Showing 174001 words to 177000 words out of 212729 words

Chapter 59 - TANGLED HEARTS BOOK COMPLETE by MAIMOON.doc

Maimoon   

09 Oct 2025

3671

kallon Salma tace

 Innalillahi wa inna ilaihi raji un, kin gani ko Salma? Duk abinda nake faWa miki bakya ji, kwanannan har gaba kika yi da ni kika bar Waga kirata kika bar zuwa gidannan duk akan suhaila, ko da yake ba yau kika fara wannan ba akan mahaifinta ma kinyi haka, gaba da ni ba sabon abu bane a wajenki tunda kinyi har da mijina wanda yake kamar matsayin uba a wajenki Salma shiyasa bai dame ni ba sam, akan Auren Ahmad da Na ima babu irin Satancin da baki faWamin akan yarinyarnan ba now u see ga yarki ta kiraki tayi akan kunnenki, ni na ma rasa me zance, kince baki san ?asar da take ba ta ina zamu fara nemanta?

Salma ta sau?e ajiyar zuciya tace  Ni dan Allah anty Mami idan muna maganar da ta shafe mu ki bar sako Na ima a ciki, na zo na same ki ne saboda bani da wanda zan faWama, bazan fara faWawa Daddynsu ba tunda tun farko na masa ?aryar ga inda take

 To miye anfanin ?aryar da kika masa? Kenan ma da Waurin gindinki take kwana duk inda ta ga dama, sai dan ta bar ?asar kuma sai ya miki zafi Salma? ke fa kika bata license Win yin duk abinda take yi, nan gidan da ta zo ta zauna da ta tashi tafiya ko sanin tafiyarta banyi ba saboda na hanata rawar gaban hantsi tana ganin kamar an saka mata idanu Shiru Salma tayi tana kallon Ammi, ba?in ciki kamar zai kashe ta dan maganar Sata mata rai kawai yake.

Ammi ta sau?e ajiyar zuciya tana mi?ewa tsaye tace

 zan yi ma Ahmad magana in ga ko akwai abinda zai iya yi a kai in sha Allah, Allah dai ya kyauta daga haka ta fita a Wakin ta bar Salma zaune tana binta da wani irin kallo har Ammi ta fita kafin ta Wanyi ?wafa ta mi?e ta nufi ?ofa itama.



Shiru Fadila tayi tana sauraron Nasir da ke faWa mata halinda ake ciki, hankalinta yayi masifar tashi, dan duk kiran da suke ma Na ima har yanzu ba na wanda ta Waga at first fadila da ta kira Ahmad yace mata ai Na ima na bacci so sai ta Wauka tsabar soyayya ce yasa bata da time Win picking calls Winsu, but Now Nasir is telling her something else, cike da damuwa tace

 Babe ban gane ba

 Miyene baki gane ba a ciki? Ahmad told me imam Win yace sihr aka mata, wlh he s very disturbed ni kaina hankali na ya tashi wa zai mata sihiri just 10 days da aure? Yanzu haka tana gidan Ammi ita Na imar, she s not fyn gaskiya

 Innalillahi wa inna ilaihi raji un na shiga uku ni fadila ta faWa tana jijjiga inaaya da ke kafaWarta, katse ta yayi dan yasan halinta da yadda take saka ma kanta damuwa too much yace

 Look baki shiga ukun komai ba, na riga na duba available flights for tomorrow morning kawai ku dawo gobe ba sai next week Win ba dama nayi kewarku da yawa ya faWa trying to make her calm down dan yasan yanzu haka in hankalinta yayi dubu to ya tashi duka

 Toh& Allah ya kaimu zanje in sanar ma Mami in sha Allah, duk kuma wanda yayi ma dis innocent girl wannan abin Allah ya isa wallahi on her behalf ta faWa tana kashe wayarta dan babu wanda zuciyarta ke raya mata face Amira.

Washegari Nasir da kansa yaje Waukosu daga Airport, bayan ya saka luggages Winsu a mota ya bata side hug ya karSi inaaya daga hannunta ya Waurata a kafaWarsa tare da ri?e hannun fadila da hannu Waya suka nufi mota, gabaWaya ta ?osa ta ganta a gidan Ammi ta ga yanayin jikin Na imar, shi dai Nasir tu?i kawai yake yana satan kallonta ganin yadda duk damuwa ya nuna a fuskarta dama yasan za a rina.

?an ri?o hannunta yayi yace  ko muje gida ki huta ta wani kalleshi hakan yasa yayi dariya da bai shirya ba

 Calm down mana, ke she s fyn fa its not like she s sick or something, ita abinta da mijinta ne kaWai

Fadila tace  to ai ba lafiyan kenan, ba gwara to tayi da kowa ba akan mijinta kuma

 Hakane ya faWa a hankali yana matsa hannunta dake cikin nasa bai sake cewa komai ba, ya maida hankalinsa akan tu?i har suka iso gidan Ammi, Tana sau?owa a motar da inaya a kafaWarta ta nufi cikin gidan tana Wan ri?e jikin tsadaddiyar abayar jikinta, ta ?arasa bakin ?ofar ta danna bell ta tsaya tana jira a buWe mata.

Na ima da rahama na zaune kan carpet, Na ima na taya ta cike wani form karatun al?ur ani na tashi a hankali a speakers Win palourn, yasmeen kuma tana sama wajen Ammi, aka danna bell Win duk suka kalli ?ofa, Na ima zata mi?e rahama ta rigata

 Bari na buWe gyaWa mata kai Na ima tayi ta cigaba da cike mata kafin ta dawo, kamar ance ta Waga kanta da biro a hannunta kawai ta kalli Fadila da ta tsaya daga bakin palourn tana kallonta, wani kalan zaro ido tayi ta cillar da biron tare da mi?ewa da gudu ta nufo fadila, fadila ta rungume ta back dan tun a bakin ?ofa Rahama ta karSi inaaya, ma?al?aleta tayi tana murnar ganinta, fadila ma tana dariya tace

 Kai nayi kewarki da yawa Na eematu ta faWa tana Wagota daga jikinta tana kallonta ganin idanunta har ya ciko da hawaye, ta dinga kallonta, tana sanye da abaya black ta Waura scarve a kanta looking fresh kamar ko yaushe ita bata ga alamun rashin lafiyar komai a tattare da ita ba ko da yake she look a little pale amma its not much she still looks calm and very beautiful kamar kullum.

Rahama dai na tsaye gefe da inaaya tana dariya tana kallonsu, Na ima tace

 Anty fadila shine baki kirani ba kince zaki zo wait yaushe ma kika dawo lagos? Fadila ta harareta

 A ta wani waya zan kiranki? Wayar da baki Wagawa? Duk kin Wagawa mutane hankali  Rahama ta karSe da faWin

 La ba laifinta bane fa anty fadila tunda yaya Ahmad ya kawo wayar Saif ya saka a ruwa mistakenly ita dai Na ima Shiru tayi tana kallonta,

Fadila tace  i hear u Rahama muje in gaida Ammi Rahama tace  okay tayi gaba Fadila ta bi bayanta hakan yasa Na imar ma tabi bayansu itama.


Kallon Nuwaira kawai Mary keyi bayan ta buWe mata ?ofar palourn da take ta dannawa ba ?a??autawa kafin tace

 Ina kwana Ma ko kulata Nuwaira bata yi ba ta wuce ta ta shigo palourn ta wuce sama abinta ba tare da ta tsaya a palourn ba, Amira da ta fito daga Wakinta kenan da niyyar sau?a taji mai danna bell haka ganin Nuwaira ta Wan ja tsaki

 Haba Nuwa wannan wani kalan danna bell ne kamar ya?i

 To wa ya sani ko ya?inne? Ta faWa tana ?arasawa cikin palourn saman ta zauna a kujera tana kallon Amira da itama ta ?araso tana faWin

 Ai kuwa in ya?i ne ba a gidana ba

 Sannu mai gida, tell person wey no get house abeg Nuwaira ta faWa tana ciro wayarta a jaka ta na tattaSa screen Win da fingers, Amira tayi dariya

 Gidan miji ai nake magana ba gidan kai ba Nuwaira ta bata wani side eye sai dai bata ce komai ba. Amira ta gyara zamanta tace

 Sai gaki yau a gidannan, rabonki da gidanna fa kin daWe Nuwa harararta Nuwaira tayi ta ajiye wayar a gefenta tana kallon Amira tace

 Saboda ba?in halin mijinki ba? Yanxu ma ji nayi bazan iya ba na zo na ganki tunda kwana 2 kin ma?ale a gida kamar matar kulle, sai dai idan ya zo ya same ni a gidansa yayi abinda ya ga dama amma dole na zo naga ?awata tana gama faWin haka ta hau ?wallawa Mary kira da ?atuwar muryarta

 Mary!!!!!, Mary!!! Amira ta tsaya kawai tana kallonta kafin ta Wanyi tagumi fuskarta na nuna damuwa tace

 Ai zaki tafi kafin ya zo bazai ma same ki ba, nikam gwara da kika zo Nuwa, ina cikin damuwa wallahi tallahi Nuwaira ta dakata da kiran mary da takeyi tace

 Damuwar me? Ba kinyi yadda Mummy tace ba and kince the result is perfect ta faWa tana mayarda hankalinta duka kan Amira

 Which kind perfect? Ni da na san haka abinnan yake gaskiya bazanyi ba, ba na faWa miki da muka je sunce bazai yiwu ayi ma Albi ba dan ko an masa bazai daWe a jikinsa ba zai karye maybe kafin ma aikin ya fara ?arfi zai karye shine yace sai dai ayi ma Na imar ba Nuwaira dake kallonta tace

 Uhum haka kika ce sai aka yi yaya ba hakan aka yi ba?

 To Nuwaira anyi kuma ya kama Na imar dan anan part Win nawa ma har rashin kunya ta masa ta ja masa tsaki, ni na san kwana biyu da sukayi a part Winta basu da kwanciyar hankali sam, shekaran jiya da sassafe naga ya fita maybe faWa sukayi ohon masa, jiya kinga anan ya kwana amma wlh ko bi ta kaina bai yi ba kuma yau ma anan zai kwana amma Nuwaira ni na san ba zai wani kula ni ba, ko magana na masa a ta?aice yake amsawa, abubuwannan sun saka sa a damuwa ko bacci baya yi sosai, ni gaskiya ba haka nake so ba, duk abubuwannan memakon ya dinga jin haushin Na ima ya san value Wina amma inaa drifting Winmu kawai yake further away from each other Nuwaira da ke kallonta tace

 So yanzu ya kenan? Amira ta sau?e ajiyar zuciya

 Zan kira mummy ta kira a karya abin kawai, akwai other ways na fitar da ita a gidannan da yawa amma dis one is not helping me in anyway, ni shiyasa tun farko bana wani son zuwa wallahi

Nuwaira ta koma ta kishingiWa tana jan tsaki

 Dont start with that ur bullshit pls na wani baki son zuwa, ke dai kawai kinbi mamarki kunje inda ba a wani iya aiki ba, kawai na zuba miki ido ne dama inga iya inda aikin zaije, yanzu wanke ?afarki zakiyi mu koma wajen Baba shi yayi aiki akan Ahmad Win duk uban taurin kansa wlh bai isa ba

Wani kallo kawai Amira ke mata, kafin itama ta ja tsaki,

 Ke ni wallahi ba gurin ko wani Malamin da zan sake zuwa, wanann ma ya isheni, ba abinda na so ya faru ba kenan kuma shima mutumin bai ce min Albi zai fita hayyacinsa saboda yarinyar ba da bazan yarda ayi ba, to kafin ayi aikinnan ma nuwa nafi gane kansa akan yanzu, yanzu banda shiru shiru da miskilanci babu abinda ya ?aro, yayi ta haWe rai dama can yaya lafiyar kura? Gaskiya ni ba haka nake so ba.


 To tunda bazaki je ba shikenan kar ki sake cemin Ahmad ya miki kaza ko kaza, its soyayya dat will kee u Amira

 Naji Amira ta faWa tana ?o?arin kwanciya akan kujera, Nuwaira ta tashi zaune da kyau tana kallon Amira tace

 Ami tashi ki zauna kiji, nima fa damuwata na kawo miki, nima ina cikin problem na rasa yadda zanyi da shi Amira ta mi?e zaune tana kallonta tace

 Matsala kuma Nuwa Nuwaira ta gyaWa mata kai a hankali kafin ta janyo wayarta ta Wanyi taSe taSe sai kuma ta ajiye wayar ta mayarda duka hankalinta akan Amira tace

 Amira ciki ne dani kallonta kawai Amira take yi not so suprised kafin ta Wage gira tace

 And? Ganin Nuwaira nata kallonta tace  Na waye?

 Hmm kawai Nuwaira ta faWa, Amira ta koma ta kwanta tana faWin

 Kin saka na tashi zaune na zata wata magana mai muhimmanci ce to ciki nawa kika yi kika zubar Nuwaira whats special about wannan

 Its special cause am keeping it Amira ta ?ura mata idanu daga kwance da take tana kallonta with suprise kafin tace

 Zaki ajiye kuma Nuwa?

 Yes Amira ta tashi zaune tana kallonta tace

 Waye baban cikin?

 Zan faWa miki, amma yanzu kinsan he s denying wai ba nasa bane, ni kuma aure nake so nayi kuma shi nake so na aura

 Lallai ma kamar ya ba nasa ba, ai wlh dole ya karSi ciki ya ma isa yace ba nasa ba ai tunda kika ce nasa ne to nasan ne, kuma girl if u feel kina son aurensa and keeping the baby am with u 100 percent, wallahi ki auresa, amma saurayine ko bazawari?

 Da matarsa fa harda yarsa babba, amma do i care?
Amira ta karSe da  we dont suka yi dariya tare, Nuwaira ta koma ta kishigiWa tana shafa cikinta tace

 Idan ma blackmail bai isheshi ba yanzu zan kai sunansa wajen Baba, ke ko zaki amso min lambar malamin mummy in haWa har da shi?amma kar kice mata ni ke nema

 Baki da matsala zan karSo miki ki ci ubansa, dama Allah Allah nake kiyi aure Nuwa

 Aikuwa lokaci yayi in sha Allah Aminiyas suka sake yin dariya kafin Nuwaira ta janyo wayarta ta tura ma daddyn Nuwaira voice Win da take recording, ta sake tura masa

 Ko in faWa mata sunan? Da emoji Win gwalo, tana tura masa ta ajiye wayar tare da mi?ewa ta zare heels Winta tana nufar downstairs tace

 Bari inje inci uban Marynki Winnan dan uwatta bata ji ina kiranta bane? Tana faWa ta fice a palourn ta nufi ?asa, ko minti Waya bata yi da sau?a ba wayarta ta fara ringing Amira ta tashi zaune tare da kallon wayar taga

 Sugar Daddy da love emoji, har kiran ya katse ya sake kira tana kallon wayar, haka ya dinga kira ba ?a??autawa hakan yasa ta fara tunanin ko shine uban cikin Nuwairaa?

Mi?ewa tayi ta Wauko wayar ta koma ta zauna tana Sliding call Win tayi picking ta kai wayar kunnenta tana gyara zamanta a kujera.



#Maimoon
09041426598


https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q

RU?A??UN ZU?ATA ( TANGLED HEARTS)

Wattpad: @Maimunah_Abdallah
ArewaBooks: @maimunahabdallah

Chapter 61: Silver linings

Muryarta cike da confidence tace  hello? dan ba Yau ta Saba magana da Alhazan Nuwaira ba, Jin ?arar yanke kiran immediately, yasa da mamaki ta ciro wayar daga kunnenta tana kallon screen Win, ta ?urawa hoton Nuwaira dake kan screen Win idanu ta sha make up da attach tana zaune gaban mota da wata shirt blue, fingers Winta all 5 da ta ma kwalliyan black nails dogaye ta cika su da rings ta wani zaro harshe a selfie Win, kwata kwata kamar bata haWa komai da musulmai ba , right above hoton kuma notifications ne na kiran da sugar daddy Win ya mammata har guda 4, swiping tayi zata buWe lock Win wayar taga Nuwaira ta canza password ta Wan tsaya jim kafin ta kalli hanyar stairs, dai dai lokacin Nuwaira ta hauro da plate na abinci a hannunta tana tauna wanda ke bakinta tace

 Ni wai miye Mary ke miki a gidannan? Ina saboda Saif ne kuma zuciyarki ta mutu kin barwa yan uwan ubansa shi, ta faWa tana sake kai another spoon of rice bakinta ta ?araso ta zauna a kujera, sai a lokacin ta lura da wayarta da ke hannun Amira, ita dai Amira sai kallonta take, Nuwaira ta ajiye plate Win a gefen kujera tace

 Whats up? Ta faWa tana kallon Amira da abinci a bakinta da ta dakata da taunawa Zuciyarta na wani irin azababben bugawa, wani tsautsayi ne ya aiketa barin wayarta anan? Ta tabbata zai kikkirata, ta banu kar dai ya kira Amira ta Waga, mi?a mata wayarta Amira tayi tana faWin

 Ana ta kiranki Nuwaira ta saka hannu ta karSa tana haWiye abincin bakinta ba tare da ta gama taunawa ba tace

 wani tsinannen ke kirana, ni fa jaraba ce bana so ta faWa tana satar kallon Amira to see her rection amma sai taga komawa ma tayi ta kwanta tana faWin

 Ki duba mana wani wai sugar daddy, ai har na Waga ya katse kiran hala shine wanda kike son auran ko wani ne daban?

Nuwaira da ke ta danna wayarta ta share goshinta tace

 shi ne

 to akan me ya kashe waya dan na Wauka? ko bai san kina da Aminiya bane?

 Shi kuwa yafi kowa sani, bai san ke bace da ba zai kashe ba ko da yake zai iya sani ma ya kashe kinsan yanzu haka ba kiran arziki ya min ba, ba na ce miki we re not on the same page da shi ba akan cikin? Kullum cikin bura uba muke da shi akan cikin, probably shiyasa da yaji muryarki ya kashe kinsan muryarki da tawa ba Waya ba na fiki babbar murya

Amira ta Wan yi dariya tace

 ai ni so nayi in ji dalilinsa na ?in karSar cikin bayan ya zage ya kwashi harka dan rainin sense Nuwaira ta janyo jakarta ta mayarda wayar ciki bayan ta saka a silent ta janyo plate Win abincin ta cigaba da ci tana faWin

 Ke ba fa shi da dalili, dalilinsa bai wuce baya so yayi ma matarsa kishiya ba kuma na faWa miki yana da babbar ?a kamar uwar da ?ar sun shanye sa ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login