Showing 78001 words to 81000 words out of 212729 words

Chapter 27 - TANGLED HEARTS BOOK COMPLETE by MAIMOON.doc

Maimoon   

09 Oct 2025

3816

unlike u, ko maganar da na maka dama har yanzu baka ji zaka bi bane?

?an shiru yayi kafin ya sau?e ajiiyar zuciya

 Hmmm

 Hmm miye? Ni bazan matsa maka ba akan abinda baka so amma at least u should try, baka ma gwada ganin yarinyar ba fa umm Ahmad

 Toh Ammi kawai ya faWa ba wai dan yana da niyyar zuwa ya ga wata Suhaila ba, shi bai ji ma yana son ganinta ba in the first place dama.

 Da yaushe zaka shigo?

 Da daddare in sha Allah

 Toh Allah ya kaimu

 Ina Saif? Ya tambaya dan kar ma ta sake waccar maganar

 Yana wajen Rahama a compound suna ball wai

 Da la asar Winnan? Ya tambaya yana mi?ewa ya zare rigarsa daga jikin kujera ya ri?e a hannu ya nufi ?ofa

 Nima yanzu na gama magana wallahi

 To su koma cikin gida wasan is okay haka ya faWa yana danna elavator ya buWe ya shiga, Ammi ta dubi Suhaila shigowarta palourn kenan tana ?o?arin kwanciya akan kujera tana danna wayarta tace

 Suhaila je ki ce ma Rahama yayanku yace su dawo cikin gida ya isa haka

?an jim tayi tafin ta juya ta nufi ?ofa ba tare da ta amsa ba Ammi ta bita da kallo, har ta nufi stairs ta Sau?a ?asa.

Kusan cin karo sukayi da Yasmeen da ke shirin haurowa, Yasmeen ta koma gefe ta bata hanya har ta sau?a ba tare da kowa yace ma kowa kanzil ba kafin ta wuce sama abinta.

#Maimoon
09041426598
[8/14, 11:30 PM] Maimoo 3: https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q

RU?A??UN ZU?ATA(TANGLED HEARTS)

Yota/014
Wattpad: @Maimunah_Abdallah
ArewaBooks: @maimunahabdallah

Chapter 33: Crossroads

Tana fitowa compound taga basa nan, ta Wan dakata kamar bazata je ba sai kuma ta nufi back garden dan kamar tanan take Wan jiyo hayaniyarsu, tun kafin ta ?arasa ta hangosu, rahama da oversize hijab Win jikinta da crocs a ?afarta, tana bin Saif dake ?yal?yala dariya dama shi akwai shi akwai son wasa, kallonshi Suhaila ta tsaya yi, Sosai yake kama da babansa though zata iya ?irga sau nawa ta gansa but hoton fuskarsa abu ne da ba zai taSa Sacewa a idanunta ba, features Winsu dayawa iri Waya ne, Ball ja dake hannunsa ta kalla kafin ta kalli yan ?ananun ?afafunsa da babu takalmi, tsayawa rahama tayi ta sunkuya tana haki kamar wacce take gudun arziki irin ta gaji Winnan,

 Saif am tired tsayawa yayi shima yana kallonta fuskarsa da dariya dan shi fa yafi so su cigaba, Suhaila ta Wan ja tsaki kaWan tana ?arasawa ciki da kyau,

 Rahama&  bata ?arasa ba taji sau?ar ball a fuskarta, ball Win ya daki kumatunta yabi shoulder Winta kan farar rigarta kafin ya sau?a dai dai feet Winta, dafe bakinta Rahama tayi, shima Saif tsayawa yayi yana kallonta dan Rahama yayi niyyar jefa ma ball Win ta shigo, rahama ta fashe da dariya duk da batayi niyyar yi ba ganin yadda Suhaila tayi da fuska kafin ta ?arasa gaban Saif ta ri?o shi tana cewa

 See what u did, nace maka na gaji now go and tell anty Suhaila Sorry ma?e kafaWa yayi ya?i zuwa dan yadda fuskar Suhaila har tayi ja na Sacin rai kaWai ya isa ya hanashi zuwa kwata kwata fuskar is not welcoming, abinka da farar baturiya, hancinta yayi ja da kumatunta tana kallonsa kamar zata halakasa da idanu. Ma?alewa yayi jikin Rahama da itama ta rage dariyar da take ta mi?e ta Waga shi tana kallon Suhaila tace

 Kiyi ha?uri bai sani bane wani kallo da Suhaila ta mata yasa itama ta Wan haWe rai ganin kamar Suhaila ta Wauki abin da zafi sosai,

Tsugunawa suhaila tayi ta Wauki ball Win tana kallon Saif dake jikin rahama ta zare masa idanu

 is this how to play? Rahama dai tayi shiru bata sake cewa komai ba, tuni har Saif ya fara ?o?arin kuka, suhaila tayi snapping hannunta tana kallonsa

 Haka aka ce maka ka dinga throwing ball a duk fuskar wanda ka gani wa ya koya maka wannan?

Rahama na kallonta tace  wa zai koya masa kuwa? Its a mistake Suhaila kema kinsan ba ke yayi niyyar jefawa ba

 Oh please ta faWa tana juyawa kan Rahama,  accident or not bashi da manners, no both of u ma, kuna abu kamar animals da basu da supervision

Sake baki Rahama tayi cause she didnt see that coming,

 What was that? Yayi abu mistakenly ance kiyi hakuri, why use those words on us

 What words? Suka ji muryar yasmeen a bakin garden Win tana shigowa fuskarta ba yabo ba fallasa, Rahama da har idanunta itama ya tara ruwa ta kalli Yasmeen kafin tace  babu komai daga haka ta wuce ta nufi hanyar fita a garden Win tana ri?e da Saif, Yasmeen ta bisu da kallo, dan ta san twin sister Winta kamar yunwan cikinta dama ta san this is how she ll bahave ita shugabar son zaman lafiya da rashin son fitina, itama juyawa tayi tabi bayansu dan ta tabbata akwai abinda Suhaila ta faWa ma Rahama da bai mata dadi ba, wanda kuma ba abin mamaki bane, Suhaila ta bi su da kallo kafin ta ja tsaki itama tabi bayansu, a palourn ?asa ta same su duka Yasmeen na ma Rahama magana, ta wuce sama fuuu ba tare da ta kulasu ba, Yasmeen ta bita da kallo kawai ta gyaWa kai,
tana haurawa sama ta samu Ammi still a palour ta ?arasa ta Zauna a kujera, Ammi ta kalleta tace

 Kin faWa musu?

 Eh, sun shigo ma

 Okay kawai Ammi ta faWa ta cigaba da danna wayarta, sai can kuma ta Wan kalli Suhaila sai kuma ta ajiye wayar

 Me aka miki naga kinyi ja? Kamar jiran tambayar take ta fashe da kuka

 Rahama ce ta saka Saif ya jefa min ball in the face , kuma dan nayi magana she started telling me trash

Ammi ta dinga kallonta  Rahama kuma?

 Eh kallon stairs Ammi tayi kafin ta sau?e ajiyar zuciya dan tayi mamaki dama yasmeen tace tasan zata aikata amma Rahama ta fi kowa sanyin hali a yaranta, kuma ko rigimar da Yasmeen keyi na rashin son Ahmad ya auri Suhaila Rahama bata saka baki ba bare ta nuna tana so ko bata so,

 Kiyi hakuri kiyi shiru zan mata magana Ammi ta faWa tana kallon Suhaila ganin sai sake ja take saboda kukan da take yi, Suhaila ta mi?e ta Wauki wayarta ta wuce Wakin da ta Sau?a tun jiya Ammi ta bita da kallo.


Bayan isha Ahmad ya shigo gidan, yayi parking motarsa cikin jerin motocin gidan ya fito ya nufi cikin gida, Yasmeen ce ta Sude masa ?ofar palour bayan ya danna bell, ya shigo ta rufe ?ofar ta bi bayansa,

 Welcome yaya

 Thank you ya faWa yana ?arasawa ya zauna akan kujera,

 Wheres everyone? Sama ta kalla ba tare da tayi magana ba, ya mike da niyyar haurawa saman,

 Yaya yasmeen ta faWa tana tsaye daga gefen kujera, kallonta yayi ya Wage mata gira Waya alamun what? Tunda ya shigo dama ya ga mood Winta is off amma baya so ya tambaya ta fara masa bayanin abinda bai shafesa ba shiyasa ya shareta dan ya san bazai wuce ita da Rahama bane,

 Abinda Ammi tayi dan Allah ya kamata? Dawowa yayi ya zauna yana kallonta, ganin tana tsaye har sannan ya nuna mata gefensa, ta ?araso ta zauna, bata jira ya sake tambaya ba ta fara faWa masa abinda ya faru Wazu, kuma Ammi ta kira rahama ta mata faWa a gaban Suhaila kuma ta saka Rahama ta bata ha?uri, ita kuma rahama bata gaya wa ammi abinda ita tace mata ba, kuma ita yasmeen da ta faWa ammi tace ta mata shiru.

Bowl Win chocolate dake kan center table ya janyo ya Wauki guda Waya ya buWe yana ci,

 Sai kuma me ya faru? Ya tambaya yana ciro wayarsa a aljihu, shiru Yasmeen tayi tana kallonshi kamar zata yi kuka,

 Inda ta san haka zata yi ai sai ta tsaya a gidansu, we didnt invite her bai sake ce mata komai ba ya mi?e ya nufi steps, sai kuma ya juyo ya kalleta

 Ina Saif?

 Ya gama kuka yayi bacci

Wacewa yayi ta bishi da kallo har ya haura kafin ta tura baki

to miye ma anfanin faWa masa da tayi.? Ta Wan harari stairs Win kafin ta kwanta a kan kujera.

Yasmeen na kwance a palourn ita kaWai tana chatting a wayarta after kamar 20minutes da haurawarsa sai ga Ammi ta sau?o, bata ko kula Yasmeen Winba, ta ?arasa ta zauna a kan three sitter, tana Waukar remote ta canza channel, Yasmeen ma shiru tayi bata ce mata komai ba, sai dai ta tashi ta zauna tana mamakin ganin Ammi ta sau?o ita kaWai kuma Ahmad Win na Sama, ganin Ammi bata bi ta kanta ba ta mi?e da nufin zuwa saman ta duba, Ammi ta kalleta tace

 Zo nan dawowa tayi, Ammi ta kalleta

 Miye zaki je ki min a saman?

 Babu zuwa zanyi na kwanta

 Na gulma koh? Rahama da ke son ta kwanta ai tana Sallahr isha ta kwanta tun Wazu, amma ke sai yanzu kika ji xaki je ki kwanta saboda gulma Sata rai Yasmeen tayi ta koma ta Zauna akan kujera tana sake bin stairs Win da kallo


Suhaila ta sake kallon inda yake zaune yana danna wayarsa kamar bai san tana wajen ba, gashi wani irin shakkarsa take ji ta rasa me zata ce masa, tunda Ammi tace taje suyi magana take zaune amma har yanzu ko kallonta baiyi ba bare ya mata magana, tunda ta gaishe shi ya amsa can ?asa kamar ta masa dole ta koma gefe ta kama kanta, ganin ta gaji da zama ta ciro wayarta itama ta shiga dannawa duk da ba wani abin kirki take yi a ciki ba, kusan 20 minutes after ya kalli agogon hannunsa, sai kuma ya mi?e ya nufi ?ofa, ta bishi da kallo, har ya sau?a ?asa kafin ta sau?e ajiyar zuciya, ta Wan ja tsaki kaWan tana mi?ewa ta wuce Waki dan kiran Mummynta ta faWa mata yadda akayi.

Yana sau?owa Ammi da Yasmeen suka bishi da kallo ganin fuskarsa babu yabo babu fallasa, Ammi na so ta tambayeshi amma kuma tayi shiru kawai tana kallonsa ganin kamar ma ransa a Sace yake, ya kalli yasmeen

 Je ki Wauko min Saif ke mi?ewa tayi kamar jira take ta nufi sama, ya ?araso cikin palourn ya zauna, Ammi tana kallonsa tace

 Ya akayi? ?aga kallonta yayi ya kalleta amma bai ce komai ba, itama sai kawai tayi shiru, than its obvious he didnt like what he saw

Yasmeen ta sau?o da Saif da ya kwanta ya lafe a jikinta, Ahmad ya mi?e ya karSe shi ganin idanunsa biyu yace

 Champ shiru Saif yayi bai amsa ba, Ammi tana kallonsu tace

 Wato shi ba a masa faWa sai ya hau ?urnanci haka kuka koya masa kenan Wan murmushi kaWan Ahmad yayi bai amsa ba, yana rungume da Saif Win yace ma Ammi

 Sai da safe

 Allah ya bamu alkhairi, tunda dan an masa faWa yayi ba dai dai ba shine zaka Wauke sa ka tafi da shi

Yasmeen tayi saurin caSewa

 ba dan haka bane Ammi dama yace ai saturday zai zo ya Wauke sa gobe polo day Winsu ne kin manta

Ammi ta harareta tana maida idanunta kan tv, mi?ewa Yasmeen tayi tabi bayansa da Sauri, har suka isa motarsa, ta buWe masa gaban motar ya ajiye Saif ya saka masa seat belt, kafin ta rufe ?ofar ya zagaya dan shiga motar ta zagayo itama ta Wan tsaya tana kallonsa,

 Kar dai Ammi saka ka tayi kayi magana da Suhailar can rufe ?ofar motar yayi, yana zuge glass a hankali

 Mind ur business daga haka ya Wage glass Win duka ta sake baki tana kallon motar ganin yayi reverse ya nufi gate, wato she should mind her business, ba shi da bakinsa ya ce ta tayasa convincing ammi akan Suhailar ba, ta Wan cijw bakinta kafin a fili tace

 Maganinki kema yasmeen maganinki daga haka ta juya ta nufi cikin gida.

Tana shiga Ammi dake waya da Salma tace  shikenan dai idan kinzo goben sai muyi maganar da kyau dan ni duk jikina yayi Sanyi

Yasmeen ta kalleta kawai bata ce komai ba ta wuce sama.

Yana hawa kan titi sosai ya kalli Saif da har lokacin yake nan moody ya kwantar da kansa da kujera kamar mara lafiya

 Hey ya faWa yana taSa kumatunsa, Saif ya kalleshi amma ya?i magana, Wan murmushi yayi ya shafa kansa,

 U dont want to talk to papa? ?auke kansa yayi bai ce komai ba ya mayar ya kwantar, Ahmad yayi murmushi,

 In kai ka wajen Anty Na ima? Kallonsa Saif yayi sai kuma ya gyaWa masa kai,

 Okay smile for me Wan murmushi yayi wanda ya kusa bawa Ahmad Win dariya, dan kana gani kasan yayi ne kawai, ya shafa gashin kan yaron mai taushi sosai,

 Okay. Ya faWa yana Waukar wayarsa da ke ajiye a gefe, yana driving da hannu Waya,


Fitowarta daga wanka kenan bayan ta idar da Sallar isha i ta zauna a gaban madubi tana gyara Waurin towel Win jikinta, taji wayarta tayi ?ara alamar shigowar sa?o wayarta, kallon wayar tayi har zata share sai kuma ta mi?e ta ?arasa ta Wauko wayar daga kan gadonta,

 Hey kawai yace ta tsaya tana kallon message Win nashi, buWewa tayi tana kallo kafin ta masa reply da

 Ina wuni ba tare da ya amsa gaisuwar ba ya mata reply da

 Send me ur address ta tsaya jim tana kallon message Win

 My address? Ta tura masa

 No mine ya bata amsa almost immediately, Wan murmushi tayi kafin ta fara typing address Win gidan tana tunanin ko miye zai yi da shi.

Tana tura masa taga ya buWe amma bai sake ce mata komai ta ajiye wayar ta fara shiryawa, har ta kusa gamawa kawai kuma sai ta Wauki wayar ganin har sannan bai ce komai ba ta sake masa magana

 How s Saif? Kusan seconds goma ta ga ya buWe

 Kina son ganinsa ne? Ta Wanyi murmushi

 Yes, Sosai

 Okay, come and see him then dariya tayi, tana mi?ewa ta nufi wadrobe dan Wauko kayanta ad the same time tana masa reply

 Where?

 Were outside ciro kayan baccinta tayi ta ?arasa ta ajiye a kan gado, kafin ta masa reply

 Outside where? Ganin bai amsa ba ta fara saka kayanta, har ta gama saka kayan kafin ta ?arasa ta fehe jikinta da turarenta. Tana Dawowa ta Wauki wayar taga ya tura mata hoto, buWe hoton tayi ta zaro ido tana kallon street Win ya nuna har ?ofar gate Win gidannasu, buWe baki tayi ta gagara rufewa tama gagara masa reply da sauri ta nufi hijab Winta da ta naWe bayan ta idar da sallah ta Wauka ta zura ta nufi ?ofa da wayarta a hannunta.

#Maimoon
09041426598
[8/14, 11:30 PM] Maimoo 3: https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q

RU?A??UN ZU?ATA (TANGLED HEARTS)

Yota/014
Wattpad: @Maimunah_Abdallah
ArewaBooks: @maimunahabdallah


Chapter 34: The game of glances

Har ta fito compound Win gidan bata gama yarda da gaske yake ba, iskan daren na kaWa hijab Winta hannunta ri?e da wayarta ta nufi gate, bata kula masu gadi biyu dake bakin gate Winba ta buWe ?aramar ?ofar ta Wan le?o waje, ganin bata ga kowa ba ya sa ta fito gabaki Waya tana bin layin da kallo.

Tun daga kanta yake ?are mata kallo har slippers Win ?afafunta yana zaune daga cikin motar ganin shes still standing yasa ya flashing mata headlight, sai da ta Wan tsaya kaWan tana kallon sleek black motar dake parke gaba kaWan kafin ta nufi motar har yanzu tana mamakin wai da gaske zuwa yayi, ta ?arasa jikin motar dake nan tinted, ganin bata ganinsa kuma babu alamar zai fito ta zagaya kafin tayi knocking glass Win aka buWe motar Sangaren mai zaman banza

 Anty Na imaa Muryar Saif ya dake ta, kafin ma ta amsa ya rungumeta ya Waura kansa a cikinta, ri?e wayarta tayi da kyau da hannu Waya, Wayan hannun kuma ta ri?oshi tana murmushi,

 Wayyo Champ zan faWi ta faWa tana Wagosa daga jikinta tana kallonsa ganin kamar he s not his happy self kamar kullum, tana kallonsa tace

 What happened ta faWa tana Wan du?owa dai dai tsawonsa ita tana daga waje shi yana tsugune kan kujerar motar. KwaSe fuska yayi kamar zaiyi kuka ta janyo sa jikinta

 Oh my baby, am sorry okay dont cry tell me me ya faru? ta faWa tana shafa gashinsa cike da lallashi duk da bata san me aka masa ba, Ahmad dake kallonsu tuntuni ya Wanyi smirking, wai a baby ne ke cema wani baby, Wago kanshi saif yayi a jikinta yana kallonta

 Anty Na ima wai i dont have manners? Ya faWa yana kallonta kamar dai ita kaWai ce zata faWa masa gaskiya, sai da ta Wan kalli Ahmad ganin har yanzu kallonsu yake yi tace

 Says who? U know what u are? Ya girgiza mata kai

 Ure passionate and ure a good boy a very good boy

Ahmad dake kallonta yace  if u two are

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login