ni Lawisan ba kan ?
Daga inda baba yake zaune ya karba da cewa ke ko Lawisan don an daura auren ki da Jatau bisa ga sadakin da uwar ku ta karba a hannun shi da niyan bashi Rahama Allah bai yi ba.
Baba na shirin ci gaba da maganan shi ai Ihun da Lawisa ta sake ne ya hana shi ya karasa zancen shi.
Lawisa ta dinga kuka tana durawa iyayyen ta ashar tana bata ga dan kazan abu kaza ba da ya isa ya daura mata aure da Jatau ba.
In gaskiya inta mama ta kashe auren ta ita da taci kudin shi taje ta aure shi mana.
Amma ita don ba a sonta shine za, a cuce ta a hada da wanan kazamin tsohon ace wai shine mijin ta.
Nan suka shiga lalashin ta amma ina kamar kara zugata sukeyi ai a lokacin.
Suma su Rukkaiya nan suka shiga fadawa iyayyen bakar magana son ran su ba wanda ya iya magana a cikin su sai sadda da kai kasa da sukayi kawai.
A take baba ya tuna da auren da sukai min na Garbati bani so amma dani da uwata ba wanda yaji bakin mu haka aka kai ni salin alin mun danne zuciyan mu dani.
Yau gashi diyan mama diyan da yake son su kamar may a ran shi gashi yadda suke masu cin mutunci a bainan jama, a kowa naji don har sun fara tara masu makwabta a gidan don ihu da Lawisa ta yanka ya jawo hankalin mutanen shiya.
Basu kai ga ci gaba da magana ba sukaji dir mota sai ga wasu mata biyu sun shigo gidan suna fadin sun zo daukan amarya ne Jatau ne ya turo su don su yan uwan ango ne Jatau.
Nan su Rukkaiya suka shiga zagin bakin suna masu rashin mutum ci sai da kyat ranan baba ya gwada masu ta maza haka suka shuga daki da ita tana shiri tana kuka.
Ga shi mama sunyi fada da aminiyar ta Larai babu wanda zata nufa a makwabta takai kukan ta.
Mama ta shiga daki cikin sanyin jiki tana cewa Lawisa kiyi hakkuri nasan amanane ya koma muna akan ki tun ba aje ko ina ba gashi Allah ya nuna min abinda naso yiwa yar wata ya fada kaina.
Nasan na cuce ki na cuci rayuwan ki abinda Allah ya kaddaro muna gani ke nan wanan daren a kan ki
Ki daure kije gidan nan don rufin asirin mu da na ki don kin san Jatau ba mutunci ne dashi ba.
Kan kudin nan yana iya ya daure ni har uban ki ko ya sayar da dan gidan nan da muka mallaka a duniya.
Muryan daya daga cikin matan da suka shigo daukan amarya ne ke cewa ayi a fito da amarya mai akori kura yace zai tafi jigilan shi ne.
Yau abinda mama ke son gani a gare sai gashi a kanta burin mama shine ko yaushe tagan mu ni da mahaifiyata a cikin kuncin rayuwa.
Idan ta gan mu a haka takan ji duniya yai mata dadi kamar ta zuba ruwa kasa tasha ta kanji a lokacin.
Haka aka fito da Lawisa zabban tausayi tana kuka tana tirje tirje aka kada ta a mota sai tabarma da filo da mama ta bayar aje mata dashi tace daga baya zata sayo mata kayan aiki a kawo mata.
Aka fito da ita sai guda yara da manyan uguwa suke yi yan gulma suka shiga motan zuwa kai amarya gidan mijin ta.
Lawisa sai kuka takeyi a gaban mota zuciyata fam da bakin ciki tausayin kan ta takeyi yadda zatayi rayuwa da tsoho irin jatau a matsayin mijin ta.
Haka aka isa gidan da ita tana matsanacin kuka suko mata sai guda da shewa sukeyi yayin da Lawisa take jin kanta kamar tana cikin kabari ne a lokacin.
Allah ke nan yadda sukai min sai gashi ya mayar masu da abin su tun a nan duniya sunga kayan su.
Har gara nawa akwai rashin sanin ciwon kai da kurriciya a tare dani lokacin kuma gara nawa mijin sau dubu da nata ita.
Wani rubaben daki daya gyara mata shi nan aka saka ta daga ita sai yar tabarman kwancin ta don ko katifa bata samu ba a lokacin.
Yan uguwa sukai mata nasiha yadda manya keyi idan an kawo amarya yi nayi bari na bari a zauna lafiya kiyi biyayya ga mijin ki da matan shi sai a zauna lafiya da kowa.
Daga can kofa sukaji wata tace kada Allah ma yasa tayi mu ai nan ko da may tazo mun fita gidan Jatau ne fa ta shigo.
Ashe daya daga cikin sarakan gidan ne tazo ganin gulma taji ana wanan nasihan ta cabe da bada amsa.
Su dai basu tanka mata ba suka fice gidan suka barta zaune saman yar tabarman ta ta hade kai da gwiwa tana rusan kuka sai Allah ya isa take aikawa mama da baba a lokaci daya



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: A Lokacin ne,,,,

IDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA YAR UWA DON HAKKIN WASU NE,,,



Zaune take a kofan dakin ta tai tagumi sai faman tunane take tana kulawa tana warwarewa ita kadai a gidan don mijin ta ya fita tun safe zuwa gurin aikin saukalen da yakeyi gurin manyan motoci ,
Sai idan ya dawo ne suke dora girkin abinda zasuci kullun a haka suke wanan rayuwan wahalan ita da iyalin ta,
Yanke shawara tayi a inda take zaune gara ta hada kayan dakin ta ta,sayar ta,dan samu koda tsohon fridge ne ta,saya tana sana,an kayan sanyi ko zata samu kobo yana dan shigo mata a hannun ta,
Ba bata lokaci da mijin nata ya,dawo gida batai nauyin baki ba tafara fada mai shawaran da ta yanke,
Shiru yayi tare da nisawa inda yake zaune saman tabarman shi, da yake shan iska a kai, yace
Halima banki shawaranki ba gaskiya amma ni a nawa tunanen da kiyi hakkuri ki zauna da kayan ki don wanan lokacin da muke ciki lokaci na lahaula ga kowa ba masu kudin ba ba tallakawan ba kowa wiwi yake yi da wanan karnin,
Koda kin sayar da kayan dakin ki don kiyi sana,a ina mai tabbatar maki rayuwa bazai bari ka mayar da ko kwatankwancin abinda ka rasa ba a baya kinga hasara da dana sani sai ya hau mutum,
Ke dai kawai ki bar kayanki tunda Allah bai hana muna dan abinda zamuci ba a rayuwan mu to ai alhamdullahi komai yanzu sai hakkuri don ba kowa ke samun yadda yake so ba,
Matar tanisa tace ni dai gaskiya nayi niyya da kabarni kawai na sayar a samu, dan gurin rage wani hanyan kuma.
Ya fahinci bazata dauki shawaran shi tayi hakkuri da jarabbatar talaucin da suke ciki ba don haka sai ya kyale ta tayi yadda take so kawai.
Don yanzu ba matan birni ne kawai ke bijirewa girmama wa dokan mazan su ba har ma da matan kauye haka suke don yadda zamani ya juya a lokaci ne muke ciki,
Bai gida washe gari baya gida takira dillaliya sukai cinikin kayan dakin ta tazo ta kwashe akan dan kudi kalilan tabar mata su,
Ba bata lokaci ta hada kudin tana jiran dawowan maigidan ta ta fada mai ya barta taje ta dan samu abin da tai niyar saye da kudin,
Bai mussa mata ba don yasan kudin ta ne don haka ya kyale ta tayi yadda take so da abinta don yana gudun yai magana ta ga kamar yana son wani abune daga cikin kudin, nata.
Bata tsaya bayan sallah magariba ta shirya sai gidan wata dillaliya mai sayar da kayan hannu, inda tai sa,a tasamu fridge har guda uku a gidan da akasa a kasuwa nan sukai ciniki ta samu dan babban wanda bai tsufa ba sosai ta saya da kudin nata,
Suna barin gidan ta turo mai baro ya daukan mata shi zuwa gida zuciyar ta fam da farin ciki a ran ta,
Da mijin nata,ya,dawo yai mata fatan alheri da,daukaka a cikin al,amarin.
Tun daga wanan lokacin ne tafara dan sana,a da fridge din nata tana dan samun kwabon kashewa ta fannin ta ita ma,
Hakan ne ya kawo mata saukin yan damuwan yau da kullun da take ciki don tana dan samun kudin kashewa a wanan fannin nata.

****** ********* ******
Safiyane duk jama,an gari sai faman zirga zirga suke kowa harkan ga ban shi yake yi ba mai kama hannun yaro daga cikin su.
Sai faman sallama ake a gidan gwago Asmau da manyan kuloli gurin sayen masan da take soyawa tun da farar safiya.
Gwago Asmau taji dadin kasancewar Bintu da ita a yau din don ba karamin taimaka mata takeyi ba.
Komai cikin natsuwa Bintu takeyi ga tsabta sai ta wanke hannu da da kayan aiki kafinta taba shi,
Sannu sannu tafara gyara ma gwago aiyunkan ta sabanin yadda take aikin ta a baya in local way,
Bintu taba gwago shawaran cewa ta mayar da masan ta na zamani don yanzu akasarin mutane suna fama da lalurar ciwa gyambon ciki watau ulcer,
Gwago Asmau tai mamakin yadda Bintu karama da ita tasan wanan dubara gashi kuma daga kauye take zaune,
Don Bintu ta bata shawaran cewa yanzu da safe zasu dinga kai nika kuma su toya shi, a lokacin,
Gwago Asmau tace kai haba Bintu ni kada ki jawo min hasaran kudi yaya zaki ce na kai nika ranan kuma na soya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login