Showing 162001 words to 165000 words out of 245996 words

Chapter 55 - AJALIN SO BOOK COMPLETE BY SURAYYA.txt

07 Aug 2025

6581

sa ya daura yana dubawa a hankali yana shafa mata su..shiru ne ya ratsa wajen,sosai massage din ke bin jinin jikin ta,..ta lunshe ido ahankali tana budewa Kuwa suka hada ido da nusaiba da tray din Strwbey drink a hannun ta,babu abunda ya tuno mata sai lokacin da suka saka ta ta akawo musu da chan ita da kawayen ta..tana tsaye ta daure fuskan ta dam
Kallo daya zaka mata kasan tana cikin yanayin haushi, da bakin cikin ganin abunda yayan ta yake yi..shi bai ma ganta ba abunda ke gaban sa sa kawai yake yi,dauke kai banafshan tayi sannan ta karaso,
Batace komai ba ta zo zata ajiye,wani wawan harara ya balla mata yace ke meye haka,baki da hankali ne zaki zo kan mutane babu ko sallamah ..kafin tayi kagama yace da Allah get up,hold it sai nace ki ajiye Ne ko iskanci?
...tare da sake wani shakakken kukkuni ta mike tsaye da tray din a hannun ta ta ja ta tsaya,..ya dubi banafshan yace ai yanzu kam zaki sha ko? Batare da ta kalle nusaiban Ta tace em...sauke mata kafan yayi ya mike tsaye yace lets go,hannun sa ta kama ya dan dago ta zuwa bakin ruwan pool din,nade kafar wandon sa yayi sama ,..sai da ya zauna sannan ya zaunar da ita a tsakankanin cinyoyin sa..tsaban bakin ciki wasu zazafafan hawaye masu daci nusaiban ta goge sannan ta iso hankalin sa gaba daya na kan matar sa,

Jingina kanta yayi da kirjin sa yana tambayar ta ko tana jin sauki a ranta data sa kafafun ta ajikin ruwan tare da nashi,..ta kasa amsawa sabida yanayin kunya da nauyin shi da take ji musamman ma da nusaiban ke aiko mata boma boman kallon barazana..da kyar ta firta zata sha drink din sannan ya juya ya mika hannu ya karba ,harara ya watsa ma nusaiban ganin yadda ta murde fuska tana hura hanci...yana karba ya fara bata abaki nusaiba tsayawa tayi tana kallon su,gaba daya mamaki da takaicin yayan ta ne ya cika mata ciki,itako ta lafe tana karba sanda ya bata sau biyu ta makale kafada cike da shagwaba tace yaya na koshi,...baice komai ba amma ya mata alaman bata isa ba,Itama karba tayi ta bashi abaki ya kurba kadan bai hadiye Gudan Berryn Ba ba ya hade bakin su waje guda ya maida mata shi suka Cinye tare,..

Kan su hankara ji sukayii ta fanjam nusaiba ta fada a ruwa...kamar wanda yake jira ya tashi da masifa,. Yace madallah,dama banda iskancin banza me kika tsaya kallo Anan.
....tafiyar ne ke miki wuya ?ohhh u just can't concentrate Huh..
Msw Ba kauyiya,will you come out and get lost? Ya daka Mata tsawa.

A sadade ta dago kanta cikin ruwan Ta fashe da kuka ba abunda ta tuno sai abunda tayi ma banafshan anan ranar Almost 2years back

..tsaban haushin kanta da kyar tafito duk ta jike har tana diga,da gudu ta nufi cikin gida tana kuka..

Sunkuyar da Kai banafshan tayi ta kada kanta ya mika mata hannu yace get up...muje ciki

Ba musu ta tashi, tana daga gefen sa suka haura cikin gida a dakin sa ya ajiye ta sannan ya fito ,

Bayan kamar mintuna goma ya daawo
Gidan yayi shiru kowa na site ana shirin gobe daurin aure da dinner still bakin su na hotels da guest house anan agidan daga daga sai su

Kwance ya same ta tayi shiru tana sauke numfashi slowly,sai tayi lui da ido alaman hankalin ta a kwance yake

....daga Bakin gadon ya zauna yana kokarin cire rigar sa. ."jeki hado min coffe " ina laundry
.....tace ok ta sauka ta nufi kitchen

Daga nan Cikin loundryn ya nufa,..boxers dinsa ya zuba a machine wash yana matsewa,

Ta hado coffen tsaf ta fito xata je ta same shi suka ci karo da nusaiba abakin kofa,wani harara ta watsa mata tayi tsaki mai sauti.

Batace mata uffan ba don tasan haushin abunda ya faru Abakin pool take kan ji ,

Sai ta basar Zata wuce ta sake shan gaban ta,tA dora hannu a kugu

Nusaiba ki ban hanya zan wuce....

Ba za a baki ba,munafuka,marar kunya, shegiya yar iska kawai.

Haushin hakan ya bata Sosai Amma kuma bata son aji hayaniyar ta Da kowa a gidan sai tayi tsuka,nidai ki ban waje xan wuce Domin Banda lokacin ki

"cikin dagon murya nusaibahn tace...iyee toh"Anki abaki wajen Sai Kiyi abunda xakiyi..
ko kije Gaban sa kiyi karuwancin da kika saba Ya xo ya daga miki ni a hanya Sai ki wuce mswww'...

Nusaiba karuwa Fa kika Ce min?
Eh, angaya miki karuwa kawai,Mswww

Dagowa tayi cikin fushi xata yi Magana charaf Suka hado ido da shi Yana jin su abakin door ya Harde hannu,

Jin Banafshan tayi Shiru Sai Jikin Ta Ya bata sai Itama Ta Juyo...
Irin Mugun kallon daya mata

A tsorace Ta Maida kanta Kasa,tuni jikin ta ya Soma rawa

Itako Banafshan Wani shaukin kuka ne ya kamata A wuya Amma Sai batayi ba,cikin sanyin bacin rai ta ajiye cup din coffe din Akan deck a sanyaye xata bar wajen

Yace dawo nan..
Chak Ta tsaya kanta kasa A kusa Da shi
"
"My friend will you come here ina tsaye kina juya min baya"Are you mad.

Take taji fitsari ya yanko mata ta juyo sai karkawa take"Kayi H..aa..kuri yayah
Cikin bacin rai yAke maganan Amma baya nunawa sosai a fuskan sa...whats going on here ?ya Tambaye Ta..

"tace uhm uhmm Gaba daya Sai ta rude Kanta a Kasa Ta kasa maimaita Masa Koda kalma Guda..Hawaye ne Suka Fara sauka mata'cikin murya tace Dama ni tamabyar ta nake yi
U sure?....nan ma ta kasa daga kai

Hm kawai yace Sai ya tambaye Banafsha itako Sabida ranta ya baci Ba kunya ko kawaici ta maimaita masa Duka..

Kuka Nusaiba Ta barke Da shi, Ta dora hannu a ka Tana kallon bakin banafsha
Gashi cikin Sanyi Da shagwba Take maida masa Zancen.

...Nusaiba Sam ba tasan Banafsha xata iya mata hakan ba.

Bai Damu Da rudewar ta ba Yace Anyi hakan?
Da kyar ta Iya Gyada kai,yace kiin Min karya...tace yaya Dan AllAh kayi hakuri "im Very sorry....Bana kara fada mata hakan Wallhy sharrin shaidan Ne

Nan Ta tsuguna har kasa Tana kuka gashi bata isa ta daga murya ba

"Me kika Zo Yi Anan... Cikin rudani ta nuna set din flat pandel na Irin muciyar Soft wood Din Nan...

Shi kika xo dauka?...kafin ta amsa yace Ma Banafsha baby daukomin Katon ciki...tace toh Taje ta dauka Yana karba taja gefen sa ta tsaya..
Get up an come...tace wayyo Allah na shiga uku Yaya kar ka buge ni
Wallhy baxan sake ce mata karuwa ba i swear It....Yaya pls

Wani maka yakai ma bakin ta Sai Da ya fashe.."Yace Ai ba ita kike xagi ba Ko!?...Nine dan iska na auro miki karuwa ko?
A firgice ta Shiga Kada Kai...
Kixo nan nace ya daka mata tsawa
kuma ya hanata sake sautin kukan.

....A firgice ta dago..."give me your hands now.

A gigice ta miko hanun tsaban kuka da tsoro kamar xata shide Masa...."
Jansu yayi a wulaknce Ya mike...
,"Wannan padel Din ya dinga Buga mata akan Yatsun hannun Tana kuka tana zillo.. Automatically ta soma rokon ta gafara Da dukkan kalmomin hakuri, Shikam Ko ajikin sa
Har Tausayi ta Fara bada banafshan...
Gashi bata isa ta kauce ba..
Sai da yaji Banafsha ta Dan riko Rigar sa Ta lafe alaman ta tausaya Mata Sannan ya hakura"Ido yayi mata ta fita..time din nusaiba ta sulale a kasa rike da yatsun hannun ta..
Dama ke baki da hankali?..the very next Time naji kina furta Hakan ma wani bama matata ba xa kiga abunda xan miki...
U most respect her ,she's my wife and not Your mate...me nace?

She...She's Your wife i must respect her...Muryan ta na rawa ta fadi

Good Go write it On your wall...wawiya comn
Bace min daga nan Ya Daka mata tsawa mai karfi saida gidan ya amsa


Arude kuma agigice ta fita Tayi site din hjy mahnoor wani Kururuwan Ihu ta fasa ta xube akasa gaban ta Tana birgima..

Arikice hjy mahNoor ta Yo kanta..nusaiba?Lpya kuwa wai Meye haka waya taba ki...
Hannun ta take yarfawa cikin Radadi da sheshkar kuka Tace Mummy banafSha ce...A kanta yayah mohan ya bige ni...

Tace What duka?.. Akan me? Bata iya magana ba
Hannun ta ta miko
Ta nuna ma hjy mahnoor,duk sunyi ja sun Kumbura Ga
bakin ta jini

Innalilhi wa enna ilaihi rajiun...a Take ran hjy ya baci"Tace ina Mohan din...?What nonsense yana hauka ne

Cikin kuka Mai ban tausayi Nusaivn tace Ah a fah mum Karkice nagaya miki Ai xai sake duka Na.

Tsaki hjy mahnoor tayi ta fito,kofar dakin sa a kulle..sai ta nufi site din hjy mamah.
Ba sallama Ta banko kofa"
Su hjy Dake Xaune Suna Hira saida sika dago

Tace Ina Banafsha? Shikowar ta Kenan Hakama Gaban ta Ne ya fadi
A Dan tsorace tace gani Nan ...Mum..

'Come here ta fada rai abace ta yo waje...Ba bata lokaci ta biyo bayan ta Suka fice.
Kallon kallon Su hjy sukayo tace kinga Bari naje inaga ba lpya..yar marainiyar Allah Dai baza su sako min ita agaba ba..
Nan ta fice ItaMa ta bisu.
I cud not edit pls Ayi haKuri
#follow surayyahmS

*🍒🌺AJALIN SO🍒🌺*


WATTPAD@ SURAYYAHMS


_Ajalin so fans for you(original)_


_41..The truth._


Daga dakin hjy mahnoor Nusaiba zama tayi tana sheshseka
kalon hannun take tana maganganun xuci
Tace"Allah ya isa min. Yar matsiya ta kawai,ciranin asara..insha Allah mumy xata nuna miki matsayin ki yau din nan..

Cikin haka taji an murda kofa charaf suka hade ido da mohan
..a birgit ta mike tsaye cikin tsananin tsoro ta sadda kai"
wani mugun kallo ya balla mata hannun sa na jikin handle din door"Yace ke!!
Meya kawo ki nan"cikin dakewa da hade rai yake kallon ta, Tace
Ba..bbu komai..
da rawan murya da sauri ta iso xata fita don ji take kamar yanzun ma ya shiga xuciyan ta yaji me tace ne.

Ina mum?...a rude
Tace uhm?mum.. Mumy tafi...ta...karamin tsaki yayi yace
Jeki kira min Banafsha yanzu..

Tace toh takara sa waje da sauri cikin fagaba duk ta birkice.

Tana fita ya biyo bayan ta,banafsha kuwa fargaba ne dam aranta, ga hjy na biyo su daf amma dik hankalin ta baiya nan...a Falo suka ci karo da nusaiba...

hjy mahmoor cikin mamaki tace ina zakije kuma?....harara mai xafi ta fara aika ma Banafshan kafin tace yaya ne ya aike ni.."ke kuma ai saiki je shine yake kiran ki tsaban bakin cikin data ke ji wani bakin kuka tafashe da shi ta koma jikin hjy mahnoor ta lafe

lallashin ta hjy mahnoor ta shigayi cikin damuwa tace
Ina shi mohan din?

Wai meye ne haka yafaru...me kuka yi mata?

.ta juyo ta kalle Banafsha wanda tuni ta sunkuyar da Kanta kirjin ta na bugu....

Sautin kuka nusaiba ta kara,a son ta lallai hjy mahnoor ta tunxira ta rama mata.

Cike da mamaki Hjy mamah tace ikon Allah..ah'a meyayi xafi haka nusaiba?meyafaru,kunyi haukar fadan naku da kuka saba ko?
Wai meyasa baku sanin kun girma ne..?

Hade da daure fuska hajy mahnoor tace ah toh.. gata nan dai ki tambaye ta..ni na mata magana tamin shiru..
me suka yi ma nusaiba?
..jibi duk yadda yarinya ta firgice.
..ki duba dai ki gani hjya yanzu wannan adalci ne
Sounding realy pissed tayi karamin tsuka

"hannun nusaiban ta dago ma hjyn itama don ta duba ta gani

Subhallah,ke Banafsha me ya hada ku haka?whats all this ta dan tsawatar mata

Take Idanun ta ya ciko da ruwa cikin rawan murya tace nannah wallhy ban mata komai ba ita da yaya mohan ne....

HJy tace Mohan shi ya buge ta a hannun haka?
..hawayen tsoro suka sauko mata ta share su tare da gyada kai

Yana tsaye yana kallon su.

Nusaiban tayi firgit tace makaryaciya ai kece kika sa shi..

Kuma wallhh.. Xata karasa sai sukaji motsin takowar sa... Hadiye maganan tayi tace
..ni kiyi hakuri ni dama bada ke nake ba hjy mamah nake gaya ma abunda ya faru..

Meyafaru? ..cikin mugun daure fuska ya tambaye ta..

Rai a bace Hjy mahnoor Tace Mohan!! Tuni Ya dakatar da ita adan zafafe yace
...mum pls... tafada miki meya faru.. right now..ya daka mata tsawa

A tsorace ta fashe da kuka ta fara fadan A-z Daga abunda ya faru..tace mum sharrin shaidan ne fa.. ai kuma na bata hakuri..

cike da mamaki hjy mahnoor tace
Nusaiba har xaKi ce ma yar uwan ki karuwa agidan nan?
Tace mumy im sorry...nayi kuskure...tafada jikin ta tana kuka sosai....

Shiru hjy mahnoor Din tayi don maimakon ta ji zimman yi mata fada aranta wani Tausayin ta taji

Hjy mamah kam kamar an kunna ta masifa take inda ta shiga banan take fita ba tace "lalacewar zamani girman bariki ko?har ke kin isa ki kira matar yayan ki karuwa ba agiciye ki?
ai dama nasan ruwa bata tsami banza sam, Ko da chan ma ai kece shaidaniyar.

Nan ta juyo kan mohan...tace
Next time ta sake fadan magana makamancin haka kafada min ni xan dauki mataki da kaina... ko kuma nakai ki gaban turaki yaji abunda kikeyi da kunnen sa.

A tsorace ta tsuguna kasa cikin kuka tace habawa hjy mamah...dan Allah kiyi hakuri kar ki fada ma dady wallhy bazan sake ba, sharrin shaidan ne kinji..
Banafsha kiyi hakuri...!pls..ta cigaba da kuka

Hakan da data ke sai baiyi ma hjy mahnoor dadi ba ko kadan"
Ita Banafshan wacece da zata sa a taru ma yrta haka da masifa.

Hannu tasa ta dago nusaiban tana cewa ya isa haka,toh waye baya laifi ai gwara ke kin bada hakuri,wasu zaka musu magana tsaban raini sai suyi maka shiru...
Kuma ba aganin laifin su..muje.... Jeki ki ki kwanta ni zan rakaki.

Hjy mamah na nan tana kukkuni ko ajikin ta...sai ma dada jaddada mata Take cewa Banafsha matar wa ce kuma matar wa tamkar uwa ce.

Karshe ma ta kadan kan Banafshan suka koma daki suka barsu anan

,..shikam yaji habaicin mahaifiyar nasa.

Dan haka bayan ta yabi, amma sai bata kula sa ba sai da ta ajiye nusaiban akan gado tana rarrashin ta...

Cikin kukkunin bacin rai tace wannan sam ba adalci bane,in wasu zasu ware nusaiba agidan nan kai ma saika goya musu baya?
Ko dan nusaiba ba jini na bane kake neman fifita wasu akan ta...

shi dai mohan kallon ta kawai yake baisan me xaice mata ba,gaba daya bai fahimci me take nufi da al'amarin banafsha Ba.

Sosai ta daure fuska tayi shiru
Chan Yace mum kin dauki abun da zafi
..kenan nusaiba tayi laifi baxan dauki mataki akanta ba sabida ba jinin mu daya ba?
A hatsale ta haura mishi tace
Wani laifi tayi...?bayan duk hakurin data bayar ...
Akan wata sa'ar ta?..,banafsha ai age mate ne da nusaiba......ya kamata uxuri xaka mata thy r both kids..ya xaka biye ana wulakanta min ya?

Xaiyi magana tace ah'a...dakata min.
gaskiya banji dadi ba,...kaima
Maza kasake tunani.
Family comes first..nafada maka kenan

A ladabce yace yes mah..im sorry.

Nan Ta fita ta barshi ko kulawa batayi ba,..

Sauke ajiyan zuciya yayi ya daga kafadan sa yana furzan iska slowly ta baki.

Washe gari da safe da shike ranar daurin aure ne ko ina ya dau dirin hidima sosai

Musamman part din hjya mahnoor da iyayen amarya aneesa don su suka fara nitsa ta da nasiha kafin su hjy mamah.

"Yau za'ayi Dinner washe gari da safe aneesa da mijinta xasu tafi chan denmark inda suka shirya honeymoon din su.....'
tun daga bayan daurin aure iyaye da kakkani suke fara jimamin rabuwa
....'duk da ma hjy mahnoor da cikin su hjy mamahn ta kwana.

Bangaren nimrah kuwa bayan jimamin rasa masoyiyar ta anisah da zatayi yau,ga wani tsananin kishi data daura cikin ranta akan Banafsha."ynxu haka abubuwa dayawa nadamun ta game da ita dama kuma hidaman ne ya rike ta a wuya.
,bacin nan Ba wanda ya san yadda take Allah Allah a koma gida ta cigaba da makircin ta

Anko din farin lace akayi gaba daya matan gidan maza kuma suka sha sky-blue getzner mai dan karan tsada da taushi sai dai su a chan guest house suka tari bakin su.


Da amarya da bridal train din ta su jamila da nimrah Ansha make up na kece raini ana daukar professional pics da bridal portraits a farfajiyan mansion din,so very colourful

,bayan kayan alatu dake jikin amarya idon kowa akan nimra yake Domin kuwa Ta tsokano kara'i bana wasa ba,

dinkin rigar lace din ta fitted ce marar hannu da tsagu gefe da gefe...
gashi ya kamata dam jan kitson attactment din daya ci (500k)ya dada haska ta.

Su jamila ke xuga ta suna mata fadanci...,wasu ke cewa ai tafi amaryan ma jan kayan kudi..

Don Daga kan jewaries din ta kowani guda na(4.5million) har takalmin ta da jakar (prada mai normal high-heel sandals shima a 15mil)ga expensive make up da sauran su sai kawai ta dawo musu abun kallo .

Irin xugin data sha a ranar,har wani jira take mohan ya dawo suyi hoto.

Ana cikin haka ,da yamma chan duk an fito kawayen amarya zasu tare a hotel din da za'ayi musu shirrin dinner .

Toh kawayen hajiya mahnoor sunzo
,..anan ma nimrah Kawai ta kira tana nuna musu kwalliyar ta da uban kudin dake jikin ta...

abun alfahari ne awajen ta koba komai a yadda take matsayin ta na high classic make up industrialist and designer
Standard din nimrah ne taga xata iya nunawa ma kawayen ta

kenan su san itama ba baya ba

nimrah kuwa an samo abun da ake so sai washe baki take tana kisisina,dan ta kara ma hjy mahnoor aji wani abun idan antambaye tasan ita ta siya amma sai tayi karya tace ai"damu kaje china da mohan ne ya siya min as gift kuma fa bance masa ina so ba..sai tayi dariyar rigima tace... hmmm
mohan is sooo soo cunny...lucky meee..

Sai ayi dariya
Sukuwa burge su take,nan sai suyi ta xuba compliments,hjya mahnoor kuwa tana jin kanta ayaba ta ayaba surkuwan ta da danta.

Tun farko shiyasa bata wani damu taji asalin labarin dayayi musababbin auren mohan da nimrah ba.

Aganin ta nimrah is not that bad for mohan ai yar lady ce,so kwarya tabi kwarya.

Ana cikin shagali Wata mata da bata cika magana ba cikin su tace yamma yayi fa muje muma mu shirya...nan Suka mimmike aka fara fitowa

Tare da nimrah hjy mahnoor suka fito ita sai tayi chan site din da motar amare yake..

Maryam ta zo ma Banafsha
Itama xata tafi sai ta fito rakata..

Ita kam simple riga da zani akayi mata classic buba bata yafa gyale ba tayi dauri mai kyau
Cikin suman kanta ta har ya fito

..shape din jikin ta da yanayin takun ta ko da kudi akace ka banbata ta kyaun ta da christiana milan baza kayi ba

Ita kan Ko kadan bata damu da wani yaga me ta sa ba,hasali ma bata san kudin komai dake jikin ta.."

Ganin su hjy mahnoor din ya sa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login