Showing 30001 words to 33000 words out of 216282 words

Chapter 11 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

d'an uwan ka ina baka shawarar ka amince da matar ka ka maida ta cikkakiyar matar ka kafin lokacin ya k'ure mana._ sake maimaita message d'in Asad yake yi kansa na sarawa ambatar Mama da yayi a cikin sakon da aka turo masa. Da sauri ya fita daga wajan message ya shiga call log da niyar kiran Mama amma sai ya tsaya cak ya dafe kansa a bayyane yace, "me ma zanyi?."

?? 'Hydar.' Zuciyar sa ta bashi amsa ya danna number Hydar a maimakon ta Mama har lokacin hannun sa yana rik'e da kansa da yake ji yana yi masa ciwo. Hydar bai d'auka ba ya kalli Rauda a kan gado yaga tayi bacci ya tashi ya fita yana sake kiran wayar Hydar, a karo na biyu ya d'auka bai bari Asad d'in yayi magana ba yace, "Mama tasan komai Asad daga yau zuwa ko wanne lokaci komai zai iya faruwa, ban so taji labari da sauri haka ba amma kasan yanayin gidan namu ba ko wanne sirri ne yake b'oyuwa ba especially da ya kasance Aliyu ya san komai."

? ? Asad ya dafe kansa kana yace, "Maamaaa!." Hydar jin sunan da ya ambata ya saka yace, "eh, lokacin da nayi maka message d'in nan ta kira ni kamar zata dake ni tana fad'a min bakin mu d'aya nasan inda kake nace ban sani. Asad ka rik'e matar ka i mean ku zama d'aya kai da ita kafin Mama ta raba ku da ita." Asad ya sake cize bakin sa kafin yace, "why nake jin wani iri in ka kira Mama? Why ban kira ta cikin kwanakin nan ba?, why in na d'auki waya zan kira ta nake forgetting Hydar?."

? ? Hydar yace, "ban sani ba Asad, ka dai cigaba da addu'a kamar yadda ka saba amma akwai tarin qalubale a gaban ka, sai ka cire wannan rashin son maganar taka ka rik'e matar ka yadda koda za'a raba ku za'a sha wahala" Hydar yana gama fad'a masa haka ya yanke wayar bai jira mai zai kuma ce masa ba.

Asad ya tafi duniyar tunani yana so ya gano dalilin da ya saka in ba ambatar Mama akayi ba mantawa yake da ita bayan a baya ba haka yake ba, inda akwai wacce yake tunawa a ko wacce dak'ik'a Mama ce, meyasa yanzu baya jin hakan a kanta a wannan lokaci?.

? ?? "Hello handsome." Muhibba ta fad'a a gefen sa tana tsayawa kusa dashi tana kallon sa. Bai kalle ta ba domin baya cikin yanayi mai dad'i ko kad'an daman itama tasan bazai yi magana ba tace, "zan iya taya ka hira?." Asad bai kalle ta ba ta sake yin murmushi tace, "na fad'awa sister ka sak'o ta fad'a maka I hope ta sanar da kai?." Kai ya dafe da hannun sa guda d'aya yaja k'aramin tsaki baice mata komai ba ya d'aga k'afa da niyar tafiya.

Hannun sa ta rik'e hakan ya saka shi tsayawa cak ya juyo ya kalle ta sai ta saki hannun nasa tana kallon idanun sa tace, "I love you!." Bai ce komai ba ya bar mata wajan ita kuma ta bishi da kallo tana murmushin farin ciki, ita kallon sa ma kawai nishad'i yake bata balle kuma yayi mata magana.

? ?? Asad fita yayi daga asibitin yana niyar shiga mota yaga kiran mai martaba bai d'auka ba ya shiga motar ya zauna sannan ya d'auka ya saka a kunne yayi sallama muryar sa a sanyaye mai martaba ya amsa kana yace, "Babar ka tasan komai Zaki, kar hakan ya dame ka ka saka a zuciyar ka komai Allah ya rubuta sai ya faru, ko meye zai faru kar ka baro k'asar nan ba tare da umarnina ba kaji ko?." Asad ya d'aga kai kamar yana gaban sa dak'yar ya iya furta, "In sha Allah."
"Ka cigaba da addu'a komai zaizo da sauk'i cikin ruwan sanhk, Babar ka bata isa tayi abinda Allah bai nufa ba komai ya faru Allah shine ya tsara faruwar sa."

Baice komai ba Mai martaba yace, "a cigaba da addu'a" yana fad'a masa hakan ya yanke wayar Asad ya sake cire wayar da sauri da niyar kiran Mama amma sai ya samu kansa da nemo number Hafiz ya dafe kansa ya manta abinda zaiyi kawai ya kifa kan a kan sitiyarin motar yana furzar da iska mau zafi.

*&&&*

? ? ?? Mama kwanan zaune tayi ko kad'an bacci yak'i zuwar mata ido da ta kulle idon ta sai ta hango Asad da Rauda a kwance a waje d'aya sai ta bud'e ido a zabure tana cize bakin ta. Mai martaba yana lura da ita bai kuma ce mata komai ba.
Asuba nayi yana fita masallacin cikin gida Mama ta zabura ta fito daga b'angaren sa ko sallar bata yi ba ta burin ta kawai ta ganta a b'angaren ta tana shiga a haukace hadiman ta na gaishe ta amma bata bi ta kansu ba ta shiga cikin d'akin ta ta kulle kanta.

Hannun ta na rawa ta d'auki waya ta kira Asad amma wayar bata shiga ta canja akalar kiran ta kira Mum hankali a tashe, Mum bata d'auka ba ta cillar da wayar tana zagaye d'akin cikin neman mafita, tayar da sallah da taji anyi shine ya saka ta yin alwala sallar ma ba'a nutse tayi ta ba tana idarwa ta mik'e ta fita zuwa d'akin Suhaima. A bakin k'ofa suka had'u da alama zata je gaishe tane tace, "Barka da asuba Mama." Mama bata amsa ba tace, "sako hijjabin ki zamu fita yanzu." Suhaima da mamaki tace, "Mama Ina zamu je da asuba?."

Kallon da tayi mata ya saka ta yin shiru tana bin maman nata da kallo ganin ta firgice kamar ba ita ba tace, "Mama lafiya naga kin koma wani iri?." Cikin tsawa tace, "Kiyi abinda nace kawai Suhaima, kije ki sako hijjabi zamu fita!." Da sauri Suhaima ta koma ciki ta sako dogon hijjabi akan kayan baccin jikin ta tana fitowa Mama ta bata key na mota tace, "ki fita da motar zan fito ta baya na same ki."
"Mama amma Abba ya hana ni yin driving" ta fad'a tana karb'ar key d'in.
Hannu takai da niyar marin ta Suhaima tayi baya da sauri ta fita tana mamakin abinda ya samu Mama haka.

Duk a tsorace Suhaima take kar Takawa ya ganta dan ya hana ta jan mota balle kuma da asuba haka, a haka ta fita da motar zuwa can bayan gidan dan tasan ta nan Mamaa zata b'ullo tana zuwa kuwa ta ganta tsaye Suhaima na tsayawa ta bud'e gaban motar ta shiga Suhaima taja motar ba tare da tasan inda suka nufa ba.

Tsoron yi mata magana take yi gashi bata san inda zasu je ba haka take mik'ewa kawai tana tafiya Mama kuma na gwada wayar Mum har lokacin bata d'auka ba, tsaki tayi ta kalli Suhaima tace, "kiyi kwana" ta fad'a tana nuna mata inda zata bi Suhaima ta bi wajan suka cigaba da tafiya.

Sunyi tafiya mai nisa sosai domin Suhaima ta d'auka ko Mama ta manta hanyar ne amma babu damar tambaya tayi shiru har suka k'araso wata ruga ta fulani da babu mutane sai gidajen k'asa suma sai ka irga su ta bata umarnin tsayawa, bud'ewa tayi ta fita Suhaima zata fito tace, "kiyi zaman ki ina zuwa." Ta fad'a tana shiga cikin gidan da tazo da Sauri Suhaima ta bita da kallo.

A zaune ta same malamin da yana jan carbi sallamar ta ya saka ya mik'e yana fad'in, "Ranki ya dad'e, Allah yaja zamanin ki, ya raya mana y'an uku yasa su mulke mu. Kece da kanki da sassafiya haka?." Mama bata iya amsawa ba ta zauna tace, "Ina cikin tashin hankali ne da dole na fito yanzu." Malamin ya zauna yace, "to ranki ya dad'e meya faru?."
"Mahaifin Asad ne ya d'aura masa aure da yarinyar da muka zo wajan ka kwanaki ba tare da sanina ba."

Malamin yayi murmushi yace, "Daman na fad'a miki auren su da wahala in bai yu ba, datse shi abu ne mai matuk'ar wahala." Tace, "Yanzu haka suna Egypt tare da yarinyar." Farantin gaban sa ya jawo ya fara duba k'asar gaban sa na wani lokaci kafin yace, "Tabbas suna can, yanzu haka gasu nan tare suna tafiya shi da ita amma kamar bata da lafiya na gani."

Hankalin Mama ya sake tashi tace, "babu ta yadda za'a raba su ya dawo gida? Bana k'aunar ta ko kad'an." Ya sake bincikawa yace,??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? "akwai kuma babu, hanyar da za'a bi wajan raba su dole sai an jira lokaci domin kuwa akwai d'an katanga a yanzu da kafin a rusa ta dole sai an jira."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yanzu ko kashe tane baza'a iya yi ba?."
"Za'a iya ranki ya dad'e, amma a ganina abi wata hanyar domin kafin a samu wannan nasarar ma za'a jima dan na fad'a miki tana da rik'o da addini ba komai ne zaiyi saurin tasiri a kanta ba."

Mama ta sauke ajiyar zuciya ta dafe kai maganar mai martaba ta fad'o ta kalle shi tace, "Kafin wannan a duba min aga akwai wata alaqa da ta had'a su da yarinyar, ina nufin auratayya ta had'a su ko a'a?." Malamin ya sake cigaba da duba mata kafin yace, "A dai yadda na gani babu abinda ya had'a su sai dai kin san ana samun tangard'a wani lokacin Allah yana yi mana hijjabi da ganin wasu abubuwan, sai mu gani muce anyi kuma ba'ayi ba, ko mu gani munce ba'ayi ba kuma anyi d'in."
"Muje a bai had'a su d'in ba daman bana fatan hakan. Abinda nake so dakai ina so a yiwa Asad aiki a lalata masa mazantakar sa, ina nufin yadda bazai iya kusantar ko wacce y'a mace ba a wannan lokacin sai da nayi niyar hakan!" Ta fad'a tana kallon sa shima ita yake kallo da d'unbin mamaki.......
[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*036.*

Mamaki ya kama shi jin abinda ta furta ya girgiza kai yana jinjina tsantsar mugunta da rashin son yarinyar da take yi ya gyara zaman sa yace, "Ranki ya dad'e Asad d'in za'a yiwa aiki?." Ta kalle shi tace, "ashe kaji me nace."
"Abin ne ya bani mamaki ranki ya dad'e, keda bakya so a yiwa Asad aiki da naji kince ayi miki shine nayi mamaki sosai."

"Yanzu tunda kaji sai kayi abinda nace." Malamin yace, "yanzu ranki ya dad'e bakya hango matsala a cikin wannan lamarin? Ayi masa aiki a yanzu nan gaba in ya auri wacce kike so kuma fa?." Mama tace, "Sai a warware shi, kayi masa abinda bazai wahalar warwarewa ba amma bana k'aunar wani abun ya shiga tsakanin sa da yarinyar nan ko meye shi koda hannun ta bana so ya rik'e." Malamin ya girgiza kai yace, "wannan ba damuwa bane ba ranki ya dad'e, za'a yi kamar yadda kika ce."
"Yau nake so ayi ba sai gobe ba."
"Babu damuwa ranki ya dad'e."

Ta d'an yi jimm kafin ta kuma cewa, "sannan ayi dai wani abun da za'a raba su bana son zaman nan nasu tare." Malamin yace, "babu damuwa ranki ya dad'e za'a yi." Bata ce komai ba ta mik'e ta fita ya bita da kallon mamaki kafin ya girgiza kai ya cigaba da abinda yake yi.

Mota ta shiga Suhaima taja suka nufi gida jikin ta duk a gajiye yake sabida dogon tuk'in da tayi. Ta inda Maman ta fita tana nan ta shiga ta wuce b'angaren ta Suhaima ta ajjiye motar ta nufi zuwa ciki. A hanya suka had'u da jakadiya Babba tana ganin Suhaima tace, "Ranki ya dad'e barka da dawowa." Suhaima tace, "barkan ki." Har zata gota tace, "Mai martaba yana kira." Gaban Suhaima ya fad'i amma bata nuna hakan ba ta juya akalar tafiyar ta zuwa b'angaren mai martaba jikin ta a salub'e.

Yana zaune shida Wambai kamar koda yaushe aka yi mata iso ta shiga da sallama ta tsuguna a k'asa tace, "barka da safiya Takawa, ina fatan an tashi lafiya." Mai martaba ya amsa kana yace, "Ina kika je naga kin fita da mota d'azu?." Shiru tayi kafin tace, "Na kai Mama unguwa." Mai martaba jin mai tace ya saka yace, "Shikenan jeki."
"A tashi lafiya" ta fad'a da girmamawa ta fita a sanyaye.

Mama kuwa tana shiga ta tarar da Mum a zaune tana jiran ta tayi tsaki tace, "Dake da Jidda wayoyin ku duka basu da amfani." Mum ta mik'e tsaye tana kallon ta cikin mamaki ganin yadda ta koma kamar ba ita ba tace, "Ranki ya dad'e lafiya na ganki haka?." Mama ta zauna tana zare hijjabin jikin ta tace, "a ko wanne yanayi ma ganina zakiyi indai a wannan lokacin ne, zauna." Ba musu ta zauna tace, "Me yake faruwa? Sarautar Kano aka bawa wani wanda ba namu ba?."

Mama taja tsaki tace, "Inda sarautar Kano aka bayar d'in ma da naji dad'i domin yafi min sauk'i a kan abinda yake faruwa yanzu."
"Me yake faruwa?."
"Mai martaba ya aurawa Asad yarinyar nan yanzu haka suna Egypt." Firgici, tsoro, tashin hankali, mamaki, rud'ani, gigita duka suka had'arwa Mum a lokaci guda ta mik'e tsaye ba tare da tasan tayi hakan ba idanun ta a waje hannun ta dafe da k'irjin ta tace, "What!." Mama da take kallon ta tace, "abinda kika ji shi nace."

Mum ta zauna tana kallon Mama tace, "Nasan dai baza ki min wasa da wannan maganar ba shiyasa na gigice." Mama tace, "na gigice ninkin wacce kika yi sau goma kiris ya rage na rasa hankalina, a fuskar ta kinga hakan ya bayyana." Mum ta sake rud'ewa tace, "Ta yaya?."
"Ina can Kano."
"To Asad ba anyi dashi ya hak'ura ba ya akayi maganar ta dawo?."
"Mahaifin sa shine yayi komai, na tabbata Asad bazai aikata hakan ba tunda yasan bana so."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Fulani kice babban masifa ce ta kawo mana kai" Mum ta fad'a a rud'e tana kallon ta. Mama bata iya cewa komai ba Mum tace, "yanzu ya za'ayi kenan?." Mama ta bud'e hannun ta alamun bata sani ba Mum tace, "kuma kinyi magana dashi?."
"Bana samun sa a waya kwata-kwata."
"Shikenan! Har sun raba mu dashi, mun shiga uku" Mum ta fad'a cikin rud'ani da ya bayyana a tare da ita.

Ba zato Mama taji tana hawaye tace, "Ban san me zanyi ba Sadiya bana son zaman su tare gashi mahaifin sa yace matuk'ar yana da rai da lafiya Asad bazai rabu da ita ba, nasan halin sa zai toshe duk wata hanya da yasan zamu yi magana da Asad, duk kuma abinda na saka a yiwa Asad ko ita yarinyar akan a raba su sai ya lalata shi. Kaina ya kulle Sadiya ya kuma ce in na sake na tafi Cairo raina sai ya b'aci" ta fad'a tana dafe kanta da hannun ta har lokacin hawaye take.

Mum ta dawo kusa da ita ta zauna tace, "dole mu san abinyi in ba haka ba burin mu bazai cika ba." Mama ta d'ago ta goge idanun ta tace, "wannan a rubuce yake dole ne na d'auki mataki na gaggawa kafin a kassara ni. Yanzu daga wajan Malam nake na bashi aiki ayi min za kuma ayi amma kafin lokacin ina so nayi wani abun da zan d'auke hankalin mai martaba daga kaina gabad'aya." Mum tace, "ya kamata kuwa in ba haka ba wallahi zasu cinye mana kurwar yaro, dan nidai nasan wannan ba aikin sa bane wallahi aikin asiri ne bata da abinda namiji zai sota dashi, sunyi nasarar asirce mana shi Fulani."

"Zan warware shi Sadiya, ke kin san zan iya. Dan na aikata komai a duniyar nan wajan ganin d'ana ya dawo abu ne mai sauk'i, zan iya salwantar da komai dan ganin Asad ya dawo gare ni ya cika min burina." Mum tace, "haka ne ranki ya dad'e. Amma iyayen ta sun cuce mu iya cuta, tsakanin mu dasu sai Allah ya isa."
"Hmmm" Mama ta fad'a dan maganar ma tak'i zuwa harshen ta.
"Bakya ganin muje gidan su ayi yiwa iyayen ta barazana da kurari ko zasu ji tsoro suce ya dawo musu da y'ar su?."

Mama tace, "ba aikin da hakan zaiyi mana, a baya munje ai me yayi?." Mum ta girgiza kai tayi shiru cikin tunanin mafita domin a ganin ta tafi Mama shiga tashin hankali.

Mum tayi tagumi kana tace, "ni Jidda ma nake tausayi in taji labarin nan bana tunanin zata iya bacci yau." Mama ta kalle ta tace, "ya zama dole ta sani kodan ta taya mu da wani abun ta dage ta kwato mijin ta." Mum tace, "wannan abu dai sam baiyi dad'i ba ji nake kamar na fashe da kuka. In na tuna irin kalaman yarinyar nan a kan mu sai naga kenan itace tayi nasara a kanmu abinda ta fad'a yana neman tabbata."
"Ki kwantar da hankalin ki Sadiya wallahi sai sun rabu."
"Ba rabuwar ba ranki ya dad'e kar muje wani abun fa ya gifta tsakanin su, hakan tana faruwa wallahi mun cutu har abada. Koda basu had'a jini ba ta shiga jirin matan da zasu yi iddar auren Asad."
"Nayi maganin wannan matsalar hakan bazai faru ba har a tashi duniya."

Mum tayi ajiyar zuciya tace, "Allah ya tabbatar" ta fad'a tana goge idanun ta kamar wacce take kuka. Mama tace, "matakina farko akan mai martaba zan d'auke shi domin shine babbar matsalata a yanzu." Mum tace, "Shine abinda ya kamata ayi ranki ya dad'e, amma me za'ayi?." Mama ta kalle ta kamar zatayi magana sai kuma ta fasa tace, "zan aiwatar dashi kowa kuma zai gani lokacin da zan dawo da Asad bai ma san nayi ba. Babban abinda yake gabana a yanzu na samu nayi magana da Asad gashi nasan ko da wasa bazai bari naje Egypt d'in ba."

"Hydar bakin su d'aya a gani na shi ya kamata ki kira ya had'a ku a waya." Shiru Mama tayi kafin Mum tace, "Kenan dana gansu a airport daman shine ba Aliyu ba?" Ta d'aki kujera tace, "wallahi naji hakan a jikina amma kalaman ki ya saka na manta da maganar ashe sune da yanzu mun d'auki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login