Showing 117001 words to 120000 words out of 212729 words

Chapter 40 - TANGLED HEARTS BOOK COMPLETE by MAIMOON.doc

Maimoon   

09 Oct 2025

3694

in bari da safe sai in girka mata da kaina yanzu ma na shiga ai na samu tana toilet Wauke idanunsa yayi daga kanta a ta?aice yace

 Ta tafi Abuja, she s done with her exams plus& .. ko jira ya ?arasa bata yi ba tace

 Abuja kuma?wani irin Abuja?

Ya gyara zamansa a kan gadon yace

 Eh ta je wajen mamarta ta zo ta miki sallama bakya nan, she had to go saboda a jiya aka & ..

Bata jira ya kai ?arshe ba nan ba tace  amma tsakani da Allah ai wannan ba yi bane, ta yaya zata tafi Abuja bazata jira in dawo daga inda naje ta min sallama ba, saboda dai bata Wauke ni uwa ba, duk abinda nake mata ba a gani, in da ni uwarta ce ai bazata min komai ba amma babu komai& 

Kallonta kawai dad yake ganin yadda take ta jaraba tana haWa zufa, abin ya bashi mamaki but bai ce komai ba

 Wallahi duk abinda ake min a gidannan ina shiru amma naga alama u guys a taking it for granted, idan ba ni Win bama wa ke ri?e Wan wani a zamaninnan? Amma har zata wuce ta tafi bazata min sallama saboda ta raina ni bata Wauke ni uwarta ba, an gama nuna mata bani da daraja a wajenta wallahi akwai hisabi tsakani na da ku akan yarinyarnan ranar ?iyama daga haka ta fashe da kuka ta nufi ?ofa ya bita da kallo kawai cike da mamaki.

Tana fitowa palourn ta hango Suhaila da ta dawo gidan a daren itama a zaune da kwanon abincin da ta ajiye a palourn a hannu ba bata san sanda ta haWiye shegen kukan da take ba ta nufe ta da gudu.




#Maimoon
09041426598
[8/14, 11:33 PM] Maimoo 3: https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q

RU?A??UN ZU?ATA(TANGLED HEARTS)

Yota/014
Wattpad: @Maimunah_Abdallah
ArewaBooks: @maimunahabdallah

Special tnks to Hafiza bashir saleh, Aanaah, mrs muhammad, oum fu ad, oum arham, hauwa ykay, habibti na tace in gaishe ku in sake gaishe ku, ur comments suna bata joy over, we love u so much d'?

Chapter 46: Tangled in truths

 Suhaila!! Mummy ta Kira sunanta tana ?arasowa cikin palourn da sauri, suhaila ta Waga kanta tana kallonta da spoon Win abincin a bakinta wanda yanzu ne ta kai first spoon dama bakinta, ko haWiyewa bata yi ba, kafin ta gama reacting har mummy ta iso gabanta ta ?wace kwanon a gabanta ta dungurar akan center table ta kama fuskarta tace

 BuWe bakin ta faWa tana Wan bubbuga kumatun suhailar, da shegen mamaki Suhaila ke kallonta dan bata gane komai dake faruwa ba, bakinta cike da abinci tace

 Whats your problem?

 I said open ur mouth ke dan ubanki mummy ta faWa tana yago tissue ta saka mata a dai dai bakinta, tofo abincin tayi reluctantly kan tissue Win tana Sata rai.

 Whats wrong with u, daga ganin abinci sai ki kama ci a gidannan, ko ke kika dafa? Ko ni na baki abincin da zaki kama ki hau ci? Cokali nawa kika ci?

Suhaila tayi rolling idanunta kafin tace  So? Ni ko Waya banci ba, to Miye ne idan naci? Whats the big deal ?Yunwa nake ji shiyasa naci, yanzu fa dawowata, to ma yaushe ya zama crime dan naci abinci mummy?

 Kar ki sake taSa abinda ba baki nayi ba a gidannan suhaila kinji na faWa miki tana faWa tana zaro wani sabon tissue tace
 buWe bakin kamr bazata buWe ba ta buWe bakin, tissue ta saka ta dinga goge mata baki kafin ta haWa kan tissues Win ta mi?e ta Wauki bowl Win abincin ma zata bar palourn, mi?ewa itama Suhaila tayi tana Wan jan siririn tsaki,  wallahi ure so extra sometimes, so dramatic daga haka ta Wauki wayarta ta nufi hanyar bedroom Winta, Mummy ta tsaya tana kallonta kafin tace  Suhaila, suhaila! Amma ko juyowa batayi ba har ta kai bakin ?ofarta kafin ta tsaya ta juyo tana kallon mummy, mummy da har ranta ya fara Saci tace

 Ni nake miki magana kina wucewa ina dan baki da hankali
 whatever.. kawai suhaila ta faWa ta juya ta shige Wakinta ta rufo ?ofarta, ajiyar zuciya mummy ta sau?e ta juya ta nufi ?asa da kwanon a hannunta tana jin wani irin relieve cause it was so close, what if bata fito ba da a minute later ? yo ya ta ?are ma da Ahmad Win yanzu akan Suhaila bare kuma suhaila taci wannan abin ai sun shiga uku.

Sai da ta zubar da abincin a waste bin ta Wauraye kwanon kafin ta koma sama amma har lokacin ba?in cikin yadda tayi asarar kuWinta kawai take yi, gaskiya Na ima ta cuce ta.


Tunda Na ima ta iso Abuja Mami ke nan nan da ita amma sam ta gagara faWa mata batun aurenta da aka Waura a jiya, sai dai tayi ta kallonta in tana wasa da su aryan, sosai take tausayinta dan sai yanzu take sake ganin ma Na ima tayi ?arama da wannan auren bare kuma wai ace mai mata ina yarinyarta zata iya da kishiya yanzu?
Da daddare Na ima na Wakinta da su aryan Mami ta tashi ta fita ta barsu jikinta duk a sanyaye, bedroom Winta ta wuce ta shiga ta rufe ?ofar ta ?arasa gaban mirrow tana cire awarwaron hannunta tana yi ne amma she s very lost a tunanin da take yi, har big daddy ya shigo bedroom Win bata sani ba, ya zauna a gefen bed yana kallonta ganin yadda take ciresu 1 by one, ko buWe ?ofar bata ji ba bare sallamarsa, kuma ya san abinda ke damunta, ya Wanyi gyarar murya yace

 Madam sai a lokacin ta dawo daga tunanin ta juyo ta kalleshi, sai kuma ta Wan Wauke kai ta ?arasa cire abin hannunta ba tare da ta ce masa komai ba, Wan murmushi yayi ya taso ya ri?o hannunta ya zaunarta gefen bed yana kallonta yace

 Whats the matter?

 Hmm kawai tace dan tun jiyan ta?i bari suyi maganar dan bata so tace komai tunda daga shi har baban Na iman suna da right Win aurar da ita.

 Akan aurenne har yanzu? Ya sake tambayanta, dan he can clearly see shes tensed, ta Wan sau?e ajiyar zuciya ta kalleshi tace

 Kana ganin hakan shine right thing to do?Na ima is still too young nake ga kamar fa, kuma fa yaron yana da mata kuka ce, ina Na ima zata iya da.. katseta big daddy yayi yana murmushi yace

 Do u trust me? Ta gyaWa masa kai, ya ri?o hannunta ya janyo ta jikinsa

 Insha Allah its for the best, kar ki damu ki bita da addu a tunda aikin gama ya riga ya gama, kinsan i wouldnt have agreed inda it was not for her good ta gyaWa masa kai a hankali,

 Nasan ure worried, but trust Allah and he ll make it easy for her, mu yi mata addu a kawai

 Amma.. bai bari ta ?arasa ba yace  i know, i understand kiyi hakuri, amma instead of tsoron da kike jiye mata, addu a zaki mata ki bar mayar da hannun agogo baya, addu ar tafi bu?ata a halin yanzu

Ajiyar zuciya ta sau?e a hankali ta gyaWa masa kai

 Ko ke fa? We re going to give her the best wedding in sha Allah ta Wan yi murmushi kaWan kafin tace

 To Allah ya sa haka yafi alkhairi


Washegari da safe Na ima har palourn big daddy taje ta gaishe sa kafin ta sau?a ?asa ta samu Mami a kitchen tare da mai aikinta suna haWa breakfast, ta gaishe su ta ja kujera ta zauna a kitchen Win tana kallon Mami, Mami ta Wan kalleta tace

 Ke dai ba zaki taSa sakawa jikinki kayan arzi?i ba sai ?ananun kaya ina? ?an dariya tayi tace

 Anjima zan saka idan zanje wajen anty fadila inga inaaya

 Yaushe zaki je?

 Later today ta faWa tana danna wayarta

 Kunyi magana da fadilar ne?

 Ah ah kawai zanje sai dai ta ganni, ai tasan na taho garinnan jiya

 Ai toh fadilar ma munyi waya da ita anjima zata zo nan gidan Win kinga ba sai kinje ba kenan

 Haba Mami? Mami ta Wan harareta tace

 habo

 Shikenan ma kinga na huta har gida za a kawo min inaaya in ganta

 Aikam Mami ta faWa tana barin gaban gas ta ?arasa ta Wauraye hannunta a sink dan ta rasa yadda zata ce mata sai ta tambayi mijinta fita, kuma amma da gaske itace ma ta kira tace fadilar ta zo gidan anjima.

Suna gama karyawa Na ima ta mi?e zata wuce sama, sai a lokacin Mami tace

 Na ima ta juyo ta kalli Mami, a tsanake Mami tace

 Jeki Wakina ki jirani, ina zuwa yanzu zamuyi wata magana haka kawai Na ima taji gabanta ya faWi, ko dan irin seriousness da Mami tayi anfani da shi wajen magaanr ne? A hankali ta gyaWa mata kai ta wuce sama, a kan kujera ta zauna tana jiran Mami, amma sam zuciyarta is not at ease na maganar da zasu yi da Mami.

Mami na shigowa bayan ta kunna ma su Aryan tv a palournta ta tura ?ofar ta rufe Na ima ta Waga kai tana kallonta har ta ?araso cikin Wakin, ta zauna tana kallon Na ima dake kallonta itama, Mami tayi murmushi tace

 Miye haka, kallon fa? Na ima ta Wan marairaice tace  ai toh ban san maganar me zamuyi ba, zuciyata sai bugawa take yi bari ma kiji ta mi?e ta dawo gefen bed kusa da Mami ta kama hannunta ta Waura a ?irjinta.

Mami ta cire hannunta daga ?irjinta tana Wan murmushi tace

 Karki damu ba wani abu bane kina jina Na ima? A hankali ta gyara zamanta ta gyaWa mata kai alamun

 eh sai da Mami ta fara mata da nasiha, da misalin rayuwa kala kala har da tata rayuwar da aurenta, da yadda ta haifeta watching her grow, yanda she wants nothing but the best for her, haka ma su big daddy da babanta, kafin ta gangaro kan maganar Ahmad da zuwan da suka yi shekaran jiya, tunda aka fara maganar Ahmad ta sunkuyar da kanta a hankali tana sauraro har Sai da Mami ta kai gaSar da ta gagara fahimta ta Waga kanta da sauri tana kallon Mami frozen.

Ji tayi kamar bata ji da kyau ba, Aure? Ita Win? To Ahmad? Ya zo har nan ya aure ta? Shes now his wife? Without even asking her?

Wani irin swirl na emotions kawai take ji a cikin ?irjinta, disbelieve, harda anger, da confusion, a can can ?asar zuciyarta kuma ache of something softer wani abu mai kama da farinciki.

Muryarta na rawa tace  amma meyasa bai faWa min ba Mami? He didnt ask for my consent

Mami ta ri?o hannunta a hankali tace  it was sudden ne Na ima bashi da lokacin faWa miki a lokacin, amma its for the best kinji kar ki Waga hankalinki tunda kema da bakinki kince min Ahmad Win mutumin kirki ne

Girgiza kanta tayi hawayen da suka cika idanunta suka gangaro, ta gagara magana, Mami ta janyo ta jikinta tana patting bayanta a hankali alamun rarrashi, har sai da ta Wanyi shiru kafin ta Wago ta a jikinta ta share mata hawaye tace

 Kar ki Waga hankalinki kinji, duk abinda kika ga ya faru to dama can a tsare yake a cikin rayuwarki hakan ce zata kasance, ko bakya son Ahmad Winne shiru tayi bata amsa ba, Mami ta Wanyi shiru tana kallonta ta sake tambayarta

 Ko bakya sonshi? Girgiza mata kai tayi, Mami ta sau?e ajiyar zuciya tace

 To Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi. Tana faWin haka ta mi?e ta nufi ?ofa ta fita a Wakin, Na ima ta bita da kallo kafin ta hau gadon da kyau ta kwanta tayi shiru wasu hawayen na sake gangaro mata da ta rasa na miye ne. Wayarta da ta ajiye a kan kujera tun shigowarta ne ya hau ?ara, yana announcing mai kiranta, ta zuba ma kujerar idanu daga kan gadon amma ta gagara sau?a ta Wauko wayar har ta katse bayan few minutes ya sake kira, juya ma wayar baya tayi ta lumshe idanunta kawai a hankali.


Nuwaira ce ke driving, Amira na gefen mai zaman banza tana danna wayarta, sosai suke gajiye dan daga wajen babalawo Win Nuwaira suke bayan sun tabbatar masa cewa Suhaila ce yarinyar da ake so Ahmad ya aura, kuma suma asiri suke yi, saboda haka suna so duk wani asiri da zasu yi ya lalata shi, sannan kar ya taSa bari auren ya yiwu, mutumin yace musu ai babu ma aure tsakanin Suhaila da Ahmad kwata kwata Ahmad bazai aure ta ba, sosai suka ji hankalinsu ya kwanta, kuma ya tabbatar musu tabbass suma suna asiri sosai kuma lalata nasun zai masa wahala amma bazai gagaresa ba.

 Ba dai kinga yadda mukayi da mutuminnan ba, to ki kwantar da hankalinki wlh, mutumin ya san abinda yake yi, tunda mun riga mun faWa masa Clear and direct inda matsalar take wato Suhaila to duk aikinsa akansu zai yi bamu da matsala.

Amira ta Wanyi ?aramar dariya tana gyara gold earring Winta da ya Wan ma?ale da gyalenta tace  ni babu abinda ma ya kwantar min da hankali irin Waure zuciyarta da yace zaiyi, she wont even know what hit her da kanta zata ?i tace bata yi ko zasu mutu bazata yarda da auren ba suka tuntsire da dariya

 Shegiya ba da ?in zuwa kike yi ba ya kika g mafita Yarinya ai rayuwa ba malamai baya tafiya dai dai 

Amira tace  hmmm dan ko mummynta abinda take faWa kenan

Not known to them cewa annashuwan da suke yi ta faWuwa ce ba ta nasara ba, dan the real battle had already begun, kuma they lost it tun kafin ma suyi participating dan Ahmad already is married to Na ima wacce sam hankalinsu ma ba akanta yake ba a yanzu.

A gate Nuwaira tayi parking tana faWin

 bari na sau?e ki a nan kafin jarababben mijinki ya sami abin magana, duk yanda ake ciki in ji labari Amira Amira ta buWe motar ta sau?a da jakarta a hannu ta Waga ma Nuwaira hannu

 kar kiji komai Nuwa daga haka Nuwaira ta ja motar tayi zooming off ita kuma ta ?araso ta ?wan?wasa makeken gate Win gidan, mai gadi ya le?o ganinta yayi saurin buWe mata ?aramar door ta shigo ta wuce ba tare da ta amsa gaisuwar da suke mata ba.

Sanyin palournta ya mata sallama bayan ta shigo ta ajiye jakarta ta zare takalmanta ta mi?e ta kwashe takalmin da jakar a hannu ta nufi sama, a palourn sama ta ganshi a zaune da ?ananun kaya a jikinsa as usual yana kwance akan sofa yana danna wayarsa, dan he has been trying number Na ima amma kwata kwata baya tafiya, duk yadda ya so yayi zuciya da rashin Waukar wayarsa da ta dinga yi tun jiya abin ya gagareshi, sai uzuri ya ke mata a cikin zuciyarsa.

Ya Waga idanunsa yana kallon Amira da ke haurowa kafin ya kalli agogon wayarsa, ?arfe shida saura na yamma, ta ?asan idanu ya dinga kallonta har ta ?araso saman, har zata wuce Wakinta ganinsa a palourn ta taho nan ta ajiye jakarta a wata kujera daban ta zuba takalman a ?asa ta ?araso kujeran da yake ta zauna a saman hannu kujerar tana kallonsa tace

 Albi. Mi?ewa zaune yayi ba tare da ya ce mata komai ba, ta Wan kalli palourn kafin tace  Saif fa wani kallon side eye ya bata kafin yace

 daga ina kike? Ta Wan yi shrugging tana gyara zamanta da kyau tace

 my mothers place

 wa kika tambaya? Ya tambaya with the edge of his voice, hes not shouting but muryarsa is firm.

Ta Wan haWe rai tace

 to ba gani na dawo ba? Daga haka ta mi?e dan bata so ma ya ja maganar da tsawo

 A gajiye nake bari na watsa ruwa tana faWin haka ta nufi ?ofar Wakinta, ya bita da kallo, sai kuma ya jinginar da kansa da kujera yana juya wayarsa dake hannunsa. Dan tun da ya dawo bata nan sai Saif kaWai a gidan shima tun da ya dawo school hakan yasa ya kira Rahama ta zo ta Wauke sa ta kai sa wajen Ammi.

Bayan isha Ahmad na zaune a bedroom Winsa Amira ta shigo ta sha kayan baccinta abinta tayi kyau sosai, yana zaune yana aiki a laptop Winsa dan akwai abinda yake so yayi rounding up gobe he needs to fly to Abuja, cause rashin Waga wayarsa da Na ima ke yi sosai yake ci masa rai, he wants to know dalilin da take ?in Waga wayarsa tunda ta tafi Abujan.

?arasowa tayi ta zauna a gefensa tana murmushi a shagwaSe tace

 Albiii ya Waga idanunsa ya kalleta kafin ya mayarda kansa abinda yake yi, ?arasowa tayi ta sa hannu ta rufe laptop Win ta cire a hannunsa ta ajiye a gefen bed ta zauna a inda ta cire laptop Win tana kallon fuskarsa tace

 Dont u think its my time now? Ya dinga kallon cikin idanunta amma bai ce komai ba, ta sa?alo hannunta a wuyansa tana kallonsa tace

 Uhmmmm? Hannu yasa ya shafa hannunta da ta sa?ala a wuyasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login