Showing 126001 words to 129000 words out of 245996 words
nasa yayi yawa.
Da kyar ta yanke hukuncin neman layin sa
Wani mummunan yanayi zuciyar ta ya shiga dataji ma baya shiga
"Daga nan kuma ammyn sa ne ke famar shan bakin nimrah agaban sa,tasan bazai kula ta idan ta dawo ba shiyasa daga saukar ta a airport ta sauke girman kai tanifi wajen ammyn sa da magiya da korafi cewar ta tana neman alfarman a barta ta bada anisah lokacin ta wajen taya ta shirye shiryen auren ta dake gabatowa in 3weeks time.
Da shike ta kwarance wajen hada makirci sa juya zance kafin ya iso tayi amfani da damar ta wajen fahimtar da ammy cewa tana haka ne sabida abun na family ne badon zallan kawancen su ba.
'Irin wayannan moves din da su take dada murza game din ta wajen samun kwarjini wajen hjy mahnoor
Ita sai taga kamar nimrah ta damu da komai dangane da famyln sa ne amma shi bai damu ba
alhali ita da aneesahn wani shu'umin hutu suka shirya zasu je na huce haushin rabuwa a kasar uruguay kafin su dawo a fara shirin biki mai gaba daya.
Yaji haushi sosai dan sam baya yarda da nimrah farat daya,kuma sosai yake gane munafurcin dake furucin ta
Ko da suka fito ya tambaye ta,wato ta zabi hidiman biki akan zaman gidan mijin ta ....
wani borin kunya take tana hura hanci cewar ta ai fushi yake da ita daga cewa zata kara kwanaki agidan su shieknan ya dena kiran ta awaya,
Wani shan qamshi take"manufar ta data bashi hakuri ta lallaba sa akan abunda tayi.. gwara ta kara da gaba kawai
Tsaki yaja kawai yayi gaba ya barta nan.:
"Ko da ya dawo gida ita kanta banafshan takasa gane kansa...
Annuri da sauyin data gani na kwana biyu chak ya yanke duk dama baiyi affecting dinta ba, amma shirun da daure fuskan dayake yi yasa ta dada jin wani iri.
Normally yayi cudling din ta har tayi bacci,da asuba tanaji ya kwace ta daga jikin sa ya gyara mata kwanciya ya shiga toilet ya kImtsa ya fito ya nufi massallci.
Yana fita ta mike agurguje tayi nata dakin wanka tayi ta hado alwala tana tada sallah sai gashi ya turo kofar ganin tana sallah ya ja mata kofar ya fice..
Yan shafe shafen ta tayi ta kimtsa tsaf cikin doguwar rigar dubai fashion baka tasai ta sauko da veil din a zageye da wuyar ta.
Breakfast mai ji da lapya ta shiga hada musu,dama flour tayi ta hada zucchini crust da garlic sauce mai dauke da jajjagen kifi,chicken casseroles dan dai dai a gefe sai washegiyar kunun daka wanda taji kayan qamshi wanda tuni ta kara dama masa shi da madara.
Tana aikin sam bata jin dadi sosai..har ta fara kawo aranta ko ita ce ta bata masa rai.
Sai da ta gama ta nufo dining da shi,lumshe ido yayi jin qamshin abinci yadda ya cika ko ina a wajen..tasowa yayi yana tsaye Sai da ta ja masa kujeran ya zauna sannan itamaa ta zauna.
Kunun ta fara serving dan dai ta mika masa kafin tace me zan zuba maka"
Kallon ta yake yi ransa cike da tunani kala kala"she's an angel"haka ransa yake furtawa...a takaice yace 'anything"ba musu tA Zubo masa daga duk abunda ta girka cikin nitsuwar da ya kara nuna masa cikakken home training dake ajikin ta.
Sai da ta gama da shi kafin ta zuba nata,ita ta riga shi gamawa amma bata bar wajen ba saida ya kammala sannan ta shiga tattare kayan zuwa kitchen...
Dawowar ke da wiya ta same sa yana famar goge bakin sa da white food napkins.miqewa yayi yace "ki je ki shirya yanzu and don't waste much time.
Cikin dan mamaki Tace 'yayah in shirya fa kace ...ina za..mu..je ta karashe da dan fargaba a muryan ta.
Wayar sa ya tarkato ya sa a aljihu ya dube ta a takaice yace "South africa.
#Surayyahms
*Barka da sallah again my people fatan kowa na lpya,of all the chats i missed my whatsap fans sosai dan anan ne natafi absent tsawon lokaci bani nake muku posting ba.. naji sakonnin ku da coments dinku da birthday wishes dinku wasu ma nayi dariya sosai sakallahu khairan.*
*Toh Allah cikin iko sa yasa nayi settling ina kuma mai muku albishir da cewa da kaina zan fara posting novel din ajalin so a whatsap grps daga weekend mai kamawa insha Allah.SAI DAI Wani hanzari ba gudu ba,zanyi typing akan lokaci da izinim Allah amma MASU Karanta labarin ku sani muddin nayi post a group ka karanta kayi shiru babu comments to fa sai dai wata tayi post ka karanta awani wajen.. Bazan dai fita a grops ba amma Duk inda za'a karanta kuma Ba'a kwaments toh BAZAN YI musu post ba"ba nayi hakan bane dan na takura kowa noo, sai dai wanda suka bada gamsasshun dalilan su akan nayo musu labari na kudi nan gaba' ..hmm toh amma duniya da mutanen ta kaf basu da tabbas kana farawa sune farkon wajen zagin ka matsiyaci bla bla bla"yin comments ko rashin sa bazai sauya ra'ayi na akan komai ba.. amma tunda na zabe shi Ku ma ina bidar ku da kuyi Adalci... Mutane na whatpad da nake tare da su i cant just describe how grateful i am kunso ajalin so kuma kuna kai more votes more happy times...nagode*
#Expect Next update weekend#
*🍒🌺AJALIN SO🍒🌺*
_Xplicit romance_
*WATTPAD SURAYYAHMS*
32
_trip to S.Africa part 1_
Dan ware dizzy clumsy eyeballs din ta tayi cikin mamaki' da taga har ya bada baya zai haura sama..
hanyar step din dakin sa ya nufa yana cewa be fast ko na tafi na barki ne ...?
Tana shiru sai Ta amsa da girgiza kai alaman a'a itama ta juya ta nufi dakin ta,ko da taje duk sai ta rasa me zata dauka guda daya.'trip to southafrica for what? Nan ne bata fahimta ba
ta kai wani 20minutes tana zagaye da kyar ta jawo handbag din jimmy choo kalar matte black ta fara zuba atms din ta da tarkacen cards da jeweries wanda basu fi biyu ba,..sai kwalban wani after bath traditonal scent da turaren humrahn ta shima guda biyu.
Tuno da dirty dishes din da suka ci yanzu yasa ta sauko kitchen ta shiga wanke wanke tana wiping tana jerawa dan kr ta barsu suyi tsami
In not less than 10minutes ta kimtsa wajen tana fitowa suka ci karo da shi a bakin stairs.
Daga nesa kadan ya tsaya alaman ita yazo dubawa bai ganta ba yake shirun saukowa..Tana kallon sa yana kallon ta,kyakkwan siffar idanun ta ta ware gaba daya tana kare ma dressing dinsa kallo...
"Wasu fitinannun kananan kaya ne fari da baki na kamfanin adidas ya kwama ajikin sa mai tafe da wata shakikiyar farar facing cap da sneakers baka kirin mai farin good logo.
Irin kallon data tayi masa sai da ya dan tsargu sai ya dan kalle kansa in quick glance...ko dai banyi mata bane ya dan ja iska ta baki aransa yana harsashe,first time dayaji fargaban dresing dinsa agaban mace duk dahaka idonsa na nan fixed akanta...
A takaice yayi scoofing ya kau da kai cikin jan aji
fahimtar fargaban data sa masa da idanun nata ya sa itama ta dauke kai"sai da nace miki kiyi sauri ki shirya..ya furta da slow but stern voice
A sadade tace eh dama kitchen naje nayi wanke wanke...baice komai ba
Itama bata motsa ba chan ya dube ta tare da galla mata harara "wai Jira na kike na zo na shirya kin?
Kafin ya kara wani word tayi gaba zuwa dakin ta.
Sauke ajiyan zuciya yayi
Ya biyo bayan ta,wayar ta ya dauka zai jawo hannun ta su fice sai tace yaya my bag?plsss... ta dan marairace ..bai sake hannun nata ba ya dauko mata bag din tare suke takowa har suka kai bakin motar ua bude mata ta shige ciki
Rufe idanun ta tayi da hannu tana jin haushin sa while yana kammala locking main house din,wato shi ya gama cin kwalliyar sa ita kuma ya barta da dogon riga ko ?kyabe kaii tayi taja tsinin baki.
'few minutes drive Har suka isa aiport tana kumbura fuska kO ajikin sa sai ma ya share ta yana harkokin sa.
"itama shiru tayi ta dauke kanta akansa Don haka ne ma bata san komai game da sirrin tafiyar nasu ba
Daga gefen sa ta zauna ayayin da yayi fastening mata belt dakan sa, ko da jirgin ya tashi time to time tana biye da idanun sa dake satan kallon ta wani bin su hade ido wani hin pretending take kamar tana bacci.
After few hrs suka diro wani kasar alaman babu nisa sosai daga Nigeria,bata taba zuwa wani African country ba don haka bata gane ina suka dosa ba.
Ko normal arrivals basu bi ba bare taga sunan airpot din
Nan taga an taho an dauke su ta sashin private exit a wata mota kirar ford formatic jeep..
_agogon hannun sa ya dage sama ya duba 'GPS location: Narok, kenya._
Sannan ya daga wayar sa ya shiga amsa kirar dake faman damun sa tun saukowar su
Bayan dan Wani lokaci taga an sauke su a wata hotel mai taken ' _Sarova mara GC: narok county kenya,_
Nan ne ta gane ashe ba south african suka iso ba kenya ne,wajen ya hadu iya haduwar da zaka so ka zauna nan har iyakan karshen rayuwar ka.
Bayan fitowar sa daga motar Wani private resort ya nufa da ita mai kofofin glass da walls da decors din hutawa na gani na fada,
shi tun daga gida yayi booking reservations din sa da komai da komai online da shike ma ba zama zasuyi anan ba...
yace ki shiga ina zuwa ya mata nuni da wani waje alaman daki ne...
Daga nan Sai ya fice.
Sama ta haura ita kam"'tana turo kofar wani sanyin dadi ya ratsa ta
dakin nasu an hada masa shiri mai tsafta
kan lallausan tuffed bed din ta zauna tana kalle kallen cikin kafin ta mike izuwa window view don ta hango abubuwan ban sha'awa dake shimfide a oudoor landscape..
Its so amazing...bata tabayin tunani a kasa kamar kenya za'a samu luxury hotel har haka ba.
Bata hankara ba taji yace u like it?...ta danyi murmushin bazata ta juyo..sai jin shi tayi daf da ita,hakan yasa ta dan kalle sa,
C'mon lets go...'ya fada cikin sauki ya kamo hannayen ta zuwa sitting room inda suka baro.
Wasu yan maza tagani suna shigowa da packaged shoping bags a sanye da kaya kamar na indian police force sai dai shi plain ne
' Yayi mata ido akan ta dauki wanda zata iya ta koma ciki,nan ya sallame su ya biyo bayan ta.
Zata ajiye yace kayan ki ne,u have to check them and c inyayi miki ko kina da wasu wanda zaki sa ne?"a shagwabe tayi masa kallon ai baka barni na dauka ba kafin tace ah a,..
hmm kawai yace ya juya mata baya
Nan ya shiga rage kayan jikin sa,tana tsaye har ya nufi toilet ya sake shower akan sa sannan ta fito da kayayyakin.
Wildrose hip up skirt guda daya da Fellini trousers royal blue sai tops da madaidaitan hair covers dinsu wanda suke matsayin mayafi sai inner wears pants da bra guda biyu da normal sandal shoes..
"komai yayi mata anan.. dan Da wuya ake samun irin wannan brand din kayar sabida mostly illegal shippers ke shigowa da shi daga design industries a india.
Bata gwada ko daya ba dan yawanci size din ta ne Yana fitowa ta shiga tattara kayan zata ajiye a gefe' yana goge kansa da hand towel yace ya baki gwada ba,
Bata son cika kallon sa a wannan yanayi amma sai ta daure tace,na duba zasu yi min"..
Yayi shiru alaman yaji sai tace..nagode' yayah..
a takaice Yayi grin.. tare da umartan ta akan taje itama ta kimtsa tayi sallah.
Agurguje tayi da jikin ta kammala komai da shike ba inda zasu je kuma lokaci ya tafi..
royal blue fellani trousers din ta kwama' irin wandon nan ne fubu masu fadi da tsayi,akai ta daura farar long sleeve shirt tayi tucking kamar yadda ake sawa
She looks serene and simple Tayi kyau sosai duk da ma babu kayan kwalliya sai chappets din data goga akan lips dinta
shigar sosai ya bayyana yarintar ta akan tsari
Just in time yasa aka shigo musu da abinci site din,don sam baya son fiye shiga mutane.
Daga nan Bacci mai nauyi tayi Bata ma samu daman ganawa da kowa ta waya ba.
Washe gari da safe sosai ta huta ma ranta bayan sun kammala komai awaje aka shirya musu breakfast a wata outdoor open air bungalow su biyun su..
'Fresh fruit juice da cooked egg and veggies'hade da sarova mara special akayi serving.
Wasu ma bata iya ci ba suka tashi suka koma daki don tun bayan sallahr asubahi yake ce mata zasu fita wani waje
kayan sa ya sauya daga karamar pitcher pink trolley da bata san sanda aka kawo sa ba, itama skirt din daya rage ta kwama da jacket top tayi rolling ta saka sandal din ta.
Humrah dama ta riko dan haka suka dai ke qamshi ajikin ta.. tayi kyau kam amma a duk sanda yayi nashi shirin sai taga kamar bata kai ba,gashi duk sai tayi fayau idanun suka fito da babu ko dan powder akan fuskan ta
Ya dan kalle ta duk ya fahimce me take ciki aransa ya tabe baki,sai ta dan turo bakin a shagwabe tana wasa da yatsun ta ..yace'muje ko?cike da yauqi ta jawo jakar ta tace ok
'Its around 10.45am na safiya Nan suka fita cikin wata sport car kirar Lamborghini ja da baki mai shegen kyau
..,daga nan suka isa wani waje wanda taga an rubuta _south west,kenya. masai mara national park reserved_ "
'kallo take bin ko inna da shi kamar idanun ta zasu fice in amusement ta furta sunan wajen adan bayyane tana kallon sa da alamar tambaya.., a takaice ya gyada mata akai in confirmation yana mai cika gaba da driving dinsa
Murmushi tayi kanta na kallon waje ta window along the line taga anja layi wato boader dake tsakanin su da Tanzania'
Sai wasu few settlements wanda ake ce ma enkangs of massai people wato village of masai tribe.
A dai dai entry yayi slow down hannun sa data ji akan nata ya sa ta dago ta kalle sa...Giran sa ya dage mata so charming wanda ya sata sacewa
Ta so ta basar da shi amma duk sanda ta duba yadda yayi kyau sosai a cikin pink tshirt dinsa sai takasa tabuka komai.
Theres no daubts that har cikin ranta tana alfahari da haduwar mijin ta .
Murmushi yayi mata yace i hope dai kin boye tsoron ki a gida,anan wajen akwai abun da zasu cinye ki...karamin murmushin itama tayi tace yaya anan Zaka barni ka tafi?
Yace,ehmm in kina so..i will,but u have to wait and see idan zaki iya zama
Tayi ajiyan zuciya a bayyane ta tabe baki,..wajen parking motoci shima ya ajiye sannan ya kashe motar ya dube ta,wani irin kallon kallo suka watsa ma juna mai sanyi da muna alaman farin ciki azukantan su,hannun sa yasa ya dan gyara mata veil din 'yace ready?wani asirtacen murmushin ne ya kufce mata Tace uhm..
Nan suka sauko suka nufi inda ake tourism services.
Ilahirin Wajen savannah wilderness ne dan haka akwai lions, cheetah hippo.. da zebras..
Wajen plain grassy landsacpe yayi da ita,inda akwai rolling hills da crossed river na mara and talek.
Basu kadai bane akwai foreing tourist da sauran mutane dai dai ku,sai dai kowa harkan gaban sa yake.
Its so beautiful ta fada da fara'a hannun ta acikin nashi tana kalle kalle.
Yace ehmm, to ni banan nake so ba,tace ni nan nake so yace ok ki zauna anan ni zanje inda nake so.
Da mamakin sa yaga ta gyada kai murmushi yayi ya barta anan ya koma fannin wild park life
Zaman ta tayi har sai da ta gaji da nan gashi ta samu yaran turawa yan iyeye sai selfies suke cikin jin dadi.
Wani pub yagani ya shige ciki direct wajen siyan ice creams da drink
Kiran sa ne ya yanke mata hanzari ta dauka yace me zakici?..tun kafin tayi deciding yace come over...ya kashe wayar sa.
Tsaban ta raba hankalin ta a wajen, Bata san ta ina yabi ba sai kawai ta bi kwatancen yar baturiyar tana tafiya
Farko taga zebras sun bata sha'awa soai,tana cigaba da tafiya ta cigaba da ganin sauran namomin jeji,
duk dama tana son gani amma tsoro ne ya fara damun ta...charaf taji an riko ta wani irin firgita tayi zata fauce da gdu yace "kamata"..ta dan turo baki tayi dariya.
Kafadan ta yayi sliding da nashi ya juyo yayi mata light kiss yana cewa wata rana zan daure bakin nan..a kunyace ta boye fuska suka shige ciki...
anan ice creams din kawai ta karba suka fito tana tambayar sa akan wild animals din sama sama.
Yadda yake bayani Har takejin sha'awar ganin su sai suka je tare,a karon farko data ji gurnanin lions a cages dinsu sai ta kankame rigar sa..
,yace ai dole ne muje ki gan su...
Suna fitowa sararin inda suke tayi saurin komawa bayan sa tare da furta innalihhi wa inna ilahi rajiun...ido ta gwalo tace yaya mu tafi ta karashe da rawar murya..
,dariya abun ya bashi amma baiyi ba anan akwai irin ta dayawa masu tsoron hakan...
yayi yayi ta dawo gefen sa amma taki,wata karamar yarinya da batafi seven years ba yagani achan gefe da su rataye da kafadar mahaifin ta tana videoing din lions din amazingly.
Yace look,kinga abunda takeyi' gaki nan katuwa kina boya abaya na.
A hankali ta firta eh din,..ta lafe da jikin sa a sanyaye..sai ya ciro wayar sa ya fara videon
mike wuya take tana leke ta bayan sa.. cahn yace c'mn zo kiyi mana kema,'ta make kafadar ta alaman a'a
amma tana ki tana so haka ya jawo ta jikin sa sukayi facing lions din,
fatar wandon sa ta kankame sosai tana numfashin tsoro,ta lafe da shi tamkar wancce zata koma cikin ruwan cikin sa..
ga lions din sai ruri suke surutun mutane da camera's na jan hankalim su'..
kansa ya daura a kafadan ta,ya zageye ta da hannun sa wani lumshe idanu tayi Ta sauke ajiyan zuciya a boye"yace oya shoot ur shots in munje gida zaki nuna min nagani..ta dago ta dan kalle sa alaman toh kar Ka sake ni..
'daga