Showing 123001 words to 126000 words out of 245996 words

Chapter 42 - AJALIN SO BOOK COMPLETE BY SURAYYA.txt

07 Aug 2025

8836

wani 30minutes ba ya ce mata zai fita Tare da sanar da ita zai dauke travel break na 2 weeks a southafrica baya so a dame shi.

"Har bakin kofar mota ta biyo sa yana mata bayanin abubuwan da zata yi in baya nan din

A duk sanda yake mata magana satan kallon sa kawai take yi tana murmushi aranta,it looks like she's content just being in his shadow muddin wannan matsayin yarda da amintan dayake nuna mata bazai gushe daga wajen sa ba.

Sai Tayi shiru komai yace tace yess sir.. Done sir.
Har suka yi sallama tana tsaye.

Sauke ajiyan zuciya tayi tare da komawa ciki dan bata ma ji komai ba sai muryan sa

she's certain that zata kula da kayan sa kamar yadda zata kula da na nata koma fiye.

Fitar sa daga nan ya nufi wani taron meeting da manyan pharmaceutical professionals wanda akallah ya cinye masa lokacin sa zuwa azahar daganan gidan su hjy mamah ya nufa.

sun sha mamaki kwarai da suka ganshi a wannan lokaci sai dai as usual bai sake ba ma bare suji meya kawo sa na asali.

Zama yayi a falon su,hjyn birni ke takura sa da hirarrarrki musamman da ake harsahsen auren anisah nan da wata guda mai zuwa kuma kowa daga cikin familyn su zai zo na nesa dana kusa.

Shiyasa ma suka laka ma bikin muhimmanci sosai sabida sada zumuncin da za'ayi da juna in an zo.

Akan hakan take jaddada masa dole ne ya kasamce a wannan hidima daga farawar sa har karshe babu uzuri.
Dago idon sa kawai tayi yana kallon ta fuska ba yabo ba fallasa yana tabe baki.

"Hjy mamah ce ta fito masa da abinci wanda daga shigowar sa ta sa aka hada shi sharp sharp,ko da aka ajiye gaban sa sai daya bude warmers din yaga kyakkywan tuwon semo ne da miyan busashhen kifi,wanda aka hade shi da stock fish da jajjagggen tsokar sukumbiya.
..,sai ya koma ya rufe bai ci ba ya dauke apples yana slicing ayangace yana ci.

Haushin sa take ji musamman idan ta dage tayi masa abu ya basar.

Yana sane da hakan ya gintse yayi kamar ko ajikin sa,gashi dama asali wajen ta ya zo da bukatar sa...

Hjyn birni ke cewa lamido ka dai ji abunda na fada maka
Wannan karon kar naji wani tashin tashin

Tun kafin ya amsa Hjyn mamah ta harare shi tana cewa"'wani lamidon banza da wofi kira shi da mohan dinsa yafi dacewa da shi'jibe shi tayi tsuka irin na masifaffun tsoffi.
Sake baki hjyn birni tayi tana murmushin mafarin draman nasu

Da Kamar bazai amsa ba sai Yace dama ni bance ina so ba ai.

Zatayi magana hjyn birni tace toh ya isa haka mana dan jikar nawa zaki sa agaba emmm,hjjy mamah tace tabbbb ai da kin barni da shi kawai'kingan shi nan a hakan zuwa yayi ya dame ni ya sa ni hushi

Sai ta jawo warmers din ta bude "tace Kinga ko abincin ma bazai ci ba sabida idan bai sani magana ba baiya jin dai dai a rayuwar sa.

Dariya yayi da gefen bakin sa baice komai ba

Hjyn birni tace haka ne kam,toh kai lamido meyesa baka deba abincin kaci ba,ko na debe maka ne nasan ka gaji ko..bisimillilahi tayi yunkuri da jikin tsufa ,kokarin tashi take da alaman zatayi serving dinsan da gaske

Yayi saurin riko ta yana cewa ah'a Gimbiya ta zauna abunki....

Ai dama baso take naci ba,..da ta so da tambaya ta me nake so zatayi.. Kada kafadun sa yayi irin ni wannan din ne bai min ba alhalin har cikin ransa yaji shawa'ar ci. ..fuskan sa Cike da neman tsokana amma kuma a daure.

Hjy mamah tace hmmmmm iyeeeeee.
Ubana Garba ya mutu wani ya dawo
To me zaka ci dan gama didi?
Ko kaina zan sa maka a tukunya

Don ya kure mata tunani sai ya gyada kai ya daga kafadun sa sama irin is upto you.
Sai ya juyo ya kuma kalle ta yace nifa yunwa nake ji....
Hannu ta daura akugu tana girgiza kai tana hararar sa gwanin dariya
Hjyn birni sai ta rasa gane komai dariya suke bata

Dai dai da shigowar su mufida ita da ahmad sun fito daga shoping Dariyar da hjyn birni ke musu ya sa suka iske su cike da fara'a sunajin meke faruwa.

"bayan sun gaisa dukan su sai ahamd ya fita snooker deen domin ya sanar da sadik mohan yazo dama abakin nan shi suka sauke sa.

Shikuwa mohan Da shike ride hard and die hard fans dinsa ne sai baya takura su thu are both 22- 23 presntly suna univesity mufida kuma tana 100level.

Bayan dr aliyu da umar,best friend dinsa sune yayan hjyn birni wato su sadik da ahmad sai kuma abokin tsokanan sa uncle bahrain half bro din aneesah wato yar gidan uncle dinsa burak.


" ..Mufidah tace yayah mohan yanzu muke shirin zuwa gidan ka dama zamuje saloon ne.. ai ta fada maka ko,

Fuska ba yabo ba fallasa Yace..'ehmm zakuje amma ita ba yau ba ...

Hjy mamah tace ehem kungani ko komin shi left,yace ohhhhh ni kije kimin abunda nake so kawai.
Tace toh me kake so din ne wai ?fitina ko jaraba

Sternly Yace no yayi rolling idanun sa ...peppered grilled chicken, oat soup and maybe zaki iya sakaya wa da garlic bread...ya daga gira irin Hey, yaji garlic fa don ina so.

Gintse dariya mufida tayi dataga reaction din kan fuskan tsoffi biyun..uwa uba da na shi gogan daya ci fuska gaban su..

Hjy maman ke faman jaddda masa cewa ita ba matar sa bane da zai hada mata oder
Shikuwa harda bata time

Mufida dake tsaye gefen sa duk dama bata ji dadin hana tafiya saloon din da yayi ba amma shirmen fadan nasu sai ya hana ta yin korafi,

kwana biyun nam sosai suka saba da hirarraki masu debe kewa da banafshan musamman ta chats..

"Duk iya kukkunin hjy mama haka Hjyn birni tace suje tare suyi masa abincin tunda ya zo musu yau basu suka roka ba.

Zama yayi cikin yan uwan sa,abincin sa hjyn tayi masa ya basar ya sa su ci dan dole while shi baifi spoon uku ko biyu yayi ba suna ci suna hira sama sama gwanin ban sha'awa duk dama hankalin sa ya fara komawa gida yanzu

After like 45minutes sai gashi an hado komai ana fitowa da shi batayi da yawa ba don haka ba abunda baiji ba gaba daya wajen ya dauke qamshi mai dadi"mikewa yayi yana cewa amasa packaging ba anan zaici ba'
Haka mai aiki ta shiga packaging masa abincin

Hjyn birni Tace dama ba anan zaici bane?mai aiki tace eh.

A hujajan hajy mamah ta fito da niyyar masa masifan ya raina mata wayo,

"nan taji sadik na tambayar mufida ko zasu je gidan tare da mohan ne akan shima zaije tare da su.

Nan shikuma yake sanar da su cewa banafshan bata jin dadin jikin ta ne.


Haka kawai hjy mamah taji Wani rass aranta sai da gaban ta ya fadi,..
Dama ta sinkayo wani yanayin mai alaman tambaya a muryan ta jiya musamman da sukayi waya na karshe da ita.

Ita data raine ta tasan bata cika jin nauyim ta da kunyar ta haka ba,amma sai gashi a jiyan ta fahimci cewa akwai abunda take so ta fada mata amma bata iya fada ba.

Wani Diffff ta sake ji,.. take ranta ya fara kawo mata wani abu mai sata jin farin ciki da faduwar gaba"tace'ko dai ciki ne? tace ah'a har banafsha zata zamo ciikakkiyar mace a dakin mijin ta banga alama ba,sai ta kuma ce toh yaran zamani 'hmm

Chak Sai ta yanke tunanin tan da cewa
Meye same ta?kar dai har kunje asibiti.

Yace ah a fah jiya ne kawai da yau'..and
she will be fine...

Kallon cikin idanun sa take tana karanto sa tasan duk yadda akayi akwai wani abu.

Don ta dada wayance masa sai tace Allah ya kara mata lpya dai nan kowa yace ameeen

sai Tace toh gashi za akai maka motar ka saura kuma karkaci abincin nan ka gani har gida zaka ga na jawo abuna sai dai kaga wayam.

Tabe baki yayi kasan wuyar sa yace ,toh ai yarki ce zata fi ci kinsan nikam ina da lpya ta..sai kiyi shirin kwacewa ta chan ki barta da yunwa"

tace'iye,kaji marar kunya kai meyey ya hana ka yi...yace
kema kinsan dan ban iya irin wannan din bane in don nine ko kallon ki bazanyi ba.

Murmushi kawai tayi
Sai yanxu ta gane draman nasa dama da sannun sa yasa kenan ta dafa abincin

Amma wani irin ciwo ne ke damun banafshh haka da bazata fadamin ba kuma bazata fita ko ina ba?
Ta kyabe baki aranta tana fatan alherin ma abubuwan data dade tana harshensu akan su.

Kamaar ba za'a rabu ba kudi ya bayar ma mufida ta siya kayan kwalliya sannnan yayi ma ahmad da sadik alkwarin cewa idan ya dawo daga tafiya zai taho musu da wani Thai wang wireless men's skeleton watch dayake sawa da suka dade basu iya nuna masa maitar su akai ba sai yau.

Yana isa gidan dakin sa ya nufa tare da sauke gajiyan sa a batrum,


Itakam Barci mai nauyi ne ya debe ta tayi har taji ba dadi sai arnd 2.45 ta tashi just 10 mints kafin ya shigo.

Agurguje tayi brush, Wanka tayi gami da dauro alwala domin gabatar da sallahr azahar dake neman gaucewa.

Tasha mamakin yadda tayi baccin kusan awowi tun fitar sa yanzu haka bata ma san ya shigo ba

Bayan ta idar da sallahr mikewa tayi Daure da towel ta zauna gaban mirror,nitsatsen kallo tayi ma kanta hango slight hikes na kisses dinsa agefen wuyar ta yasa ta jin wani sabon kunyar kanta.

She can't believe what her life is turning into...komai faruwa yake bazata gashi Duk wani mafarkin ta da burin ta akan rayuwa bai zo mata yadda tayi tunani ba tukun

Shafa mai take kamar mara laka tana tuno da iyayen ta musamman ma mahaifiyar ta,tasan dasu na nan da ba haka ba ne.

Wani irin silent tears ne suka gangaro mata tayi saurin tarewa tare da bada kanta karfin gwiwar cigaba da karban qaddarar rayuwar ta.

Izuwa yanzu Ta amince cewa ajalin su wani babban ajalin so ne a duniyar ta wanda ba mai cike shi a birnin zuciyar ta ayanzu.

Cikin haka taji an murda kofa an shigo tsaye yayi da keys dinsa a hannu jikin shi sanye da complte set na kananan kayar marks and spencer rigar fari wandon brown sai normal roaming sleepers akafar sa

...,mikewa tayi adan razane ayayin da suka hada ido towel dinta ta shiga karewa tana sunkuyo da kai..
...sai yayi sallamah.

"da kyar ta amsa shi, Irin Kallon dayake mata ne bata so sai ta sunkuyar da kanta sosai,kallon ko ina yayi yace lallai ma yarinya..sai yanzu ma kika tashi ko? Hw u feeling now

Ta dan turo baki kasa kasa tace im ok.."yace good...arent you lonely?to sai kiyi sauri ki taho kasa kuma ai zaman dakin ya isah haka ko.

Cikin ranta tace lallai ma kamar wanda ya damu- ba fitan sa yayi ya barni ba,ni dama yunwa nake ji
Tayi kwafa tana kallon sa.

Shiru shima yayi ya ja mata door din Yana fita tayi sauri ta shiga kimtsa ko ina tayi dan shafe shafen ta ta fito sanye da rigar da skirt na voil lace bright yellow simple fitted akan 8pieces skirt.

Hanyar falo ta nufa atakaice,turaren ta data shafa wato sandalwood mai sanyin qamshi da kwarjini shi ya fara isar masa da sakon tahowar ta.

A hankali take saukowa bata damu da kallon dayake mata ba,don bayan bakar yunwar dake cin ta har iyanzu jikin ta na mata ciwo.

Ganin sa akan dinning ya bata mamaki amma sai bata bayyana hakan akan fuskan ta ba,
Kafin tayi wani motsi yace har kunje saloon din?

Wani gwalo ido tayi ta dafe kai alaman ta manta,sai yanzu ta lura da lokacin da sukayi zasu je din yayi har ya wuce da kusan awa guda
....tace bamuje ba,

Yace kodai kinyi bacci kince musu su tafi.

Tace ah'a yayah inaga ma kamar basu zo bane
Lemme call them yace not now kitchen zaki shiga akwai aika da suka kawo miki..

Cikin rashin jin dadin missing wannan damar Tace ok,..ta nufi kitchen din

Binta yake da ido har ta lume...shi dama kawai so yake tayi magana dan yasan yadda ta fito a sadaden nan da wuya tace masa komai.

A kan slab ta hango warmer din garlic bread din ne kawai akayi rolling dinsa a foil paper.

Tabe baki tayi,abubuwa da yawa na bata mamaki
2days bata ga iya masifan gidan ba ga kuma wani abincin na daban shida bai cika son outcasts a gidan sa ba.

Hannu ta sa zata bude taji mltsin mutum abayan ta,ta juyo kadan yace" arent you hungry nifa yaunwa nake ji.

Adan harnzar ce tace serving zanyi.
Baice komai ba ya matso gefen ya suma jeru da juna suka tsaya kamar tare zasuyi komai,

Hannun sa ya sa ya dauko 2 spoons da forks ita kuma ta dauko 2plates farare ta jera yana kallon ta ta zuba a plates daban daban.

'Jin hannun sa tayi akan nata wani plate din ya dauka ya maida abincin waje daya,kallon sa tayi yana juya hannun ta kamar mai koya mata zuba abincin ba wanda ya tanka sai da ya gama yace"yaya da harara ta?baki ji dadi ina tayaki ba ko?ya tabe baki yayi kwafa

Dan Boye face din ta tayi Ta dan turo baki a sakalce,ciki ciki tace ai zan iya,bai amsa ta ba ya dauko plates din ya kamo hannun ta da hannu daya suka dawo palour.

Daga tsaye yace go get some water "
Tace toh ta juya ,kafin ta dawo ya zaman sa a tsakiyar falon abincin ne agaban sa so cute ya nade kafa yana jiran ta,

Goran Mixed Citrus drink da na normal botle water ta ajiye gaban sa tare da 2glass cups.
Irin kallon dayake mata yasa ta zauna itama

Sosai abincin ya shiga ranta ga yunwa amma sai tayi shiru bata motsa ba'bayan ya dauki cutleries bismillah yayi ya kai bakin sa,sai da yayi 2 spoon ya dube ta baice komai ba ya debo quantify amount ya kai mata baki..

She can't resist his sexy infidel eyes sai ta bude bakin slighty ya turo mata ta amsa,....

'Wani lumshe ido tayi ta kumtsa shi abakin tukun,sabida rabon ta data ci mai dadi har hakan tun jiya da safe

Jikin ta ya bata hannun hjy mamah ne yayi wannan girkin but how comes?Waya fada mata suna bukatar abincin ko mai ya faru oho?...

'Cikin wannan tunanin taji yana cewa bazaki min rigima ba u have to eat,sai ta dago ta kalle sa...
Wani abincin ya kawo saitin bakin ta,anan ta sa hannu akan nashi zata karba..a tare suke nutsar da idanu cikin juna zata dauke nata...

yyi smirking irin ai kinsan dalilin baki abinci abaki u won't get that chance tomorrow...cikin yauqi ta dan makale kafada tana laulayar da idanu cike da shagwaba
Tace,..ai zanci da kaina murmushi yayi haka kawai ya mika mata spoon din suka shiga ci tare gwanin sha'aawa...'
Shiru ne ya ratsaa wajen"
Zan daya gwafi idanun ta sai ya fara tari tamkar wanda abincin ya shake sa....da wuri ta dago ta zuba ruwa a cup yana miko hannu, ta lura da tarin iskanci kawai yayi dan ta dago ta kalle sa.
...sai bata iya mika masa ruwan ba suka tsaya kallon juna..wani kunyar shi ne ya lullube ta ta dukar da kai

Shikuma haka kawai yaji a duniya ba abunda yake masa dadi kamar duk lokacin dayake tare da ita.
Her warm and innoncent eyes..ta sunkuya kadan sai ya murza hannun sa akan nata yace thanks"tare suka sauke cup din kasa ba tare da yasha ruwan ba.

Kif kif take yi da idanun ta cikin saibi...
sometimes sai Ya lafe yayi lumui yasa ta basa abincin baki...duk dama bata son hada ido da shi amma yanayin su yana mata wani iri,
Sai taji kamar soyayya ce mai karfi ke son tashk tskanjn su

Shikam ko ajikin sa sakewa yayi yana debar yanayin da jin dadin kasancewar su ya taho masa da shi a zuciyar sa.

Sunyi kusan rabin abincin tare da shike ma dukan su ba maciya abinci dayawa bane
Ko da cikin ta ya fara cika nan tafara kokarin saka ruwa a dayan cup sai yayi amata alaman shima zai sha ..nan ta debe a tsanake satan kallon sa take cikin mamaki aranta tana tabe baki,'irin kallon daya mata yasa bata tsaya ba hannun ta akan nashi takai baki bata wani sha dayawa ba yayi hamdala alaman ya koshi.

Shirin ajiye nata spoon din take yace hold on?
Meye hakan...ta dan kalle sa tace yaya na koshi ne.

Yace Baki isa ba,yayi mika yana kokarin komawa kan cushion da zama...shiru tayi tayi zugum ta sake baki a shagwabe tana taro ruwa idanun ta...
Ci zakiyi fa..ko dan kinga bake kika girka ba zaki wulakanta?..
Kyabe baki yayi haka ya sata taci dan dole da a ranar ma da hawaye suka rabo kowa yayi site dinsa.

Tsokana ta yake tayi cikin boyayyen raha don ana ne take jin cewa nimrah tafiya tayi.

Sai dai ita haka kawai take jin haushi idan yayi comparing dinsu don ta tsani yadda yake nuna nimrah ta fita iya komai.





Haka rayuwar su ya kasance cikin kwanaki hudu,bai sake kusantar ta sexually ba,amma duk wani aikin gida mopping yakan karba ya taya ta..,haka a kitchen tare suke serving din abinci ko kuma yayi zaman sa shiru yana kallon ta tana yi

Daga tarairayar dole har ta fara ganin burgewan abun ajikin sa,musamman yau da tafito tayi saurin kammala wasu aikin ta bule gidan da turare masu qamshin fitinah ko ina yayi warm ..
Sai yake teasing din ta cewa,bata so ya taya ta aiki wato zata hana sa bin sunnahr manzon Allah S.A.W.

Sometime kallon sa ma bai isan ta.
Yau ake kuma cika sati guda da tafiyar nimrah...

Misalin karfe 9 na safiya ne,.. sanye take da da neat white silky nite gown wanda yakai zuwa rabin gwiwar ta sai ta daura karamar hijabi akai Ta rufe kirjin ta,..

Dakin Sa ta nufa Kayan sa dake kan gado
Take nadewa don yau ta makara don ko fitowa bayan sallahr asuba bata yi.


Shima Da alaman yayi fitan sauri,haka har ta gama ta gyara masa gado ta feshe dakin da turaren wuta dana kanto masu dadi ta fice bai shigo ba.

Daga nan Ita kadai ce har wani wajen karfe 3 da rabi na yammah,haka kawai taji hankalin ta ya tashi da taji shirun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login