Showing 171001 words to 174000 words out of 212729 words

Chapter 58 - TANGLED HEARTS BOOK COMPLETE by MAIMOON.doc

Maimoon   

09 Oct 2025

3818

?amshin vanilla da butter ne kawai ke tashi.

Na ima ta saka spatula na hannunta tayi flipping Winshi, bayan kuwa ya gasu yayi golden brown abin gwanin sha awa.

Yana gama gasuwa ta cire shi a wuta ta sake saka wani, haka ta dinga yi a tsanake har ta gama tass.

Ta kalli Rahama tace  ur turn ke kiyi scrambled egg sai inyi hot chocolate shikenan mun gama

Rahama tayi dariya tace  easy work tare da buWe drawer ta Wauko wani bowl Win ta zo ta fasa ?wai a ciki da pinch na gishiri sai pepper ta kaWa su kafin ta juye a frying pan dake kan wuta ta saka wooden spoon tana jujjuya shi tana kallon Na ima da ta Wauko pack na sassauge, ta Wauko wani Wan ?aramin frying pan ta ajiye shi tana buWe pack Win ta ciro sassauges Win tana jerawa akan pan Win har ta gama kafin ta kunna different stove ta Waura shi akan wutan.

Ta barsu suna grilling har sai da suka yi brown ?amshinsu na tashi da Wan haya?i kaWan daga pan Win. daidai lokaicin yasmeen ya shigo kitchen Win da doguwar rigar bacci a jikinta ta tsaya daga bakin ?ofa tana kallonsu kafin ta ?araso tace

 Ina kwana anty Na ima Na ima na jujjuya sussages Win tace

 ba mun gaisa da asuba ba

 Haka! Ta faWa tana ?arasawa ta le?a abinda rahama ke juyawa a wuta kafin tace

 Oshey! ashe gwara da na tashi yanzu rahama ta harareta tace  ai wallahi ban so kika tashi ba sai mun cinye yasmeen ta ?yal?yale da dariya

 Sannu muguwa, to tun Wazu ido na biyu ta faWa tana jan kujera ta zauna tana kallon Na ima itama cike da burgewa.

Ita dai murmushi kawai takeyi tana kallonsu dan gasu dai yan biyu amma theyre pole apart kowa da halinsa a cikinsu kamar yadda kamanninsu ma ba Waya ba kowa da kamrta.


Sai da Rahama ta sau?e ?wan, itama ta sau?e saussages Win kafin Na ima ta Waura milk akan stove Win ta dinga zuba cocoa powder da sugar tana stiring har sai da ya narke ya haWe into a smooth and rich hot chocolate. ?amshi ne kawai ke tashi a kitchen Win. Ta kalli Yasmeen tace  ur turn, ke sai ki tayamu jerawa a dining tunda mun gama dafawa Rahama tace  aikuwa kin iya raba aiki Yasmeen ta mi?e tana gyara hularta ta harari Rahama tace

 and so? Ai wannan dai ba komai bane Duk sukayi dariya, Na ima ta ?arasa tana wanke hannunta a sink, sai da yasmeen ta fara kai golden pancakes Win da Na ima tayi drizzling Winsa da honey ta jerasu gwanin sha awa kafin ta dawo ta kai scambled egg Win da ke ta tiriri shima, saussages Win da jug na hot chocolate shine ?arshe tana ajiye shi ta wuce sama, a stairs suka kusa cin karo da Ammi, Ammi na kallonta tace

 gulma ne yau ya tashe ki da sassafe kenan

 Ina kwana Ammi!

 Lafiya lau Ammi ta faWa tana sau?a ?asa, Yasmeen ta biyota a baya ?asa ?asa tace

 Surukarki ta miki breakfast

 Ah ah surukarki dai Yasmeen Ammi ta faWa murmushi ta escaping lips Winta

 Dama fa zuwa zanyi sama wajenki sai ga ki kin sau?o

 To yayi kyau! Ammi ta faWa tana kallon Rahama da Na ima da ke tsaye kusa da dining, Na ima ta ajiye jar Win honey akan dining Win ko da wani zai so ya ?ara ta ?araso palourn ta Wan tsaya bayan kujera tace

 Good morning Ammi Ammi tayi murmushi tace

 Morning Na ima kin tashi lafiya?

 Lafiya Alhamdulillah Rahama ta ?araso itama tace

 Ina kwana Ammi

 Lfy lau rahama, ki ce har kun gama breakfast Win

 Anty Na ima ce tayi ta faWa tana kallon Na ima da kunya duk ya isheta, Yasmeen tace

 Mu mukayi dukanmu Rahama tace

 To wallahi Ammi yanzu sakkowarta ta samu mun gama

 Okay! Wa ya jera a dining? No tell me wa ya jera ke kika jera Rahama? Ko kulata Rahama bata yi ba ta kama hannun Ammi tace

 muje kici Ammi har dining ta kaita ta ja mata kujera ta zauna, kafin Rahama ta ja wani kujera tana kallon Na ima tace  anty Na ima.. ?arasowa tayi itama ta zauna, yasmeen kam dama ta rigata ma zama kafin Rahama ta zauna bayan tayi serving Ammi, suka soma cin abincin a nutse, Ammi ta Wan kalli Na ima dake Wiban egg a plate, tun randa ta fara ganinta ta burgeta but today Sosai taji ta sake shiga ranta, more especially da bata da duhun kai ko ?umbiya ?umbiya irin na surukai, yadda su rahama suke abinsu haka take yi, kamar dai a gidansu take abinta. Kuma bata taSa tunanin zata iya girki ba ma but ji yadda ta iya abinci mai daWi sosai. Sunyi nisa a cin abincin Ammi na ta commenting on how delicious abincin is

aka danna bell, mai aiki dake goge goge a palour ta ?arasa ta buWe ?ofar, Ahmad ne ya shigo palourn sanye da ?ananun kaya da suka amshe shi ba kaWan ba da alama bazashi office ba yau ma, kanshi sanye da face cap ba?a, tuni Na ima tayi stiff da cokalin hannunta da take ?o?arin kaiwa bakinta kamar mai jiran ta gama tabbatar da shi Winne ya shigo dan ta bashi baya ne amma ?amshin turarensa tuni ya tabbatar mata shi ne, tana ri?e da spoon Win ta juya ta kalli hanyar ?ofa, suna haWa idanu ta sake spoon Win da sauri tare da mi?ewa tsaye tana kallonsa, shima dakatawa yayi ba tare da ya ?araso sashen dining Win ba yana kallonta, Ammi tace  Naima? Ai ko rufe baki Ammi bata yi ba ganin Ahmad na ?o?arin ?arasowa wajen in a blink of an eye tayi sama da gudu, mayafinta har yana sulewa ya dawo kafaWarta, duk suka bita da kallo shocked, kamar ya san dama abinda zatayi kenan, saurin bin bayanta yayi ya so ya rigata isa bakin stairs ya tare amma sai ta rigashi, da gudu ta shiga haura stairs Win shi kuwa yabi bayanta, Ammi da Rahama da yasmeen duk suka bisu da kallo dan duk sun mi?e ne sun tsaya suna kallon ikon Allah, Yasmeen ta zazzaro idanu amma ta gagara cewa komai.

Wani tsinannen bugawa xuciyarta keyi jin ya biyo ta burinta kawai ta shige Wakinta ta kulle da makulli amma kash tana Waura hannu a handle Win da niyyar buWewa ya iskota tare da ri?ota jikinsa ?am?am yana faWin

 Na ima!

 Leave me!, leave me alone! Ta fashe da kuka tana zizzilewa tare da ?o?arin SanSare hannunsa daga jikinta,  pls ta faWa tana fasa kuka da ?arfi, muryarsa har rawa take yace

 Why are u doing this? Me na miki baby? Wallahi bansan me na miki ba, u love me remember?i know u do, why are u pushing me away?

Girgiza masa kai ta shiga yi tana kuka ta shiga dukan ?irjinsa da hannu bibbiyu dan ra rabu da ita burinta kawai ta bar ganinsa ta shiga ko ina ne ma in dai bazata ke ganinsa ba

 Bana sonka! Ni ka ?yaleni leave me ta faWa da ?arfi tana ?o?arin dambe da shi. Dai dai lokacin Ammi ta hauro saman Yasmeen da rahama na biye da ita dan duk efe efen da takeyi suna jiyota, jin kukan na ?ara ?arfi ya sa Ammi haurowa ba shiri, ?in sake ta yayi yana kallon yadda take struggling na ?wace kanta a jikinsa idanunsa suka kaWa suka yi ja, tuni kansa ya shiga wani irin sara masa, rahama tana kallonsu har idanunta ya ciko da hawaye tace

 Yaya dan Allah ka ?yaleta please but Ahmad couldnt let go, ya sa hannunsa a shoulder Winta hannunsa har trembling yake  come back to ur senses pls Na ima dakatawa tayi da dambe da take yi da shi ta tsaya tana kallon cikin idanunsa da suka kaWa har kamr suna yal?i, kamar wacce ke shirin dawowa hayyacinnata kamar yadda yace sai kuma ta fasa wani gigitaccen ihu wanda yayi daidai da haurowar Salma saman dan tun Wazu take danna bell amma ba a buWe mata ba sai yanzu faty ta buWe mata tana shigowa ta jiyo ihun hakan ya sa ta nufi saman da sauri itama da kumburarrun idanunta dan ko baccin kirki bata yi ba ganin bata da mafita ya sa ta taho wajen Ammi dan bazama ta fara faWawa Daddy ba tunda ta faWa masa Suhaila na gidan friend Winta da aka sallama daga asibiti.

da Sauri Ammi tace  Sake ta Ahmad ta faWa tana ?arasowa ta saka hannu da ?o?arin cire hannunsa a jikin Na ima, Tuni Na ima ta ?an?ame Ammi ta fashe da sabon kuka, Ahmad ya Wan ja da baya yana jin kamar jiri ke neman Wibarsa, Ammi ta rungume ta back tana shafa kanta tace

 Its okay! Kallonsu kawai Salma take confused, Me Na ima ke yi a gidan? Like whats happenening babu ma wanda ya kula da tsayuwarta a wajen.

?agowa Na ima tayi daga jikin Ammi muryarta har bata fita sosai tace  dan Allah ki ce masa ya tafi pls i dont want to see him pls&  sai kuma tayi baya luuu Ahmad yayi saurin matsowa amma kafin ya ri?ota ammi ta rigasa, ta sume a jikin Ammi bata numfashi, sosai Ammi ta ri?ota jikinta tana nanata

 innalilahi wa inna ilaihi raji un

Yasmeen da rahama kam kuka suka kama yi, Ammi ta kalli Ahmad tace

 kwantar da ita kan gadonta bari in kira Malam idris ya zo yanzu kawai yanzu subhanallahi tana faWa ta nufi hanyar bedroom Winta gabaWaya hankalinta a tashe yake, Salma ta bi bayanta da Sauri jin ba asin abinda ke faruwa.

Wagata caWak yayi bayan ya karSeta a hannun Ammi nufi cikin Wakin bayan yasmeen da ta tsuguna ta Wauki mayafin Na ima ta ri?e a hannunta ta buWe masa ?ofa, ya kwantar da ita akan gado ya zauna a gefen bed Win bayan ya ajiye wayarta da ya kawo mata a gefen bed Win saboda yadda Mami da fadila har da big daddy suka kikkkirata shi kuma ya gagara picking calls Win, ri?e hannunta yayi ya kai hannun fuskarsa kawai ya lumshe idanunsa yayi shiru, only he knows what zuciyarsa is going through!, the pain! he cant explain it.

Su yasmeen duk suka tsaya cirko cirko a Wakin suna kallon yayannasu. Ammi bata jima sosai ba ta dawo Wakin Salma na biye da ita a baya, Ammi ta Wan kalli Ahmad tace

 Malam na hanya yanzu! GyaWa mata kai kawai yayi amma ya gagara tashi a wajen, itama Ammi matsowa tayi ta zauna a gefen bed Win, salma ta Wan taSe baki dan Ammi tace mata suma basu san me yake damun Na imar ba haka kawai take misbehaving idan taga Ahmad a zuciyarta tace kaWan ma suka gani.




Rosewood Psychiatric & Wellness Centre, Abuja.


?akin shiru, like too Quiet, Sadiq na zaune akan gadonsa ya jingina bayansa da jikin cream wall dake cikin Wakin, ya ?urawa window dake Wan moving a hankali, Wakin sanyi ?alau saboda Air condition dake kunne, hasken rana da ke Wan shigowa kaWan kaWan daga jikin window Win yana haske ?asan Wakin da yake nan ?al ?al, kwata kwata wajen baiyi kama da asylum ba rather a hotel. Saboda private suit ne dake Wauke da banWakinsa a ciki harda bookshelf half filled da littatafai harda tv a Wakin. Amma to sadiq Non of it really mattered, tunda yake Wakin ko sau Waya bai taSa kunna tv ba, ko kusa da book shelf Win bai taSa zuwa ba, dan dole sometimes yake taSa abincin da suke kawo masa ko herbal teas da suke kawo masa kullum kullum. Haryanzu akwai scar kaWan na dukan da ahmad ya a goshinsa amma bayannan ya wawwarke sai abinda baza a rasa ba.

Nurses Win lallaSasa suke kamar yaro ?arami wanda hakan ke sake soya masa ransa, kullum suka tsaya kansa da wannan hopeful smile Win nasu saying  good day Sadiq ji yake kamar ya tashe ya kashe dukansu, haka zasu ajiye medications Winsa a bedside su Salla su basa, ko gardama baya yi da su yake karSa ya saka a baki amma maimakon ya sha sai ya danne a ?ar?ashin harshensa ya sha ruwa, suna fita yake tofarwa a tissue ya yar a tsakar Wakin.

Doctors da suke zuwa wajensa kullum tambayarsu baya wuce

 Whats ur name?
How re u feeling today?
Would u like to talk?

Bai taSa amsawa ko Waya a cikinsu ba,ko kallonsu ma baya yi, zuwa yanzu sun fara zama frustrated yau ma suna fita daga Wakin Wayan doctor Win ya kalli Wayan yace

 Bana tunanin we can break through cause he doesnt wanna come back shiru Wayan yayi cause gaskiyar maganar kenan! Baya son dawowa dai dai, baya son treatment Win shiyasa baya basu haWin kai tunda aka kawo shi bai taSa cewa kowa ci kanka ba kwana 5 kenan he s not violent kamar sauran mahaukata amma kuma he s not responsive.

Nurse Win da ta kai masa Abinci ce ta haWu da doctor musa a hallway da fari tass Win coat Winsa yana ri?e da shi a hannunsa Wayan hannun da file, yana ganinta yace

 Fatima how was he today?

Ta sau?e ajiyar zuciya tace

 same, yanzu kam ma ya bar ko kallona file Win sadiq ne dama a hannunsa ya Wanyi shiru yana kallonta kafin ya buWe file Win yana flipping da duba growing report na Sadiq, ko wani page iri Waya ne da na baya wato he s non verbal, refusing therapy, eating little, babu aggression kuma babu progress. meaning babu improvement at all ya girgiza kanshi a hankali ya dube ta yace

 we re wasting time gaskiya idan muka cigaba da d same method babu abinda zamu samu

Matron dake bayan desk ta Wago ta kalli Dr musa tace

 to ya zamuyi da shi kenan?

Rufe file Win Dr musa yayi yace

 mu jira Dr Zarah ibrahim, ita kaWai ce inaga zata iya handling case Winsa gaskiya

Nurse Fatima tana kallonsa tace  the trauma specialist? Wanda bata jima da dawowa daga abroad ba?

Firmly Dr musa yace  eh ita! Next week zata dawo until then a rabu dashi, no more forcing sessions, kawai a dinga monitoring Winsa a tabbatar he s stable, He s hers to handle

Matron Win ta gyaWa kai tace  okay Sir


#Maimoon
09041426598



https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q


RU?A??UN ZU?ATA ( TANGLED HEARTS)

Wattpad: @Maimunah_Abdallah
ArewaBooks: @maimunahabdallah


Chapter 60: Healing beyond Pain

Ammi na zaune a gefen bed Winta tana ta kallon Salma dake zaune kan kujera tana share idanunta, ita kanta she s shocked with abinda Salma ta gama faWa mata game da Suhaila, tun bayan tafiyar Malam idris Hankalinta ke matu?ar tashe dan ya tabbatar da sihr ne a jikin yarinyar ba aljanu ba, amma sosai ya kwantar mata da hankali kafin tafiyarsa ya kuma tabbatar mata komai ya zo ?arshe, kuma kamar yadda ya faWa Allah subhanahu wa ta ala ya faWa cikin al?ur ani mai girma

 Wa nuzzilu minal Qur ani ma huwa shifa un wa rahmatun lil mu mineen& 

 Kuma Mun saukar daga cikin Al?ur ani abin da yake magani da rahama ga muminai& . Tabbass al?ur ani waraka ce, kuma babu wata matsala da ba a bamu solution Winta a cikinta ba, saboda haka ya sa aka kawo masa bowl da ruwa yayi reciting suratul fatiha, ayatul ?ursiyyu da falaq da Nass, ?arshen suratul ba?ara wato amanarrasul da sauran ayatusshifa a kamar suratul taubah aya ta 14, suratul yunus aya ta 57, suratul Nahl aya ta 69, suratul isra i aya ta 82, suratul shu ara aya ta 80, da kuma suratul fussilat aya ta 44 da sauran addu o i kamar  Allahumma rabbannas, adhhibil ba asa, ishfi anta ash shafi, la shifa a illa shifa uka, shifa an la yughadiru saqaman Da dai sauran Addu o i ya bata ta sha aka kuma shafa mata, sannan yace a dinga mata haka ana bata tana sha tana kuma shafawa,kuma a nemi ganyen magarya da na kuka ko Saure ko Neem a tafasa su a haWa da karanta ruqya a ciki, ta dinga wanka da shi da shan kaWan kullum in sha Allah it will all come to pass, sannan ya sake jaddada musu su dinga karanta suratul baqara a gidan idan ma bazasu iya karantawa da baki ba su kunna shi, hadisi ne ingantacce wanda manzan Allah ke cewa

 Laa taj aluu buyootakum maqabir, inna ash shaytaana yanfiru minaal bayti allathee tuqra u feehi Sooratul Baqarah ma ana

 Kada ku mai da gidajenku kamar ?aburbura. Lallai shaiWan yana guduwa daga gidan da ake karanta Suratul-Baqarah a cikinsa. Sosai hankalin Ammi ya Wan kwanta duk da yace ba lallai ta warke farar Waya ba a cigaba da mata zai iya Waukarta 3 to 7 days ko fiye ma da haka depends on yanayin sihr Win Allahu a alam, waraka a hannun Allah yake in sha Allah komai zai wuce, kuma idan Ahmad Win zai iya ya bata space har ta gama maganin in sha Allah da zarar ta gama shikenan kuma.

Hakan ne ma yasa bayan tafiyarsa har Ammi ta samu daman sauraren Salma only for her to tell her another tashin hankali. Ammi ta sau?e ajiyar zuciya tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login