Showing 210001 words to 213000 words out of 245996 words

Chapter 71 - AJALIN SO BOOK COMPLETE BY SURAYYA.txt

07 Aug 2025

6573

shima Kuma kallon ta yayi

Kai Lpyar ku kuwa?Ya fada da dagon murya Yana kallon yanayin su...

Cikin wani munafukin kuka mai kunshe da sinadaran makirci Nimrah tace Mohan na shiga uku,ohhh thank god ure here, walllhy
Matar ka zata kashe ni.

Cikin kuka Banafsha Ma tace karya kikeyi zaki kashe kanki dai

Wani sake baki Nimrah tayi har yana bari Yana zubda yawo, tace Daga cewa ta taimake ni tabani pcm shine zata hado min da wani maganin?

Cikin kukan tace mohan Look at me,i don't know what's happening Sai bleeding nakeyi,mohan i think lost my baby ..jinin dake bin kafar ta talakato a tafin hannun ta tana kukan fitan rai tana kallon shi kamar ta zare.

Tunda Banafsha taji me take cewa ta shiga shock Tana kuka bata farfado ba A durus ta tsaya ta waro ido tana kallon nimrah ji take kamar Komai a film

"anty Ki kace Ni Banafsha na baki wani magani?Ta iso gaban ta a hargitse,are you mad or something?Inaga fa baki da lpya ke Ki fada masa abunda kika ce min Mana?
Why are you implicating me For god sake

Sai Ta dawo gaban sa tace
Yayah She's lying To you,ai tace plan takeyi Dan ta raba ni da kai, yanzun nan Fa Ta ce na bata magani bata jin dadi what will i gain da har zan baki maganin zubda ciki..? A mugun fusace Banafsha ta fada dan bata masan ta fada ba,.

Mohan shiru yayi yana mamakin su,he was like so sun ma zubar da cikin?

Banafsha kuwa kirjin tane ke bugu tuni taji hankalin taya tashi dayayi mata shirun

Ga Nimrah sai tsuma take Agaban su tanacewa cikin ta cikin ta ancuce ta

Cikin takaici mai tafe da bacin rai,Tace Kema Baxaki fa fada masa gaskiya Bako? ni bansan meke damun ki ba kuma baxan dauki alhakin komai ba

A haukace Nimrah tace shut up bitch,muguwa kawai azzaluma walllhy nafi karfin munafurckin Banafsha

u cannot cheat me twice,ga asaran ciki ga munafurci da karya ?yaushe nayi miki magana

Ai dama nasan baki kaunata,komai xaki iya cewa,Wato dan kin san nafiki gindin da zai haifo Da namiji shine bari ki cika mumman burin ki akai na ko?

Wani yunkuri Nimrah tayi kamar zata tashi ta cahkomo Banafshan sai kuma ta xube akasa ta kara sa da ihu tuni jinin ya fetso sai gashi tafara karkawa

"Shikam tsaban mamakin su sai ya zamto musu dan kallo,nimrah najin jiki amma haka ta zake tana cewa Banafsha ta zubar mata da ciki dan bakin cikin zata haifo da namiji..

haka itama Banafsha ta zage tana cewa bata san da hakan ba,karshe kuka Kawai ta fashe da shi Bata iya cewa Komai
Nimrah ta xautar da ita tasa ta bayani har makokoron ta na mata zafi Har ciwo kanta ya soma yi tasan inda da halin da zuciyar ta zai fado kasa Shima da tuni ya sauko,

Yana shiru

Sai da suka gama musun su Sukayi shiru,ya tsuguna gaban Nimrah yana observing zuban jini,

kafafun ta ya dan ware kadan sai ya ciro handkerchief daga aljihun sa ya dan share jinin da suke biyo sawun kafar ta
Ya Bashi critical look...

Dan sosai Ya dago furucin kowa gani yake kamar Yasan mai gaskiyan acikin su

Nimrah Sai wani washhh washhh take,cikin kuka tana cewa wallhy bazata yarda ba.

sai ya daga ido ya kalle ta yace Nimrah relax Pls zan kira aliyu yanzu yaduba ki ,ko kinajin jiri ne?,tace ba sosai ba Kuma wallhy sai ta biyani baby na..yace to ki nitsu kifada minene ya faru Kar kuma naji Muryan kuka

Nan ta sauya kama kamar tsohuwar makira tace"..naxo gida kaina na ciwo nace ta taimaka min da pcm bansan me tayi ba daga nasha sai nafara bleeding,Ni nasan dai aruwa kika xuba mun wani abu

charaf Banafsha ta yanke maganan tace ohon miki,nidai ba abunda nayi miki kuma kema kinsa ni,Aniyar ki tabiki abunda kike so Ya faru dani bazai Faru Dani ba, mugu..wa kawai

wani mugun kallo ya dago ya bita da shi yace waya Sa bakin ki?
Ina wasa dake ko?

hawaye masu xafi ta sauke ta dauke kanta Gaba daya jikin ta na karkawa

wallhy ciki na ya zube bazan yafe miki muguwa kawai...

Yace Nimrah, its kk muje dakin ki kijira shi anan ina xuwa.

Tallafo nimran yayi akafadan sa
suka fita su ukun
Banafsha na bin su a baya gaba daya abun duniya ya dameta

Ashe dama haka take?babban munafuka,har agaba na ma tana hada min Sherri,?kawai dama tana so yaya ya daura min laifin komai ne Ya kOre ni..

Mohan Aje ta yayi akan gado,ya nemo abu ya goge ta dashi

wayar sa ya cire yayi kira aka zo aka duba ta inda Wani doctorn daban ke tabbatar masa da lallai wani magani mai karfi tasha a ruwa ya zubda mata cikin...

Alluran da aka mata Alokacin ya na sa ta layi amma Haka ta bude ido tanace masa Mohan kaji ko?

Ko likita ya fada ita ce tabani maganin Im sure acikin ruwan ne..

Banafsha sai jikin ta yayi sanyi rungume da babyn ta ba abunda take sai hawaye

....a haka Har nimrah tayi barci bai juyo ya kalle ta ba..
Maganganun da Nimrah tayi tayi yayi mummunan mata illah Acikin ranta

Ita hurts her to know that gaskiya yana gaban ta amma bazata iya bayyana Ma kowa yagane ba"

Tunanin makomar ta take Tayi A wajen mohan,Don tasan bai isa yace ua gane kan fadar sun ba,abu daya ne Kawai afili Shine Nimrah ta laka mata alhakin zuban cikiN ta

...sai da Taga ya mike xai koma dakin sa tayi sauri ta aje babyn ta biyo bayan sa...

Tace Yaya,...yaya mohan pls wait and hear me out"basar da ita yayi...bai tsaya ba sanda ya bude kofar dakin shi,..

Wasu mugayen kallo yabita da shi,a sukwane ta dago ta Kalle shi
Tace Wallhy ba haka bane ya faru,ita ta ce na bata maganin zata sha bansan niyyar ta bakenan da bazan bata ba"She said she wanted to ruin me...Allah kaji na rantse maka Sharri take min.

Cikin dakewa Yace ok doc ma yayi karya kenan?
Kin bata wani abu ki baki bata ba

Tace eh, ai shima baisan abunda ya faru ba..."Yaya kayi hakuri kar kace na xubda mata ciki wallhy banyi hakan ba

...da taga irin kallon dayake mata har kasa ta nemi silalewa tana kuka xata roke shi,hannun shi take da niyyar kamowa yayi saurin kwacewa ya hade rai,,a masife yace don't you dare touch me again,"kin dauka xan kashe kaina akan ki ne?...im not even surprise inkinyi hakan
Ba abunda kika
Ga dama shi kikeyi ba?,ok Allah ya bada sa'a,..and just get out of my sight....right now.... ya daka mata tsawa dai da ta razana taja gefe

a rude tace yaya no,pls don't take it that way wallhy walllhy karya anty takeyi min,i just helped her dan naga bata jin dadi kuma ita tace nayi mata hakan bansan mesa doct yace maka nabata magani ba..yanzu har ka yarda zan iya yin haka...?

Kukan Ta sosai yaKe Ruguza saitin brain dinshi Da shike hankalin sa da tunanin sa basu kusa Shikam Baima jin me take cewa kawai sai
Yace eh,and i said get lost bana son ganin ki nace ko?Tsaki yaja...zai rife kofa tasa hannu zata tare ko ajikin sa ya buga da hannun nata saida tayi kara Taja da baya..

Anan ta xube a kasa Tana kukan Tana tapping kofar sa Tace Yaya mohan Pls don't send me Away,kayi adalci ka ji abunda zan fada maka,yaya Mohan Pls Open the door...Kayi hakuri Kaji?Pls im sorry.

Haka tayi tayi har ta gaji tayi shiru,

ShIma Bai iya motsawa ba Tun tuni jingine yake abakin kofar ya lumshe Ido yana jiyo ta.

Banafsha Sosai ta zuciya Abun ya matukar kona mata rai,sai Shessheka take tayi shame shame akasa tana zaune A kofar dakin sa..cikin ranta take cewa yanzu ta hada ni da shi kenan?in ya kore ni A gidan sa fa?She's a devil,She used Me...
munafuka Ce kawai shegiya,makira annamimiya Muguwa bazan yafe miki Ba, kuma bazan bar gidan nan ba..
Hawayen ta ta goge tas Kasan makoshi ta Furta
Ai wallhy kuwa bata isa ba,sai ta gaya min yaushe na bata maganin xubda ciki Kona xame mata Babban fitina agidan nan..a masife ta tashi ta nufi dakin nimrah fuuh ta bangaje kofar Babu ko tsoro aranta..

Gani tayi har bacci ya debe ta,bata hakura ba dan kwata kwata bata yi tsammanin haka Asalin halin Nimrah yake ba..

Yarta ta dago ta rike sannann ta shiga kallon nimrah dake bacci tana cewa

"I was respecting you sabida na dauka kin girme ni ashe ke banza ce Baki cancanci komai daga waje na ba girman ma nafasa baki

Kinyi kuskuren nuna min kazamin halin ki in rashin imani kike ji dashi wallhy nafi ki,..ashe har xaki Iya zubar da ciki dan kawai ki hada ni da miji na?,only god knows wHat uve been Saying to Fool me agaban sa Im sure that's not all,...toh da kina ji na da bakiji na
Ki sani kinci bashin da bazai Taba wuce Miki awuya ba,

I will teach you a lesson you won't eva forget...

Daga ni saike a Wajen yaya mohan,Daga yau sai kin gwammaci da baki Fada min Ke wacece ba bare ki hada min wannan sharrin rainin wayo,u think im a fool,toh even a fool at forty cannot be a fool forever

Uve Bring It on Ko? i will take you to the finish Insha Allah da bakin ciki na zaki bar gidan nan.

Wani zazzafn Tsaki taja a xuciye ta wuce dakin ta,akan gado ta Ajiye maysam ta Shiga rarrashin ta Har tayi bacci

Just 3months da haihuwar ta amma har yanzu babu Wani sassaucin da ya shigo mata

Mikewa tayi ta doro alwala ta yi nafila Tana rokon Allah,zuciyan ta cike take da tsoron matakin da mohan zai dauka akanta gobe,gashi ta kwallafa Son shi aran ta,ji take Kamar idan yace Ya sake ta ta bar Masa gidan zata iya zarewa.

gado Ta koma tana mai cusa kanta cikin pillow tana kukan zuci,..yau Kama tasan ranta
yayi matikar baci

Ita banda tsoron Nimrah datake ji Tuntuni ba Da babu wani mumuman zargin data ke mata akan komai tsakanin su

...sai gashi Nimrah ta bata mamaki yau ta nuna mata wacece ita boro boro

Tace uhmmm,ai daga yau ko mutuwa take Na asali bana kara yarda da ita,shima Mijin da take gadara akai sai na kwace shi kuma nayi yadda naso dashi

Idanun ta har sun haura tsabn tayi kuka Juyi take ta furta,.hmmm she think she's smart ko har da cemin dump mswww,i maybe dump, but im not stupid.

Da safe ma haka ta tashi da shi aranta..Sosai tayi zuciya.,sai dai ko kadan bata jin zata hakura ta karbi defeat

instead ma wani karfin gwiwa take ninko ma zuciyan ta nacewa lallai itama sai ta nuna ma nimrah irin mata salon kissar Komai ma yafaru bata damu ba

Shikuwa mohan Tun jiyan ya kasa aje kansa Waje daya bare ya yarda cewa Banafsha xata iyayin haka Ma Nimrah

But Wani zuciyan nace masa kar ka amince da mata kishi ma kawai yana Iya haukatar da tunanin su,su aikata komai

Ajiya cikin daren Faisal ya kira

Tun Kafin Faisal din ya shigo Sai yayi packaging Handkerchief din daya goga jinin Nimrah akai ya rufe Awani envelope

sai ya ce masa kayi Sauri ka kai ma aliyu Wannan sakon kafin ya bar asibiti.

Yace yeS sir Ya wuce Ya tafi

sako ya Zauna ya tura ma aliyun Mai dauke da Kalmomi kamar haka

"Dude,nasan xaka iya gane min siffar Wannan abortion din,I want everything In details And i want the result Today Xan jira ka a kofar gidan ka by 10ocl In ka tashi.


Daga nan Wanka yayi,ya fita agidan bai sake dawowa ba sai da 10 na dare yayi ,ya nufi wajen aliyu.

Acikin mota suka xauna ,Dr Aliyu Ya mika masa report,yace Mohan What's going on Ne?Jinin waye?

Mohan Bai Amsa Saida yagama karanta result din Ya lumshe idanun sa tare da sake ajiyan zuciya yace Aliyu Nimrah ce ta zubda ciki and she was claiming that Yar uwan tane ta zubar mata

.....AliyU yace what?Nimrahn bata da hankalin ne Da Banafsha zata bata drugs harda pill Dinshi?

Yace Bar rainin wayo, i just found Out now Dama kawai gaskiyan nake so nagani
,tace wai pcm ta bukata Sai ita kuma wancen ta bata wani..

Aliyu yayi dariya ya kada kai yace But this Result isn't saying that at all,ko ba kagani bane?
Wannan Cikin nata ma anxubda Shi almost 16hrS ago..Jinin ne kawai aka ingizo

To meyasa Ita Nimrah take haka Ne?Kai mata akwai fitina wallhy

Tabe baki Mohan Yayi yace forget dama kawai nasani Ne...tayi ma kanta.

Aliyu yace pls kayi haKuri Mohan

Wata Miskilin Murmushi Ya sake yace I have to go now Saida safe Kawai Sukayi sallamah

Mohan Tunda yajI hakan hankalin sa Sai ya kwanta Sosai.

Sai dai Maimakon yayi reacting Ya nuna Musu yasan komai Sai ya basar Musamman Ma Nimrah,

sai yayi Shiru Yana kallon
Su duka kowacce da abunda take ayyanawa Domin Ya bi nata qudirin....

A ransa Yaji haushin zuban cikin amma bazaka san Da haka ba

a safiyar ranan Nimrah tayi sheme sheme tana jira yazo ya mata hidima ya kula da ita,amma sai shiru take ji har 10 Ya wuce batayi wanka ba bare taci abinci..

Mai aikin data ke kyama ita ta Koma dafa Mata shayi Ta taya ta shiga bathrum Ta tsaftace kanta

Sai tace Tunda aranar farko Ne bazata dauke abun komai ba Maybe Mohan yana bakin cikin Xuban cikin ne,Gashi ta jira taji Ko an kore Banafsha Agidan shima sai shiru

Gashi an bata 2weeks bed rest Babu fitowa

sHikuwa Tunda yasan metayi sai Motsa Motsan bakin halin shin suka Sauka A kanta gaba daya sai ta dena gane kansa

Zai Dai shigo duba ta amma sai yaga dama sannan bazai fi minti 10 ba xai fita,sometimes Na a tsaye Kuma Duk Iya kisisinan ta baiya kulawa

Shi bai rarrashe ta ba,Shi bai mata fada ba, mata komai ba sannan hannun shi baya kaiwa jikin ta da Sunan taimaka min na tashi ko zan sha ruwa

Wani bin intana fade faden ta sai yayi shiru ya tSura mata ido Ko tana koke koke Ya basar Ya juya kai yana latsa Wayar sa

Ya Gama Lura Damuwar ta kawai shine ya wulakan ta Banafshan shi,Acikin ranshi sai dai yayi murmuShi yace yarinya Ai kin makaro ita din ma ina nan A kanta...

a fannin Banafsha Sam Baya sake mata Itama,.shi tunda yaga ta kafe akan maganan Tana so ya saurare ta,sai ya fara punishing din feelings dinta,

A kullum xai Nuna kamar 100% ya na kula da Nimrah kuma yana tare da ita kodan ya bata haushi,.

Wani bin ba dakin Nimrahn yaje ba amma Inta fito zata wuce zata gansa sau dubu a kofar dakin

Daga tayi magana Tana son ganin shi sai Yace baida lokacin sauraron ta shi Nimrah bata da lpya yana kula da ita

Haka Banafsha Tayi ta danne zuciyan ta taki tayi fushi,har abun ya kai ta makura Sai ta Dena bibiyan sa

Shi baiyi hukunci ba kuma vaice Musu komai ba,nimrah ma dataga wulakncin san yayi yawa sai tayi zuciya da shi tace Ma hasis ai Banafsha ta tsafe shi Ne ta lashe masa zuciya.



Bayan kwana biyu Dayaga dukan su sun sha jinin jikin su da shi,Sai ya shirya tafiya conference abinsa

Ranar da zai tafi da safe Banafsha tana kwance da babyn agefen ta ya shigo Bata sani ba Don Sai da yakai tsakiyar dakin kafin yayi sallamah sai ta dago Kai.....

Kallon da yake mata yasa bata iya hade ido dashi ba ta gaishe sa Cikin sanyin murya

Gaban shi na yawan faduwa aduk sanda yaga fargaba a fuskan ta Yace ki shirya,gobe zakije gida...bayan kwana biyu zamu zo.

Wani garas taji maganan ya sauka a kunnen ta Tace "Ya Allah, ko dai korata Yaya mohan yake so yayi?. ,Tuni sai taji Bugun zuciya

a gaskiya bata so taje ko ina ta barshi agidan da Nimrah,
Tace yaya mezan je yi agida? Why not na jira mu tafi tare da kai.

Yace a'a..haka Kuma yaki fir karshe ma Data takura sai yace Kawai ta tafi shixai kula da matar sa ne..

Abun ya mata ciwo Haka ta kwana da maganan aranta Tana jiyawa,da safe Data farka gani tayi an dora maysam black diamond brace a wuya mai shape din love mai kyau Tsadadae

data bude sai taga Hoton shine da na babyn sa aciki
Murmushi ta
danyi Tana kallon yadda sukayi kyau,sai ta Shiga kimtsa Kanta Amma da niyyar babu inda zataje sai Da shi

Tana sane da bayanin family function din da aka shirya gaba daya familyn za'ayi,Dama hajy tace on 23th ne gashi Yau its just 18,ita dai sam bata so tabar gidan

gashi ma ba acikin garin abuja za'ayi ba a kauyen da su hjya mamah suka taso ne..
Cikin tunanin ta sai tace toh meyesa tun ranar tafiya baiyi ba zaice naje gida?
...tace Toh nidai bazanje ko ina ba.

Haka tayi ta zaman ta bata gansa ba Kuwa gashi yanzu basu ko ga macici da Nimrah

, shikam Tun Yana mota zaije kano Ajiyan hjy tace masa ya bataga Su banafshn ba?
Yace mata Nimrah bata da lpya amma Banafsha zata zo

Yana isa kano Driver ya Kira ya aiko Akan yace mata maza ta shirya Ya kaita,Bata ma san baya garin ba

Gashi tsaban bata so taje ba da kuka ta fita Haraban gidan Da kayan ta

Nimrah ma farkawa tayi bata ganshi ba gashi bata san da maganan family function din ba Bare tafiyan dayayi.
,Daga tsayawar ta jikin window zata daura towel sai taji hayaniyan mai gadi da driver she tot ma ko mohan ne zai fita Baizo ya duba lpyar ta ba, tana kuwa lekowa ta hango ana dura kayan Banafsha a mota,

Ita kuma ta bata rai sai jijijiga babyn take agefe

wani Kyakyawan murmushi Nimrah tayi thinking that Mohan ne ya kore Ta duk Ba'a yadda taso Din ba .

Itama xaman jiran dawowar Sa take yaxo suci rayuwar su su kadai amma sai shiru har dare ya rufa,gashi zata kira shi bazai daga ba. .

Bai tashi kula ta ba sai chan dare yayi nisa anan ma"ya turo mata sakon cewa yayi tafiya zaikai 1 week bai dawo ba.

Taji haushin haka Matuka Wai shi wani irin mutum ne Dabai damu da damuwar kowa ba? ,but tunda taga babu Banafsha a gidan bata wani daga hankali ba..

taso ace Ya kula da ita Wanka,cin abinci Abaki,Taga Dai yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login