Showing 207001 words to 210000 words out of 245996 words
ji tsikan jikin ta na tashi,.
Takasa gane Ma'anan mafarkin ko ince idayar,smiling face din mahaifiyarta ke mata ziriya a ido tana tunowa da kuma yadda ta bata assurance da murmushi n ta cewa komai zai wuce
ganin tunanin yana neman mata over Ga tsoro ya shige ta,Tasan Ko yana nan bazai bata izinin fita ko ina ba amma Sai taurin kai yadebe ta Tayi sauri ta shirya ta nufi gidan su maryam#surayyahmsFollow@
#SURAYYAHMS
*🍒🌺AJALIN SO🍒🌺*
_WATTPAD SURAYYAHMS_
Brilliant writers association
_50 medicine_
Tun daga fitar ta ta kira layin maryam tace mata tana nan A hanyar zuwa maryam Tace Toh Kizo gidan ummah Kawai ina wajen
Nan Din ta wuce driver ya aje ta,
Bakowa harabar gidan Sai ta shigo Falo da sallamar ta,Maryam din ne a zaune Ganin ta yasa ta mike da fara'a tana cewa maraba Da xuwa, ta bata wajen zama
..gidan shiru kamar ba kowa sai su biyun...aje maysam Banafsha tayi gefe tana sauke boyayyen ajiyan zuciya Don har wani iska na daban ta ke ji naratsa ta
Maryam tace kaga amaryan doc hjy Banafsha...,sai wani pale pale kike kinyi haske, Banafsha anya ba wani katon kwallon kika chabe ba?
Murmurshi kawai tayi tace wannan ai sai ku yaushe zan iya mantawa da azaban danaci a nakuda?
,. . yah Yaya ameer ango na Fatan kuna lpya?
maryam Tayi Murmushi tace lpya Lau fatan dai zaki zo min, dan nan dai ba gida na bane.....sukayi dariya Banafsha tace Ke kadai ce?naga bakowa Inche Lpy?
..tace eh fa daga shiga kitchen nafito sai banga ummah ba,bari dai na duba mana abincin sai naxo..
Sai Ta gyada mata kai,bby maysam ke Neman fara kuka sai ta dago ta ta aje ta kan cinya tana bata nono
,...yadda yarinyar tayi shiru ta nitsu tana tsotsar ta sai ya sa takafe ta da ido tana ganin kamannin mijin ta,.ranar ma tanaji hajy na fada cewa mohan bai wani sha nonon uwa ba sabida hjy mahnoor ba ita ta raine shi ba
...tace hjy mahnoor ta samu cikin shi ne a lokacin da take kokarin fara kafa career ta na fashion and desing a duniya kuma tana so yayi karfi sai kawai ta fi bada muhimmanci achan fiye da shi.
Sometimes idan hjy na bada labarin yarantar sa har abun dariya yake bata,yanzun ma wani abun ta tuno zatayi dariyan amma saiga hawaye sun sako mata
...wani mugun mugun son mijin ta da kewar sa ke neman mata illah,'dan kadan tahade goshin ta dana maysam tana kallon kamannin sa anan tana kukan zuci.
Maryam Tray din hannun ta ta aje Ra karaso kusa kanta tace Banafsha?...
Bata ma ji ma ta kuma cewa
nafsha... adan firgit ta dago cikin sauri Ta kuma sadda kai tana goge hawayen ta
..maryam da shiKe ta dade tsaye kusa da bayan ta tana kallon abunda take tuntini tuni ta karbe baby ta ajiye gefe ta Dawo ta tsuguno gaban ta
tace Banafsha lpya kuwa,meya sameki kike kuka? Bata Amsa ba Tayi shiru...ko maysam ne bata da lpya Kin fada ma doc?what's going on....
Da maryam ke tambayar ta A haka sai taji She cudnt hold it anymore,wani matsanancin kuka ta fashe da shi tana cewa babu komai kawai wani abu nake tunawa..sai kuma tayi shiru Ta cigaba
..hankalin maryam Kuwa tuni ya tashi,but she's very tactfull dan haka ta nitsu ta riko hannun Banafshan gently Tace kawata"..kar kice min iyayen ki kike tunawa...ko su hjy sun bata miki rai ne?...Tayi saurin girgiza kai
tace ah'a Maryam...tun daga nan bata Sake cewa komai sai kuka...
Gefe da ita maryam ta Dawo zauna ta jawo ta jikin ta Tafara rarrashin ta,Maryam duk wani kalma na hakuri ta fada mata da kyar ta dago Ta hadiye kukan tace Mata maryam Im not happy....my marriage,... ni bansan ya zanyi Da shi ba,It s alwys hurting Me..what shud i do pls..?
sosai maryam ta shiga halin tausayin ta Data ganta a hakan ayanda suke rike da amincin junan su itama tuni ruwan hawaye ya taro a idanun ta,tace Banafsha dama yaya mohan ne?Kar kice mun fada kikayi da shi,Pls talk to me Nasan ki da boye damuwa Aranki,Kuma ba yadda xaki rike abu aranki ki samu saukin shi...pls whats wrong?meya faru ne nafsha kefa ta Yaya Mohan ne shi kadai, shima naki ne ke kadai.
Cikin shessheka Banafsha Tace ah'a kam, yaH mohan baya ma kula ni yanzu Ni tunda na haifi maysam na dena gane kansa,i just wonder if he care about me or not he changed alot
....i think he doesn't like me Anymore..Dan yamin abu nayi fushi Then he dosnt want to talk to me again,kuma wallhy ina son shi Bazan iya jure hakan ba..
Yanzun haka anty Nimrah tanada ciki,hanklin sa gaba daya yake so ya maida shi chan..naga ko maysam din ma yana so ya dena kulawa Da ita kamar da.
.shikenan Ni Sai na dawo musu hoto agidan Ko?
Wani kukan ta saki Ta hade kanta da gwiwa,
.
Maryam sai ta danyi shiru chan ta kalle ta tace toh kiyi hakuri Banafsha,but i can't believe that haka kawai yaya mohan zai canza miki bayan kin haihu masa..,ni a yadda nake gani yake tarairayar ki gaskiya inaga kinyi masa wani abu ne.. So fada min..Banafsha me kika masa?
Dagowa tayi kamar zatayi Magana amma sai tayi shiru
Maryam tace "look Kar kiyi min shirun nan naki, idan ma baki sani ba we have to think right now,bazan iya barinki acikin kuncin nan ba..
Banafsha Share hawayen ta tayi
Ta gyara zama tace inaga Fa tun akan lokacin da nafara nakuda ne,anan tayi highlighting ma maryam abubuwan da suka faru,ta Karashe da cewa ni Da farko dai sai naga kamar babyn sa Dama ya so bani ba...maryam what do you think am realy confused About him,kuma fa kinji abunda anty nimrah tace min
...kafin maryam tace zatayi magana sai su kaji gyaran murya akansu
Ummahn ta ne tafito daga bayan gida a daki, toh data jiyo abunda Banafsha ke fada sai taki tayi interupting dinsu
Komai aka fade shi a kunnen ta..
Banafsha A sanyaye ta rusuna tace ina wuni ummah ashe kina ciki..
Ummah da tuni tadade da shiga kundun nazarin abun da tajin bata ko amsa ta ba A masife tace
Mena ke ji haka Banafsha,dama A haka kike rike auren ki?ashe ni ba uwa bace da baxaki kawo damuwar ki waje na ba?
..wani hawayen ne suka zubo mata kirjin ta na Bugu,.. tace ummah Kiyi hakuri, baya bari na fita ko ina Ne yau ma dan baya kasar ne na fito Bai ma sani ba"
...ummah tace yimin shiru awajen,ai kin bata min rai Banafsha,
Banso naji haka daga gareki ba.
nan ta hada su Biyun tayi musu fada tana cewa bawani uxurin da kuke dashi a wannan lokaci,
ure just 16-17 ai tunda kuruciyar ku zaku ji dadin aure ba sai jikin ku yayi nauyi ba,
ga yan mata nan ire iren ku sun bude ido sunsan meye duniya take ciki
'Yara yan 16-20 duk ina ganin su suna xuwa nan siyan kayan gyara,wani bin mu manya ma sai su nemi sufi karfin mu Ta Fannin Rike miji da tattalin shi,amma wai ku da kuke yara na Har zaku zauna kuna shirme ana cin tuwo akanku haka?
..Banafsha ko dai baki son shi ne?
Tace ah'a ummah,..ina ....... .. son shi..
Ummah tace Banga alama ba, To tashi maza ki biyoni daki, ke kuma maryam ki kula min da jika na.. tace toh ummah.
Ayayin da Banafsha ta bi bayan ta daki ummah tana zama Banafsha ta nemi Waje itama kusa da ita ta zauna A kasa ta sunkuyar da kai..
Dan shiru ummah tayi tana kallon ta,cikin nitsuwa da lallashi tace,ba fada nake miki ba yata Share hawayen ki muyi magana ki dena kuka kinji!?
A hankali ta dago jajayen idanun ta tace kiyi hakuri ummah nasan nayi kuskure Aure na ya lalace min.. wallhy bansan yazanyi bane Shiyasa.
Ummah tace um um Banafsha Kidena fadin baki san ya zakiyi ba...,ke kuma fisabillahi haka akeyi!? Da kika haihun shi yafada miki baya sane dake?ai Wanda yaso abunda ka haifa yana son ka Ne..Wato ke duk wannan baki gani ba ko, kishi zakiyi har da Yar cikin ki?Banafsha Lafewa tayi kadan ta sharo fuskan ta Cikin jin kunya
...."umma ta cigaba da Cewa haba Banafsha ta, Ina kike kai tunanin ki Ne? kefa Ya mace ce,keda nake ganin kwarjinin ki afili ashe har akwai kishiyar da zata xuga ki Kiji ta? yanzu fa kin girma, ke ba yarinya bace da zaki tsaya ki kafa hujja da maganan kishiyar ki kowa takansa yake a gidan miji ko cemiki Tayi Ita bata Kishin shi?,mijin ki might be having problem somewhere else wanda baya son ya shafe ki a condition din da kike a lokacin da kika haihu,kece yaka mata ki dinga bada uxuri kafin ki yanke masa hukunci,shi aure ai ba wasa bane he is ur life partner,alwys stay put and be open to him Kifadi masa damuwr ki,kar kiyi shiru da abu aranki dan wata rana zaki tafka mummanan kuskure.
Sannan The very next time naji kin korashi ajikin ki da sunan kina fushi dashi har gidan zanzo na same Ki naci kaniyar ki,dan baki da hankali Mijin kin xaki raba gado da shi wayace miki ana haka..
Ummah tace,Toh kar nakara jin kinyi hakan dai, don ba tarbiyar mace mai kamala bane,..aure ai bautan Allah ne don haka bason ranki zaKi rikayi ba,maza ki sa ma zuciyan ki ruwan sanyi ki san me kikeyi
go back to your man now, ki bashi hakuri kar ki yadda Ki kyale shi har sai ya hakura
Dan Siririn hawayen ta ta share Kafin tayi magana umma tace Oya Tashi kije ki dauko maysam kizo..ina tana dai karban nonon ki da kyau tace eh ummah
",yawwa to dauko ta..
A sadade ta mike ta fice kafin ta dawo ummah ta fito dawasu special packages daga cikin kayyakin siyarwan ta Ta aje Domin ta,tace goya ta maza ki koma gidan ki kar ki kara makanki laifi,Babu kyau fitowa haka kibari yabaki izini Sai kizo kuyi hiran ku
Tace toh ummah nagode...
"nan ummah ta debo kayan tace Ungo karbi Wannan Turaren da kin gama wanka kizuba a clean water ki shiga ciki na minti 10,Ga Kuma wannan kije ki shanye yau da gobe duk sun ishe ki..Banafsha Abun ta karba tana juyawa a hannu Wani hadin kutungwila na pure zuma dabino kwakwa da sauran hadin da bata san me ajiki ba,ansa shi well packaged agoran yoghurt tsaban Abun ya tsumu har oil Din fruits din kwakwan dake jiki na kama goran gashi coffe brown Yana gamshin dadi kamar Wani Yummy chokolate,sai wasu tsumin Suma agora anma tace mata kar ta bari Ya kwana ta shanye shi A yau Din..
Banafsha Har bata san kalman da zatayi godiyan da shi ba Don kuwa sosai taji sanyi aranta
,rarrashin ta ummahn maryam ta Dada yi zuciyan ta cike da tausayin ta"
tunanin ta itama shine yanzu da ace bata duniya wazai rike mata mata nata yar?
Ko da taga Yanayin rayuwar Banafsha da sauran Kananan Yara Irin ta wanda Suke rayuwar auren Kuma Basu da uwa a duniya,
takan jinjina masu Sosai tasan Hrdly suke sanin inda xasu aje kansu a kafadar wani suyi kukan damuwar su..
Haka Banafsha tayi sallama da su ta koma gidan ta ko kiran driver ma bata yi...'
'Wanka ta fada tayi sallahn magrib,tunda ta samu taci abinci kadan ta shiga kundun tunanin abunda ummah tace
.. After 9 na dare ta kwantar da maysam,abubuwan da ummah ta bata ta shanye sannan ta bi gado n ta ta kwanta,
Ji Take kamar ta gama saita tunanin ta akan komai,Sai dai har yanzu Tunanin salo da yadda zata bi ta bashi hakuri ke damun ta, by 8am na safe dama ranar monday ne a tsanake ta gama komai har ta yi breakfast ta shirya maysam cikin all white baby set na jimmy chuu yarinya ta fito angelic as usual
Tunda tayi amfani da turaren wanka da umma ta bata qamshi ne kebin ta a dik inda ta tashi ko ta zauna"
Da safen Dakin sa ta nufa ta bude tana kallo Daga bakin kofa,
kwana biyu da bata zuwa nan akai akai sai da taga banbanci
nan ta shiga kintsawa tana buge kura,within some minutes ta share ko ina ta goge, wani hadadden bedding set ta fito da shi pure sea blue mai laushi ta shinfede gadon sa da shi,bata fice ba sanda ta tabbata har toilet din dakin na qamshi da sheki
Sai chan da yamma wajen karfe 3 saura taji driver ya ce shi xai je dauko
Shi a airport...
nan ma ta sake wanka ta shirya kanta cikin wani pingelin gown marar hannu pink da ita babyn Ta suka zauna a daki..
Bata sani ba ashe tana shigowa daki Nimrah ma ta shigo gidan
agurguje ta haura sama Dan dama ta riga ta gama setting plan din ta. .
Dakin mohan ta fara lekawa Taga ko ya dawo ganin an sauya komai an tsaftace yasa ta fashe da dariyar mugun ta"irin wato har anzo dubawa ko ya dawo ko?
Tabe baki tayi ta Shigo
A Kan kujeran dakin ta zauna ta aje wani magani In form of pill akan stool nesa da ita
..,dama wanda tasha na abortion din already ya fara aikin sa tuntuni Don har ta fara serial bleeding,dama lab scientist din ladyn tace mata muddin ta sha wancan karamin pill din jinin zai zubo mata dayawa har yabi kafar ta and is very risky duk da haka bata damu ba..
Wayar ta ta daga ta kira faisal,shi sam baya son muamala da ita amma tsoron ta yake ji,.
nan ta tanbaye shi inda mohan yake,shi ya kayyade mata
Cewa nan da minti goma ma driver zai iya shigowa da shi Gidan,
Tana katse wayar ta mike ta bude kofar dakin San
sai ta wani irin sake shi da karfi yayi kara kamar an shigo ne aka rufe....
Sau biyu tayi hakan,kafin Banafsha ta ji,Ita Kuma sai ta dauka ko shine ya dawo
ba wani bata lokaci ta taso dan ta zo ta tabbatar Da hakan,
Wani malak nimrah ta kwanta kan cushion dinsa ta sake takalma da jakan ta akasa ta riko cikin ta tana wash wash,..
Wani dada kara sautin nishin ta tayi ta rikota kasa musamman data ji sallamar ta...
Itako Banafsha mamaki da tsoro ne ya cikata,tace antyy lpya kuwa. .?
Wani munafukin
Kuka nimrah ta sake,tace ciki na kemin ciwo Banafsha .. Can you Pls help Me ga magani na chan dauko min nasha.
Arude Banafsha tace ok, sai ta aje babyn ta akan gadon sa ta dauko pill din,
gefen condenser tabi ta tsiyayo ruwa ta zo gaban ta rusuna tace sannu anty ga shi nan na kawo miki,
Ba laifi Nimrah ta karba ta hadiye agaban ta Tasha ruwa.
Cup din ta mika mata tana rike dashi tana kallon yadda take wash washhhh,jim kadan kawai Nimrah tasa ihu sai zirrrrr jini yafara bin kafar ta.
A rude Banafsha tadafa kafadan ta tana furta innalillahi wa enna ilaihi rajiun..sorry
sannu
Nimrah Tace sake debo min ruwan zansha,ba jira ta mike tana dawo mata da ruwan,Ta karba ta sha..
Cikin tausayawa Banafsha tace
Anty Ko na kira driver akaiki asibiti"
Dan gyara zama nimrah tayi Ta Kalle Banafshan,
"ita dama already anyi inducing mata pain reliever,duk murde murden munafirci take Kawai dan ta zulma ta, tana jin zafin Dai amma is bearable"Sai tace bazan je asibiti ba sai dai Za'a Akaiki,dan kuwa yanzu xaki samo Ciwon tabin hankali
Cike da mamaki Banafsha tace mene?Ki kace me
Nimrah tayi dariya tace Yes u heard me Right,Dago rigan ta kadan tayi ta Gwada ma banafsha jinin Dake bin ta. ,tace Wawiya Kawai Toh This is all planed Dama so nake Kisan kin bani magani da hannun ki...,Ni zan fada ma Mohan kin bani maganin zubda ciki a ruwa Nasha Cikin da yayi min ya xube,
So mrs Banafsha Can you Deny it?tayi dariya Mai shake da tsegeran ci
Ganin Banafsha ta shiga shock tayi durus Cikin rashin sanin Zatace, yasa ta kyabe baki Tace
"ki ce masa karya ne Mana, or are you two fighting?ta sake fashewa da dariya,
well basai kin amsa ni ba nasan komai tunda nina hada ku,amma kinsan makomar ko kuwa? mohan Zai ki ya yarda dake sai ki dawo mahaukaciya Ya kora ki agidan sa. .simple.
"nan Banafsha ta dago kai Wasu takurarrun zufa ne suka fetso mata Cikin tsananin mamaki ta sake karamar dariyar takaici tace
Hmmm Heheheh"
..Lallai fa, So What do you mean now anty?kina nufin sharri Za kiyi min Yanzu yanzun nan ko? Toh Menayi Miki haka? Ko duk sabida yaya mohan ne? I tot ure in pain Ni sam ban fahimce ki ba Fa are you for real?..,Tayi kwafa ta na kallon nimrahn Kanta har na mata kaikayi
Nimrah tace i am,ba wasa nake miki ba,kwanan ki ne ya kare..gwara Ki Sake ki fadi abunda ke ranki Don gida na xaki bari yau,.
Idanun Banafsha take sukayi ja cikin rawan murya tace akan me?zamanki nake ne..
Nimrah tace ai ba mai zamani Dani dama,I have neva liked you Kuma kin sani,dokar zama na dake shine duk abunda zanyi na tarwatsa rayuwar ki sai nayi shi.....
Wasu hawaye Masu zafi ne suka sauko mata tace anty Shine Har da kashe dan cikin ki?Ure this wicked? No wonder kikace yaya baya so Na abun ciki na yake so,so it was all your plan right. Muryan ta har na rawa ta karashe
Wani dariya Nimrah tayi tace Hmmmm Banafsha kenan Ure dump,stupid blind..Wato wannan kawai kika sani ko?It's ok,wasa Dai ya kare Kinga wanda yaci baya zaiyi ouuuuut...
A zafafe banafsha tace Wallhy Baki isa ba,munafuka kawai"Allah ya tuno asirin ki,ashe Dama hada mu kawai kike dan ki raba ni da shi?
"Basar da harzukan tan Nimrah tayi tace
Deny it Mana bake kika Ban magani nasha ba?
Wani Kukan Fushi da takaici Banafsha ta fashe da Shi Cikin ranta ji take kamar Ta kashe Nimrah dama ashe Haka take?
Tace toh,In na fice Anan ai zanga wa zaki lakama sharrin akace Miki kike kadai kike da bakin sharri,zan fita kuma ba Wanda ya isa yace nazo nan na baki wani abu
Banafsha nasa kafa Nimrah ta shake ta
Charaf sai suka ji sallamar sa
Wani Ihu Nimrah ta sa Tace wallhy baki isa ba Sai kin fada min meyey kika saka min aruwan ciki na ya xube
Wani baru jikin Banafsha Keyi kuMa ita ce ta fara daga ido ta kalle shi