Showing 105001 words to 108000 words out of 245996 words
aranta..
Gashi wannan weknds din bayan ta tashi a islamiya har saloon ya kaita dakansa ya biiya aka wanke mata kai aka gyara ta tsaff, har da kunshi Ya kuma jira ta abakin kofar for hours sannan suka dawo gida tare.
Duk basu lura ba Nimrah ta riga ta saka su a target din ta ba
Yana zaune shiru yana latsa wayar sa ta fito,
zama tayi kusa da shi ,bai kalle ta ba sai da ta jawo jaridar dake gaban sa ajiye ya fara juyawa...kallo daya mata ya dauke kai yace babe ..lpya kuwa?
Tace emm,lpyar kenan..baby .. i was thinking...tunda yaji haka sai ya ajiye wayar ya dago yace ina jinki...
Nan sai ga banafshan ta fito da coffen a tea cups farare masu kyau.
Bata fasa ba ta watsa mata harara ita kuwa ta daure fuskan ta, zama tayi gefe da shi ta ajiye masa agaban sa, bata gaisheh ta kuma bai ce komai ba shima.
Ya dago yana shakar qamshin da alaman burgewan sa.
Haushi abun ya bada nimrah sai ta harzuka Tace,babe ..em em,why not nima na fara islamiyan nan im kind of bored here ..
Banafshan ce ta fara kallon ta cike da mamaki
shikuwa har Wani bumbs ya sake saura kadan ya kone bakain sa,...a yangace ya yarfa yace ochh
ta wani tashi tsaye cikin kisisina tace sorrry baby are you hurt,? Ta kama hannun tana hurawa...wani kazamin kallo banafshan ta bita da shi bata lura va...yace its ok..banji me kika ce ba.
Nan ta sake maimaitawa, mamaki gaba daya ya cika su ,musamman da ta zauna ta tsara musu bayani cewa a dole itama zatayi participating don haka a dawo da karatun gida.
Yasan akwai wani abu a akasa amma tunda neman ilimi ne kuma na addini, sai kawai ya amince..yace idan ya ma malamin maganan sukayi zasu fara..
Har da murnan ta tana rungumar sa salon da banafshan zata ji wani abu aranta, its actually worked sabida tunda ta kafe kofin akanta bata sake ba sai da nimrah ta rabu da shi ta haura sama ta barsu..
Ya juyo ya kalle ta yaga tana turo baki,murmushi yayi yace kina so kema kina yi agida ko kina da plans din ki..ta girgiza kai alamn a'a,dan karamin mika yayi
Yace ok good...i cant wait to see the bigheads competition nasan dai mata na tana da shegen ilimi....dan karamar dariya ne ya kufce mata, ..ya jiyo ya dube ta irin nayi miki karya ko,ta turo baki
Hannun sa ya sa ya dan buge lips din yace last warning,..tuni idanun ta suka ciko, bai damu ba ya sa hannu abayan ta kamar zai rarashe ta zip din ya zuge ya shiga shafo ta, tuni ta dada rikicewa...tace yaya ka bari, ni bana so,yace nima ai kin ishe ni da kuka ne,..ciwon cikin ya tafi? Ya kashe murya seducively ya tambaya hannun sa ya kawo kan marar ta yana latsawa... Dagan dan yayi tambayar dama don ya sa hannun sa anan ..
Hakan kuwa akayi yadda yake cusa hannun sa kan marar tan yana shafawa kadan ya rage su kwabar da sauran cofee, .
Ta shagwabe Tace nifa zan fada ma nannah?im not joking..
Ya dada cusa hannun sa ciki ciki kamar zai sa hannu a cikin pants din ta "ta dan matse kafa ta lumshe ido ,bakin ta har na rawa tace yaya zan fada fa ,ai har da anty ma sai na gaya mata,..ta sauke wasu mahauktan shagwababun hawayen
nan ya fashe da dariya yace,gwara dai ki fada ma hjyan naki.. ai da yau din na kin bar mata gidan ta kuwa.
Haka suka dinga yi har suka bar wajen
A cikin satin yadda nimrah ta matsu akan maganar karatun yasa ya samu aka shirya akan malamin zai na zuwa a wknds 3.0 to 5.30 pm
Idan kuma weekdays ne sai yana zuwa bayan magrib zuwa isha'i..dai dai lokacin dawowar sa ya sa masa kudi akan zaina biyan sa...
Tun da aka fara Ko kwana uku cikakke basuyi ba nimrah ta fara gajiya abun yabi ya ishe ta.
.gashi ko idon mohan basu gani.
Sunan malamin malam dalhatu,irin ustazun nan ne masu shegen kinibibi da azarbabi..
Yaso ace suna saka nikab idan zasu fito amma haka nimrah ta turje sam tace hijabin ma ya isa
Da shike banafshan ta saba idan yazo takan ta yake fara bita..
Don kwata kwata girman kai ya hana nimrah saurarar abunda akeyi..
Dama ranar friday aka fara har akaci zuwa monday nimrah tana layi daya da karatu...
Haka zaiyi ta nana ta mata amma tana gajiya zatace ya barta haka,zatayi da kanta..
Wani bin Wato idan ta chapko wani hadin ta gwamutso sai ya rasa greek take yi ko roman...
Sai kaji ya doka salati yace naamm....uhum uhmm, astagfurullhi yah malama nimrah. .kayyyah...ki dai dada maida hankali...
a haka sai Ya gyara mata amma yana yin shiru zata sake chapkoo wani shirmen ,haka zaita sake astagfurullh yana kada kai yana shafa gemun sa...yana kayyyah... .kayyah
Irin wannan wani irin dakikanci ne
Shidai Yace mata tashi ki tafi ne kawai yake tsoro
Itako banafshan abun har ya fara dara ta..
Wani bin tana satan kallon su, har kirga astagfurullah da naama din take yi
Wani bin sai yayi sau goma sha biyar haka zai gaji..ya kyale ta
Sai ya dauka ko don bata iya baki ne ya fara koya mata,idan abun yayi zafi sai ta mike tsaye tana sose sose cahn tace malam mai gemu pls xcuse me,sai ya kada kai yana girgizawa gashi da dan banzan qalkaala yake magana sai yace naamm... laaa lah laaa lah..amsa waya zakije ko?haram alaiki yah malama nimrah..
Ki daure dai ..kiji tsoron Allah ki rungume qur'ani
Wala Allah wahidun zaki samu duk abunda kike muradi dake kunshe a wayar ...
Wani bin a sadade zata zauna ranta ba dadi hararar gefen ido kam yana shan ta..
Ranar da abun ya ishe sa,yace ya malamah nimrah ko zaki fada mana ma'anan wannnan layi dana karanto acikin hadisi na daya wato araba'u hadith..yace inna mal aamalu binniyaati, ..fassara min sai kiyi mana bayani...
Banafshan na gefe ta nitsu dama ita bata cika tankawa anan hasali ma kanta akasa yake kullum
Nimrah Tayi shiru..cahn ta tsame bakin ta rasa me ake nufi da wannnan kuma fa jiyan yayi ta nanata mata kamar gemun sa zai hura wuta cahn tace ,,yah malam ai yana nufin.""lallai mutum yana cikin hasara. ...
A hujajan Malam ya ce iyyye..Astaghfurullahil azeemun,ghaffar...
Yace kayyyyyah...
Ai wannan kina maganan ,aya ce dake cewa,innal insana lafi khusr..tace ohhh ashe ma shine?sai yanzu na tuna.. sam sam ita bata son gyaraa arayuwan ta
Malam yace Ohhhh ohhh oh ashe dama kina tune naga kamar baki iso nan ba,kiji tsoron Allah...
Tace na sani fa malam mai gemu,..wai ance maka komaai ne sai anan zan iya ?islamiyan na dai munyi shi a da...
ya tabe baki
abun ya dan zafe shi..
yace toh yah malamah nimrah
A wani mudu'in kika samu wannnan fassarah?wala Allah, wala Allah kin san abunda bamu sani ba
Tace maudu'i????Tuni sai ta shiga dube dube irin bata son ta yarfa kanta
akan table taga tarin books din daya ajiye tayi saurin karance title din na farko
Tace emmm malam mauduin "bari wa biba...
Malam ya dube sama ya dube gefe,yace kashhhh kayyyah malama nimrah maudui nake magana tace yess ko kana da ja ne...nan ya shiga girgiza kai cikin rudani yace
Laa laa la laa lah ,haza kazzzabbb wannan ai katon kazzabii ne.
Tace ohhh namanta ashe kazazzabi kace jiyan ko???i tot ko bari wa babun din ne..
Dariya ya so ya kufce ma banafshan amma ta tsime
Yace yah Qhadirrr nooo,..nace kazzabbbb...kazzabb...
wato liees...
Tace what?nice nake maka karyan..ta bata rai
Tace ah'a fa malam me gemu im not lying,
Dada nitse kai banafshan tayi kasa don bata so tayi dariyar su tana ji musu ya tashi ,malam nace karya nimrah ta dage akan shi ya koya mata hakan jiya
Daga bisani,idan abun ya bata dariya sai ta toshe kanta tana rufe bakin ta tanayi kar nimrah ta gane.
Idan zasu tafi yakan so yayi musu dan karamin nasiha,toh ranar da hakan ya faru,ana tsakiyar sati ne ranar talata bayan ya gama nasihan sai
Yace son samu ke malama banafsha,ki nemi lada wajen dada koya ma yar uwarki bita dan kin mata nisa,ke kuma malama nimrah ki dage ki koyi ..tun kafin ya gama tace meka ke nufi ne malam mai gemu ,da girma na zaka na gaya mata wani tayi min bita sai akace ban iya bane ko me ..ta watsa masa harara dama haushin sa take ji
Yace subahaalllah ,ya fara mata wa'azi kota ta kula karshe ma tashi tayi ta barsun anan.
Washe gari ranar alhamis ne Mohan na tambayar su anan nimrah ke cewa ai malamin shegen fifiko ne da shi,amma yau zata bashi mamaki.
Shikam sai dai ya tabe baki,
Da dare yayi aka zo karatu,yau qur'ani ne..
Banafshan ta danyi nisa tana wajen izu biyar da haddan ta don haka ma wa ita ya fara bita tana bin sa a tsanake.
Ganin yadda banafshan takeyi yasa nimrah ta bada hankali irin yau zata kada gemun malam ita da ko layi daya bata kama da littafi ba sai gashi tace itama hadda zata bayar...
Da Ta fadi hakan kowa yasha mamamki amma ganin yadda ta bata rai yace naaam to bisimillahi...
Tafara, da gyaran murya,
Yace dakata,iya yadda mukayi jiya ma kawai zaki kawo wato aya daya kacal...tayo bisimllah har da qalqalar ta
Tace "wa'in...bai gane ina ta cahfko ba amma sanin halin ta sai ya waske yace saka masa Gunnah..nuunun.. Wato zakice innnnn tace ok wa....innnn...wa ...in"
Yace gunnah,ta kuma kara sauti ta dage tace wa" innnn..yace masha Allah muje zuwa ..ta dada cewa wa..innnn..amma ba cigaba ,sai naaam naaam,naaam malam yake,yasa alif yasa ainun.
Abun sai ya dame sa yace cigaba malama nimrah ehem
wa'innn sai kuma gaba akace"
Ta kuma cewa wa''inn..
Yace kayyyah..ko za'a tayar ki ne? Tace ahhhh tsaya malam..cikin kukkuni tace wa inn din ne duk yabi ya goge sauran..amma zasu zo..lokacin dariya ya fara damun banafshan sai ta cigaba Da wa'innn ba sassauci....malam ya girgiza kai yace kaffar,..bai karasa ba tunanin sa ko nan ne amma sai ta cahpke shi shima..tace wa'inn kaffar...kaf..kaff kafff... Kaff...malam ya nitse kai yace naaam ...yana zaro ido yana shafa gemu
astagfullhiii..kayyyah..
Watoh malama nimrah kina so kice
Wa'innnn kaffartum ne koko wa'inn kuntum..
Tace yawwwa dayan ne a farko daya kuma a karshe ko...
Uhhhh ta wani sake nunfashi kamar irin ta tuno din nan
Malam ya gwalo ido gaba daya ya shiga confusion gashi suda suke nass farko farko yaji ana wani yanko masa wa'innn Yace ehhmm?
Toh Maimaita min su naji su..
Tare da dagiya Ta kuma cewa wa..innnn har da saka kalkala mai zafi
Amma still ba cigaba, gashi ita kanta bata san
Gintse dariya banafshan tayi ta juya kanta ba..
Nan Malam ya shiga tofe tofe yana kada kai yana da aiki...gaskiya da aiki..
Zata sake magana yace,naaam.. ah ah..laa laaa lah dakata,dakata..subahaaanakallahuma rabbiyal al'azeem sadaqalllahul azeem karatu ya kare mikki sai gobe...ya dube ta yace malamah nimrah to Allah ya tashe mu lpya.
Inaga anan zamu dasa aya dake...
Abun ya matukar bata haushi ta mike zumbur Tace ah ah a malam mai gemu,daga wa''innn din zamu tsaya bakaji sauran ba..
Ai bai tsaya sauraron ta ba Tuni yayi sallama da banafshan Ya tattara littafan sa yayi gaba..
Sai taga abun ya damu nimrah sosai sai leken sa take yi a hankali tana furta malam mai gemu wa'innn..wa' innnn..
abun yayi mata zafi don taso yau ace ta burge sa ya dena ganin kasawarta agaban banafshan
Itako banafsha Yadda taga malam yasa kai agaba yana tafiya yana kada kai yana jinjinawa yana mai maita wa innn wa''innn din shima yasa ta fashe da wani mugun dariyar bazata har tana rusunawaa..
Ta kasa daurewa nimrah Ta juyo suna hade ido da tace anty wa'innnn...wa' innnnn
Ta fashe da dariya kamar zata fada kan kujerah..
Nimrah tace kutuman uban cahn...mani kike dariya..
Ta dada fashewa da karfi har sauti na fitowa...
Tuni nimrahn ta harzuka tace dan uban ki mani kike kulewa? Sai zirr hawaye suka sauko .
wani dariyar ne ya cika ta ta toshe baki tana girgiza kai,..alaman ah'a
But idan ta tuno da wani abun sai ta sake fashewa da dariya
Zagowa nimrah tayi zata kamo ta,tayi tsalle ta ja da baya tana dariyar still gashi dama hijabin nimrah azuyee take saawa sai ya zamo da ita kamar mama mai saida karago
Garin masifa tana bin banafshan Charbin malam ne ya so ya yarda taa akasa yadda ya manta ya fadi bai daga ba..
banafsha ce ta dago tace naaamam ochhhh...kayyyahh..anty wa'innn kar ki fadi pls..nimrah ta dago cike da hanzari suna hade ido
tace lahhhhhhh ohhhhh Anty,..dama Malam
wa"innnnnn...ya manta da charbin sa ne? ...ta sake tuntsirewa da wata muguwar dariya...
Ita kanta batasan meyeke sata ba
Borin kunyar da nimrah keyi ya dada zafafa abun
Yanzun kam da gudu nimrahn ta saka ta agaba suna zaga falon har cikin ranta take jin haushi ita kuwa banafshan taka sa daurewa ne yau abun ya matukar bata dariya Kuma bazata iya bari ba..
Tace, idan na kamaki yau sai kinsan waye kikece ma anty wa''inn ni sa'ar ki ce..
tace bake kike cewa waiinnn din ba...
Tace kutuman uba,da ma uban ki nake fada ,.
Tace ah'hah fa ba ma uba na bakam ma malam waiinnn dai kike fada,ta toshe baki wani dariyar ne ya kufce
Nimrah tace wait till i catch you yau agidan nan Zakiyi spelling doom Tayi yunkuru zata cahkumo ta da sauri takama hanyar waje ..tace shegiya mayyah yauwwa jeki cahn ki same sa dama bakin ku daya yar iskan yarinya kawai..
Na sake jin kince wa'innn din nan ..
Tun kan ta karasa banafsha Ta fashe da dariya tace toh wanne daga ciki ne? Mai zallan wa'inn din ne ko mai kafffar..kaff ..kaf..to kema ki dena fada mana anty..tana dariyar ta murguda mata baki cikin salo
a tsawace nimrah tace bazan dena ba...ke kuma uban ki zakici dan uban ki
Tasha mamakin yadda banafshan yau ta bankade mata a take tana mata gautsin ko tsoron ta bata ji ba
Ta dan kunburo baki tana gitse dariyar ta tace anty.. wai'innn kaffartum ne ko waiinn kuntum...
'Ni dai gaskiya ina so nafada ta toshe bakin ta cike da tsokana
Rarumo vase din flower nimrah tayi zata wurga mata ta tsala ihu ta riga a guje
zata fita cahraf sai ga shi nan ya shigo, bayan sa ta shige ta damke rigar sa ta buya..
ya kare ma wajen kallo garin guje gujen su dik trow pillows akasa suke yace menene kuma da ga karatu sai fada?
Guntun hawayen bacin rai nimrah ta goge A zuciye tace sai ka tanbaye wanna marar kunyar,dariyar me take min
Itako sai lafewa take ta riko rigar sa dam tana biye fuska abayan sa tsammanin ta fushi kawai nimrah tayi don malam ya basar da wainnn din ta sai taga kuma abun ya mugun bata mata rai...sai yanzu take ganin hakan boroe boro
Ya juyo kadan Yace ke kuma dariyar me kike yi,ta dan leko kadan suna hade ido da nimrah taji abun ya gulle ta, sai ta daure ta fito kadan tace dama... dama...sa muke karatu ne malam....yace..nimrahn tace wallhy kika fada sai na tattakaki anan.
Yace meye wannan din..tace anty ne fa dan tace wa'innnnn sau dayawa bata cigaba ba har malam ya gudu,..sai nake maimaita mata shine taji haushi...
yace mene? Tace Wa'innn..yace wa'inn ...what?
bangane ba tace uhmmmm anty,wa'inn kaffartum ne ko waiin kuntum..?
Wani kukan kura nimrah tayi ta harzuka, tayo kansu..yayi saurin maida banafshan bayan sa yace dakata mana malama..ni fa na tambaye ta..
a fusace tace tsokanata take yi fah mohan...
ta bata rai
Yace to ke kifada mun mana miye ya faru..
Ta bata rai tace ai ba abaki na ka fara ji ta fito fili mana ta karasa maka taga yadda zanyi daita..
Ya dan juya kadan yace
Ma banafshan Wai meye sauran labarin,daga bayan sa bata fasa ba tace yaya nifa ban sani ba ..haka fa malamin ya tambaye ta to ni meye nawa aciki dan na maimaita?
Ni fa dama tanayar ta nake yi ko antyy..
A fusace Tace da Allah min shiru..ai dama uban ki ne aciki dan ubanki mayya kawai
Yace ah'a ya isa hakan..
tace Ba tambaya na kikeyi ba ko?tabb hmmm ..irin yau zakiga gamu dani ,,cike da salon lallabin yaudara yace comn baby relax mana....tace ah a bawai fa ban iya bane , baby toh meye ne aciki dan nace.. Wa'innn,..wa innnn ..sai ta kasa cigaba tana ii..ii ii na..tana zaro ido
Yace ehenm cigaba mana baby,..ta kuma cewa wa..innn..muryan ta har na rawa ta rasa me zatace tace kafff..kafi..
Sounding very funy and amused Yace ah'a ah tsaya.. babe wani surah kenan zaki karanto, nan ta zije gashi bata son accepting defeat kamar zatayi bursting da kukan tace suratul munafikat.
Tare suka fashe mata da dariya mai sauti mai kularwa
Cikin dariyar banafshan tace yaya kagani ko abunda ya faru kenan.. Tsaban dariya Ya kasa magana Ya mata kallon irin really?
ta gyada kai tace for hours,kaga ma malam har ya gudu
Ya dada tuntsirewa Yace Allah?sai ya tuno da mutumiyar tashi nan ya toshe baki ya dago yana duban ta yana gintsewa
A haukace nimah ta dauki pillow ta wurga mata, ta sake wani huci
Ta razana amma bai hanata rikicewa tana cewa wayyoo anty waiin dan Allah kiyi hakuri...
Tayo kansu baki daya
da gudu ta sake shi ta wuce daki,
Dariyar su gaba daya ya hanasa sakat,sai Ya kamo hannun nimrahn dake shirin bintaa haukace ta fauce tare suka isa kofar dakin,
Nan shikuwa ya cigaba da shan cikin banafshan da tambayoyi daga cikin dakin ta cigaba da bashi labarin abunda ya faru cikin salo da shike ta hada da shagwaba da yarinta sai ya kasa conroling kansa suka cigaba tuntsirewa da dariya ..
Sai dai yanzun tsoro ya fara taba banfshan musamman yadda nimrah ke baraza itama
Idan nimrah tayi diri tayi diri sai yace mata calm down mana..cahn
Sai ya juya Yace baby,? Ashe haka kike da kokari,
Toh ina carbin malamin
Gashi duk sanda ta bude baki zatayi defending kanta sai ta sake kawo masa wani labarin kwaben da tayi ,yayi dariya har yana tsugunl
Karshe Wurga masa charbin tayi,ta wuce dakin ta ta fashe da kuka..
Ko da yaga hakan sai ya hakura da tsokanan yazo zai rarrashe ta ko kula sa batayi ba ,tafara surutai akan cewa yasa yarinya ta raina ta..
Ganin abin ya mata zafi sosai ya sa ya tashi, ya dauko keys ya bude kofar dakin banafshan..
Ta