Showing 153001 words to 156000 words out of 212729 words

Chapter 52 - TANGLED HEARTS BOOK COMPLETE by MAIMOON.doc

Maimoon   

09 Oct 2025

3677

Wan mi?e ya tsuguna a wajen kamar kneel down yana kallonsu da kumburarren fuskarsa da jini ya Sata, ta haWiye miyau ganin ya dawo kanta ta girgiza masa kai a hankali amma ta gagara magana sai kuka kawai take, wanda kukanne ke ma Sata masa rai fiye da komai, like is she crying all this cry saboda Sadiq? This son of a bitch ?hannu biyu ya sa ya ri?o kafaWarta ya jijjigata yana kallon idanunta da idanunsa da sun kaWa sunyi jajir yace

 He pressed u to the wall! Kinsan me hakan ke nufi? He touched my wife!

Hawayen idanunta na gangarowa tace  amma ure going too far

 Too far kika ce? Ta gyaWa masa kai tana kai bayan hannunta ta goge idanunta

 Bashi da lfy, kuma.. kuma He s not an animal, ka kalleshi ka ga abinda ka masa juyawa yayi ya kalli sadiq Win kafin ya dawo da idanunsa kanta, sake kafaWunta yayi a hankali ya ja da baya, wani azababben zafi ?irjinsa ke masa na bala i yana kallonta sannan ya kalli sadiq dake tsugunne a wajen har sannan yana kallon Na imar, idan ya cigaba da tsayuwa a wajen tabbass zai kashe Sadiq har lahira, dai dai lokacin motar yan sanda suka shigo wajen a tare lokaci Waya da Nasir, ko jiransu Ahmad baiyi ba ya juya tare da tsugunawa ya Wauki makullin motarta a ?asa kawai ya wuce ya buWe motar ya shiga, Nasir da yayi parking ya bishi da ido ganin yadda ya figi motar ya bar harabar wajen leaving Na ima behind tare da Nasir Win da kuma sadiq da ko attempting guduwa bayayi dan sosai ya daku, sai yan sanda da Nasir ya ?arasa wajensu dan suyi magana, itakam banda wata irin rawa babu abinda jikinta keyi gyalenta a hannunta ?afafunta ma ba takalmi.


 Maimoon
09041426598


https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q

RU?A??UN ZU?ATA(TANGLED HEARTS)

Yota/014
Wattpad: @Maimunah_Abdallah
ArewaBooks: @maimunahabdallah


Chapter 55: Holding on tighter

Kallon hanyar da ya bi da motar kawai take yi hawaye na cigaba da sintiri a idanunta cause bata ma san tunanin me zata yi ba, she didnt mean to hurt him ko kaWan thats the least thing da zatayi a rayuwarta amma at the same time tana tausayin sadiq bata so ya masa lahani, tears Winta suka gagara tsayuwa, duka jikinta is trembling dan ko sake kallon inda sadiq ma yake bata yi ba ta kai hannunta dake shaking ta Waura gyalenta a kanta she just couldnt think straight.

Nasir da ya gama magana da yan sandan, dan shima waWanda ya kira kafin ya taho wato asalin masu handling case Win sadiq are on their way, dan wancan karan da yayi kidnapping Winta dama friend Win Ahmad wani Soldier kamal shine ya taimaka aka kamasa before a mayar da case Winsa wajen waWanda ya kamata, ya ?arasa inda take amma ya gagara ce mata komai dan already yayi sensing akwai matsala, ganin ?afafunta ba takalmi ya juya ya fara kalle kallen wajen, a can kusa da lungun ya ga takalman ya wuce ya Wauko su ya ajiye su a gabanta yace

 Saka takalmanki tana cigaba da tsiyayar da hawaye ta zura ?afafunta cikin flat shows Win, ganin ta saka takalman ya sa ya wuce inda sadiq ke tsugune har lokacin kamar wanda aka saka kneel down, ya Wan tsuguna shima yana kallonsa, ganin yadda fuskarsa ta kumbure sosai ba kaWan ba idanunsa suka yi ?ananu, ga jini a gefen bakinsa da ya fashe da kuma goshinsa inda Ahmad Win ya buga sa da gini, gagara magana yayi kawai ya mi?e yana zaro wayarsa a aljihu yayi dialing wata Number ya koma gefe yana magana a wayar bai jima yana magana da su ba yace  alright ya kashe wayar cause dis time around ba zai bar guy Win ya sake suSuce masa ba, he ll try his best ganin ya sama masa lafiya ko dan albarkacin mamarsa da kullum cikin kiransa take da ro?o duk da yanzu ba kasafai ma ya cika Waukar wayar ba but he s taking Sadiq to a psychiatric ayi retaining Winsa a can he really needs the help, Sadiq dake kallon Na ima har sannan ganin Nasir ya tafi waya ya fara jan gwuiwarsa yana matsowa gabanta muryarsa bata fita sosai yace

 Ni ima ai kamar ya tsikareta da allura ta koma baya da sauri, ya haWe hannayensa yana kallonta wasu hawaye masu zafi na bin kuncinsa yace

 Kar ki manta old times Ni ima, ure my life, kar ki bari a rabamu dan Allah, he doesnt deserve u, ke watarana zai daka i promise u this Ni ima  yana faWan haka ya fashe da kuka ya saka fuskarsa a tafukan hannunsa yana kuka sosai jikinsa har na jijjiga, ganin abinda ke faruwa gashi Na imar ma sai kuka take yasa Nasir ya taho wajen, ya kalli Sadiq kafin ya kalli Na ima ganin duk kuka suke sosai yace

 Je mota ki jira ni Na ima ta kalleshi ya gyaWa mata kai a hankali ta juya ta nufi motar har sannan hawaye ke bin fuskarta ta rasa me take ji a ranta, lokaci Waya damuwa ya mata yawa har ji take kamar zata faWi ta nufi motar Nasir, buWe motar tayi ta shiga ta rufe ta kifa kanta da gwuiwarta ta cigaba da kuka, har police officers da doctors Win da Nasir ya kira suka iso tana cikin motar, Waga saWiq sukayi da jikinsa yayi tsami sosai carefully taking him away, Nasir ya bisu da kallo har suka saka shi a mota suka bar harabar wajen suma police Win farko suka wuce abinsu bayan Nasir ya sallame su tare da nuna musu medical report Win Sadiq Win da kuma tabbatar musu from here za a wuce da shi asibiti ne, kafin ya wuce motarsa leaving few mutanen da suka ga dramar har ?arshe a wajen, ya buWe mazaunin driver ya shiga yana kallon Na ima da ta kwantar da kanta a jikin ?ofa tayi shiru dis time around ba kuka take ba sai hawaye kawai da ke zubowa a idanunta, bai ce mata komai ba har dai ya tada motar, sai da suka hau titi sosai kafin ya Wan kalleta kaWan yayi Wan gyaran murya yana mayarda hankalinsa titi yace

 Tell me what happened, ya aka yi sadiq ya san inda kike wasu hawayen ne suka gangaro mata ta kai bayan hannunta ta share tace

 Nima ban sani ba kawai munje munci abinci ne shine.. shine yace zai siya abu and he insist i go in with him& & . Tiryan tiryan ta faWa masa duk abinda ya faru tana yi tana goge idanu

 Ni ban ce masa haka to hurt him or anything ba, amma yaya Nasir ai kaga yadda ya masa, where s his humanity? I only tried stopping him kar yayi abinda zaiyi regretting amma shine yayi fushi ya tafi ya barni tana kaiwa nan hawayenta suka ?aru ta rufe fuskarta da hannu tana kuka a hankali. Nasir ya Wan yi shiru kamar ba zai ce komai ba kafin a nutse yace

 U shouldnt have said that to him though, ko miye zai faru nan gaba bama fata amma koma miye ne u should side with ur husband ba wani daban ba, zaki iya hana shi in other ways ba tare da kin faWi abinda kika faWa ba, amma dai kar ki wani damu, haka yake fa shi dama iya da zuciya sosai, he ll calm down later kaWan, its normal gyaWa Masa kawai tayi a hankali ta mayar da kanta tana kallon taga, yadda suka tashi yau har zuwa fitowarsu bata taSa tunanin haka ranar xai ?are musu ba, bata taSa tunanin zasu koma gida seperately ba, har cikin compound Win Nasir ya sau?e ta, muryarta ciki ciki tace  thank you tare da buWe motar ta sau?a ya mi?a mata wayarta da ya Wauko mata ta amsa ta juya tana kallon motarta dake parke a compound Win ta nufi part Winta tana tafiya kamar ?wai ya fashe mata, juya kan motar Nasir yayi ya bar gidan ya bi bayansu sadiq cause so yake ayi komai a gama a yau.

A buWe ta samu ?ofar palournta ta Wan tsaya a bakin ?ofar jim kafin ta nufi ciki zuciyarta na bugawa kamar yaron da ya san yayi laifi ya dawo gida za a hukuntasa, ta mayarda ?ofar ta rufe a hankali tana kallon palourn ganin babu kowa.

Sama ta nufa jikinta duk a sake dan sai yanzu take sake jin rashin daWin fushin da yayi da ita, ta shiga bedroom Winta ta ?arasa kan gadonta ta faWa ta Waura fuskarta a pillow ta cigaba da kukanta abinta.

Tun tana kukan har bacci ya Wauke ta tana sau?e ajiyar zuciya, kiran Sallar la asar ya sa ta mi?e zaune a hankali tana jin kanta na ciwo sosai, ta sau?a a gadon ta wuce toilet tana sake jin yadda kanta ke sara mata duk ta motsa, kayanta ta cire ta watsa ruwa ta Wauro alwala ta fito ta shirya cikin simple egyptian gown tayi sallah, tana idarwa ta zauna akan sallayar ta juya tana kallon ?ofa, to ko ya shigo tana bacci ne? Mi?ewa tayi a hankali da hijab Win da tayi sallah a jikinta ta nufi ?ofa ta buWe ta fito,
duk da bata saka ran ganinsa a Wakin ba dan tunda suke gidan bai taSa ko zama na 1 hour a Wakinsa ba sai dai nata amma still ta nufi can, ta murWa ?ofar Wakin a hankali ta tsaya a bakin ?ofa tana kallon cikin tamfatsetsen Wakinnasa ganin baya ciki ta ?arasa ciki a hankali ta zauna a gefen bed Winsa tana jin kamar zai iya shigowa maybe anytime sai da ta kwashe kusan 1 hour da kaWan ganin ba shigowa zaiyi ba ta mi?e ta koma Wakinta ta rufe ta kwanta idanunta na sake cikowa da sabon hawaye, ta janyo wayarta ta shiga kiran layinsa amma har ya katse bai Wauka ba ta sake kira nan ma bai Wauka ba, ta tura masa text tana share idanunta amma no reply haka ta ha?ura ta cire hijab Winta ta hau kan gadon ta kwanta tayi shiru tana tunane tunane wanda duk nasa ne ta rasa yadda zata yi da ranta.

Har aka kira magrib tana kwance ji take kamar zazzaSi ma zata yi ta daure ta sau?a a gadon ta wuce toilet tayi alwala ta zo tayi sallah tana idarwa wayarta dake kan gado ya fara ringing ta mi?e da sauri da tunanin ko shi ne amma sai taga Fadila ce ke kiranta ta san maybe Nasir ya faWa mata abinda ya faru hakan yasa ta Waga wayar, a hankali tayi sallama, aikuwa ta canka dai dai dan straight Fadila ta soma tambayarta what happened, ta fashe mata da kuka tana labarta mata yadda ta faWawa Nasir Win ma, fadila ta sau?e ajiyar zuciya tace

 Babe yace min Yaya Ahmad left u there shi ya dawo da ke gida, kin same shi a gidan da kika dawo?

Ta share idanunta tace  ban same sa ba, da na dawo ban duba ba na zo na kwanta da na tashi kuma baya gidan

 Meyasa baki dubasa ba sanda kika dawo Na ima

 Babu ta faWa a hankali, fadila tayi shiru tace

 Ni gaskiya Sadiq Winnan abinsa ya fara wuce gona da iri haukar tasa ma ai ba ta masu hankali bace, ta ya za a yi ya cikaba da bibiyarki bayan ya san da aurenki ya dinga causing problem tsakaninki da mijinki a banza da hofi, ke kuma kamar wata wawuya fisabilillahi bayan kin san kin masa laifi u picked side Win ex Winki bayan duk abinda yayi its because of u yayi shi sannan ki dawo instead of u ki neme sa ki basa ha?uri shine kika je kika wani kwanta Na ima?

 Ai na je yanzu na basa ha?urin na samu baya nan

Fadila da haushi duk ya cikata tace  to wallahi kar ki kuskura ki bari ya kwana yana fushi da ke, kar ki mayar da kanki wawuya kishiya ce da ke da take neman slight opportunity da zata ganku a rana dan ni har message ta min dogo ta zage ni tas tas akan ni ce munafuka da na haWaki da mijinta ni dai ban kulata ba dan bani da lokacinta saboda haka kar ki sake ki bari ta san kun samu issue da mijinki after just 1 week da aurenku kina jina? GyaWa kai tayi a hankali tace

 Eh

 Yanzu yaushe zai koma Wakin Amira

 Yau ta faWa tana jan hanci,

 Kash! Ba dai komai ki samu ki basa ha?uri kafin ya koma can kar ya tafi can da fushinki dan Allah

 Toh ta faWa a hankali

 Kuma ki bar kuka haka kar kanki yayi ciwo, this is officially ur first fight ta faWa tana Wan dariya so that Na imar ma zata Wan sake ranta, Na ima tayi ?arfin halin Wan yin murmushi tace

 Amma anty fadila fa yayi fushi sosai

 Ke haka yake fa, Babe ya sha faWa min wallahi cewa iya da zuciya sosai guy Win, ke baki ga Nasir kaWai yake shiri da shi ba? Baya cika shiga harkar friends Winsu ma saboda abu kaWan ke provoking Winsa to bare kuma ke da yake so da ya Wauki matter Winki for head, shima Babe Win sun san halin juna ne kawai da shi, to shima sai su kwana biyu basa wani magana zuwanki gidana ne fa ya zozzo gidan namu amma baya zuwa wallahi, shiyasa da ya nuna interest Winsa a kanki nayi mamaki sosai ba kaWan ba wallahi

 Hmmm kawai Na ima ta iya cewa dan kuwa yanzu ai ta sake sanin halinsa, ashe shima yana da ba?in hali, sun jima suna waya da fadila tana kwantar mata da hankali kafin suyi sallama, sosai kuma taji hankalinta ya Wan kwanta.

Har tayi isha i bai shigo gidan ba, zuwa yanzu kam hankalinta ya soma tashi, sai a lokacin ta lura babu laptop Winsa dake Wakinta da other stuffs Winsa, mamaki ya kusa kasheta does that means ba zai mata sallama ba shikenan ya koma part Win matarsa? Ai kamar hakan ya dawo mata da sabon kuka, ta tafi jikin window Winta ta tsaya tana kallon part Win Amira kafin ta koma gefen bed ta zauna a hankali. Ko yunwa kwata kwata bata ji ba bare ta nema ma kanta abinci, haka ta kwanta abinta, amma sam bacci ya?i ya sace ta, har wajen ?arfe 2 tana juye juye kafin da ?yar bacci ya Wauke ta around 2:30, shima kiran sallar farko ta buWe idanunta da har sun mata nauyi, tana buWe idanunta shine ya fara zuwa ranta dan dama da shi ta kwanta a ranta, ta sau?a a gadon a hankali ta wuce toilet tayi fitsari ta fito sai ta gagara komawa ta kwanta ta tafi jikin window Winta tana kallon part Win Amira dan kam ta san in har yana gidan zuwa yanzu zai fita mosque, ilai kuwa bata jima da tsayuwa ba ya buWe ?ofar part Win Amira ya fito yana sanye da jallabiya ba?a against his very fair skin, duk da duhun asuba hasken compound Win tarrrr yake kamar rana, ta zuba masa idanu har ya buWe ?aramar gate ya fita a gidan, ajiyar zuciya ta sau?e a hankali ta juya ta koma cikin toilet ta Wauro alwala itama.


?arfe 6:10 ya shigo cikin gidan from masallaci, har ya nufi part Win Amira ya Wan dakata ya kalli sashen Na ima duk yadda ya so ya Wauke kansa ya wuce sashen Amira kasawa yayi, ya haWe rai ya nufi sashenta yana tafiya a nutse kamar babu abinda ke damunsa, Amira dake tsaye jikin nata window ta bishi da kallo, dan tun jiya what shes been witnessing a gidannan ita ta san wallahi definitely akwai abinda ya haWosu da matar gwal Win nasa, cause akan idanunta suka fita dan ita dan yanzu ta mayarda wajen permanent wajen tsayuwarta a Wakin, slight motsi taji zata yi maza ta le?a, akan idanunta suka dawo seperately shi ya fara dawowa kamar ma a zuciye ya dawo ya wuce sashin Na imar kafin Munafukincan Nasir shi kuma ya kawo ta after kusan more than 30minutes da dawowar shi Ahmad Win, from then kuma bata jima da shiga ba Ahmad Win ya fito a part Win ya nufo part Winta and hes been here tun lokacin har zuwa yanzu da ya tafi mosque bayan ya katse mata barcinta dan dole wai ta tashi tayi sallah, duk da jiyan ba wani shiga harkarta yayi ba, sama sama yake amsa mata maganarta but still she was happy, abinda ya bata mamaki shine rashin baccin da yayi dan a bedroom Winsa ma ta kwana infact a jikinsa but she can swear har tsakar dare da ta tashi ta je toilet idanunsa biyu, yanzu kuma ta ga ya nufi sashin Na ima, to ko dai ba faWa suka yi bane? Idan ba faWa ba mai zai sa ya tattaro da wuri haka ya dawo sashinta ya bar matar so, ?wafa tayi tana kallonsa a ranta ta riga ta san today is the end of it su gama abubuwansu wallahi yau shine ?arshen tsinannen love story Winnasu.

Da mamaki ya ?arasa cikin palourn nata ganin ?ofar babu lock an tura but ba a rufe ba does that mean ?ofar part Winta a buWe ta barshi ya kwana? Ya dinga kallon palourn ganin yana nan yadda ya barsa jiya ya wuce sama fuskarsa ba yabo ba fallasa, sai da ya Wan tsaya jim a bakin ?ofarta kamar ya juya abinsa sai kuma ya tura ?ofar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login