Showing 6001 words to 9000 words out of 373688 words

Chapter 3 - A LOKACIN MUKE BOOK BY ZAINAB .I. MAKAWA.txt

dashi gida amma mama tana gani ta kwace ta rabawa yayan ta lokacin ni kadai ne a gurin inna ta ban da kanne baya na.
Wassh nace don jin zafin kan da anty taja min da karfi tace yaya akayi kuma nace babu komai idanuwa na sun ciko da hawaye da zata gani kila zata barni don akwaita da tausayi sosai.
Tana gamawa ta sa asayo mata clean ta wanke min kan tas dashi sai da naji wani iska yana shiga na sosai acikin kaina.
Mun zauna tafara min kitso ke nan sai ga Rakiya diyar mama tashigo babu ko gaisawa tace to akwadaita mama tana kiran ki.
Nace cikin daure jin zafin kitso kice kitso ake min gani nan zuwa idan angama min.
Tace mama tace tana kiran ki shine zakice wai ana maki kisto ne barin je na fada mata kince bazaki zo ba.
Anty tace bari na sake maki idan kin dawo sai mu karasa ko ?
Nace taci gaba don nasha zafi daya yanzu idan na tafi bazata bari nadawo maza ba.
Ban tafi ba Rakiyan ma bata dawo ba daga sakon har aka gama min kitsona nai wanka wasu kaya daga cikin tufafin ta sun min yawa sosai amma haka tasa na saka su na fito wata shar dani.
Sai da na gama komai na kama hanya na nufi gidan mu nan na tar da balain dake jirana na mama.
Ina sallama tako haukaina da balainta tana fadin mai kwadai baji dadi ba wallahi yanzu don kina isar sa ke kinga gurinci shine na aika kizo kikace ace min bazaki zo ba sai kin gama kwadayin ki ko.
Bari mahaifin naki ya dawo gida yau ai ayita akare don wanan abin baku kadai da uwarki za, a zaga ba harni sai an hada dani an muna suna indai kauyen gane.
Kuma ki tafi ga diban ruwa can yana jiran ki tunda babu bawan ubanki da kika aje da zai debo maki ruwa ai aiki dashi.
Ban tanka mata ba don nasan ko na fada mata yadda mukayi da Rakiya ba yarda zatayi ba.
Kayan jiki na na cire na daura tsuman zanina na fara diban ruwan don nasan idan banyi har inna ranan sai ta yabawa ayya zaki.
Saida na cika mata randunan ta na fara cika na Inna na don ban isa na fara zuba a namu ba naja bala,i kuma.
Ban koyi rabin randan mu ba sai ga Lawisa tafito da roba tana diban ruwan rabi a cikin roba rabi a kasa .
Kasa daurewa nayi nace haba lawisa wanan ai hainci ne idan ma zaki dibane ai ki tara roban dakyau mana amma kina diba kina zubarwa akasa don baki san wahalan diban ruwan ba ko ?
An zubar din ko zaki hanani amfani da ruwan ne kuma tunda wuyanki yai kwari yanzu ya isa yanka don kina ganin kina hurda da yar birni ana hure maki kunne kiwa mutane rashin kunya.
Nace ashe hurda da yan birni isa ne ai ban san kina hassada da hakan ba sai da kikai magana yanzu?
Kafin tabani amsa sai ga mama tafito daga dakinta tsagal tace eyye Rahama lalai kuwa ashe wuyan ki ya isa yanka yanzu yarki kikewa shamaki akan ruwa don ta diba.
Saboda kina kurin kece kika debo ko may ai kafinki fara diban ruwa su suka fara kuma akai amfani dashi.
Kamar ince bako ga Inna ta ba don da wayo na akai fadan ruwa agidan mu wai don may babana yake debowa innata ruwa.
Kuma alhalin ita bata bari yaranta su diban ma Inna ruwa anata randan haka inna zatai ta zama ba ruwa koda kuwa girkin gida ne zatayi.
Tun ranan baba bai sake diban wa inna ta ruwa ba sai dai ta dinga tarataran yaran mutane suna dibo mata.
Tun ban kai munzalin iya jan ruwa arijiya ba dole haka na fara zuwa bakin rijiya wanda yaga Allah ya taimaka ya zuba min har na samu Inna ta dan samu na aikin ta.
Muryan mama ne ya katse min tunane na tana fadan ta da cewa yanzu don kinga kin girma kin iya hassada da kyashi irin na uwarki shine zaki hana ai amfani da ruwan ko ?
Ni dai ban kara magana ba na fita raina bace daga gidan sai magariba na gama diban ruwan a gurguje na shiga naiwa anty sai da safe.
Tana ganina a jiki cikin tsuma babu dadin gani tace yaya haka kuma Rama na ?
Na turo baki gaba nace ba mama bace saida tasa na cika duk kayan ruwan dake gidan mu kuma ban gama ba Lawisa tana diba tana zubarwa nai magana kuma ta hauni da zagi wai don naga ina hurda dake ne nake wa mutane rashin mutunci.
Kai ikon Allah yanzu har nima na samu shiga cikin ran mama daga zuwa na ko ?
Nace ai har yaranta bakin ciki suke da ke wai don naga kin fito daga birni nake lake maki ina kwadayi.
Allah sarki ni may nake baki da zasu ce haka Allah dai ya rufa asiri wallahi shaf na manta da zancen ki da sun ga aikin gaiyya kuwa.
Nafita da sauri na koma gida kada aga na dade inna tai min fada don ni ko tallah naje bani kai magariba koda kuwa ban sayar ba ne.
Sai bayan sallah ishai baba ya dawo daga kasuwan kauye yana jaye da wani dan karamin rago da yasayo daga can kauyen da yatafi.
Baya ya daure ragon wanda ya cika muna gida da kuka irin na dabbobi kowa yasan an shigo da dabba.
Mama tafito daga dakinta tai mashi shimfida inda yake zama yaci abinci ya huta idan ba zai fita ba hiran dare wanda shi ba kasafai yake fita ba don yafi fita ne idan suna siyasa ko wani abu mai muhinmanci a garin.
Bayan ya zauna muka dinga fitowa muna mashi sannu da zuwa wanda zance kusan mu yan dakin mu ne keda wanan halin.
Sai nice nafito karshe don ina sallah koda ya dawo lokacin na gaishe shi na juya zan wuce ne naji Mama tana fadin dama kai nake jira ka dawo tun dazun.
Yace to ai gani kuwa Allah ya dawo dani lafiya cikin ku tace dama akan Rahama ce .
Don dakai da uwarta kun daure mata gindi akan bakuwar birni da tazo don kunga kudi idanuwan ku sun rufe .
Shine take ganin kowa tana iya takawa ta zauna lafiya yanzu wai har na aika don ta samu daurin gindi daga uwar ta tace min wai bata zuwa tana kitsone.
Ni zata gwadawa kitso tunda tun uwarta bata san duniya ba nakeyi a kaina.
Yanzu dai may tayi baba ya katse dogon sharhin data fara cikin tambayan ta ba, asi don baison suyi jidali daita gashi ranan itace da girki a gidan.
Yasan idan yaja zance cikin shi tayi don daren shi ke nan zai kashe a ranan.
Tace ruwa fa zata debo bayan tasan cewa itace da alhakin diban ruwan gidan nan akanta amma uwarta najin amsan da ta aiko min bai sa ta dauki mata ki ba jifa ?
Yanzu ita Asiya da taji abinda tace bata dauki mataki ba akai ?
Tace ta dauka ran yar gwal din ta ya baci ita ma nata ya baci, yanzu ta debi ruwan ko bata debo yar kwal uba ?.
Tace ta debo amma kuma sai rashin mutunci yabiyo baya nan tai muna tas nida Lawisa wai don may tana wahala ana zubarwa jifa wai aikin gidan ubanta ne wahala ?
Ina daga daki daga ni har Inna ta muna sauraren maganan da mama keyi karya da gaskiya .
Cikin bacin rai ya kwala muna kira ni da Inna ta bamu dauki lokaci ba muka fito inda yake zaune.
Tambayan dalilin dayasa Inna tanajin sakon rashin kunyan da na aikowa mama dashi taki daukan mataki a lokacin.
Cikin murya mai sanyi Inna ke magana tana cewa haba malam yanzu don ban da kunya zan saka baki ga maganan yarinyar nan da maman ta ?
Aikuma sai ace nayi rashin kunya kuma baba yace ke nan kina nufin karya Lauratu tai mata ba amsan banza ta aiko mata dashi ba ke nan?
Inna tace ni bance karya yaya tayi ba dakai da ita sai ku dauki hukuncin daya dace akanta basai kun fada min ba.
Au to haka ma zakice ke nan ko ?
Inna tace idan ba haka zance ba ni may kake so nace yar tace tana iya daukan matakin daya dace akan ta duk sanda taso.
Mama tai karaf tace wace ni na dauki mataki abi gari dani ana nazalunci uwa da yar ta don cin amanan dana iya
Sai ranan naji Inna ta ba da amsa mai ingaci da tace uhumm zalunci kan ai sai dai kada a kara don kullun a cikin sa muke raye, sai ranan da mai ramawa zai rama muna idan ba yafewa mukayi ba.
Ai Inna ta na fadin haka da ga baba har mama sukoyo cikin ta da masifa kamar zasu cinye ta danya a ranan.
Wai tayi masu Allah ya isa shi da mama ke nan take nufi akan yar ta na suka sakata gaba da wullakanci kowa yana fadin albarkacin bakin sa.
A take naji jikina yahau tsumi ina ta dan karkarawa daga inda nake a tsugune kamar na tsoma masu baki ga zancen su wata zuciya ta haneni da hakan.
Na rasa yadda zanyi a inda nake yadda ake ciwa uwata mutunci yau akaina gaba daya kwanakin nan baba ya karkare birkicewa akan mama a gidan.
Duk abinda ta fada ya zauna ke nan daram ba canji cikin sa .
Nasan idan na saka bakina ga zancen abin zai kara muni gashi yau alama ya nuna inna ta fara gajiya da halinsu har takai ga fara bada amsa da bakin ta .
Don haka na mike tsam na juya zan tafi daki muryan mamace ke cewa dani ina zaki rasa kunya an sallamay ki ne ?
Bari ta nuna min ta isa mana tunda uwarta ta daure mata gindi inji baba yake fadin haka.
Ke maza shiga daki kada ki dawo gurin nan kinji na fada maki so kuke da ni da ita ku turke mu kuyi muna wankin babban bargo don bamu dagata kuke gani ko?
To bari kuji gatan muni dayara na Allah a gidan nan da duniyan nan kai nagaji da wanan halin cin amana kullun mune dai masu laifi a gidan nan ku bakwa yi.
Idan wani laifi ne ai babu dan da baya laifi ni dan wa nataba kawowa kara duk da urin kuncin rayuwan da ake min a gidan nan ina sa kafa ina takewa daga haka ta juya tabi bayana zuwa daki.
Ranan daga ni har Inna babu wanda yaci abincin dare ba, a ma taya muna balle muci.
Shekaruna da kurciya na bai hanani fahintan ranan Inna tana cikin kunci da bakin ciki akan dalilina.
Daga inda nake zaune takure bakin gadon karfen ta na mike zuwa inda take zaune saman tabarman sallah ta na tsunguna nace.
Nace Inna don Allah kiyi hakkuri duk nice na jawo maki wanan bacin haka da ba don ni ba bazaki shiga wanan bacin ran ba yau.
Batai magana ba sai na kara cewa don Allah Innan mu kiyi hakkuri ki yafe min.
Tace ke nagaji ne da irin cin kanshin da ake min a gidan nan don may har in suna ganin kinyi laifi ne bazasu hukuntaki ba sai sunkirani don raini sun hada dani.
Saboda yana son gyarawa matar raine zai dinga min wullkanci a duk lokacin da ya bushi iskan shi ko may ?
Nagajine wallahi ni may ye yaran yaya basuyi min a gidan nan waya taba jin nayi magana balle nace itace ke daure masu gidin sai ni da aka raina za aiwa cin fuska yadda akaso.
Shiru shiru aiba tsoro bane don sunga ina basu girman su shine zasu dinga takani yadda sukaso.
Inna na kaiwa nan sai ga baba ya daga labulen dakin mu yana fadin ke Rahama daga yau sai yau kada na kara ji ko ganin kin kara hurda da bakuwar birnin nan don ba yar uwarki bace ban san dalilin ki na manne mata ba to na hana wanan hurdan daga yau.
Yana fadi haka a cikin daga murya nasan yana fadi ne don mama taji ya yanke alakata da Anty.
Abinda take muradin gani daji don tasan zamana da ita babban alheri ne ga rayuwan mu idan bata hana ba.
Zama guda ta kashe min kudi haka har jakka sittin ba gaira ba dalili akaina.
Yana gama fadin haka ya juya ya cuce a cikin hasala babu wanda ya tanka mashi yabar dakin dama yayi ne kawai don dadin ran mama takuma ji dadin.
Sai bayan tafiyan shi Inna ke ce wa an daiji kunya wallahi mutum har mutum amma baida ta cewa a cikin iyalin shi sai yadda akace mai.
Hakkuri na kara ba Inna don nasan yau kan ancin ma rashin hakkurin ta a gidan.
Duk da karancin shekaru na ina iya fahintar wasu al, amuran da akeyi a gidan mu wanda ko kadan bai dace ace anyi shiba a tsakanin iyali.
Amma gashi da karancin shekaruna yakai har na fahinci hakan a gidan mu, kai bani kadai ba duk yaron dake gidan mu yasan irin zaman rayuwan da akeyi a gidan.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,

IDAN KIN BIYA KIKA BA WA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YAR UWA, , ,


Tafe nake da robar talla na yau doya ce dafafa gishiri sai kuli, kuli da yaji aciki wana nake barbadawa mutum idan ya saya.
Daya daga cikin tufafin da Anty ta bani na saka wasu material ne masu walkiya walwal idan kana tafiya da su.
Tafe nake nayi irin digirgire din kaya a saman kai din nan hankalina a kwamce nake tafe .
Kai kai kai da sauri dayan mutumin da suke zaune a tare ya juya yana kallon gurin da nafarkon mai magana yake kallo,
Da sauri suka kawar da kan su daga kallo na don na kusa karasowa inda suke a zaune.
Dama yarinyar nan haka take da kyau ashe kamar wata matar gwauna haka da ita ?
Wai may ne ne haka salla ni duk ka cika ni da zancen yarinyar nan yace wallahi ranan da kuke zamcen ta bani kusa sai yanzu nai mata kallon tsab ai.
Garbati idan kana son abinka kawai ka shige kai tsaye nan ai babban iri ne ga wanda ya samu.
Allah na tuba ko kyawawan yaya ake haifa wa mutum a gida ai ya wadatar akan su.
Ni fa ko da kukaji nai magana a ranan ba wai har zuci nake zance na ba amma naga kuna gidada abin haka ku ?
Garbati kada kaiwa kan ka salalalan tsiya walahi in har kana so kasa kai kawai na fada maka kada ka tsaya garin kallon ruwa wani yai maka tsalle.
Kaga dama ina ga ba ai mata wani matsayi ba zuwa yanzu yan uwan tane kawai nake gani suna fitowa hira da dare amma banda ita.
Wanda ake wa fadancin ake kuma zuzuta shi a kaina sai yanzu yai magana yace.
Kai salla, banki ta naku ba fa akan maganan yarinyar nan sai dai gaskiya a yadda shekaru na yakai yanzu sai nake gani ai na wuce tsayawa koda akan yyayyenta ne da kake magana balle ita.
Sannan kaga yarinyar ga ta dai karama ce amma akwaita da kwarji a fuskanta kamar ba karamar yarinya ba.
Gashi kuma bata bada fuska kamar sauran mata ko yaushe fuskan ta a daure yake ba fara, a agare ta.
Sau tari da yawa nakan so na dan mata magana koda na wasa ne amma da na dumfare ta sai naji gabana yana faduwa tana matukar yi min kwarjini sosai a idona.
Salla yace assha Garbati kada ka zama ragon maza mana yanzu kuma manya mata ma mun sha gaban su babu gezau balle wanan yar ficiciyar karamar yarinyar zata kayar maka da gaban ka.
Don haka idan har kana ciki ka bari zan maka iso har gida na gabatar dakai tun wani bai riga ka ba.
Da zaran nema iso a gidan su insha Allahu komai zaizo daidai koda baka zo tadi ba gurin zance sai kawai ayi yadda za,a a daure aure batare da kowa ya farga ita din taka ce ba.
Kai haba salla yaushe rabon da ai irin wanan neman auren yanzu da kai ya waye wa mutane.
Sallah yace kai dai in har kana ciki ce min eh kawai kasha mamaki indai har zaka bude bakin aljihun ka komai zai tafi daidai insha Allahu.
Har na kawo daidai gurin da suke zaune suna zance na ban ko gaida dasu ba don rabin hiran su ya dan zo a kunne na naji.
In ba gulma irin ta mutanen yau ba ina ni ina su Lawisa da koda aka haifesu ba, a auri uwata ba a gidan.
Don an kawo sadakin auren su zasu yi aure aiba abin mamaki bane hakan idan anyi la, akari da irin girmuwan da sukai min.
Ban saka zancen dattijan banzan nan a raina ba don nasan ba abu bane wanda zai yiyu suke magana don jin dadin fatan bakin su ne kawai sukeyi.
Nikan inda naji zance tsofin banzan kamar yadda na sa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login