Showing 39001 words to 42000 words out of 212729 words

Chapter 14 - TANGLED HEARTS BOOK COMPLETE by MAIMOON.doc

Maimoon   

09 Oct 2025

3643

tambayarki kince ba komai kuma har yanzu u look moody

 Mi?ewa tayi tana ?a?alo murmushi  babu komai fa anty faWeela stress ne kawai na makaranta

 Okay amma&  cije bakinta tayi ta gagara ?arasawa

Da sauri Na ima ta ?araso wajenta tana ri?e ta,  baki da lafiya ne?

FaWila ta Wanyi murmushi  lafiya ta lau fa, kawai cikina ke Wan ciwo ba sosai bane amma

 To ai da kin zauna kin huta

 Eh kar ki damu zamu je asibiti da baby Gobe its not serious amma dai gwara muje muji miye ne

 Eh ya kamata

 Toh tun da kince ba komai ai sai ki fito kici abinci koh? Tunda kika dawo fa baki ci komai ba faWila ta faWa tana nufar ?ofa

 Toh Na ima ta faWa a hankali tana bin faWeela da kallo, sosai take jinta a ranta kamar uwarsu Waya ubansu Waya, ko dan yawan kulawarta gareta, ko dan bata saba da irin wannan bane oho, back in newyork babu wanda ya damu taci abinci ko bata ci ba, ba wanda dan bata fito ba ta wuni a Wakinta zai damu kamar yadda FaWeela ke damuwa haka, tayi murmushi ta Wauki hula ta saka ma kanta da tama 2 braid ta dawo da jelan ta gaba ya sau?o har chest Winta ta nufi ?ofa ta fita.

Ko da dare yayi kasa bacci tayi, ta buWe text Win sadiq tana bi a hankali amma sai ta kasa masa reply, wanda zuwa lokacin ya sake kiranta ba adadi ya tura mata messages da har suka fara bata tsoro, cause gabaWaya gani take kamar ba sadiq Win da ta sani bane wannan. ?arshe littafanta ta kwaso da laptop Winta da niyyar karatu amma shima ta gagara.

Da ?yar bacci ya Wauke ta around 1:30 na dare, ?arfe biyu cif taji ana ?wan?wasa ?ofarta, ta mi?e da sauri tana mutsuka idonta, jin muryar Nasir yana kiran sunanta yasa ta sau?a daga gadon da sauri tana ture books Winta da ke baje akan gadon ta zura hijab Win sallarta ta buWe ?ofar, yadda ta gansa kaWai ya tabbatar mata ba lafiya, kafin ma ta tambaya taga yayi gaba da sauri, da sauri ta biyo bayansa dan sai lokacin ta lura da jinin da ya Sata masa kayan baccin jikinsa kaWan, jikinta har rawa yake take bin bayansa ganin kamar zai tashi sama, ya buWe ?ofar palourn ya fita da gudu ta bi bayansa dan yadda yake tafiya yafi ?arfin saurinta, motarsa ya nufa ganin back seat a buWe ta ?arasa wajen da sauri tana kallon faWila dake kwance tana mu?ur?usu tana kiran sunanta bata san sanda ta faWa motar ba ta rufe motar tana ri?o faWeelar jikinta da kiran sunanta, tuni Nasir ya tada motar mai gadi da tun fitowarsu na farko ya buWe gate yana tsaye yana kallonsu cike da tausayi ya Waga musu hannu yana faWin  Allah ya tsare  ganin yadda Nasir ya figi motar da banzan gudu ya fita a gidan.

Yadda faWeela ke kuka haka Na ima ke kuka tana jijjiga faWeela da jini ke bin ?afarta yana Sata kan kujera zuwa ?asan motar har suka isa babban asibitin da take ganin likita, tuni likitoci suka rufu a kanta son sanin miye matsalar, Na ima ta zauna a kan kujera tana kallon ?ofar Wakin da aka shiga da ita tana hawaye, Nasir dake tsaye jingine da bango ya harWe hannayensa ya dube ta ganin har lokacin kuka take ya sa ya ?araso ya zauna a kujera Wan nesa da ita  she ll be fyn stop crying ya faWa yana kallon ?asa dan shima da da hali hawayen zaiyi, ta gyaWa masa kai tana kallonsa  amma me ya same ta? ?ago kanshi yayi ya kalleta  ta farka zata je toilet, shine sai ta faWi then dis.. ya faWa yana juyar da kansa gefe dan ya riga da ya cire rai sunyi loosing Win baby Winsu shi yanzu damuwarsa they should save his wife.

Na ima ta share hawaye amma ta gagara magana, anan suka zauna a waiting room Win wanda sanyin ac Win ya fara saka ta jin kamar zatayi zazzaSi itama, ta haWe hannunta waje Waya tana jijjiga ?afarta da addu a a zuciyarta.
sai gabanin asuba likitoci suka fito, Nasir ya mi?e da Sauri likitan yace ya same sa a office Winsa, da sauri Nasir ya bi bayanshi, ita dai komawa tayi ta zauna tana binsu da kallo, after mintuna Nasir ya dawo yana kallonta ganin expression Win fuskarsa ya sa ta sau?e ajiyar zuciya tun kafin ma taji me zai ce  Alhamdulillah, both the baby and my wife are safe Na ima  Alhamdulillah itama ta faWa tana murmushi,  amma baza su discharging Winmu ba sai nan da 2 days, bari in yi sallah sai in kaiki gida ki huta, thank you Na ima ya faWa yana wuceta ya fita daga gurin ta bishi da kallo tana murmushi kamar ba shine ya daburce ba jiya, Alhamdulillah ta sake maimaitawa tana kallon ?ofar.

Wajen ?arfe 12 Na ima na zaune a kujera a gefen gadon faWila da bata jima da bacci ba, a hankali take Sare ayaban da ke hannunta tana kallon machines Win da ke aiki a Wakin kafin ta mayarda dubanta ga faWeela da ke bacci hannunta dafe da cikinta, stress Win last night har ya saka ta faWa lokaci guda Naima tayi murmushi kawai ta kai ayaban bakinta ta gutsura tana kallon wayarta da ta Wauko Wazu da Nasir ya maida ta gida jin yayi ?ara

 why wont u just talk to me? Ita fa zuwa yanzu abin sadiq ya fara bata tsoro, dan ko da ta dauko wayar ta tararda missed calls Winsa da messages Winsa sunfi a ?irga, is he even okay? Ta tambayi kanta tana ?ara kallon message Winsa da ya sake shigowa  Navy colour yana miki kyau sosai ta kalli navy colour abaya dake jikinta ta sake kallon wayar baki sake dai-dai nan aka buWe ?ofar Wakin da sallama ta Wago kanta tana amsawa, Nasir ne ya shigo first kafin shima ya shigo da sallama can ?asa ?asa, da mamaki take kallonsa har ya ?araso cikin Wakin same posture, same authority. Ta Wauke kanta a hankali ta mayar kan Nasir da ya zauna gefen bed Win faWila wacce ta buWe idanunta just now  how are u? Nasir ya faWa yana taSa forehead Winta, ta masa murmushi  naji sau?i but am weak ta faWa tana ?o?arin tashi zaune ya taimaka mata ya saka mata pilow ta zauna, sai lokacin ta lura da Ahmad dake tsaye a bayansa, cikin muryar marasa lafiya tace  ina wuni yaya Ahmad ajiye abin hannunsa yayi a bedside yana kallonta  u scared us ai faWeela ta Wanyi dariya kaWan,  ya su Madam?  Lafiya lau Wago kanta Na ima ta yi ta dube sa jin faWeela ta tambayeshi madam ashe ma yana da mata, Nasir ya dubi Na ima yana murmushi  Na ima ya jinya? murmushinta mai kyau tayi masa  Alhamdulillah ina wuni yaya Nasir sai kuma ta Wan dubi Ahmad  ina wuni Nasir ne kaWai ya amsa, ko kuma Ahmad Win ya amsa bata ji ba oho bata sani ba, Nasir na kallon faWeela yace  jiya fa kuka ta dinga yi, ?arshe ni na ha?ura da nawa tashin hankalin ina bata ha?uri FaWeela tayi dariya kaWan tana dafa cikinta  u alright? Ta gyaWa masa kai kawai.

Nasir ya dubi Ahmad da ya koma jikin window ya tsaya Wan nesa kaWan sai kuma ya kalli Na ima da ke danna wayarta, maida kallonsa yayi ga Ahmad yace

 dude, meet Na ima my wifes cousin sis

 Na ima, this is Ahmad

?ago kanta tayi suka haWa ido, a hankali ta Sake gaishe shi bayan ta ajiye wayarta duk da bata yi niyya ba dan sarai ?in amsa na farko da yayi ya mata zafi bata yi niyyar sake shiga harkarsa ba, amma rasa abin cewa bayan abinda Nasir yace ya sata gaishe shi  Lfy ya faWa a ta?aice yana maida dubansa ga FaWeela  Allah ya ?ara sau?i ya faWa yana ?arasawa ya ajiye mata bandir Win kuWi kusa da ledan da ya ajiye da farko faWeela na murmushi tace  thanks for coming a gaishe min da anty Amira pls  Zataji in sha Allah ya faWa yana nufar ?ofa, Na ima tabi bayansa da kallo har ya fita, ita sai taga ma kamar ko bai gane ta bane? Ko is he still holding grudges tun rannan ne? Amma ai ta bashi ha?uri ai koh? Sai yanzu ma ta ?ara gane fuskarsa ashe ba sau biyu ?adai suka haWu a jirgi ba ashe shine ta buge a kamun faWeela sannan ta sake haWuwa da shi wajen dinner before ta haWu da shi a airport, thats why his face looks familiar from day one.

Nasir yayi kissing hannun faWeela yana faWin  ill be right back baby ya shafa cikinta sannan kafin yabi bayan Ahmad da sauri.

Ruwan goran gefenta Na ima ta Wauka ta buWe tana ?o?arin kurSa wani message Win ya sake shigowa wayarta, sai kuma wani again wani ya biyo bayansa.

 Baza ki amsa ba?

 Tell me what i did wrong

 I thought u miss me kamar yadda nayi naki

 Talk to me pls

Kallon sa?wannin kawai take yadda suke shigowa Waya bayan Waya, mamaki ya?i barin fuskarta

 Answer ur damn phone

Why are u doing this, it hurts

 Ni eema

 Pls

Wai miye hakan ke nufi ne? When did friendship Winsu ya kai har haka? A iya saninta weeks ago sadiq was someone da zata iya kira her bestfriend, wanda zata iya faWa ma komai ba tare da War War ba, wanda babu wani abu mai kama da soyayya tsakaninsu sai ma zallar relating da each other, he relate da duk wani abu da take going through, yana sa taji damuwarta is his, yana sa ta manta damuwarta yayi boosting confidence Winta, amma ko kaWan abu mai kama da soyayya baya tsakaninta da shi, ita sai yanzu take sake tunanin meyasa ya?i bari ta sansa kamar yadda shi ya santa? Me yasa bata san komai game da shi ba even the smallest of things banda sunan siblings Winsa da adadinsu? ta ?urawa wayarta idanu kafin ta Wago idanunta ta kalli faWeela da ta koma ta kwanta ta lumshe idanunta, kamar amsar tambayarta wani sa?onne ya sake shigowa


 I Love you Ni eema, i always have, u owe me something, and i swear by my life ull be mine only mine Ni eema, babu mai sonki duk duniya bayan ni, ill protect you, i promise u, dont ignore me, i can do anything!


Afwan lovelies =?? kaina bisa wuya, ko wuya bisa ?afa ne? How una dey talk am sef=ؔ?=?? gabaWaya kun gigita ni =??


#Maimoon
09041426598
[8/14, 11:27 PM] Maimoo 3: https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q

RU?A??UN ZU?ATA(TANGLED HEARTS)

Yota/014
Wattpad: @Maimunah_Abdallah
ArewaBooks: @maimunahabdallah


Jumu at kareem my discussion board gang, sonku nake fisabilillahi, my day one s, u guys are always in my Du a, Allah ya muku albarka ya raya muku zuri a, yan matan cikinku Allah ya baku mazaje na garid'?


Chapter 19: Meant to heal

Washegari ?arfe bakwai na safe, Na ima na zaune gefen gadon faWila tana sanye da loose wando da shirt kanta da gyale amma bata yafashi da kyau ba loosely ta sake shi, ta naWe ?afarta a kujeran tana sipping black tea da aka kawo mata daga kitchen Win asibitin, kwata kwata bata wani samu bacci ba jiya, sosai al amarin sadiq ya tsaya mata a rai fiye da zatonta, a hankali take kurSan tea Win tana kallon yadda machines Win cikin Wakin ke beeping amma sam hankalinta ba a wajensu yake ba.

Ringing Win wayarta ya dawo da ita daga tunani tayi saurin kashe ?aran kar ya tashi faWila dake bacci kafin ta duba mai kiranta, ganin Mami ce ya sa ta mi?e a hankali ta fita a Wakin tana gyara yafin jersey veil dake kanta.

 Whats wrong baby? Are u okay? Jiya kwata kwata baki kirani ba Mami ta faWa bayan ta amsa gaisuwar da Na iman ke mata

 Lafiya lau Mami wallahi. Anty faWeela ce bata da lafiya tun shekaran jiya da daddare, yanzu haka ma muna asibiti

 Subhanallah, me ya same ta? Is she alright? Shine kuma baku faWa ba kwata kwata? Hows she? And the baby?

Ajiyar zuciya Na ima ta sau?e tana zama akan Waya daga cikin kujerun dake wajen,

 Taji sau?i fa sosai Mami kawai dai basu sallame mu bane, amma da sau?i jikinnata both she and the baby are perfectly fine

 To Allah ya raba lafiya

 Amin Mami ina su Aryan

 Gasu nan suna ?iriniya, yanzu kam ai sun ha?ura sun bar nemanki

 Allah sarki Wan shiru sukayi duka sai can kuma Mami ta fara magana

 Kamar yadda nake faWa miki kullum, Nasan FaWila na da ?o?ari, i trust her, but be careful Na ima pls, zaki haWu da mutane kala kala dan Allah ki dinga kiyaye wa kinji?

 In shaa Allah Mamina

 Allah ya miki albarka

A hankali ta amsa da  Am?n tana jin wani irin kewar Mami

Sun Wan jima suna magana kafin Suyi sallama ta koma Wakin, tararda faWila tayi tana waya da mummynta ta ajiye wayarta a kan kujera ta wuce toilet.

?arfe 12:30 na ranar aka sallami faWila daga asibiti ganin babu wata matsala, duk da haka sai da likitar ta jaddada musu duk wani slight abdominal pain kar suyi ignoring su taho asibiti, sannnan ta huta na weeks though baby Win is stable. FaWila gyaWa kai kawai tayi tayi Nasir kuma na saurare shima.

Likitar ta dubi Nasir  ill write prescriptions before discharge Win, Allah ya tsare gaba and pls be more careful, no lifting, no stress, no driving

Duk amsa mata sukayi tare da mata godiya, ko da aka sallamesu Na ima ce ta ri?e jakan faWila, Nasir kuma na ri?e da hannunta tana tafiya a hankali har mota, ya buWe ya taimaka ta shiga, itama Na ima ta zagaya ta shiga tana tunanin 2 days kenan bata je school ba, sai yanzu hankalinta ya karkarta can.

Ko da suka dawo gida sama Nasir ya haura da faWila bayan yace da Na ima ta huta itama cause kwana biyunnan shima ya san how stressed she was, hakan ya sa ta wuce Wakinta, sai da tayi wanka ta shirya kafin ta janyo takardunta ta shiga karatu cause gobe definitely zata shiga school.

Zuwa dare ta je ta duba faWila yafi a ?irga, wacce ta warware sosai sai abinda baza a rasa ba, bata jima sosai da kwanciya ba bayan ta kaima faWila mint tea da ta mata da kanta bacci ya Wauke ta kasancewar da wuri take son shiga makaranta washegari.

Washegari da wuri Yusuf ya sau?e ta a school, ta wuce lecture building Win tana rataye da designer tote bag Winta kamar kullum. Bayan angama lecture cafe Win makarantar taje ta nemi abinda zata ci kafin next lecture Winta.

Zuwa yamma sosai ta gaji, ko da yusuf ya zo Waukarta ma da ?yar ta amsa masa gaisuwar da yake mata ta shige motar tana sau?e ajiyar zuciya.

Tunda aka buWe musu gate yusuf ya shigo da motar Na ima ke bin Mercendes maybach Gls 600 da akayi parking wanda bata san da shi ba a gidan da kallo, da tunanin motar wayece cause bata taSa ganin motarba a gidan. ba tare da damuwa ba ta sau?o a motar, ta nufi cikin gida, a hankali take tafiya har ta ?arasa ?ofar palourn ta tura ?ofar ta shiga da sallama ?asa ?asa, takalmanta ta cire, tana gyara gyalen abayan jikinta ta nufi cikin palourn, tana jiyo muryar Nasir sama sama ta ?arasa bakin palorn, Wan dakatawa tayi daga bakin ?ofa na yan seconds tana kallon living room Win da mutanen cikinsa,

Ahmad na zaune a kan sofa ?afarsa Waya akan Waya ya jingina bayansa da kujera yana sauraren Nasir dake sake masa bayanin yadda abin ya faru wanda zuwa yanzu ya faWa masa yafi a ?irga, beside him wata mata ce wacce ita dai Na ima bata santa ba, kyakkyawa sosai black beauty, doguwa sosai saidai bata da wani aukin kirki, fuskarta ba kwalliya amma sosai fuskar ke glowing tana sanye da silk Win doguwar riga da ya mata kyau sosai da scarve Winsa, tana zaune very close to him tana danna wayarta kamar zancen da ake a Wakin bai dame ta ba sai ma chewing gum da take taunawa fuskarta a haWe.

FaWila dake zaune kusa da nasir ta naWe ?afarta a hankali tana saurarar hirar da Nasir ke ma Ahmad dan tun bayan gaisuwa da kawo musu kayan motsa baki babu abinda ya sake haWa ta da Madam Win ta dubi Na ima da ke tsaye bakin ?ofa  kin dawo? Hakan yasa duk suka Waga kai suka kalleta including Ahmad da Amira.

 Assalamu alaikum ta faWa daga bakin ?ofar tana ?arasowa ciki duk suka amsa mata ta ?araso ta zauna a kan kujera opposite Amira tana ajiye jakarta akan kujerar a hankali, gaishe su tayi a hankali tana kallon Saif dake Waya gefen na babansa, wanda Nasir da faWila ne kaWai suka amsa mata gaisuwar suna tambayarta school, Amira kam sake ma haWe rai tayi fiye da da ta mayar da kanta wayarta dan nan take kawai taji Na imar bata mata ba babu dalili babu mafari, zuba ma Saif idanunta Na ima tayi ganin yadda sosai yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login