Showing 69001 words to 72000 words out of 245996 words
ba
Don Tamkar wance za'a sabon auren ta haka suke jibge kudi ana siyar abubuwan da zasu kaita da shi na zamani..
Har ya kasance Yau saura sati guda mohan ya iso Nigeria alhj muamar da babban aminin sa alhj yakubu sune suke shirin zuwa badge and honour partyn gamawar sa don suga achivements din da mohan din ya samo
Bangaren hjy mahnoor kuwaa tunda su hjy suka kawo maganan tarewar banafshan dama take kaucewa amma yau da
Dika aka taro anan gida akayi magana bata iya daurewa ba ta nuna rashin jin dadin ta sosai
Hakan ya jawo hatsaniya tasakanin ta da tsoffi biyu...
Cewar hjy mamah ai dama bata mata alkwarin cewa sai banafsha ta kai wani shekaru ba kafin ta xauna da mijin ta dama cahn sabida rashin lpya ne akayi jinkiri...tafiyar mohan ya dada karasawa
Hjyn birni ma ta goya baya cewar ai yanzu kam ma yarinya takai tunda ta riga tayi 16 a gida..
Zaman gidan miji kamar ta kama
Sosai hjy mahnoor tayi fushi aranfa,tunanin ta auren nan gaba dayan sa cin zarafin yarinya ce hadi da yadda nimrah take bata salon karfin gwiwa kullum akan abar ta tacika 18
amma ba yadda ta iya yanzu
Yanzu dai an tsaya acewa mohan yana dawowa da kwana biyu banafsha zata tare da shi gidan sa.
Da kyar alhj yayi sulhu tsakanin su aka samu daidaituwa...
Don Sosai ran hjy mahnoor ya baci fiye da yadda ake zato ita sam gani take idan banafshan bata kai 18yrs ba bata mallake hankalin kanta ba ..
And she hates to think that danta ne zai yi sha'anin aure da premature girl.
Ita dai bawai ta gamsu bane ta amsa ne kawai don bayadda ta iya da mijin ta da iyayen sa
Tsimewa tayi ta bar musu wajen Don ko sallama mai kyau bata yi musu ba
Shikam alhj tabe baki kawai yayi a tsakiyan su..
Ranar A duk rigima da facts din da hjy mahnoor ta baje masa bai ce komai ba sai dai nasihan ta hakura ta yi abunda ya dace ma danta tasan kuma gaskiya yake fada idan ta sa pressure akan maganan auren mohan bazai ji dadi ba tunda ya riga Ya amince...
Daurewa tayi ta shiga hidimar shiri bikin kamar yadda suke so.
Gashi ba wani sakewa da ita banafsha take yi ba amma Kullum idan ta xo sai ta jawo maganan da zai sa banafshan taji a ranta cewa bata kai na aure ba.
On the other hand kuma su anty rawiya ..hjy mamah da hjyn birni ba hakan suke rainon ta akai ba.
nuna mata suke ta kai kuma dole ta zauna a dakin ta
Duk dama ba damuwar ta bane auren amma Tafi daukar nasu
Musamman data ga fazilah na zaman ta shiru gidan miji gwanin shawa'a so why not her...
Tana zaune tayi tagumi Ajiyan zuciya tayi a kasale tace no no no..ni ta dabance ba kamar fazilah ba..
Im sure her husband loves her kuma sun fahimci juna ni kuma fa....sai tayi shiru ta sadda kai kasa tana taro hawayen ta da suka cike mata idanu..
2minute silence tayi tana calming kanta sannnan ta mike ta shige bathrum ta dauro alwala.
Bayan kwana biyu.
_medical college russia rwsk_ .
Cross wall building ta ciki dan karamin luxury apartment ne all white mai dauke da tambarin zanen damisa a dark lead plate dake jikin entry.
Fararen curtain ne ke yawo dakansu cikin sanyin iska mai dadi da sa nitsuwa sunyi yale yale suna bayyana marvelous view na blue beach din dake shimfeda a resort din ta waje..
Remote din tv ne agefen sa yayi kwance da baya idanun sa a lunshe baya ko motsi
Sanye yake da simple armless shirt bright yellow na dolce and gabana mai dauke da wandon sa iya gwiwa
He's 31-32yrs now..
bayan dada bayyanan sirrin kyaun sa da fuskan sa yayi har a jikin sa sai daya sake nuna sabon nitsuwa da sauyawar yanayi..
Yau burin sa ya cika he is the best in works and character
An bashi girmamawan kwarewa na musamman tare da membership award na babban kungiyar likitoti dake india da germany in respect of world health org da united nations organisations.
ajiyan ba zallan Alhj muamar ba hatta su dr aliyu da suka hallacin taro sun nuna masa kyakkwan jinjina da yabo..
They were all proud of him musamman iyayen na sa
yana daya daga cikin abun daya sa shi gode ma Allah ..
Duk dama ya dauka ko nasaran zai iya sha masa kai ne amma sai yake jin ba hakan ba aransa..
Burin sa yanzu bai wuce ya sanya albarkan karatun ta yadda zaa amfana ba..
A matsayin da yake yasan wasu masu kudin ma ba lallai su iya daukar sa jinya ba..
he's a world class doc
Samun Lokacin sa da aikin sa a fadin kasashen is worth a huge amount of money bare kuma aje ga dawainiyar jinya a zai dauka.
Akan Hakan ya yanke hukunci kawo generic medicines a asibitin sa a as of major project din da zai kawo na cigaba
Wanda zai tallafo marasa karfin da galihu..
A wannan tsarin duk wani kudin magani zai sauke farashin su suyi kasa sosai inda al'umma zasu fi amfana..
Sannan masu fama da cututtuka wanda samun saukin su yake da wuya da tsada kamar cancer da sickle cell shi kadai yasan tana di mai kyau dayake shirin yi musu idan ya dawo bakin asibitin sa.
A ido bawani banbancin sauyawar yanayi amma a zuciyar sa Yanxu mohan ba kamar da yake ba
Domin kuwa abubuwa dayawa na ban tausayi da taba xuciya sun faru da mata da yara kanana babu wanda bai gani ba
Yanzu Gani yake rayuwar ma nawa take? imani ne ya shige ransa sosai
Can cikin zuciyan sa All he wants now is a simple and peaceful life baya son yaga ya sa kansa aikata ba dai dai ba musamman ma wani na kasa da shi..
Nimrah tasha zuwa nan wajen sa ,
Sai dai har yau bata samu fuskan daga masa hankali ba
Mamaki yake bata matuka yau shine gobe ba shi bane
Har ta gaji ita dakanta ta dena zuwa wajen sa ta this week ta koma lagos da zama don next year ake shirin fara sabon election a nigeria lady bata zama.
Gashi tunda taji anyi maganan banafsha xata tare da su bata sake dawowa abuja ba bare ta kira hjy mahnoor.
Borin nata agaban mahaifiyar ta tayi,don tayi masifan tayi kuka har ta yi ma mohan barazanan bazata taba yarda banafsha ta xauna agidan ba aamma ba abunda ya sauya
Haushin sabon dabiun shirun da yake mata take ji..musamman idan Tana masifa
He only say's what he had to say sannan bazai yi musu ko muhawwara da ita ba...she really hates that
Bata hakura ba sai da lady xineta tayi mata fada akan ta kyale su
Don lady tana sane da idan nimrah tana fushi bata iya hakura sai tayi kisan kai
kashe banafsha kuma tamkar karewar rayuwar su ne
Sai Tayi mata huduban cewa tunda hjy mahnoor tana da ja akan zancen gaba daya da ita kawai zasu yi amfani su daga musu hankali
Tarasa meyasa har banafshan ta yadda zata dawo despite plan din su da sukayi akanta
sai ta soma tunanin ko anga mijin ta kyakkwa ne son kowa ana so a like masa
Who wudnt love mohan ?ita da ta kashe rai akansa ma Of cous wata ma zata iya mancewa da shi ya kshe iyayen ta bare ma karya ne
Duk hakan na ci mata rai ko bacci bata iyayi Da jiji da kai da kuma karfin ikon mallakan cewa zata baza mugun ta da fadin rai ma banafsha tayi shiri
Tayi tayi tagane ta wajen sa ko tsanan ne kawai a tsakanin su basu shiri.
Amma inna
Sai wani bori da yauqi take yi amma sam yaki daga kansa akan maganan.
A daren ranar ya tattara komin sa ya shigo dubai hotel ya kama ya zauna akan washe gari zai bi jirgin nigeria ya dawo.
Hjy mamah da hjyn birnin
Dun dade da masa bayanin komai amma bai sa kansa tunanin matan sa ba tukun.
Abu daya ke cinsa arai
Don ko ya mance idan suka gama waya sai ta sake maimaita masa
Ko yanzu ma abunda ta fada masa kenan
"mohan ka tuna alkwarin mu,please let the girl be for now...kaji.?
Kabari ta mallake hankalin kanta kafin ta zama matarki atlesat let her be 18..kayi min alkwari..
He noticed much more tension in her voice tasa abun a ranta sosai..gani yake kamar tana tausayin banafshan ne.
Of cous aure is not a small issure,amma meyasa ta damu hakan shine bai sani ba
Kawai sai ya amsa mata da emmm...amma bai cewa komai bayan hakan.
Anan kuma angama shiri tsaf
Su mufidah da su sadeek ma suna faman shirin kammala jaraabwan su su iso abuja..
Haushin banafsha kenan gashi bata da waya tasan baza su same ta anan ba sabida taji ance gobe mohan zai dawo kuma jibi zata tare gidan sa..
Hjyn birni kanta tana shan mamakin yadda suka saba lokaci guda duk dama sun girme ta kadan..
Yanzu mufida tana 2oolevel a univsty..
Amma da shike bata da girman kai hatta maryam idan tazo ma banafshan sai sun gaisa
Washe gari da safe Angama komai an kintsa ko ina kowa na zumudin dawowar mohan itakam ma ciwon cikin period ya hanata sakat
Da sassafen ranar nimrah ta dawo Abuja itama..
Wani masifa take ji da shi tasan dole za akawo banafsha but bata yi alkwarin saukin kai daga wajen ta.
Kishin na damun ta fiye da yadda ake gani a kwayar idanun ta
Sai take ganin in har kishi ya sa tayi kisa akan son mohan
How can she eva cope wit a teenager a matsayin kishiyar ta .
She wished it was aysha again..
Yarinyar da bata san komai ba.. so innocent and pure hearted kullum cikin murmushi..haka duk muguntan mugu bata judging dinsa da sharrin sa sai alherin sa.
Amma hakan ta kashe ta
amma banafsha?
Gani take cin ubanta kawai yakamata tayi da kyau agidan ba sassauci tunda lady bazata amince ta kashe ta ba..
Tuno da irin wayannan maganganun yasa ta kasa samun kwnaciyar hankali..
wanka ta fada ta shirya kanta tsaf cikin gayu..tasha fleeky make ups dark brows and smoky eyes takalmin 5inches heel na gucci iri daya da kayan ta take takowa mostly tafison saka dogayen riguna na kanta masu fadi sabida girman nonuwar ta dake dan bata mata shape..
Dark red Loose braid ne akanta dogaye tayi kyau amma sallon ta wuce wajen kawar ta jamila don ta rage zafin da kirjin ta yake mata .
Tasan dai Ita kadaice zata tula mata kasa sam bata ce mata batayi dai dai ba sabida gulma da hada waje duk abunda nimrah tayi ko ta fada dai dai ne..
Da chan ita ta soma bata shawaran ta kwace mohan daga wajen iyayen sa ta rike sa makanta ita kadai..
Amma tunda tayi masa yayi mummunan fushi ta sha bakar wahalan shwo kansa ta soma kama kanta akan tsoma bakin ta akan iyayen sa
Amma yanzu she dont care idon ta arufe yake da guguwar kishi ji take ma ta tsane kowa agidan nasu..
Musamman su hajy mamah
Tun da taje cahn saloon din suke hiran auren har kiran sa bata daga ba,tasan maybe ya dawo ne
Kuma zai iya cewa suje gidan iyayen sa anan zai sauka.
Ita sam tayi rantsuwa bazata shiga hidiman dawowar wata shegiyar yarinya gidan ta ba.
Karshe Haka shima ya share ta ya isa gida
Hjy mamah da hjy birni tuni suka hallora banafshan ne kawai agida bata iya motsawa.
Duk dama baison maganan da yawan dariya amma yau din ta dabance domin kowa ya nuna masa gata da kewa yadda baiyi zato ba..
su nusaiba an kara girma
Ana kan shirin fara registration a university of nigeria nssuka inda ta zaba karanta business administration..
Sabowar desiner box ya bata na watches da turare masu tsada aciki pink ....duk daga clothing brand and collection na kamfanin mawakiya nicki minaj...kamar an tsoma ta a aljanna haka taji
She was soo hapy ita duk dama baya sake mata amma sosai take kaunar sa aranta.
Da kyar suka barsa yayi bacci ,.
Musamman su hjy mamah da ke jaddada masa cewa gobe yazo ya dauke matar sa ya kuma ga sabon gidan su..
Yasha albarka har ya gaji sai dai da safen ba wanda ya gansa don kuwa tunda ya shirya ya fice ya shiga gari harkokin gaban sa bai kO yi tunanin hutawa ba...
Anan kuma hjy mamah sun shigo ma bata sani ba don tayi bacci
Da safe ne anty rawiya ta biya gida itama don ta masa maraba amma baya nan sai ta taho gidan su hjy mamahn itama
Duk wani nasiha da waazantarwa sunyi mata
Angama tatttara komai by 10am har ansa profesionals sunje sun tsala ma banafshan dakin ta..
Wani irin gata su alhj sukayi mata tamkar wance akayi auren huce haushi da ita
Gaba dayan kayan ta daga QATAR aka yo su..
Set din structures na huge wardrobe...princess sized mirror ...kana shigowa kuma Akwai lallusaan small size chinese carpet mai touch din black da burgendy da Royal king-size bed da cushions dinsa mai dauke da lallausan puffy matress an cike ta da designs masu kyau na trow pillows da bead warmers
Tsaf cikin Tsadadden linen da duvet mai taushi aka shinfedata all complete in pure burgendy sai kyalli ko ina yake..
Akwatunan ta 36 din nan tun na aure komai dai ya samu maxauna ras ras tubrkallah
Nimrah bata nan yau ma don haka bata san lokacin da suka shigo sukayi aikin ba.
By 6pm maryam ta koma gida sukayi bankwana gwanin tausayi fazilah ma dake uk tanace sosai akan sam zata zo suyi mata wunin tare amma hakan baiyuwa ba .
Bayan isha'i tana fitowa daga wanka suka ci karo da hjyn birni
Dan daure fuska tayi tana shagwabewa musamman dataga me ta shigo dashi ahannun ta..
Itakam ma Bata kula ta ajiye kaskon wutar akasa tace oya...
Kiyi da jikin ki lokaci ya tafi...
Tana turo bakin amma haka ta amsa da toh ta taho kusa kamar yadda ta saba tayi tsuguno daf da hayakin kan kaskon ya tirare ko ina towel ne ajikin ta babu komai bayan nan don haka Har wani zufe ke keto mata
Ita sam wannann abun ya dade yana takura ta amm Ba yadda ta iya a Cewar su hjyn birni"mace zinariya ce sarauniya yar gwalisa ado da kwalliya sune tsaftar ta bata na zama kamar lami ba komin tsufan mace kwalliya da kwalisa yana fito da ita...
Cewar hjy mamah kuwa komin arziki da ilimin mace idan bata cika mace a gadon namiji ba banza ce a rayuwa...
Haka suke rudin ta da kalaman su wanda bata ma gane wasu ma'anan
Of cous tasan bazasu fito fili suce ga abunda suke nufi ba amma ita ta fahince su sosai.
Sun kashe kudi iya kudi wajen tsala ta tayi kyau tayi tsantsi duk jikin ta yayi smooth..
Olive green material mai kamar lace da designs kamar na manyan dark emirald stones riga da skirt fitted mai bazuwan da fadi sosai akasa.
Hour glass shape din ta ne ya bata wani irin sirrin kyaun shape yanzu nonowar ta sun ciko fiye da da cahn girma ya dan nuna sosai ajikin ta but her face dosnt hide her age.
Couple with light make up din da aka mata sai ya haska kyakyanwan flawless and impeccable caramel skin tone din ta her lips appears natural and shiny with nude picht lipgloss yadda tayi kyau sai kace ita kanwar Mowgli ce ko ita ta haife sa.
Normal dauri akayi mata mayafin mai dan kauri aka yafa mata suna daki sau kuka take zuba musu suna rarashin ta..
Bata dassauta ba sai da antu rawiya ta tafi ya rage ita da su hjy mamahn ne agidan..
Ta daga hankali sosai haka suma amma sai suke dannewa a ransu sabida ta samu tayi shiru..
Sosai take jin zafin rabuwa da su ba irin borin da batayi musu ba
Wani bin suyi hawaye wani bin suyi mata fada..
Don su kwantar mata da hannkli ba abunda basu ce ba,
Cewar su idan mohan yayi mata wani abu bazasu barsa ba..
Don kuwa awajen sun baifi karfin duka ba..
Duk dama taga shirmen nasu amma sosai ta sa abubuwan da suke cewa aranta .
A duniya idan ta cire familynn ta bata da kamar su su biyun
Ko A littafin novel akace mata za asame irin wayannan mata masu riko da amana da gaskiya bazata yarda ba..
Gurbi na musamman ta ajiye a zuciyan ta na kaunar su da girmamama su
Yau tasan ko da iyayen ta na raye its obvious bazata samu irin wannnan kyakkwan tabbacin kulawar da suke bata ba.
Suma hakan ne aransu don tuni suke dauke ta jinin su abun alfaharin su....
Gaba daya sun dauki so da burin duniya sun daura akanta..
Gani suke itace dai dai jikan su kuma shm maybe ita zata share musu hawayen su tunda zata ji magana su ba kamar nimrah ba..
Shikuwa mohan By 8.30pm ya bar site din mahaifin sa ya dawo dakin sa yana kimtswa dan kayan aikin sa ya hade gaba daya adan karamin trolley ya yi musu sallama ya kama hanyar gidan su hjy mamahn...
Wani daddaar Qamshin 30 ocean lavender scent ke tashi ajikin sa Yasha yadin shadda mai laushi sosai cool sky blue colour da hula zanna bukar wanda ta mugun dacewa da aikin zaren kayan sa.
Hannun sa manne yake da wacht din Daniell welingtong matte black yana murxa stairyn sa majestically..
fuskan sa Normal and calm yake tukin sa shiru ba abunda ke tashi sai sasaayanr muryan sheik abdl rasheed minshary ta suratul ibrahim cikin motar sa kiran bentley GT ba mai kaman benz din ba dukulalliyar jeep waccce take tafiya kamar bata taba kan hanyar..
Yana isa gidan bai yi wata wata ba yayi parking ya shigo..
A falon ya dakata yana kallon ko ina yana tabe baki a kasale Komai ya burge sa
Tsarin gidan a yelwace take babu takuri..
Cikin hakan saiga mai aiki ta wulga tana gaishe sa amma bai amsaa ba yace tace musu ya iso.
anan ne ma daya jingine kansa ya soma kawo tunanin yadda idanun sa zaiga banafshan..
Shi sam baya son tuna ta amma he cant deny it
In his own little way he misees her alot.
He's just wondering how she will look now...yaji nace ta gama secondry schl few months ago
Shin Ta dena shagwaba sakalaci da yawan kuka? Ko ko fitinan ta har hau bai kare ba..?
Murmushin gefen baki yayi,ayayin da ya gyra azama jin motsin shigowar mutum inda