Showing 81001 words to 84000 words out of 245996 words

Chapter 28 - AJALIN SO BOOK COMPLETE BY SURAYYA.txt

07 Aug 2025

6596

da nake so sai ki fara karatu na gani..and only if u do ur duties well agidan nan zan saka ki a wanda kike so

Ta gyada kai tace ok...
Can i go now?

Bai amsa ba wayar sa tayi kara..
Ya daga ya duba sannan ya dago ya kalle ta da wani irin mean grin yace salam ..
Nan Suka shiga gaisawa da hjy maha tanaji kuma ta dago da waye ya ke magana

Murna Kamar tayi tsalle ta karbe wayan haka take ji aranta shikuwa kamar yana lura da ita don haka
Yaki ya hada su suyi maganan yace ma hjy mamahn baya gida.

Tun kafin ya kammala ta sulale tayi waje.

Da shike komai yayi setting mata sai ta shiga phone book tana duba contacts din dake ciki..

burin ta baifi taga ta kira mutanen ta ba..
Amma sai gashi ba numbers daga nata ne sai na shi guda daya yayi mata saving da doctor MM...

Tayi zugum cike da zullumin yadda zata tambaye sa ya bata number hjyan ko zata samu simcard din ta na da chan tayo copyn numbers cikin haka wayar dake hannun ta yayi ringing

Da Kamar bazata dauka ba amma ta dauka cikin sanyin murya tace salama alaikum...

Wani murmushin dadin hjy mamahn tayi tace auta na ...ta mike ta tarr da dan sake kara tace nannah? Kamar kuwa kinsan tunanin ki nake

Su kayi dariya tare inda take jiyo tsantsar kewar dake muryan yar nata..

Tace inche kina lpya ko? Ki fada min duk abunda yake damun ki yanzu ina jinki....

Sai tayi shiru tana murmushi Tuno da rabuwar su da abunda ta tarar jiyan agidan mohan din ya sa ta sauke wasu silent tears

Hjy tace banafsha? Yaya kikayi shiru yayi miki wani abu ko?
Fada min kar ki boye min komai ai jiya kwana nayi ina mafarkin ki.

Karar budewar kofar sa ne ya fargan da ita tace kai nannah mafarki? ah'a..ni lpya ta kalaau..

Ya fahimce komai sai ya karaso kusa da ita yana jin abunda suke cewa.

Haka ta kasa samun sukuni sama sama take amsawa ta tana kauce ma idanun sa har sukayi sallama

Tace nannah ki turo min numbers din kinji ?.
Tace toh shikenan sai da safe ..ko katsewa wa batayi ba ya karbe wayar ya kashe...
Ya juyo da ita "wayace ki fice nagama dake ne?

She can't control her attitude tayo pouting lips ta dan harare sa sai gwaff taji saukan palms dinsa a kan lips din ta.

Tace ochhhh....tayi saurin rikewa.

Yayi tsuka yace ive been watching you do that many times mani kike pouting lips..?

Ta rike bakin nata tayi shiru sai zirrrr hawayen ta suka sauko

Yace i will slap you right away idan baki goge wannan abun ba ya daure fuska

Meyasa kika fice ban baki izini ba...
Ko ke kika kirawo kanki ne?
Hawayen na dada bulubulowa Tace ai waya kake yi nikuma nagaji..

Yace tabb kin gaji..yai karamar dariya.yace so what? Kar ki sake yi min haka...
Cikin haka sai ga karar wayan ta..
Hannu ta kai zata dauka bai ce komai ba sai da ya bari ta dauko ko bude sakon batayi ba ya fauce wayar.

A boye Turo bakin tayi tana buga kafa kadan ta xauna abakin gado ta hade rai tana kallon sa yana scroling sakon da ya shigi

Gaba daya hjy mamah ta turo mata email din contacs din ta amma bai dauke sa wani 5minutes ya tsame numbers din da bai san su ba ya bar mata zallahn wanda yake so.

Yana mika mata ta kau da kai taki karba bai ce mata uffan ba ya zauna kusa da ita yace fine tunda baki son kiyi magana da kowa i wll keep the phone for you

Taki ta jiyo ya kamo fuskan ta ta dan kauce yace wai me hakan? Baki san kin girma bako..ai duk wacce take da miji ta girma so quit this nonsense.... dan dole ta dube sa irin yau kuma?

Tace yaya mohan toh yaushe xan je gida? Ta makele wuyar ta sounding very childish abun ma dariya ya bashi irin nace ta girma she's now acting the opposite..

Yace babu rana sabida ba kiji ...jiya kika zo gidan nan amma duk kin jawo ma mutane masifa..
bazata tayi pouting lips din ta

Ya gwalo idanun waje irin again? Ta mike da sauri ta makela wuya gashi cewa sorry yana mugun mata wahala musamman idan ma shi ne...
Yace zo nan?ta dada matsawa baya yace i said come here..Waya koya miki wannan abun

Cike da i i na tace ai ban sani bane..ya yi wuf ya kamo hannun ta ta dan tsala ihu tace kayi hakuri yaya mohan bazan sake ba...yace too late..

Kan cinyar sa ya daura ta ya kamo duka hannun nata biyu ya daure su ya hade bakin su waje daya slowly..

Wani shocking ne ya xiyarce ta anan ta sake Wasu razanannun tears ke bin kuncin ta jikin ta lokaci guda ya shiga virabrating..
Bai sake ta ba sai da ya gama juya virgin lips din nata..shi tun dazu da yayi kisssing din ta ya kasa dena missing din lips din nata

Komin ta na burge sa he neva tot that har kisses don ta ma will be that infectious..

Da kyr ta kwace hannun ta daya ta samu ta kwaco lipss din ta
Tace yah mohan bana son wannnan ...yaya mohan...jikin ta duk ya sace ta fashe masa da kuka a hankali..

Hannun yasa Ya riko ta ta shiga fincikewa a kasale
yace hey stop

Jawo ta yayi jikin sa ya rungume ta gefen kunnen ta yace kin tuna? i said i hate pretense, wai sai da kika bari kika sha yawu na zakice min wani baki so?
Kinsan minti nawa kina kisssing dina...out of rudewa da salon maganan nasa yasa ta girgiza kai gwanin ban dariya aransa yace silly girl.. yace..20minutes...Amma wai "yaya mohan bana son wannan "yayi mimicking voice dinta...yana hararar ta seducively

Abun ya bata haushi amma ta ksa nunawa Tace Allah bana so ni bana so...ka dena min

Yace akan me? To wanne zanyi miki ..wani irin kallo mai kashe jiki yabita da shi lips din ta ya shafa yace wannnan Yana daya daga cikin aikin ki anan..
Kin aure ni kina zama da ni ai dole zaki na min kisses...ko baki aure ni ba?

Ta dago ta dube sa zata turo bakin sai ta tuno da baya so sai ta sunkuyar da kai kasa dagowa da ita yayi ya sauke ta a kasa..

Yace wata rana is not gonna be just kisses ko?"ya dan ja chin din ta playfully ayayin da ta lumshe idanu tana jin kunyar sa sosai..yayi grin kamar ba shi ya fada ba...ita ko tsoro ma ya bata ta kasa cewa uffan..
Yace ok go to bed now...and
Don't forget anything

Ta gyada kai wanin irin lumshe idanu ta dadayi ayayin da ya sake daura mata slight peg a lips din ta ya fice

Da kyar ta rage wutar dakin ta bar lamps din ta batayi bacci ba ta rufe kanta baki daya cikin bargon tana sauke nunfashi

Bata iya bacci ba sai da ta kira numbers din maryam suka sha hira.

Ita ta debe mata kewa inda take sanar da ita cewa ai fazilahn ma dazu ta kira haka zumudi da kewa yasa suka hada conference call su ukun cikin farin ciki a bugu na farko kowa yana bada labarin sabon rayuwr sa kamar ba zasu rabu ba tsaban surutu da kewa.

Whats life witout friends atake taji saukin duk wani damuwar ta a hakan tayi bacci mai dadi..

Washe gari da safe ranar jumu'ah ce still shi ya soma fitowa cikin tsadiiyar jumfar sa pure white yana tafiya yana gyara zaman rolex din dake hannun sa alaman sauri yake don haka bai kula kowa ba ya fice.

Alokacin Its around 6.00am meeting ne mai muhimmanci ya sa shi sammako..

Cahn wajen bayan awa guda da fitr sa banafshan ta fito sanye da atamfa riga fitted da skit dinta 8 pieces mai manyan design din fari da ja da grey nell sosai kalar atamfar ya haska ta tayi kyau ta fitar da kuruciyar ta afili.

Aikin gidan baiya daukan ta wani 20minutes sabida gidan baida daukan datti sosai Nan ta kimtsa ko ina tsaf komai ta maida sa inda yake turaren dake cikin kayan da hjy ta bata ta kunna a electric pun ta ta kunna shi ya cigaba da fetso wasu da dadan qamshi,hirar su da su fazilla take tunowa don babu labarin da bata basu na yadda take jin dadin auren ta ba,haka kawai take admiring dinta musamman in taji anacewa mutum yana kwance cikin kwanciyar hankalin sa bai da damuwar komai.

Amma tasan nata daban ne don haka yau ta sa aranta wannan aure destinyn ta ne and she have to make her peace out of it ...

Tana mopping floor din kitchen din tana ayyanawa aranta yadda zata dage ta sama makanta sauki da su biyun..

Tasan matsalan mohan bai son raini amma ta kasa gane meye matsalan nimrah?

Gani take ba zallan kishin bane har da tsananin tsana don kuwa tafi kowa ganin hakan a duk sanda take mata magana.

Tayi nisa cikin tunanin ta ko ina ya dau annuri da sabon yanayi mai kwantar da hankali da ta wanzar..

By 8.00am dai dai tagama komai saiga sautin takun takalmi as usual dogon riga ta sa
Sai cuno hanci take tana shakar qamshin dake dada gauraya gidan tace"musah? Tk..
Sunayen masu kula da harkokin gidan amma shiru ba wanda ya amsa.

A hatsgitse ta sauko har heels din na shirin kaucewa tace wai waye yake min bokanci da sihiri agida na ?
Ta wani ja birki ta tsaya tana huci..

Ita kam banafshan Kwata kwata bataji takun mutum ba bare sautin ta kuma dama kitchen din baida nisa da dinning 2 luxury step ne kuma ya raba wajen da main falon su don haka zaka iya kallon wanda yake kitchen idan ya bude kofar

Nan kuma gas ta kunna ta riga da tasa oil a wuta alaman zata yi deep frying

Juyi nimrahn takeyi tasan ba wanda zaiyi hakan sai mutum daya amma ina take...Jin shirun yayi yawa Tuni Taje ta kashe dayan burner ta yi hannyan kichen tunda taji shiru tasan dole ne akwai mutum aciki..

Tana bankado kofar banafshan ta dago kai wani kallo ta maida mata.
Itama ta daure fuska ta sauke kanta kasa kasan makoshi tace ina kwana anty

Tace eh mm ehemm jeki cahn ki nemi antyn ki awani waje no ba antyn ki bane
Meye wannan kika kunna min agida? "wani tsubbun aka baki kizo kisa kih kashe ni ko?

Tayi mata shiru..ko sake juyowa batayi ba haka ma bata dena abunda take yi
Dama Flour take kwabawa ta rasa yadda za tayi ta motsa fargaba ke cikin ta arai
Sai yanzuma ta soma wondering ina yaya mohan din yake yau bata gansa ba ko dai tare suke? tasan idan yana nan ai bazai bari ta taba ta
Bata hankara ba taji an fincike ta sai da flour ta kife a kasa.

A dan tsorace Tace anty nifa ban san mekike nifi ba
sai tassss ta wanka mata mari bazata...

Cikin zafin rai tace
Ai bazaki sanin ba sabiida angama lalata ki tun baki tafasa ba an kona ki ya kuwa zaki san me nake cewa?
Toh Waya ce ki saka min wani abu agida na are you mad?

Hawaye suka sauko mata ta tare tayi shiru tana Kokarin zamewa ta bar wajen amma da nimrah ta shagaban ta sai abun ya wice tunanin ta

gashi size dinsu ba daya ba kana ganin su kaga banbancin shekaru da girman jiki
Kokarin xamewa take
Tana jin nimrahn ta cahkumo ta ta tsala ihu tace dan Allah ki saake ni
Ni ki barni ta watsa mataa harara masu zafi

Ta ce bazan sake ki ba dukan tsiya zanyi miki wanda zaisa da kafan ki zaki bar min gida na munafuka kawai..
Idan ma an turo ki ne kizo kih raba ni da miji na to ki sani kece zaki fita waje muttaciya bani ba..

Kasa banafshan ta sulale tana kuka don fa sosai take jn tsoron nimrah qaurin man gyada ya sa ta mike ta kai hannu zata kashe gas din

Wani irin tumble da kayan table din nimrah tayi don ta dada razana ta tace nace kiyi waje ko..

Tace Shegiya munafuka yar iskan yarinya mutum baiya son ki ma kin nace ke wai wata irin mayya tsinanniya ce?.
Kin fice ne ko sai na kwara miki hot oil din nan?
Da sauri ta janye jikin ta amma zuciya yana hanata yin shiru. ..

Bata bata hanya ba yasa Tace ni meye nayi miki anty,..ni bance zan zauna miki da mijin ki ba ni bance miki ina son shi...why are you pestering me ...

Ta dada kawo hannu zata maka mata mari ta kauce..haushi abun ya bata tace ki fita ki bar gidan nan kiga ko zan shiga damuwar ki..just get out now.. ta daka mata tsawa.

Hawaye take kan saukewa tana rakubewa Abun ya mugun firgitata kuma nimrahn tana bata mamaki kwarai yaddda har ta iya wanka mata mari sai tayi zuciya itama ta cije..
.
Tace toh wallhy babu inda zanje kuma sai na fada ma hjy abunda kike min.....Allah ya isa min muguwa kawai

Bude baki nimrahn tayi Taace bura uba mani kike fadan hakan banafsha ?

A hatsale tace eh an fada din..toh me ruwan ki dani..you have ur husband so let me have my peace..ai nan gidan aure na ne.. ni wallhy ki fita a harkata ai ni ba yar ki bace..

Tace oh yeahhh ai dama nasan bakin kin nan na rashin kunya ne...ashe duk kinsan da hakan kika aure min miji ko? Wani wawan yunkuri nimrah tayi Bata damu da zafin pan din ba ta wasuso zata watsa mata hot oil din tuni ta hankade ta fice aguje tare da tsala ihu ...
Itama tana biyo ta da pan din sai charaf sukaji motsin mutum

Da sauri nimrah ta ajiye pan din ta tura bayan curtain ta fara masifa mai cike da munafurci

Shikam da ya shigo He can't believe what he saw banafshan ne tayi saurin komawa bayan sa ta lafe aka bar nimrahn a tsakiya

Yace meye hakan
Are you guys crazy surutun me haka...

Tace sai ka tambaye ta kafadar ta ne yayi tsayi wani ni take cewa zata buga can you believe wai ni take cewa shegiya muguwa..

A firgice banafsha Tace karya take yaya ai ita tace min sai na fita
itake ce min yar iska kuma wllhy ni ba tsinanniya bace kece muguwa asarariy..
Kuma ni wallhy kar ki sake mari na

Mamaki yasa shilll slowly ya furta what

Tace idan na mare ki zaki rama ko? Mohan Are you hearing ? kanajin abunda take fada min ko
A zafafe nimraah ta taho kansu duka tana huci irin ga babba zatayi hukunci

Mamaki ya gama cika shi
Kirjin sa har wani dif dif take ya riko ta ya tura ta gefe

Ya kalle banafshn dake makele a bayan sa
Yace Ke asje Baki da hankali sa'ar kice kike fada mata hakan..are you insane ?

Cike da dauriya tace tohta kyale ni mana.
meye nayi mata
ai da baka zo ba watsan min oil zatayi..
ni menayi mata...nan ta fashe masa da kuka
Ni ka mayar da ni gida t ni gaskiya bazan zauna ta kashe ni ba

A tsawace Yace quiet .

Tayi shiru ta sunkiliyar da kai jikin ta sai bari yake tana bulbulan hawayen tsoro shikan sa ya gane wani abu ya afku marar dadi..

Amma hakan ya cije yayi mata fada agaban nimrahn
Yace kar ta sake raina masa mata don tun kafin tasan zata shigo gidan sa yake tare da ita ..and the next time yaji tana mayar mata da magana hakan bazata ji dadi ba.

Sosai ranta ya baci,
Sosai ta kuma nuna fushin ta akan fuskan ta amma sai yayi kamar bai damu ba
Yace oya ki bata hakuri

Fuskan ta duk ya kunburo idanun ta sunyi ja Tace yayah ai baka tsaya kaji abun da ya faru ba.., .yace i don't care ..zaki bata hakuri ko sai na saba miki

Tayi shiru tana calming kanta...
Itako nimrah har da harde hannu tana wani cuna baaki irin gata nan babba irin uwar gida bata laifi.lol

Nan dai Ta sauke ajiyan zuciya tana tare sheeshkan ta tace kiyi hakuri ..anty

1 minutes bata kara ba
Ta haura sama da gudu ta fashe da kuka wanda yaji sautin na buga sa har cikin ransa

Tsaki nimrahn ta ja tayi yatsine

Ya juyo ya dubi nimrahn Yace shine ke kuma zaki watsa mata hot oil? Ita dai tasan ta boye pan din kenan har ya yarda da magaanan banfshn
Zatayi magana yace Akan me..U shud have told me that yha all need a mental home
Amma Ba agida na ba.

Baki a wangale Tace babe"
Ya daka mata tsawa cikin bacin rai "Ki bace ki bani waje i just don't have ur time now
Azafafe Ya wuce ya barta anan tasan ranshi ya baci sosai..

She just dont fully understand why baya son bata laifi agaban banafshan amma tasan yasan for sure bata da gaskiya

Amma da shike bata da kaifin tunanin sanin meyasa yayi hakan yasa ta juyo ta biyo bayansa.

Akan gado ya fada ya lunshe idanun sa tamkar ba yanzun ya shigo ba yana sauke ajiyan zuciya

gani yake kamar nimrah zata bata masa shirin sa.
Yasan idan bai tsare ta ba Zata kawo masa koma baya wajen shirin yadda ya tsara tafiyar su agidan
Shi sam baya son hayaniya abubuwa dayawa ya sa gaban sa yanzu and he neeed peace of mind definately

Wannan wai kishi ne ko hauka..Toh Why must she maltreat that girl ? Wai mata duk yadda kayi da su sai sun neme su kure ka... yayi karamin huci bai hankara ba yaji
An bude kofar dakin sa
Mutum ne a kansa

Ta kure sa da ido cike da tsiwa da rashin sanin ya kama ta

tace'mohan ka tashi kafada min akan me zaka na daka min tsawa ko dan ka auro karamar yarinya marar tarbiya da sanin nagaba da ita zaka maida kowa irin ta?

Dada lunshe idanun sa yayi yayi luff luf akan pillow baya ko kallon ta yau ne rana na farko data ya soma jin aransa lallai yayi sake wannan ai rainin wayo ne..

Haka ya mata shiru yana jin zancen nata har sai da ta kai aya tana cewa sai ta fitar da banafsha agidan.

Sanna Ya dago rikitattun idanun sa "yace idan gidan naki ne sai ki je ki fitar da ita.

Now, get out ya daure fuskan sa sosai bai taso ba tukun

Tace what?
Zata sake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login