Showing 30001 words to 33000 words out of 212729 words

Chapter 11 - TANGLED HEARTS BOOK COMPLETE by MAIMOON.doc

Maimoon   

09 Oct 2025

3642

hannunsa a kan kujera yana fara Salle buttons Win shirt Winsa ya nufi bedroom Winsa.

Mamaki ne ya kusa kashe shi a tsaye yana bin Wakin da kallo, wait me yake gani haka is he even dreaming or what?

Nuwaira ce a kwance a kan gadonsa Ware Ware tana barci, da wani yan iskan kayan bacci pink a jikinta da tsabar bacci duk ?afafunta a buWe, ga plate a bedside drawer na small chops da bata ?arasa cinyewa ba, da kwalin lemo, wig Winta a ?asa gefen gadon, the audacity da yake witnessing yanzu nearly knocked him off

Juyawa yayi ya kalli Amira da ke sallah wanda ya tabbatar na asuba ne a Wakin itama da zumbulelen hijab, ya kalli agogon hannunsa tara saura.

Amira da taji buWe ?ofa a tunaninta Saif ne ko Mary dan Allah Allah take ta idar ta koma bacci, dama ita Nuwaira ta tashe ta Sallar ma bata tashi ba kasancewar sai kusan 3 tayi bacci.

Ta sallame sallan ta juyo da niyyar ganin waye ya buWe ?ofar idan Mary ce ta faWa mata kar ta bari Saif ya hauro ya dame ta, bata san lokacin da tayi tsalle ta mi?e tsaye daga kan sallayar ba

 Albi?

Yadda ta faWa da ?arfi ya saka Nuwaira buWe ido, ta gyara kwanciwarta  wannan wani irin& .. bata ?arasa ba idanunta suka kai bakin ?ofar ganin can Amira ke kallo idanu a waje, da sauri itama ta mi?e zaune ta janyo duvet tana rufe ?afafunta itama tana zare idanu than tabbass bata mata warning Win da ya mata akan zuwa gidansa ba bare kuma yau sun shiga uku akan gadonsa a Wakinsa ma ya ganta.

Komai bai ce ba ya juya ya bar bakin ?ofar, Amira ta Waura hannu aka tana nufar Nuwaira dake kan gado itama ta rasa me zatayi next

 Nuwa na shiga uku me zan ce masa? Ke ki faWamin me zan ce masa? Sai da nace miki kar mu zo nan Wakinsa kika ce in ma bazan kwana ba ke anan zaki kwana kinga abin da kika jawo min koh?

Nuwaira tayi gyaran Murya jin muryarta ta ma?ale

 Ke dillah miye kike abu kamar wani laifi kikayi masa? Sai kace ba mijinki ba ji yadda kike wani rawar jiki, to miye a ciki? Dan mun kwanta a Wakinsa, Wakinnasa na gwal ne da baza a kwanta ba?

 Haka ma zaki ce min? Bayan kema kinsan yadda muka yi last time akan zuwanki gidannan Nuwa? Kinsan in Mummyna taji sai ta kusa yanka mu daga ni har ke

 Ta yanka ki dai ke kaWai, ni me nayi?

 Haka zaki ce min?

Nuwaira ta kamo hannunta  kinga Amii, kwantar da hankalinki, kema amma me yasa baki ce min yau zai dawo ba?

 Nima ai bansan yau zai dawo ba fa bai faWa min ba 

 Toh kinga ni bari in wuce gida kawai, dont worry babu abinda zai iya, fushi zai Wan yi kaWan shikenan ya wuce, ki daina nuna kina tsoronsa dan Allah kamar wata wawuya haba sai kace ke ba mace bace mijinki ne fa zai sau?o ne

Ta faWa tana jan zip Win skirt Win atamparta da ta ajiye a cikin sif Win Ahmad Win.

Tagumi kawai Amira tayi tana kallonta, dan ta gagara ma tashi tabi bayansa, har Nuwaira ta gama shiryawa ta yafa Wan mitsililin gyalenta,

 Bari na wuce Amii, call me when ur oga calm down small, haba shima wlh ya cika Waukan komai serious

Daga haka tayi ?ofa da Sauri ta Sau?a downstairs ganin baya falourn da Sauri ta fice daga gidan da makullin motarta a hannu.

BuWe ?ofar da aka sake yi ya saka Amira mi?ewa tsaye tana kallonsa ta ja da baya da Sauri amma ta gagara magana, kan gadon ya kalla ganin bata nan yayi ?wafa ya juya zai bar Wakin

 Albiii Amira ta faWa tana kallonsa da ?yar ta tattaro kalmomin ma ta haWa ta ambaci sunannasa.

A fusace ya juyo  Dont call me that, Amira Sau nawa nace miki kar na ?ara ganin wanann yarinyar a gidana?

Shiru tayi ta kasa magana

 one simple instruction  No Nuwaira in this house ba haka nace miki ba but No u even bring her to my space

 Wallahi fa& 

Kallonta kawai yake cike da dissapointment kafin ya juya ya fara tafiya sai kuma ya dawo

 Duk ranann da na ?ara ganin Nuwaira a gidana, then ull no longer be in the house either

Daga haka ya fice ya barta a tsaye tana binsa da kallo.


Wallahi bani da lafiya, tun jiya but i dont want to disappoint u guys shiyasa na daure nayi typing Winnan, idan kun jini gobe jikin da sau?i, idan baku ji ni ba ku min uzuri.


#Maimoon
09041426598 whatsapp only pls no calls
[8/14, 11:26 PM] Maimoo 3: https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q

RU?A??UN ZU?ATA(TANGLED HEARTS)

Yota/014
Wattpad: @Maimunah_Abdallah
ArewaBooks: @maimunahabdallah

This page is for u merhmerh na, nasan ba lallai ki gani ba =?? but still na baki shi kyauta, yahanasu ta, my supportive fwend d'?('

Chapter 15: Fires Rekindled

Bai dawo gidan ba sai Dare, shima kuma da Sabon Sacin rai ya dawo, ko kula yadda falon ke zuba ?amshi bai yi ba ya haura sama duk ransa a dagule, a falon sama ya tarda Amira da Saif a kwance suna kallo, Wage Saif yayi cak daga wajen yaron ya Waga kai ganin babansa ne ya mayarda kansa jikinsa, ba tare da ya kula Amira da ke masa Sannu da zuwa ba ya wuce Wakinsa da yaron, Amira ta bisa da kallo ganin har kaya ya sauya, toilet ya kaisa ya masa brush ya masa wanka sannan ya shirya sa cikin kayan baccinsa da akwai a Wakinsa. Yana taje masa gashinsa a gaban Madubi Saif Win ya dube shi sai kuma ya shafa fuskarsa  Papa why are u not smiling? ?an Murmushi kaWan yayi  papa is in a bad mood today gyaWa kai yaron yayi kamar ya gane me yake nufi, Ahmad ya Wauko turarensa ya feshe yaron da shi ya Waga shi Sama yaron ya saka dariya, dire shi yayi a kan gado yana murmushi ganin yadda Saif Win ke dariya kamar ya masa cakulkuli, haka yake da son wasa, ya zauna gefen Gadon yana kallonsa ya shafa kansa

 Mummy ce ta je ta Wauko ka daga granny s place? Girgixa kai Saif yayi yana ?o?arin hawa jikinsa ya kwanta  No aunt Maryam and Yasmeen ne suka dawo dani da granny tace su dawo dani ya faWa yana taSa buttons Win rigan Ahmad Win

 Meyasa tace su dawo da kai?

 Saif ma bai sani ba saif Win ya faWa yana ?o?arin sau?a a gadon

 Okay Saif ya kwanta anan yayi bacci tare da papa ya faWa yana Wagosa daga ?o?arin sau?a da yake yi ya Waura sa a kan gadon

 Saif zai je wajen Mary ya faWa yana Sata rai, tsayawa yayi yana Wan kallonsa kafin ya shafa kansa  Okay da gudu ya sau?a a gadon ya nufi ?ofa ya bishi da kallo har ya fice kafin ya mi?e yana ?are ma bedroom Win kallo ?arasawa yayi ya Wauki wayarsa ya fita a Wakin, guess room dake Saman ya buWe ya shiga Amira ta bishi da kallo dama tasan bazai sake kwana a Wakin ba ta sau?e ajiyar zuciya. Sai kuma ta mi?e tabi bayansa, a rufe ta samu ?ofar da key tayi knocking kusan sau uku bai buWe ba, gagara tafiya tayi ta cigaba da knocking, ya buWe ?ofar yana Waure da towel da alama lokacin ya fito daga wanka, ta gefensa ta ?are ma Wakin kallo ganin har ya canza bedshit Yayi gyaran Murya yana goge gashinsa da ?aramin Towel Win hannunsa

 How can i help u? Marairaicewa tayi tana kallonsa ganin yadda ya mata tambayar kamar bai taSa saninta ba, ganin bazata amsa ba ya sake ?ofar ya koma ciki ba tare da ya kulata ba ta ?araso cikin Wakin a hankali ta tsaya daga bakin ?ofa kawai ta fashe masa da kuka, lumshe idanunsa yayi ya buWe bai kulata ba ya cigaba da abinda yake yi, ganin tana tsaye tana kuka still ya zauna gefen bed yana kallonta

Ta ?araso ta tsugunna a gefen bed Win kusa da shi tana kallonsa  Albi dan Allah kayi ha?uri bazan sake ba kallonta kawai yake yi yadda take shessheqan kuka, duk yadda ya so nuna mata Sacin ransa kasawa yayi yana kallonta yace  Amira ta Waga idanunta tana kallonsa, hannunsa ya sa ya kama hannunta ya Wago ta ya dawo da ita kusa da shi ya zaunar da ita  meyasa bakya jin magana? Shiru tayi bata amsa ba,  Amira na sha gaya miki times without Number stay away from Nuwaira amma bakya ji, ke a rashin hankalinki har zaki bar ?awarki ta kwanta a Wakin mijinki a kan gadonsa? And again why did u went ahead ba tare da amincewata ba kika je kika Wauko Saif daga wajen Ammi?

Tana kallonsa ta Marairaice  Nuwaira ce tace muje mu Wauko sa wlh ka yarda dani ba laifi na bane cije lips Winsa yayi kaWan ya ma rasa me zai ce mata, ta mi?e daga zaunen da take ta shige jikinsa ta kwantar da kanta a ?irjinsa tana sau?e ajiyar zuciya  amma na maka al?awarin bazan sake ba, daga yau duk abinda kace min zanyi kayi ha?uri pls Albi shiru yayi bai ce komai ba ya sa hannu yana shafa kanta a hankali lost in thought cause Nuwaira itace problem Win Amira gabaWayansa, for the past 5 years da suka yi aure duk wani matsala da suka samu wanda zuwa yanzu bazai iya lissafa su ba Nuwaira ce take janyo musu, it went as far as da ?yar Amira ta yarda ta haifi Saif cause Nuwaira tace mata zata Sata jikinta idan ta yarda ta haihu she wanted aborting cikin Saif ba don Allah ya ta?aita kuma ya ankara da wuri ba.

?ago ta yayi daga jikinsa ya maida iya gefen bed Win ya shafa fuskarta ya mi?e tsaye ya wuce closet dan shiryawa, wani murmushi Amira tayi tana binsa da kallo dan kwata kwata bata yi tunanin zai sau?o da wuri haka ba, wannan ya sake tabbatar mata da irin son da Ahmad ke mata, mi?ewa tayi tabi bayansa closet Win, ya saka dogon wando yana ?o?arin saka riga ta shigo ta tsaya daga bakin ?ofa tana masa wani naughty look, sau Waya ya kalleta ya cigaba da abinda yake yi, ta ?araso ta tsaya a gabansa tana kallonsa Wage mata gira yayi ta girgiza masa kai ta kai hannunta duka biyu ta sa?ala a wuyansa tana kallon cikin idanunsa kafin ta Wan Wage ?afafunta ta haWe bakinta da nasa, ajiyar zuciya ya sau?e a hankali ya sa hannunsa ya cire hannayenta daga wuyansa ya maidasu bayanta ya jingina ta da bangon wajen kafin ya zare bakinsa daga nata yana kallon cikin idanunta, murmushi ya mata ya sa hannunsa ya shafa fuskarta kafin ya sake ta ya koma ya Wau rigarsa ya cigaba da sakawa, sai da ya gama sakawa kafin ya juya ya kalleta yanda ta jingina da bangon tana kallonsa jikinta duk a mace, ya juya ya fita daga closet Win, gaban dresser ya ?arasa yana feshe jikinsa da turare ta fito daga cikin closet Win sai kuma ta nufi ?ofa fuuu ta fita, binta yayi da kallo sanda yayi murmushi ba yana shafa kansa.

____
Satinta biyu kenan da dawowa Nigeria, zata iya cewa life has never been happier, sosai take jin WaWin zamanta da Mami da big Daddy like dis is home, anan babu mummy da fuska biyunta, babu Suhaila babu Daddy though sometimes tana kewan Dad sosai, a yanzu ma makaranta ake ?o?arin nema mata cause big Daddy yace babu abinda za a jira.

Yau ma suna zaune a palour da Fahad da tunda ya ?yalla ido ya ganta sunje gidan uncle Aminu da Mami shikenan gidan Mami ya zama gurin zuwansa, kusan kullum sai ya zo har ta saba sosai da shi. Mami ta fito daga kitchen tana kallonsa tace  Fahad zaka ci abincin a dinning ko a kawo maka palour? Girgiza kai yayi  No Mami wallahi am full daga gida fa nake Mami ta hararesa tana ajiye warmer akan dining  Wazu kuma kace daga wajen aiki kake, My friend zo kaci abinci Na ima tayi dariya tana kallonsa ya harareta ya mi?e zuwa dinning Win dan da gaske yunwa yake ji, yana kallon Mami ya zauna a kujerar dining Win ya langaSe kai  kin dai yi insisting Mami amma ba wani yunwa fa nake ji ba Mami bata kulashi ba ta dubi Na ima da ta mayarda headphone Winta kunnenta tana gyara kwanciyarta akan kujera ta Waura mackbook Winta akan cikinta tana kallo

 Na ima pausing abinda take kallo tayi ta Wago kanta  zo kici abinci  Mami a ?oshe nake nikam, besides bana son in ci anything heavy da dare harararta Mami tayi bata sake ce mata komai ba tana kallon Fahad tace  jiya big Daddy ya maka maganan Makarantar Na ima koh?  GyaWa kai fahad yayi yana cin abincin gabansa  eh wai yace i should handle it, amma ke a ganinki base ko Nile wanne zaifi? ?an kallon Na ima tayi sai kuma ta maida kallonta kan Fahad  ina zan sani, ita wanne tafi so wai? Sai da ya kurSi lemon juice dake gabansa kafin ya dubi Mami  FaWila ce take zugata wai taje Pan-atlantic tunda accounting take so Mami tayi tsaki kaWan  haka FaWilar tace min, banda shirme tayaya Na ima zata zauna a gidanta, itama duka duka yaushe tayi auren? Wata na biyar kenan fa har kuma ace ?anwarta ta dawo wajenta da sunan karatu? Nikam ai nace mata bazai yiwu ba Big daddy ma ba yarda zaiyi ba Fahad yana cin abincinsa yace  Ah toh, akan wani dalili ma kawai sai ta koma Lagos, ance mata ita kaWai ke son Na imar a dangi Mami tayi murmushi bata ce komai ba tana kallon Na ima da ta saka musu cartoon a laptop ita da su Aryan suka koma ?asan carpet suka kwanta.

Wayarta da ya hau ringing ya sa ta dubi wayar ganin faWila ke kiranta video call, ta matsa daga gefen su aryan tana dariya ta Wauka, faWila dake kwance a palornta tana kallon Na ima ta cikin screen Win tace  Hiiiii Na ima tayi dariya  hellloooo itama ta amsa FaWila tace  ina Mami? Juya mata camera Win tayi zuwa wajensu Mami kafin ta sake juyo da shi fuskarta, FaWila ta kwaSe fuska  yaya Fahad ne? Na ima na murmushi ta gyaWa mata kai  shikenan yanxu zai zuga Mami a hanaki zuwa pan atlantic when am telling u its the best univerity Allah da gaske Naima tace  its the best ko dai someone wants to be seeing me everyday, ni na ha?ura ma yaya Fahad yace kawai zai nema min base Fadila ta haWe rai  Lallai ma Na ima amma haka muka yi da ke? Naima ta marairaice  ai dama ce miki nayi in Mami ta yarda to ta ?i yarda ya zanyi? FaWila tayi shiru, Naima tana kallon yadda ta Sata rai tace  kinga haka Mami tace Yaya Nasir ma ai bazai ji daWi ba tunda baku daWe da aure ba kuma kawai sai in dawo gidanki da sunan karatu Nasir dake gefen FaWila ya le?o ta cikin wayar  haka muka yi da ke Na ima? Ya kuna ma matata haka ne? Cant u see shes lonely here? Ya faWa yana taSa kumatun faWila, Naima tana dariya tace  good evening  evening Na ima ya gida? Tace  lafiya ?alau FaWila tayi wani murmushj tace  nasan wa zan ma magana, big Daddy zan kira anjima in faWa masa ko kuma in kira daddyna shi ya faWa ma big daddy, kuma ai bani da lafiya i need Wan uwana kusa dani Nasan bazai hana ki ba, babe ull tell him too kaji? GyaWa mata kai yayi  in sha Allah shiru Na ima tayi kafin a hankali tace  toh Allah ya sa ya yarda

Washegari a wajen karyawa big Daddy ya dubi Na ima dake juya tea yace  daughter da base da Nile Abuja da kuma pan atlantic Lagos wanne kike so? ?an satan kallon Mami tayi ganin ba ita take kallo ba a hankali tace  ko wanne yayi Murmushi  okay jiya uncle Winki Aminu ya kirani akan ?yar uwarki ta damu tana so ki je wajenta ki zauna tare da ita kina so kije? Sake kallon Mami tayi, ita dai Mami ta?i kallonta tana cin abincinta ba tare da ta kulasu ba, gyaWa ma Big Daddy kai tayi alamar  eh yayi Murmushi  okay then pan atlantic its, zan ma Fahad magana zuwa upper week sai ya kaiki Lagos Win yayi duk abinda ya kamata, ke kuma make sure kin mayarda hankali kinyi abinda ya kaiki, duk hutu sai ki dinga zuwa kina mana okay?  GyaWa mishi kai tayi  yes Daddy big Daddy ya kalli Mami  Madam babu abinda zaki ce? Mami ta Wan dube shi kaWan  to me zan ce ? Allah ya bata ilimi mai albarka da anfani yasa can Win yafi alkhairi duk suka amsa da Amin
Sai bayan da big Daddy ya fita kafin Mami ta dubi Na ima tace  kun kyauta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login